Showing 39001 words to 42000 words out of 133697 words

Chapter 14 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt

inda zani" ya faɗa hadi da tashi ya nufi part ɗin su, tashi ita ma fatima tayi ta nufi nata bedroom ɗin....


✨SHAZIM✨


Zaune yake a office ɗin shi ya bar baza ta kardu kan table ɗin shi ya zuba masu ido yana kallon su da alama hankalin shi baya kansu, yayi zurfi cikin tunani ya ji ana nocking, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya bada izinin shigowa, hidaya ce ta shigo hannun ta ɗauke da files, gaishe da shi tayi hannu kawai ya ɗaga mata, ganin hakan ne yasa hidaya fahimtar yau baya san magana dan haka kawai ta matsa kusa da table ɗin ta ajiye mashi files, ɗago da kanshi yayi yana kallonta, fahimtar mi ya ke nufi ne yasa ta cewa "dama files ɗin patient ne dake waje" sai yanzu ya buɗe baki ya ce "kwashe su ki kaima dr kabir, bazan samu damar du ba kowane patient ba yau" daga ganin yana yin da yake maganar zaka san cewa baya jin daɗin," dr baka jin daɗin ne" hidaya ta tambaye shi, kai kawai ya ɗaga mata, ɗaukar files ɗin tayi ta fice, direct office ɗin dr kabir ta nufa, nocking tayi aka bata izinin shiga, shiga tayi bakin ta ɗauke da sallama, zaune ta same shi yana aiki a laptop "good morning sir "hidaya ta faɗa, ɗago da kansa yayi yana amsa mata gaisuwar da tayi tana kallon files ɗin sa ke hannun ta"lafiya dai koh hidaya, ina zaki da wannan files ɗin? " amsa ta bashi da "dr Shazim ne yace na kawo maka, bazai samu da mar duba patient ba yau"
"ok ajiye " ya faɗa yana maida kansa kan aikin da yake yi, hidaya tana ajiyewa ta fice daga office ɗin, saida ya gama aikin da yake yi sannan ya miƙe ya fice daga office ɗin, ya nufi office ɗin Shazim, shiga kawai yayi batare da yayi nocking ba, samun shi yayi zaune kan sofa dake office ɗin dafe da kanshi, jin alamar an buɗe ƙofa ne ya sa shi ɗago da kanshi yana kallon dr kabir da ya shigo, amsa mashi sallamar da yayi yayi, ƙara sawa dr kabir yayi haɗi da ne man wurin zama ya zauna kusa da shazim yana faɗin "hi dude, what's wrong with you, naga kasa nurse hidaya ta kai man file ɗin patient " kallon shi Shazim yayi sannan ya ce " am not feeling better "
"ya salam, mike damun ka " ɗan nisawa shazim yayi sannan ya ce "wallahi ammy ce wai dole sai natafi abuja, da na kawo mata excuse fushi ma tayi dani " kabir ya ce " to minene aciki da har zaka sama kan ka damuwa irin haka, shawarar da zan baka anan kawai kashirya ka tafi, hakan ka ɗai zai sa ammy ta huce "
"baza ka gane ba kabir, kwata kwata bana son zuwa abujar nan "
"to ya zakayi haka nan zaka yi haƙuri ka tafi tun da ammy ta ce katafi, yaushe ne tace ka tafi "
"gobe fah "kabir ya ce "to Allah ya kaimu gobe, kai ka ɗai zaka tafi "
"a'a harda su noraiz "
"ok, Allah ya kaimu goben, karka wani damu "shazim ya ce "ameen nagode"
"bakomai kar ka damu "
"ina ma tuna nin tashi zanyi na tafi abnoor dan ban gaya ma majeed ba, sannan zan koma gida daga chan"
Kabir ya ce "eh gaskiya ya kamata, da ƙarfe nawa zaku tafi ko dai sai munyi waya "
"ina tuna nin da safe, dan wallahi ammy tayi fushi sosai "
"to Allah ya kaimu "
"ameen " Shazim ya faɗa hadi da tashi ya nufi table ɗin sa ya fara haɗa kayan shi yana maidawa cikin briefcase, yana gama haɗa wa kabir ya taso domin yi mashi rakiya, su hiday na zaune a reception suka zo suka wuce, suna wuce maryam tace "lafiya naga dr ya tashi lokacin tashin shi bai yiba " hidaya ta ce "baya jin daɗi ne, dan koda na kai masa files ɗin patient cewa yayi na kaima dr kabir, ina tuna nin ba zai iya zama ba shiyyasa zai tafi gida " maryam tace "Allah ya bashi lafiya " da ameen hidaya ta amsa, chan maryam tace"kinsan wane tuna nin nayi? " hidaya ta ce "a'a sai kin faɗa " maryam tace "kawo kunnan ki kiji" matsawa hidaya tayi kusa da maryam, magana ta faɗa mata, sauran nurses ɗin dake wurin suka ce "dan muna kusa shine abun harada su raɗa ko maryam" murmushi maryam tayi sannan ta ce "komai fa na son sirri, wannan magana ce tsaka nina da ita" wata acikin nurses ɗin ce ta ce "in tayi wari maji" ƴar dariya maryam tayi haɗi da cewa "bama zata yi ba "


