Showing 51001 words to 54000 words out of 133697 words

Chapter 18 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt

miƙama mansoor ɗin wayar, amsa yayi yan kara wayar a kunnen shi, gaisawa su kayi ammy na faɗin "mansoor kayi mana hijira koh "
"a'a ammy aikine ke riƙe ni"
"dama ku ai baku da wani excuse sai na aiki, yaushe rabon ka da zuwa lagod"
"insha Allah ina nan zuwa "
"to Allah ya yarda, ka gaishe man da su baban ka"
"za su ji insha Allah "
"to nagode "ammy ta faɗa haɗi da yin rejecting, miƙama shazim wayar yayi, amsa yayi yan dialing number, malam ringing ɗaya biyu malam yayi picking, gaishe da shi shazim yayi, cikin kulawa ya amsa mashi yana tambayar ya abuja, sun ɗan jima suna magana daga bisani suka yi sallama, majeed ya kira amma tana ringing ba'a ɗauka ba, mai da akalar kiran yayi kan a hashim, shima tana ringing ba ai picking ba, ajiye wayar yayi kusa da shi, fira suke shiga yi shi da mansoor jefi jefi, har lokacin sallar zuhur yayi, ta shi suka yi suka ɗauro alwala suka fice a main parlor suka ci karo da kairiyya ta fito daga kitchen mansoor ne yace ta shiga part ɗin shi ta kwaso kayan breakfast ɗin da takai ma shazim da to ta amsa haɗi da nufar part ɗin sa, ficewa suka yi zuwa masallaci, da aka gama sallah mansoor yace su shiga part ɗin innah, da sallama suka shiga part ɗin bakowa sai mai akin innah da ta fito daga kitchen jjn ana sallama, amsa masu sallamar tayi tana gaishe su haɗi da cewa, innahr ta shiga sallah yanzu, ok mansoor yace wuri suka samu kam sofa suka zauna, shazim wayar shi da ke cikin aljihu ya ciro yana ɗan daddana ta, fitowa innah tayi hannun ta riƙe da ɗan kwalinta kanta duk furfura an mata kitson zane guda shidda da gake tana da suma ba laifi, kallon su tayi tan riƙe haɓa "ku kuma daga ina da wannan ranar" mansoor yace "ina wuni innah " lafiya lau ta amsa, kallon shazim dake ta aiki dan gwala waya innah tayi tana cewa "shi kuma wanccan ya fi ƙarfin ya gaishe ni ne ko mi"ɗan taɓa shi mansoor yayi "ana magana"
ɗago da kanshi yayi yan kallon mansoor yace "ni wai "wani kallon raini wayau mansoor yayi mashi jin tambayar da hake mashi bayan yasan tun da innah ta shigo ya san da shigowar ta, innah ce tace "a'a ba kai ba mu ɗan rainin hankali " murmushi shazim yayi haɗi dacewa "anwuni lafiya, ai ban san kin fito ba ranki ya daɗe "tsaki innah ta ja tana faɗin "da ban wuni ba zaka ganni haka ne "
d murmushi a fuskar shi yace"ai ban sani ba "
"ai kin banza "shine kawai abun da innah tace, basu wani jima ba suka fice daga part ɗin, da harara innah ta raka su harsuka fice, parking lot suka nufa, motar Shazim suka shiga, estate ɗin suka bari


