Showing 78001 words to 81000 words out of 133697 words

Chapter 27 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt

ta furta hadi da kiran sunan sa'ada, jin muryar momy ne yasa ta tashi zambur kamar wacce aka zungura " momy ina fatima, ina ƴar uwata take, momy dan Allah ki faɗa man in da take " ta ƙarashe maganar tana kuka
"kiyi haƙuri sa'ada ƴar uwar ki bata ɓata ba kiyi shiru kijin, kar ki ja ma kanki ciwo "
"amma wacece a part ɗin dady naji kuna faɗin ya luqman yayi raping" da ta faɗi haka har sai da gaban momy ya faɗi " momy kinyi shiru,idan har ba ƴar uwata bace pls momy wacece " hawaye ne suka taru a fuskar momy, girgiza mata kai tayi " sa'ada nima ban san wacece ba, dadyn ku yaƙi bari naga ko wacece "
"momy amma a ɗakin na same ki pls momy ki faɗa man " shiru momy tayi batace mata ƙala ba, tana son kowa ya san halin da ake ciki amma ta tsoron wane irin hukunci luqman zai fuskanta take, ganin tayi shirune yasa sa'ada faɗin "momy ki faɗa man, ko naje na kira ya shazim da ya mansoor su zo su ɓalle ƙofar ɗakin dady "
"sa'ada karki kira su ba fatima bace "
"idan har banga kowa cece ba hankalina bazi taɓa kwanciya ba" tana gama faɗa ta fice daga ɗaki da gudu,k'wala mata kira momy ta shiga yi tana fad'in ta dawo ,amma ina ko wai wayen momy bata yi ba , fashewa momy tayi da kuka "ya Allah ka kawo sassauci a wannan lamarin ya Allah "
sa'ada ɗakin momy ta faɗa dagu ta maida ƙofar ta rufe, wani sabon kukan ta sake fashewa da shi, sai da tayi mai isar ta sannan ta tashi ta kamar wacce ciwan hauka ya kama hau buɗe buɗen drawer's tana neman extra key's gaba ɗaya ta hargitsa ma momy ɗaki ta hauka ta shi kayan ta da ke cikin wardrobe duk ta watso su ƙasa, har da su ɗaga mattress sai nishi take ta haɗa uban gumi amma bata gan su ba fitar da rai tayi da ganin su sai hawaye take kayan da ta watso ta fara kwashe wa tana mai dawa cikin wardrobe,sai da kwashe su tasa ta maida ta rufe wardrobe ɗin, zama tayi ƙasa dirshan tana share hawayen dake ta zarya a kumatun ta, tazo tashi kenan zata fita idanun ta suka sauka akan keys ɗin da take ta wahalar nema, ashe wajen watso kaya ta watso da su batare da ta sani ba , ɗaukar keys ɗin tayi ta fice da sauri.


Dady na fita daga part ,part d'in uncle Ahmad ya nufa ,a parlor ya same shi shida su mansoor da ya usman ,noraiz ,mahmud sai gwaggo halima da mama ,sunyi jugum jugum,kowa hankalin shi tashe yake da rashin ganin fatima, ya usman ya yanke shawarar kiran police ya sanar da su halin da ake ciki , Abba ne yace kana ganin za su zo,na ga dare yayi kuma ka san yana yin jami'an tsaron k'asar nan yan da su ke"


"haka ne Abba,ai wanda zan kira aboki na ne kuma nan kusa office d'in su yake "
"to shikenan " Abba ya fad'a,
ya d'aga waya kenan zai kira su sai ga dady ya shigo ,fasa kiran yayi,amsa mashi sallamar da yayi su kayi ,wurin su dady ya k'ara so ,Abba ne yace " wai dama kana nan?, amma dai baka san mike faruwa bane ko?"