har parking lot dr kabir ya raka shi, saida dr kabir yaga tafiyar Shazim tukun ya koma cikin hospital ɗin, ya zo zai shiga office ɗin shi yaji maganr hidaya tana cewa"doctor " juyowa yayi yana kallonta sannan ya ce "na'am " duƙar da kanta tayi ganin ya kafe ta da idanu "lafiya dai koh hidaya,? kin tsayar dani kin kuma yi shiru " magana ta fara yi bata re da ta ɗago da kanta ba "dama dr tambayar ka zanyi mike damun dr ne " kallon ta kawai dr kabir keyi, sannan ya ce "baya faɗa maki baya jin daɗi ba "
"eh haka ne "
"to baya jin daɗi ne, gida ma ya tafi yanzu"
"ok, am dan Allah ko zaka bani number shi nakira shi nayi mashi ya jiki"magana take still kanta na duƙe, wani kalar kallo dr kabir ya shiga binta da shi, ita kuma jin baice komai ba yasa ta ɗago da kanta, tana ɗago wa idanun ta suka sauka cikin nashi daya kafe ta dasu, kusan 5 seconds bai ce komai ba, chan ya ɗan nisa sannan ya ce "dama baki da number shi" girgiza mashi kanta tayi alamar eh, "ok shikenan ina wayar ki na sa maki number " hannu ta sa cikin aljihun rigar uniform ɗin ta ta ciro wayar ta ta miƙa masa, amsa yayi ya sa mata number, miƙa mata wayar yayi tasa hannu ta karɓa tana faɗin" nagode" shi dai dr kabir kallonta kawai yayi ba tare da ya ce mata komai ba harta juya ta bar waje bai daina kallonta ba, sai da ya ga ta ɓace ma ganin sa tukun ya murɗa handle ɗin ƙofar office ɗin shi ya shiga.....