✨KATSINA ✨


zaune suke kan sofa part ɗin abie,jinkin sanye da riga da skirt na material Aairah tace
"abie wai yaushe zamu tafi ne"
"yayan ku zaku tambaya"
"yaya fa abie "
"eh, shi zai kaiku "
"amma dai baza mu wuce gobe ba ko, tunjiya mun gama shirya kayan mu "
"to wannan ne ban sani ba, idan ya dawo sai ku tunbaye shi "
"to abie "
wayar abie ce ta fara ringing, miƙa masa Aaimah tayi tana faɗin uncle mustafa ne, amsa abie yayi yana picking, ficewa su kayi zuwa bedroom ɗin a kan bed suka ya da zango, Aaimah tace "Allah ya sa ya ce gobe zamu tafi "
"ammen Aaimah , wallahi na gaji da zaman gidan, ko ba komi zaka ga wurare kala da ban da ban "
"Allah dai yasa yace goben "
Aairah tace
"to ameen,harna ƙosa na ganni a can nasan zamu sha ya wo da Ameera, bari na kirata ma"
Aaimah tace
"eh ki kira ta "
wayar ta ta ɗauko tayi dialing number Ameera, ringing ɗaya ta ɗauka tana faɗin sister wai yaushe zaku zo, abba yace yau amma gashi har dare baku zo ba"
Aaimah tace"ke ko sallama babu "
"bazaki gane bane na ƙosa na ganku ne, yaushe rabon da na ganku"
"sai ya abdallah ya dawo shi zai kawo mu ne"
"aikuwa kiran shi zanyi ince dan Allah ya kawo ku gobe"
nan sukai ta labari kan school, har time ɗin sallar asr yayi, alawala suka yi suka gabatar da sallar suna nan zaune kan carpet mom ta shigo jikinta sanye da gown ta shadda white color anmata kwalli da black ɗin net, hannun ta riƙe da hijab da jaka da alama fita zata yi, gaishe da ita suka yi Aairah na faɗin"mom jar kin shirya"
"eh na shirya, ku tashi kuje kitchen baaba larai na can tana aiki ku kama mata "
"to mom yau she zaki dawo "
"sai dare gaskiya, dan daga gidan granny zan shiga gidan safiya, sai dai dare"
Aairah tace "da na san zaki can da tun ɗazo muka shirya muka bi ki "
"A'a ko da ku shirya bazan je ko ina da ku ba"
"saboda mi mom "
"koma saboda mi ku bari wani lokacin kun tafi "hanyar fita mom ta kama tana faɗin "ku taso kuje ku kama mata aikin "da to suka amsa suna tashi suka bi bayan ta, har compound suka rakata abie suka samu tsaye jikin mota yana jiran mom, tare zasu fita zai ajiye ta gidan granny shi kuma zai wuce gidan dadi, a dawo lafiya suka yi masu sannan suka koma ciki, kitchen suka nufa wurin baaba larai, kama mata aikin suka yi suna ɗan fira, sun ɗan jima suna aiki sai gaba da magrib suka kammala, cema baaba larai su kai ta tafi kawai zasu gyara kitchen ɗin da jera abinci kan dinning, da to baaba larai ta amsa haɗi da ficewa ta nufi ɗakin t, Aairah ta kaima su bala na su dinner ɗin Aaimah kuma ta jera kan dinning, sai da suka tabbatar sun kammala duk wani abu da ya dace sannan suka nufi ɗakin su domin yin sallah, bayan sun gama sallah parlor suka dawo zama suka yi suna kallo,har akayi sallar isha, ɗaki suka koma domin gabatar da sallar, sai bayan sallar isha mom da abie suka dawo, dinner su kayi, bayan sun kammala su Aairah suka nufi ɗaki domin bacci .......




Episode 26_27


'''''''''''''''Wayar Aairah ce ta fara ringing, Aaimah cewa tayi "to ni sai da safe, dan nasan indai ya mus'af ne to ke kam ba yanzu ba, duba mai kiran tayi, mus'af ne picking tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace "hubby barka da dare "
"barkan ki dai my love, ya gida "
"lafiya lau "cikin sauƙin soyayya suke wayar, anan mus'af yake sanar da ita next week zai wuce uk ( can ya kuma da karatun ) , Aairah kamar tayi kuka dan taso ace suna ƙasa guda da shi, bata son yayi mata nisa, ta dai yi mashi fatan alkairi sun ɗan jima suna waya daga bisani suka yi sallama.


