Showing 102001 words to 105000 words out of 133697 words
Chapter 35 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt
kunya iri iri feenah ta iya ta , abu ƙaɗan tace innah ko faɗa dadyn ta yayi mata tana kuku zata faɗa ma innah, ita kuma tai ta bala'i,saɓanin kairiyya da ba ruwanta, kuma tana son su noraiz dan kusan kullum tana part ɗin ammy,ita ba ruwan ta shiru shiru ce, mari shazim ya kaimata ta ruga da gudu tana kuka ta shige bedroom ɗin momyn ta,yazo fita yaci karo da mansoor da faisal zasu shigo part ɗin, cakumo wuyan rigar mansoor yayi, faɗa sosai ya kyaure tsakanin su har sai da momy {turai} ta fito ta raba su, mansoor na kuka saboda ciwan da shazim ya ji mashi, wuce wa shazim yayi zuwa part ɗin su, yana tura ƙofa yaci karo da ammy tsaye , "daga inah kake? " shine abun da ammy tace, shiru yayi bai bata amsa ba,jin yayi shiru ne yasa ta sake mashi tambayar, shiru ya sake yi , saukar mari kawai yaji a kumatun shi, abun da ammy bata taɓayi mashi ba, rufe shi tayi da faɗa sosai,tana gamawa ta juya, yana dafe da kumatu yace "dan Allah ammy kiyi haƙuri " wuce wa tayi batare da ta kalli inda yake tsaye ba, bin ta yayi har ɗaki yana bata haƙuri sai da ƙyar tace taya fe mashi kuma ya ɗauko key ɗin daya ɗauko ɗakin innah ya kawo mata, da to ya amsa haɗi da ficewa ya bar ɗakin, key ɗin ya ɗauko ya bata, ƙarar buɗe main ƙofa sukaji da ƙarfi, sai kuma haya niya fita ammy tayi zuwa parlor, innah suka gani ruƙe da hannun feenah su luqman na bayan ta tana ta zazzaga masifa, uncle Ibrahim ne ke bata haƙuri yana faɗin
" dan Allah innah kiyi haƙuri"
"wlh ba zan haƙura ba, yan da ya dake su wlh sai na rama masu "
ammy ce tace "mike faruwa ne? "
tun kafin ya bata amsa innah tayi saurin cewa " munafuka annamimiya, kina iya cewa baki san mi wannan fitsararen ɗan naki yayi ba, bayan ke kika sa shi munafuka kawai "
muryar shazim suka ji yana cewa "gaskiya innah ki dai na ce ma ammy na munafuka dan ba munafuncin da tayi maki, dukan noraiz su kayi ni kuma na rama mashi, kuma wlh suka ƙara dukan shi sai nayi masu mafiyin haka tun da ba jakin su bane "
tsawa uncle Ibrahim ya daka mashi yana cewa " kai baka da hankali ne shazim, innar kake faɗa ma wannan kala man, kar na sake jin bakin ka "
innah tace "ai da ka barshi yayi man abun da uwar shi ta koya mashi, na san nan gaba har duka na tana iya sa shi tun da ba sona take ba"
uncle Ibrahim yace "kar Allah ya nuna mana hakan, dan Allah kiyi haƙuri ki koma part ɗin ki"
tasa ƙeyar su feenah tayi zuwa part ɗin ta tana tafiya tana zagin shazim,Aisha tayi tsaye ta kasa ko motsi,
uncle Ibrahim ne yace "dan kiyi haƙuri da halin innah, karki sa abun a zuciyar ki kinga dai halin da kike ciki,ce mashi ta bakomi nagode haɗi da nufar part ɗin ta, faɗa tayi ma shazim har da duka, tana faɗin saboda zuwa makaranta yayi abokai marasa kunya shine zai zo gida yana ma manya rashin kunya, ta kuma gargaɗe shi kar ta sake jin yayi faɗa da wani cikin estate ɗin,
cemata yayi to, bawai dan ya dena ba, ya zame ma yaran gidan abun tsoro dan ko kallon da bai yi mashi ba kayi mashi to zai hauka da duka ne ba ruwan shi, tun ammy na mashi faɗa har dai ta zuba mashi ido tana adu'a Allah ya shirya shi, dan komawa yayi mar kunyar ƙarfi da yaji har jira yake wani ya tsokane shi ko noraiz, dole tasa yaran tsoron shi.