✨ Shazim ✨


yana barin eko direct abnoor ya nufa, yana parking ya fito ya nufi main entrance ɗin hopital ɗin ba tare da ya ɗauki briefcase ɗin sa ba, yana shiga direct office ɗin dr majeed ya nufa
nocking yayi, daga ciki aka bashi izinin shiga, kama handle ɗin ƙofar yayi ya tura ya shiga, bakin sa ɗauke da sallama, zaune dr majeed yake yana duba files dake gaban shi, amsa mashi sallamar yayi, wuri shazim ya samu ya zauna, hannu ya miƙama dr majeed suka yi musabaha, dr majeed ya ce " lafiya kuwa yau nagan ka a wannan lokacin? "
"lafiya qlu majeed, maganar tafiya abuja nan ce ta taso, ammy tayi fushi dole sai mun tafi gobe "majeed ya ce "to fah, kwana nawa zaka yi "
"kai dai bari kawai wai sai nayi sati biyu inji ammy"
majeed ya ce "shiyyasa fa tun time ɗin da kace tace ku tafi ya sa nace maka ka tafi kawai ni zan kula da komai, amma kaƙi, yan zu ga irinta nan ta soke kwana biyar ɗin da tace "
"bazaka gane bane kawai majeed, wallahi bana son zuwa ko nan da chan shiyyasa "
"to ya zaka yi zumunci ne dole ayi shi"
"haka ne"
"yanzun goben da ƙarfe nawa zaku tafi? "
"da safe"shazim ya bashi amsa " ok Allah ya kaimu " da ameen ya amsa , sun ɗan jima suna magana akan magunguna da allurai da zasu yi order, sai da shazim yayi sallamar asr bayan yaba ma majeed duk abun da zai bashi, sannan suka yi sallama ya nufi gida, tsit ya iske parlor alamar ba kowa, hakan yasa shi nufar bedroom ɗin ammy amma nan ma ba kowa, fita yayi ya nufi up stairs part ɗin noraiz ya shiga, samun shi yayi a parlor zaune kan sofa yana aiki cikin laptop, ɗagowa noraiz yayi jin anbuɗe ƙofa , yana ganin shazim ya miƙe yana faɗin "sannu da dawowa yaya"da yawwa shazim ya amsa yana cewa "ina ammy? , naga kamar bata gida kuma banga motarta ba a parking lot, nama yi tuna nin kokai ka fita da motar"
"tun da ka fita ta fita ko breakfast bata yi ba, na tambaye ta ina zata, sai cewa tayi yanzu zata dawo, amma haryan zu bata dawo ba" jinjina kai kawai shazim yayi haɗi da ficewa ya nufi part ɗin sa, yana shiga parlorn shi wayar shi dake cikin aljihun wandon shi ya ciro number ammy ya shiga kira, tana ringing amma ba'ayi picking ba harta katse ya sake kira sai da yayi kusan 3 times amma bata ɗauka ba, fita yayi ya koma part ɗin noraiz, yana shiga yace "noraiz ina wayar ka? "
"gata nan yaya " noraiz ya bashi amsa "kira number ammy "da ok noraiz ya amsa, nan shima ya shiga kiran wayar amma ba'ayi picking ba, ƙofar parlorn suka ji an buɗe fatima ce ta shigo da waya a hannun ta "yaya na shiga ɗakin ammy naji wayar ta na ringing, sai da na duba naga ashe kai ke kira, shazim bai ce komai ba ya fice daga part ya koma nashi, number malam yayi dialing, picking malam yayi haɗi da Sallama yana faɗin "likita bokan turai"
"ina wuni malam"
"lafiya lau, ya aiki"
"alhmdllh "
"to masha Allah "
ɗan shiru Shazim yayi, jin yayi shiru ya sa malam ce wa "lafiya dai koh shazim? "
"lafiya lau malam, dama ammy ce " sai kuma yayi shiru, malam " yace miya samu aishar? "
"bakomai malam, tayi man magana ne akan zuwa abuja to nace mata ina da uziri wirin aiki, to sai bata sake maganar ba tun daga ranar, yau kawai " nan ya shiga bashi labarin yan da suka yi da ammy yau , har fushin da tayi da kuma dawowa da yayi yanzu bata gida da kuma kiranta daya ke bata ɗauka, ɗan nisawa malam yayi sannan ya ce "ta faɗa man komi ke faruwa, gaskiya banji daɗi ba, baka kyau ta ba, shi zumunci Allah ne yace ayi sa, kuma komi ya faru tsakanin ka da su ai kai ne baka kyauta ba " sosai malam yayi mashi faɗa da nasiha, akan bai kyauta ba daya bari har sai da ran ammy ya ɓaci "ayi haƙuri malam insha Allah hakan bazata sake faruwa "
"shikenan Allah ya kyauta gaba " da ameen malam ya amsa, sannan shazim ya ce "to malam ammy tana nan ne "
"eh tana nan " ajiyar zuciya shazim ya sauke, sannan suka yi sallama da malam, bedroom ɗin shi ya wuce, jifar da wayar shi yayi kan gado yana shiga, kayan jikin shi ya cire daga shi sai boxer yanufi bathroom, kusan 15 minutes ya fito ƙugun shi ɗaure da towel, shiryawa yayi ciki ash ɗin jallabiya wuri ya samu kan sofa ya zauna, laptop ɗinshi ya jawo yashiga dan dannawa....