✨SHAZIM✨


tsaye ya ke bakin window ya riƙe curtain (labule) yana waya da a hashim, fuskar shi a sake suke fira, a hashim na cewa "saboda mansoor ne kawai zan shigo gobe amma da dan kai ne bazan zo ba "
"to ko yanzun ma kakar ka shigo tun da ina nan"
"kai dai kawai saboda mansoor "
"ai da kayi zaman ka "
sun ɗan ɗauki tsawan lokaci suna fira sannan su kayi sallama,ya juya kenan zai bar bakin window ya hangi wasu manyan truck's guda ukku suna shigowa cikin estate ɗin da alama ta ƙaramin gate suka shigo,mamaki ne ya kama shi,waɗannan truck's daga ina kuma minene suka ɗauko, ya jima tsaye yana kallon truck's ɗin har suka yi parking a bakin babban store ɗin estate ɗin, mutum uku uku ne su ka fito daga cikin kowace truck, bayan truck ɗin da ke gaba suka nufa, mutum biyu ne suka buɗe truck ɗin suka shiga miƙoma sauran wasu manyan kwalaye suna shiga da shi cikin store ɗin, barin bakin window yayi ya nufi toilet ya ɗauro alwala, sallah ya gabatar ko da ya gama sallah ya jima zaune kan carpet bai ta shi ba, tunani ya shiga yi game da kwalayen da yaga masu truck ɗin na shiga da su cikin store,shin kwalin minene kuma na waye, ya jima a zaune har sai da ya fara jin bacci sannan ya ta shi ya kashe light ɗin ɗakin ya nufi bed ya kwanta, bai jima da kwanciya ba bacci yayi awan gaba da shi.
washe gari kamar jiya feenah ta kawo ma shazim breakfast kamar yan da ya tsallake jiya baici ba haka ma yau baici ba ya nufi part ɗin uncle Ahmad a can yayi breakfast tare da mansoor,fita su kayi shi da mansoor.


✨KATSINA✨


......... zaune su ke kan dinning suna breakfast, kallon abie Aaimah tayi tana faɗin "abie dan Allah idan zaka je gidan dadi ka tafi da mu"
"safiya ce yanzu ku bari sai da yamma sai kuje "
Aairah tace
"dan Allah abie, muna so ne muyi mata wuni "girgiza kai mom tayi tana faɗin "ku shikenan tun aka ce ba school daga nan ƙafa fuwan ku suka dai na zama wuri ɗaya "
"ba haka bane mom mun jima ba muje gidan ba ne "
"ba ma kunjima baku je ba, ina tunanin ko ranar friday kuje gidan" Aaimah tace "dan Allah dai mom "abie ne yace
"kuyi sauri ku shirya "
haɗa baki sukayi wurin cewa "yawwa abie mungode "da sauri suka bar dinning area suka nufi bedroom ɗin su.