Dady yace
"na sani ,akan maganar ne ma nake son mutattauna"


" in taso ne " da eh dady ya bashi amsa had'i da juyawa ya fita ,bin bayan shi Abba yayi, garden su ka nufa ,zama su kayi akan kujerun dake wurin ,shiru dady yayi bai ce komai ba har sai da Abba yace " kace za muyi magana mun kuma zo kayi shiru ,ina fatan dai lafiya ,d'an nisawa dady yayi sannan ya fara magana
"yaya kasan halin yaronann luqman bai da hankali koko alama ..." sai kuma yayi shiru, ganin yayi shiru ne yasa Abba da sauri yace " kayi shiru kuma mi luqman yayi ,kar dai kace man duk neman yarinyar nan da ake luqman ne ya d'auke ta?"


"da ace d'auke ta yayi yaya ai da sauki , saboda bai da hankali bai san in da ke mashi ciwo ba k'okarin yi mata fyade ya so saboda kawai ta nuna bata son shi "


zanbur Abba ya mike yana fad'in "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un ,dama yaron nan bai da hankali ban sani ba ,amma Ibrahim miyasa tun d'azun baka sanar da ni ba, yanzu tana ina"


"tana bedroom ɗina, na so tun lukacin na sanar dakai ,amma ganin kuna asibiti ne yasa ban sanar da kai ba"


"haba Ibrahim idan bana nan ka kirani ai dole na dawo ,kuma ai da ka sanar da shazim ,yanzu idan ya san cewa tun d'azu tana part d'in ka ,mi kake tuna nin zai biyo baya ,kana gani d'azu cewa kawai fa yayi yana son ta amma ji irin bacin da ranshi yayi da maganganun da ya fad'ama,"


"wallahi yaya tsoron irin hukuncin da zai ma luqman ne yasa ban sanar da shi ba "


"ai da ko mansoor ka fad'a mawa shi zai iya controling d'inshi ko halima, da sai su kai ta hospital adu bata ,amma yanazu ba k'aramin kuskure kayi ba na kin fad'a tun d'azu "


"ya salam amma yaya minene ma fita "


"mafita d'aya ce a sanar da shi halinda take ciki "
"amma yaya yana iya illata luqman da duka "


"to koma mi zai mashi ai shi ya ja tun da bashi da hankali ,kuma zamu k'i fad'a ne saboda kar ya hukunta shi, kuma idan mu kayi haka ba muyima yarinyar nan adalci ba kamar yan da luqman yake a wurin haka take a wurin mu "


"hakane, bari na kira dr sai ta zo ta du bata " dady ya faɗa haɗi da ciro wayar shi daga aljihu yayi dialing number dr su.


_*✨SHAZIM✨*_


"Shazim ni ina mamkin in da fatima zata je ,ko ina a estate d'innan kun du ba kuwa " a cewar Abdallah


d'agowa shazim yayi yana fad'in
"duk in da nake tunanin zata iya shiga mun duba amma ba mu ganta ba"


"gaskiya abun nan da mamaki ,tun da dai ba inda zata je,nifa zargi nake tana cikin estate d'innan"


d'an nisawa shazim yayi had'i da cewa" nima zargina kenan,sai dai duk inda nake tunanin zata iya shiga ko za'a iya kaita sai da na duba,dan na daina tunanin wani wuri ta tafi yanzu nafi zargin sace ta akayi "


"abun da kawai ya kamata yanzu shine mu kira police kawai dan wannan zaman da muke bawai zai amfana ma wani abun arzik'i bane ,amma ya ka gani"


"gaskiya wannan itace mafita kawai "


Abdallah wayar sa daya d'aura kan hannun sofa ya d'auka ,number wani police abokin uncle ahmad yayi dialing
Mansoor ne ya shigo part ɗin wuri ya samu kan sofa kusa da Abdallah ya zauna, kallon shi Abdallah yayi yana faɗin " mansoor har yanzu ba wani labari "
"
"babu Abdallah,gashi tun ɗazu ya usman ya kira wani abokin shi police amma har yanzu baizo ba, na rasa gane lamarin ƙasar nan "