ammy bata dawo gidan sai da yamma liƙis, ta shigo, gaishe da ita fatima da noraiz dake parlor zaune, amsa masu tayi, haɗi da samu wuri ta zauna kan sofa, hijaba ɗin ta ta cire ta miƙa ma fatima tan cewa "kai man ɗaki" da to fatima ta amsa ta tashi ta kaima mata, tana fitowa ammy ta ce "ina innah asabe? " amsa ta ba ammy da "tana ɗakin ta"
"ok "
Noraiz ya ce "ammy wai ina kika je ne, yaya ya dawo tun ɗazu yana ta ne manki " fuska a ɗaure amma ta ce
"in da ya aike ni chan na tafi"
noraiz ya ce "dan Allah ammy kiyi haƙuri ki dai na wannan fushin, goben zamu tafi kamar yanda kika ce"
"karma ku tafi " ammy ta ce, magana noraiz zai yi, ta ɗaga mashi hannu tana ce "ya isa haka kar ka takura man daga dawuwa ta " da jin haka dole noraiz ya kama baikin sa yayi shiru, sau kowa shazim ya ke daga up stairs ya nufo parlorn, hango ammy da yayi, yana isowa parlorn ammy ta miƙe ta nufi ɗakin ta, tsayawa yayi chak ganin tana ganin shi ta tashi, binta yayi har ɗakin, yana shiga ya ganta tsaye bakin dressing mirror, ta cikin mirror ta hange shi, yi tayi kamar ma bata san da shigowar shiba, ƙara sowa yayi har gaban dressing mirror ɗin yana faɗin "ina wuni ammy" amsa mashi tayi da "lafiya " daga nan ta ɗauke kanta ta koma bakin gado ta zauna, binta yayi har bakin gadon, durƙu sawa yayi yana dafa gwiwar ta, haƙuri ya shiga bata, da ƙyar ta haƙura, ganin ta haƙura yasa cewa "dan Allah ki rage satin da ki kace zanyi zuwa kwana biyar "
"idan har kana son zaman lafiya da ni to kawai kayi shiru "da to kawai ya amsa mata, sannan ya fice daga ɗakin ya koma part ɗin shi domin yin alawala saboda lokacin sallah da yayi,yana fita ita ma ammy tashi tayi ta nufi toilet domin alawa, yana ko mawa part ɗin shi alawala kawai yayi ya fito suka wuce masallaci da noraiz dake parlor yana jiran shi yana saukowa suka wuce, anagama sallah suka wuce gidan malam basu bane suka dawo gidan ba sai wurin ƙarfe 10 sannan suka dawo, koda suka dawo ammy da fatima har sunyi bacci, suma part ɗin su suka wuce kowa ya nemi ma kwancin shi .........🖊


Episode 20 _21


Washe gari...


Iliya ne ke saka trolleys ɗin su fatima a booth ɗin mota da zai kaisu airport,
ammy da fatima da noraiz sai Shazim zaune suke kan sofa a main parlor, ammy nayi masu nasiha sai da ta gama faɗa masu duk abun da zata faɗa masu sannan suka tashi suka kama hanyar fita daga parlorn, fatima da noraiz harsun fice ammy ta tsaida shazim, tana faɗin "dan Allah shazim karnaji kar na gani dan Allah, kayi haƙuri da komi zaka gani har Allah yayi maku dawowa "
"to ammy insha Allah "fitowa suka yi ammy ta raka su har parking lot suka shiga mota, tana masu Allah ya tsare hanya da ameen suka amsa mata, sannan ilya yaja motar suka fice daga gidan ammy na ɗaga masu hannu, saida taga mai gadi ya rufe gate sannan ta juya ta koma ciki, cike da kewar su yanzu sai ita kaɗai cikin gidan, fatan Allah ya kaisu lafiya ya dawo dasu lafiya..