abie ne a parlor tsaye yana jiran su Aairah , mom ce ke sau kowa daga stairs case jikinsa sanye da jallabiya black color, wurin abie ta nufo tana faɗin "ba su fito ba ko "
"eh kinsan su da shiririta, duk ta ƙare tafiya zanyi idan ya so daga baya mudi ya kai su"
"afuwan abie ga mu nan" cikin sauri suke taka stairs case ɗin, sanye su ke da hijab har ƙasa onion color ,ƙara so wa su kayi, kallon mom abie yayi yace "sai mun dawo "a dawo lafiya tayi masu haɗi da juyawa ta nufi kitchen, fita su kayi abie na gaba suna bin shi a baya har compound, motar su ka shiga, Aaimah na gaba kusa da abie yayin da Aairah take baya, fira suke cikin kwanciyar hankali har suka iso gidan dadi,horn abie yayi a bakin gate mai gadi ne ya leƙo ganin motar abie yasa shi komawa ciki da sauri,ya buɗe mashi gate, ya shiga ciki parking lot ya nufa, sai da ya gama dai daita parking ya kashe motar Aairah ce ta fara fitowa sannan sai Aaimah, jiran abie su ka yi har ya fito su ka shiga cikin gidan tare,cikin parlor su ka shiga suna sallama tsit parlorn yake babu kowa,wuri abie ya samu kan sofa ya zauna har zasu nufi ɗakin Aunty Rabi sai gata ta fito tana amsa masu sallamar da su kayi, gaishe da ita su Aairah su kayi da fara'a a fuskar ta amsa masu sannan ta nufi wurin abie "yaya ina kwana "
"lafiya lau, ya gidan "
"Alhmdllh"
"mama na ciki ne?" abie ya tambaya
"eh tana ciki "
"bari na shiga mu gaisa "da to Aunty Rabi ta amsa, ta shi abie yayi ya nufi bedroom ɗin dadi, zaune take kan sallaya ta gama sallar walha tana adu'a, zama abie yayi gefan gadont har sai da ta gama adu'a, waigowa tayi tana kallon abie ta ce "Muhammad kai ne tafe "
"eh mama, ina kwana "
"lafiya lau, ya su kubra "
"suna nan lafiya, tana gaishe ki "
"ina amsawa"su Aairah ne su ka shigo da gudu su ka nufi dadi suna faɗin "dadi munyi kewar ki" basu ƙarasa ba abie ya dakatar da su da faɗin "lafiyar ku lau kuwa,za ku wani nufe ta da gudu hak, salan ku danne mata ƙafafu fa bayan kun san fama take dasu, Allah yasa in ƙara ganin irin haka " ya faɗa cikin faɗa, tsaya wa su kayi suna kallon dadi kamar za su yi kuka
dadi tace "a'a da ka barsu ƙafafu ai sunyi lafiya ba abun da zasu man"
"kar kice haka mama,ji fa yanda suka nufe ki da gudu, waɗannan yaran wani lokacin jinsu su ke kamar wasu ƙananun yara"
"duk da haka dai da ka barsu, ku zo nan"dadi ta faɗa tana miƙa masu hannu, matsawa su kayi kusa da ita su ka zauna "inakwna dadi "
"lafiya lau, ya gida "
"lafiya lau"
"masha Allah" fira su ka shiga yi da dadi, abie dai na zaune yana jin su, tashi yayi yana faɗin "mama ni zan wuce "
"zauna ina son magana da kai" komawa abie yayi ya zauna yana faɗin "to Allah ya sa lafiya"
"lafiya lau" ta faɗa tana kallon su Aairah ta ce ku ɗan bamu wuri " da to suka amsa haɗi da ta shi suka fice, dadi tace " dama magana ne akan ɗana, tun ranar da nayi maku magana kai da mustafa ban sake jin wani ya ce komi ba dangane da maganar " ɗan nisawa abie yayi sannan ya ce
"haka ne mama, naje har garin na ku, amma ban samu wanda yace ya san inda ya koma ba, an dai ce man a kwai wani abokin baban sa da suke kasuwanci tare, amma yanzu baya garin, lokacin da bai da lafiya babban ɗansa yazo ya tafi da shi, sun dai faɗa man ɗanna sa yana kaduna da zama"hannu dadi ta ɗaga sama tana faɗin
" ya Allah, Allah ka bayyanar da shi, hankalina ta shi yake duk lokacin da nayi mafarkin habiba,ban riƙe amana ba " ta faɗa hawaye na sauka a fukar ta,lallashin ta abie ya shiga yi, hannu yasa ya share mata hawaye yana faɗin
"ki dai na kuka mama, insha Allah za'a gan shi, ki daina cewa ba ki riƙe amana ba Allah yaga niyyar ki"
"Muhammad dole na ce haka, amanar yaron nan ta bar man , da ace da ubansa ya nuna bazai bar man shi ba na cigaba da kula da shi ina ziyartar shi, amma sai na fita batun shi, kaga kuwa ban kyauta ba "
"kiyi haƙuri komai zai wuce da izinin ubangiji, za muyi iya bakin ƙoƙarin mu ganin mun samu inda yake "
"to Allah ya yarda "
"Ameen " abie ya ce
"Muhammad wai ya jikin abokin ka, kwana biyu ba muyi waya da safwan ba da mahaifiyar shi , ban kuma tambaye ka ba "
"jiya munyi waya da safwan, ya sanar min an ma kusa sallamar shi , ya nemi alfarmar a bar shi can wurin su"
"ai gara yayi zaman shi can, ko dan saboda azzaluman mutanen nan "
"gaskiya a gani na gara ya dawo nan, har Allah yasa memoryn shi ya dawo"
"to Allah ya ƙara sauki , amma kana ganin idan ya dawo ƙasar nan mutanen nan zasu barshi, baza su cigaba da bibiyar rayuwar shi ba "
"haka ne muddin suka san yana raye baza su ƙyale shi ba,ko da nace ya dawo nan bawai zai koma can bane, a nan zai zauna tare da mu har memoryn shi ya dawo ya tuna da iyalan shi,ta hakan ne za mu iya samun sa'a akan su, amma idan yana can ba lallai ne ya iya tuna baya ba "
"gaskiya hakan shi ya fi, dan ya ji jiki da da ƙarar kwana da tuni sun kashe shi, kuma yan da ya manta da abun da ya faru za su iya ƙara cutar da shi muddin ya koma " ɗan nisawa abie yayi yace
"haka ne, shi da yake mahaifin safwan kwanan shi sun ƙare shiyyasa suka samu galaba a kan shi har su ka kashe shi"
"insha Allah , Allah zai toni asirin su"
"Ameen, burina kwai ya dawo cikin hayyacin shi, ya tuna da baya "
" ameen, Allah ya bashi lafiya " da ameen abie ya amsa, sun ɗan jima suna tattaunawa akan abokin abie, daga baya yayi ma dadi sallama, parlor dadi ta nufa wurin su Aairah da Aunty Rabi.