Wata rana wasu mutane suka zo da ga hukumar efcc, har part ɗin ammy wai ana zargin marigayi Abubakar, da satar kuɗin gomnati,dan haka ammy ta tattaro duk wani takardun dukiyar sadiq ta basu tun daga kan filaye har zuwa na company, abun yayi matuƙar bama ammy mamaki haka ma su uncle Ibrahim,ai kuwa kaca kaca ammy tayi masu ta kuma ce "babu wan da ya isa yasa ta bada koda allura ce daga cikin dukiyar sadiq, mutumin da yake hukunta duk wan da aka samu da laifin sata shine zaku ƙullama wannan sharrin , kuma abun ta kaici bayan ba ranshi, wallahi Allah bazai bar kuba"
wani daga cikin mutanen ne yace " hajiya ki kwantar da hankalin ki, mu bamu zo dan rigima ba aikin mu kawai muke yi, muna so ki fito mana da duk wani takarda daya shafi Abubakar in ba haka ba zamu sa jami'ai su duba mana"
ammy ta ce" sai dai kuyi duk abun da zaku yi amma ni bazan ba ku komai ba, tun da na san ƙarya kuke munafuncin ne kawai "
ganin dai da gaske bazata yi masu abun da suke so ba ya sa suka miƙe suna faɗin " to shikenan tun da haka kika ce, Ibrahim mu zamu wuce, amma bawai hakan na nufin baza mu sake dawowa ba " suna gama faɗar haka suka fice da harara ammy ta raka su, har inda suka yi parking Ibrahim ya raka su sannan ya dawo part ɗin ammy, magana ya fara yi ma ammy yana cewa "ina so ki fahimce ni "
"ina sau raron ka "ɗan nisawa yayi sannan ya ce " ina so ki gane cewa tun da kikaga an turo su to daga hukumar sune, kuma ba sharri zasu yi ma yaya ba dole akwai abun da mu ba mu sani ba, amma ina so kiyi haƙuri mu bi komi a sannu ko dan halin da kike ciki, insha Allah komi zai dai dai ta " ko mi akayi sai yace saboda halin da take ciki bai da wata magana bayan wannan
"to shikenan Allah ya shige mana gaba kuma zan yi magana da lawyern, sadiq, tun da a high court yake aiki " uncle Ibrahim ya ce "hakane ni da kaina zanyi magana da barrister, ba sai kin kira shi ba " sun ɗan jima suna tattaunawa ta yan da zasu bullowa al'amarin, uncle Ibrahim na barin part ɗin ya kira barristern sadiq ya faɗa mashi duk abun da ke faruwa,sannan ya samu uncle Ahmad ya faɗa mashi lokacin da suka zo baya gida, ammy ma ta kira su malam ta sanar da su,lallashinta su kayi,ko da su uncle Ibrahim suka sanar da innah abun da ke faruwa cewa tayi to sai mi su ɗauki haƙƙin muta ne su ba su mana , sadiq ɗin waliyyi ne shi da bazai iya satar ƙuɗin mutane ba , abun yayi matuƙar basu mamaki dan basuyi tsammanin jin haka daga wurin ta ba, kwana uku da zuwan efcc ammy ta haihu ta haifi ɗiya mace kyakyawa mai matuƙar kama da noraiz, farin ciki wurin ammy ba'a cewa komai dan tana matuƙar san ɗiya mace,kwanan ammy biyu da haihuwa turai ita ma ta haifi ɗiya mace kyakyawa, farin ciki wurin uncle Ibrahim ba'a cewa komai, duk wani abu da uba zai yima ɗiyar shi sai da yayima babyn ammy da tashi,da ranar suna ta zagayo aka sama babyn ammy fatima babyn turai kuma sa'adatu suna kiranta da sa'ada.