suna fita daga gidan direct gidan malam suka wuce dan suyi mashi ban kwana, sosai malam yayi masu nasiha da fatan isa lafiya, suna fita ilya ya kama hanyar airport, koda ya kaisu sai da ya jira har jirgin su ya tashi sannan ya dawo gida.....


✨Abuja✨


Airport, passengers ne suka fara fitowa ta ƙofar da aka rubuta exist wacce aka tana da domin passenger, su shazim ne suka ɓullo ta wannan ƙofar yana gaba fatima da noraiz na biye da shi abaya da trollys ɗinsu a hannu, wata kyakyawa matashiya ce wacce zasu yi sa'anni da fatima fara ce sai dai bata kai fatima haske ba, ta nufo fatima da gudu tayi hugging ɗin ta tana faɗin "oyoyo sister" fatima da fara'a a fuskar ta tace "ya kike sa'ada" wacce aka kira da sa'ada, tayi murmushi tana faɗin "lafiya lau ya hanya" sannan ta juyo tana cewa" ya Shazim ina wuni" amsa mata yayi da "lafiya lau" sannan ta juya tana gaishe da noraiz, da fara'a a fuskar shi yace "ai nayi tunani fatima kaɗai kika gani " da murmushi a fuskar ta tace "a'a ya noraiz kuma ai na gan ku " suna nan tsaye wasu ƴan mata kyawawa su biyu suka iso farare ne sai dai ɗaya tafi ɗaya haske, mai hasken sosai tana kama da sa'ada sai dai ita daka ganta zaka san tana ƙara wa dana kanti, jikinsu sanye da ɓakar jallabiya sunyi rolling da gyelen jallabiyar, wurin su suka nufo, mai kama da sa'ada cike da yanga take faɗin "hi ya shazim "haɗi da nufar Shazim da nufin tayi hugging ɗin shi, kasa ƙarasawa tayi ganin wani mumunnan kallo daya bita dashi fuskar shi a ɗaure kamar bai taɓa dariya ba, kwal kwal tayi da ido kwalla na taruwa ciki tace " haba ya shazim miyasa kake haka , daga na nuna farin cikin ganinka " banza yayi mata kamar ma ba da shi take ba,gaishe da shi ɗayar tayi, cikin sakin fuska ya amsa yana faɗin "ya kika kairiyya "
"lafiya lau, ya hanya?"da alhmdllh ya amsa mata,hugging ɗinta fatima tayi tana faɗin "nayi kewar ki aunty kairiyya" da fara'a a fuskar ta tace "nima nayi kewar ki", wasu maza ne suka ƙaraso wurin su su biyu sanye da uniform, suna ƙarasowa suka ce "barkan ku da zuwa ranka ya
daɗe " kallon su shazim yayi yana cewa "barkan ku dai aminu ya kwana biyu"
"alhmdllh ranka ya daɗe" wanda aka kira da aminu ya ce, ɗayan ne ya ce "yallabai ya lagos " shazim na kallon shi ya ce "alhmdllh kamal, ya aiki"
"lafiya lau ranka ya daɗe"sannan suka gaishe da noraiz fuska ɗauke da fara'a ya amsa, sannan fatima ta gaishe da su, amsa mata suka yi cikin kulawa fuskar su da fara'a, suka amshi trollys ɗin noraiz da na shazim dake hannun noraiz aminu na cewa "mutafi koh ran ka yade "ok kawai shazim yace ya kama hanya, su aminu na gaba da trollys ɗinsu, sa'ada ce ta amshi na fatima, wannan budurwar wuce su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login