"sai haƙuri, nima yanzu na kira wani abokin uncle na san shi insha Allah zai zo "


" Allah yasa " Mansoor ya faɗa, shazim dai na gefe yana jinsu baice ƙalaba wayar sa ce tayi ringing , dafe kai yana faɗin
" ya Allah, wallahi na rantse duk wanda na kama da sa hannun shi hmmm... " kawai yace ba tare da ya ƙarasa ba, kiran ne ya sake shigowa wayar mansoor ne yace "idan bazaka ɗauka ba ka kawo na ɗauka, dan rashin ɗaukar ka shi zai ƙara jefa su cikin tashin hankali "


"idan na ɗauka mi zance masu mansoor?, idan har su ka sani hankalin su sai ya fi tashi akan wanda suke ciki yanzu saboda rashin ɗaukar kiran su da banyi ba "


"duk da haka shazim da ka ɗauka sai kace masu kun fasa dawowa ne yau, amma hakan zai sa su cikin tashin hankali matuƙa "


"uhmmm " kawai yace


suna nan zaune jigum sa'ada ta bankaɗo ƙofa ta shigo har tana tuntuɓe tana shirin faɗuwa,sai haki take kamar wacce wani abun tsoro ya biyo, fuskar ta sharkaf da zufa mansoor ne ya taso da sauri yana faɗin "wai miyasa ba zaki zauna wuri ɗaya bane sa'ada , ji yan da ki ka shigo kina shirin illata kanki, yanzu miya ya dawo da ke nan"


sai haki take maganar ta ma da kyar take fita "yaya dama.... " maganar ce ta sarƙe mata sai sauke numfashi take
"dan Allah ki kwantar da hankalin ki kiyi man baya nin abun da ke faruwa "
bata ba shi amsar tambayar sai ma nufar shazim da tayi da sauri, keys ɗin dake hannun ta miƙa mashi tana "ya shazim gashi "
ɗagowa yayi yana kallon ta "key ɗin ɗakin dady fatima na can " kamar saukar aradu haka su ka ji maganar ta mansoor da Abdallah da sauri suka nufe ta suna faɗin "da gaske kike sa'ada " ɗaga masu kai tayi tana faɗin " eh yaya da gaske nake tana can ita da ya luqman "
"luqman kuma?, kin tabbata sa'ada? "
"yaya fatima ce fa, wallahi tana can "
"ya Allah, amma mi ya kaita can mi ta ke yi tare da luqman a ɗakin uncle"
ƙarar rufe ƙofa su kaji da sauri ko wannen su ya kalli ƙofar basu ga kowa ba mansoor ne yace "shazim tashi mu je.... " bai ƙarasa ba ganin sofar wayam ba kowa, basu san da ya bar wurin ba sai yanzu su ka fahimci cewa ashe rufe ƙofar da suka ji shi ne ya fita, ba yan sa suka bi da sauri ko da suka fita ko mai kama da shi basu gani ba a compound, zuciyar mansoor sai bugawa take yana tsoron abun da shazim zai yima luqman,da sauri suka isa part ɗin direct sama suka nufa shazim har ya shige ya maida ƙofar da key ya rufe, bubbuga ƙofar su ka shiga yi suna kiran sunan shi amma ko motsin shi basu ji ba bare su sa ran zai buɗe masu, sai haɗa shi da Allah mansoor yake akan ya buɗe masu amma shiru.