Shiru har tsawan wata uku efcc basu dawo ba kuma basu shigar da ƙara ba.
watan fatima da sa'ada biyar da haihuwa kwatsam sai ga sammaci kama uncle Ibrahim da ga court efcc sun shigar da ƙara, hankalin kowa yayi matuƙar tashi musamman uncle Ibrahim da akayi arresting, Innah sai kuka take tana ma ammy masifa uncle Ahmad na bata haƙuri akan tayi shiru , amma ina sai zagin ammy take tana cewa
" mijinta yaje yayi sata shine zata liƙama ɗan ta, wallahi duk abun da ya samu Ibrahim sai ta gane bata da wayau"
Allah sarki ammy ban da kuka babu abun da take,noraiz ma sai kuka yake ganin mahaifiyar shi na kuka shazim kuwa in ban da haɗiyar zuciya babu abun da yake, zazzaɓi ne ya rufe ammy bayan ta shiga part ɗin ta,wayar ta shazim ta ɗauka ya kira malam ya faɗa mashi abun da ke faruwa, hankalin malam yayi matuƙar ta shi sosai, ya kuma cema shazim insha Allah suna nan zuwa shi da ummy.
innah taci kuka kamar ranta zai fita ta tsine ma ammy yafi aƙira akan laifin da bana ta ba, takuma ƙara jin tsanar ta, turai ma sosai taji zafin ammy in ta tuna saboda laifin sadiq aka kama mijin ta duk da bata nuna mata a zahiri ba,kwana biyu da kama uncle Ibrahim uwani da halimatu suka zo daga kurfi su da ƴaƴan su , har suka yi kwana ɗaya da zuwa ammy bata san sun zo ba, dama halimatu ce mai zuwa wurinta to innah ta hana, sai washe gari da safe ta shigo part ɗin ammy suka gaisa, sai a sannan ammy ta san da zuwan su, daga ranar kullum sai halimatu ta shigo sun gaisa saboda tun da abun ya faru ammy ta dai na fita tana part ɗin ta koda yaushe ita da ƴaƴan ta, ta ɗan samu natsuwa saboda kullum sai malam da ummy sun kira ta sun kwantar mata da hankali sun kuma faɗa mata sunan zuwa hakan yasa ta dai na damuwa sosai taci gaba da adu'a, kullum lawyern sadiq sai ya zo har aka tsai da ranar shiga court, ana gobe za'a shiga court malam da ummy suka zo amma basu sauka a estate ɗin ba sai suka sauka a gidan da sadiq ya fara zama , can ammy taje ta same su ita da su noraiz, anan suka kwana, washe gari da zasu tafi court gida aka bar su shazim tare da mai aikin ammy, suna isa court ba'a daɗe ba alƙali ya zo aka fara gaba tar da ƙara, da lawyer ya fara gabatar da ƙara abun yayi matuƙar bama ammy mamaki dan anƙara akan abun da efcc suka faɗa time ɗin da suka zo gida, an mai da zargin kan ana zargin sadiq da reƙe hannun jarin abokanan kasuwan cin shi, sannan gomnati na zargin shi da satar maƙudan ƙuɗin da sunan aiki, an kuma kama container biyar da kayan maye da sa hannun shi, alƙali ya buƙaci ganin abokan kasuwan cin sadiq da wanda sune maƙa su dun shigar da ƙarar, abun yayi matuƙar ba ma ammy mamaki , saboda waɗan da suka shigar da ƙarar abokai ne ga sadiq na ƙut da ƙut wasu daga cikin su tun kafin ya shiga shiyasa yake tare da su, haka ƙara ta ciga ba da tafiya duk yan da lawyer sadiq ya so kare sadiq abun ya ci tura dan mutanen sun gabatar da hujuji masu matuƙar ƙarfi, ammy na ji na gani aka ɓata sunan mijinta bayan ran shi kuma aminan shi,duk wani company na sadiq sai da kotu ta amshe har da wasu gida jen shi, a taƙaice daga gidan shi dake lagos sai estate ka ɗai kotu