✨Abuja✨


Zaune ya ke kan carpet a parlor yana aiki a laptop, sanye yake da short black color iya gwiwar sa, sai t_shirt ita ma black color, wayar sa da kan hannun sofa ce ta fara ringing , jawo ta yayi haɗi da du ba mai kiran, murmushi yayi ganin A hashim, picking yayi tun kafin yace wani abu A hashim yace " hey man gani a bakin gate ɗin estate, kasan halin securityn ku da ɓakar tambaya "
"kai kuma tambayar ce baka so?"
"ni dai ka kira su bana son surutun tsiya"
"ai kuwa sai dai kai ta tsayuwa, dama ba kace wurin mansoor ka zo ba, to mi ya hana baka kira mansoor ɗin ba, shi sai ya kira su "
"ok dan na kira ka shine zaka ɓata man lokaci, Allah ko ka kira su su barni na shigo ko na koma in da na fito "
"yo ka kuma "kashe wayar a hashim yayi ba tare da yace komai ba, number ɗaya daga cikin security ya kira yana faɗin "ɗan rainin hankalin yana iya ko mawa " picking security yayi yana faɗin "good evening sir"ba tare da ya amsa gaisuwar ba yace "friend ɗi na na waje ku bar shi ya shi "
"ok sir "security ya faɗa, rejecting kiran yayi, aikin sa ya ci gaba.


security ne ya nufi motar A hashim da ke bakin main gate , baƙar mota ce ƙirar ferrari 250 ta sha tinted, security na ƙara so wa, hannu ya sa yayi nocking window motar , sauke glass a kayi a hankali, arba nayi da kyakyawar fuskar ( DR ABDALLAH MUHAMMAD HASHIM , A HASHIM, BI MA'ANA YA ABDALLAH ) sanye yake da farin yadi, ya sha ɗinkin zamani, kallon security yayi yace"barka da aiki"
"alhmdllh, dama yallaɓe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login