Lokacin da ya shiga parlorn ba kowa hakan ya sa shi wu cewa bedroom ɗin dady tura ƙofar yayi ya shiga, kwance ya hangi fatima kamar matatta an rufe mata rabin jikinta da blanket, ƙara sawa yayi bakin gadon saitin in da fuskar ta take,sai fitar da numfashin wahala take kanta ko ɗan kwali babu sumar kanta duk a ya mutse fuskara tayi fayau da ita bakin ta ya bushe ƙamas duk ya faffashe goshinta ma a fashe yake da gefan bakin ta fuskar ta tayi jawur , siraran hawaye ne ke fita daga gefen idanuwanta da suka kumbura su kayi suntum,wuyan ta da ƙirjinta duk sawun ya kushi, sai jan numfashi take da ƙyar ta fitarwa, wasu zafafan hawaye ne suka taru a idon shi zuciyar shi sa ta farfasa take, hannu biyu yasa zai ɗauke ta ƙarar buɗe ƙofa da yaji ne yasa shi juyawa dan ganin wanene ya shigo, ido biyu su kayi shida luqman da ke tsaye bakin ƙofar bathroom ɗin dady daga shi sai bathrobe, tun ɗazu yake cikin toilet ɗin jin motsin mutum ne yasa shi fitowa duk a tunanin shi dady, ai kuwa yayi daya sanin fitowa, wani mumunnan faɗi gaban shi yayi ganin wanda bai yi tsammani ba da sauri ya juya zai koma toilet ɗin sai kafin ya ja ƙofa ya rufe tuni shazim ya cimma sa, roƙwanshi ya fara akan dan Allah yayi mashi haƙuri wallahi ba da gangan yayi mata haka ba, kuma ba abun da yayi mata " sai magiya yake mashi amma ina shazim bai ma san yana yi ba, buga mashi kai yayi da bango nan take goshin shi ya fashe ya fara zubar da jini, wani wahalallen ihu luqman ya saki yana cigaba da rokwan shi da yayi mashi afuwa bazai sake naushi shazim ya kaima bakin shi dake yake rokwan na shi,naushin shi ya shiga yi ta ko ina yana buga mashi kai da bango tun luqman na da bakin bashi haƙuri har ta kai muryar shi bata fita saboda azaba.
Su mansoor na bakin ƙofar part ɗin suna aiki bugawa da roƙon shazim akan karyayi ma luqman wani abu amma ko alamar yana jin su basu jiba, hankalin su duk ya tashi akan halin da luqman yake ciki, sa'ada sai kuka take tana kiran sunan luqman da fatima, momy ma sai kuka take tana ro kwan shazim karya kashe luqman, ganin da gaske shazim ba jinsu yake ba yasa momy fita da part ɗin a hargitse ta nufi part ɗin uncle Ahmad kamar an jeho ta haka ta faɗo cikin parlorn su mama da gwaggo Halima da su ya usman da sauri suka miƙe cikin tashin hankali su ke tambayar ta lafiya, momy sai hawaye take ta nuna masu bayan ta bayan nata suka kalla su basu ga komai ba, sai da ƙyar ta samu ta kalmomin " sha zi m zai ka sh e luqman " ta ƙarasa maganar a rarrabe,salati gwaggo halima ta rabka tana faɗin " na shiga uku ni halima, mi ya haɗa su kuma Innalillahi "
da sauri su ya usman suka nufi part ɗin su momyn, bin bayan su su mama su kayi momy sai sharar hawaye take, a bakin ƙofar part ɗin suka tsaya suma su ka hau bubbuga ƙofar suna rokwan shazim da ya buɗe amma ina ya usman ne yace su sa ƙarfi kawai su ɓalla ƙofar kawai dan ko zasu kwana a nan shazim ba wai zai buɗe masu bane har sai ya fitar da mansoor daga hayyacin sa, haka su kai ta ƙoƙarin ɓalla ƙofar, duk wanna budirin da ake dady da Abba suna garden jiran dr basu san mike wakana ba, ba irin ƙoƙarin da su mansoor basu yi ba ganin ƙofar ta buɗu amma ina, momy ce tace mahmud yaje ya kira su dady a kwai key a jikin shi, da sauri luqman ya tafi kiran su, su kuma su mansoor na ta aikin ɓalla ƙofar yayin da Abdallah yake sake kiran number wannan police ɗin dan yaga sun jima basu zo ba gashi ana shirin kisan kai.
sai ga dady da Abbah sun shigo hankali a tashe da sauri dady ya nufi ƙofar yana ciro key ɗin dake aljihun shi matsawa su mansoor su kayi suna bashi wuri key ɗin yasa ya shiga kiciniyar buɗe ƙofar amma ina ta ƙi buɗuwa saboda key da shazim ya bari jikin ƙofar da ya shiga, kuma yayi hakan ne dan kar ma su samu sa'ar buɗer ƙofar