ta bari, rayuwa tayi ma ammy zafi, taci kuka kamar ranta zai fita, sai da malam da ummy suka yi ta bata haƙuri da nasiha, malam yace ta yita yi ma mijinta da ƴaƴen ta adu'a,sun kwantar mata da hankali sun kuma nuna mata mahimmanci haƙuri da ƙaddara, hakan ya sa ta ɗanji sauki a ranta,amma abun na damun ta ba ita kaɗai ba har da malam da su uncle Ahmad dan sun san wannan duk sharrine, innah kuwa kamar ta zuba ruwa ƙasa ta sha saboda tsabar jin daɗi an saki uncle Ibrahim,kwata kwata bata damu da halin da Ammy take ciki ba, yanke shawara ammy tayi idan su malam zasu koma lagos ƙafarta ƙafarsu kuma da ƴaƴen ta zata tafi komi innah zata ce sai dai tace dan a yan da take ji har kotu tana iya kai ta idan tace zata amshi ƴaƴen daga wurin ta,ko da ta faɗa ma su uncle Ibrahim shawarar data yanke, haƙuri suka shiga bata har da halimatu amma ina, sunyi sunyi amma taƙi haƙura, har zuwa su kayi wurin malam ko zai sa baki ta zauna amma sai yace shima yana buƙatar ta a kusa da shi, ya dai yi masu alƙawarin zata riƙa ziyartar su insha Allah ita da yaran,sun so ko noraiz a bar masu amma malam yace a'a,ba yanda suka iya haka suka haƙura, tsab ammy ta haɗa duk kayan ta dana yaranta dake part ɗin su, duk wani abu da tasan tana so sai da ta ɗauka sannan ta fitar da wanda zai lalace taba ma'aikanta estate ɗin sannan ta kashe duk wani abu na wuta, har part ta samu innah tayi mata ban kwana tayi tunanin innah zata ce wani abu amma sai taga saɓanin haka, turai da asiya sun sha kuka da ammy zata tafi ,maƙalewa kairiyya tayi akan dole sai ta bi ammy, haƙuri ammy taita bata, mansoor ma sun shirya da shazim shima har da kukan shi innah har gida ta samu su malam tayi masu sallama, tun da safe suka kama hanyar lagos cike da kewar mutanan abuja.
Tunda suka koma lagos malam da ummy suke bama ammy kulawa ta musamman dan ganin ta kwantar da hankalin ta,hakan baƙaramin kwantar da hankalin ammyn yayi ba ta rungumi ƙaddarar ta, kullum cikin yima mijinta adu'a take da ƴaƴen ta, malam ya saka shazim da noraiz makarantar boko da islamiya,shazim na jss one noraiz kuma primary two, makarantar su ɗaya, su noraiz ƙarfe 12 ake tashin su amma noraiz baya komawa gida sai an tashi su shazim 2:30 pm sannan su tafi tare, da sun dawo wanka suke su ci abinci sai su wuce islamiya, malam ya tsaya tsayin daka akan rayuwar su duk wani abu na rayuwa wanda uba kema ƴaƴen shi malam na masu shi,hakama ummy babu abun da ba ta masu, uncle Ibrahim da uncle Ahmad ma suna matuƙar ƙoƙari akan su sosai su ke basu kulawa duk da basa a tare da su, kuma lokacin bayan lokacin uncle Ibrahim yana kawo masu ziyara har lagos, haka suka taso cikin soyayyar kakannin su da mahaifiyar su,
malam ya so ammy ta ƙara wani auren musamman da uncle Ibrahim ya nuna yana ra'ayin auren ta, malam ya so tayi ko da ba uncle Ibrahim ɗin ba mutane sun sha zuwa suna nu na ra'ayin aurenta amma tace a'a tafi son ta zauna tare da su malam da ƴaƴen ta, ƙyaleta malam yayi sai ma nema mata aiki da yayi, da farko ƙin amincewa tayi da aikin sai da malam ya zaunar da ita yanuna mata amfanin yin aikin sannan ta amince tafara aikin.
haka rayuwa ta cigaba da tafiya ammy na zuminci sosai da su asiya, suna waya time to time, lokacin da turai da asiya suka haihuwa har abuja taje ita da fatima bata tafi da su shazim ba saboda makaranta.
Akwana a tashi shazim harya kammala secondry school lokacin noraiz na jss one fatima kuma na nursery one, uncle Ibrahim yazo lagos ya roƙi ammy da ta bashi shazim yayi karatu a hannun shi tare da su mansoor, ƙin amincewa ammy tayi da zaman shazim a abuja saboda innah, tana tsoron zaman su tare saboda ta lura kwata kwata innah bata ƙaunar shazim, da kuma shi kan shi shazim ɗin ta san bazai taɓa raga ma innah ba tana tsoron abun da zai biyo baya, babu yan da uncle Ibrahim bai yiba amma tace a'a,ganin bazata amince bane yasa ya sanar da malam da ummy, faɗa malam yayi ma ammy dan mi zatace a'a, Ibrahim ba uba ne wurin shazim ba yana da ikwan da zai iya mai da shi wurin shi da zama bama karatu ba, ba dan ammy ta so ba ta haƙura,sosai uncle Ibrahim yaji daɗi da ta amince kafin ya tafi sai da ya amshi takardun shazim duk, ko da ya koma abuja addimission ya nema ma shazim da mansoor cikin ikwan Allah suka samu
kiran ammy uncle yayi ya sanar da ita ya kuma faɗa mata time ɗin da zasu fara lectures, malam ta samu ta sanar da shi yaji daɗi ya kuma kira uncle Ibrahim yayi mashi godiya, ya kuma ce mashi insha Allah ana saura sati biyu su fara lectures ɗin shazim zai zo,hakan ce ta faru ana saura sati biyu su fara lectures ɗin shazim ya shirya ya tafi abuja, da zai tafi noraiz harda kukan shi, ko da ya isa abuja mansoor ne yazo har airport shi da driver ɗaukar shi, farin ciki sosai mansoor ya nuna na zuwan shazim ɗin da kuma kasan cewa da zasuyi a tare,ko da suka isa estate ɗin tarba ta musamman shazim ya samu daga wurin uncle's ɗin shi da matan su, sosai suka nuna farin cikin zuwan shi har da yaran su, feenah ce dai da innah sai luqman ko a jikin su, lura da hakan da shazim yayi ne yasa ya ɗauke kan shi daga innahr yayi kamar ma bai san da zamanta a estate ɗin ba, feenah kuwa ko kallon banza bata ishe shi ba daga ita har luqman ɗin dama ba son rainin wayau yake ba kuma ita da ma yar rainin wayau ce ga rashin kunya, da zasu fara zuwa makaranta uncle Ibrahim ya sai masu motoci masu kyan gaske, sunyi farin ciki sosai, da farko shi da mansoor kowa tafiyar shi yake shi kaɗai har da haɗi da ba department ɗin su daya ba shazim na karantar medicine and surgery mansoor kuma yana karantar medicine,abokin shazim ɗaya a department mai suna A hashim,shaƙuwa ce sosai tsakanin shazim da A hashim, mansoor kuwa yana da abokai ba laifi , sai