Shazim sai da yayi mashi lilis duk ya farfasa mashi goshi da bakin shi shaƙe mashi wuya yayi har sai da yaga baya motsi ko ɗan yatsa baya iya motsawa tukun ya sake shi ya faɗi ƙasa yarab ba numfashi, bai bi ta kanshi ba ya nufi gadon da fatima take hannu biyu yasa ya ɗauke ta irin ɗaukar da ake yima jarirai ya fice da ita yana zuwa bakin ƙofar su mansoor na samun nasarar ɓalleta suka shigo da sauri ganin shi da fatimar ne yasa suka nufe shi sa'ada da sauri da shigo tana kuka haɗi da cewa "ƴar uwata miya same ki, ya shazim naga kamar bata numfashi " sai tambayar shi suke wane hali take ciki dan ganin fatima. ya sa sun man da luqman da ke can yashe a bedroom ɗin dady, dadyn kawai ya nufi bedroom ɗin da sauri har sai da gaban ya faɗi da yayi arba da luqman yashe a ƙasa babu alamar ma yana numfashi, bayan shi Abba ya biyo da sauri shima ya ja burki ya tsaya yana bin luqman da ke kwance ƙasa, kuka ne ya kubce ma dady yana faɗin "luqman dan Allah ka tashi kar ka mutum, dan Allah na roƙe ka katashi " sai jijjiga shi dady yake yana roƙwanshi da ya tashi amma ina ko motsi wannan bai yi ba Abba ne ya ƙaraso kusa da su dafa kafaɗar dady yayi " Ibrahim ai shuma yayi " sai a lokacin dady ya lura da cewa suma luqman ɗin yayi jiyawa Abba yayi ya nufi toilet ya ɗebo ruwa yazo ya yayyafa ma shi a fuska a firgice luqman ya farka sai sambatu yake yana faɗin "dan Allah ya shazim kayi haƙuri wallahi babu abun da nayi mata, dan kar ka kashe ni wallahi bazan sake ba plea.... " da sauri dady ya kira sunan shi, zambur luqman ya miƙe zai nufi toilet dan duk a tunanin shi shazim ne tashin farko bai gane muryar dady bace sai da Abba yace "dawo luqman ina zaka ba shazim bane mune " sannan luqman ya tsaya yana sauke numfashi da sauri ya nufi dady yayi hugging ɗinsa fashewa yayi da kuka kamar wani ƙaramin yaro
"dady ya shazim kashe ni yaso yi, baya ƙaunata sai ce mashi nake ba abun da nayi mata amma sai da ya dake ni , miyasa ka bar shi ya shi go "


dady yace "luqman duk laifin ka ne, yanzu ai kaga irin abun da nake guje maka ko "
"dady wallahi ban yi mata komai ba, Allah bazan sake ba, dan Allah kar ka bari ya raba ni da ita wallahi ina son ta "
"kama dai na faɗar haka luqman dan yanzo ko mutuwa zaka yi shazim bazai taɓa bari ka aureta ba ba shi kaɗai ba har ita kanta fatimar da su Aisha "
"dan Allah dady"
Uncle Ahmad ne yace "ya isa haka, zo muje mansoor ya duba ka ko mu tafi asibiti goshin ka da bakin ka sai zubar da jini su ke "


"Abba banzan iya zuwa wurin ya mansoor ba nasan shima fushi yake da ni kuma ina tsoron na fita mu sake haɗuwa da ya shazim, momy dai ta zo nan ta duba ni "

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login