Showing 126001 words to 129000 words out of 133697 words
Chapter 43 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt
haɗi da nufar ƙofa ya kashe mashi light ɗin ɗakin tare da jawo mashi ƙofa, cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba da shi........
_*Allah sarki babban mutum da shi amma bai san komai ba a rayuwa ya dawo kamar ƙaramin yaro komi yanzu sai an koya mashi, wannan zalunci har ina, mutane wallahi muji tsoron haɗuwar mu da ubangiji mu *_
_*NA KUSA KAMMALA SEASON ONE*_
_GA MAI SON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN DOCTOR SHAZIM_
_KHADIJA M ABDULWAHAB ( KAINAAT ) 09132289761_
_WHATSAPP KAWAI BANDA PHONE CALLS_
_Episode 64_65_
............... Abie ɗakin shi ya koma, shima alwala yayi sannan ya zo ya gabatar da safa'i da wutiri sannan ya kashe light ɗin ɗakin ya kwanta, duniyar tunani ya shiga, yanzu baya da wani buri face yaga Allah ya toni asirin mutanen nan, ya jima a kwance yana saƙawa da kwan cewa ba tare da bacci ya ɗauke shi ba, sai da dare ya raba sosai sannan bacci ya fara kama idon shi,ta shi yayi yaje ɗakin da uncle sadiq yake a bakin ƙofa ya tsaya leƙashi yayi, hango shi yayi ta hanyar hasken bedside lamp dake kunne yana ta sharar baccin shi hankalin shi kwance, mai da mashi ƙofar abie yayi ya rufe, bedroom ɗin shi ya koma kwanciya yayi dan da nan bacci yayi awan gaba da shi.....
_*WASHE GARI*_
Masallatai na fara ƙwala kiran sallar asuba abie ya farka,toilet ya nufa ya ɗauro alwala sannan ya dawo ya canza kayan dake jikin shi zuwa jallabiya, fita yayi ya nufi ɗakin da uncle sadiq yake ciki, lokacin da ya tura ƙofar hango shi yayi a zaune a bakin gado da alama ma har alawala yayi saboda danshin ruwa dake jikin shi, da sallama Abie ya shiga , ɗagowa uncle sadiq yayi yana kallon abie, yace" yawwa harka tashi kenan"
"eh" uncle sadiq ya bashi amsa
"ta so to mu tafi masallaci " abie ya faɗa haɗi da kama hanyar fita, bin bayan shi uncle sadiq yayi, a main parlor su ka samu uncle Ahmad da su Abdallah, su na sakkowa ficewa su kayi zuwa masallaci,lokacin da su ka dawo abie da uncle sadiq a parlorn abie suka zauna abie na koya mashi karatun al'qur'ani mai girma, sun jima abie na koya mashi, har sai da gari ya waye sosai tukkun su ka ajiye karatun, uncle Ahmad ne ya shigo parlorn da sallama a bakin shi, amsa mashi sallamar su kayi, wuri ya samu kusa da abie ya zauna yana faɗin " ina kwana yaya, fatan an tashi lafiya " amsa mashi abie yayi da
"Lafiya lau alhmdllh" sannan uncle Ahmad ya kallin uncle sadiq yana faɗin " ina kwana, an tashi lafiya"
"lafiya lau Alhmdllh " ya amsa shi ma kamar yanda yaji abie ya amsa, fira su ka ɗan shiga taɓawa,nocking ɗin ƙofar parlorn akayi abie ne ya ba da izinin shigowa, turo ƙofar su Aairah su kayi su ka shigo bakunan su ɗauke da sallama hannun su ɗauke da manya tray da mom ta shirya ma su abie breakfast ɗin su, amsa ma su sallamar su abie su kayi, table ɗin da ke tsakiyar parlorn su ka nufa, trays ɗin su ka sauke su ka ɗaura kan table ɗin haɗi da gaishe da su,cikin sakin fuska su ka amasa ma su musamman uncle sadiq,tsayawa su kayi sai da su kayi serving ɗin su tukun su ka nufi hanyar fita, parlorn su ka nufa wurin su mom da ke zaune kan dinning suna breakfast, dinning ɗin su ka nufa har sun ja kujeru za su zauna mom tace " yayan ku fa, kun kai mashi abinci ne "
"mom bari mu kayi sai mungama, ba su isa tashi ba yanzu " Aairah ta faɗa
Carab Ameera ta ce " ba su tashi ba fa mom" daƙƙuwa ummah tayi ma Ameerah, mom na faɗin " kunfi kowa sanin halin Abdallah kar Allah ya sa ku kai masa zai fito ne ya same ku "
"mom Allah ba isa tashi ba yanzu"
"ku dai kuka sani amma ni ba ruwana ya fito ya same ku ba ku kai ma shi abinci ba"
Ameera cewa tayi " ni dai Aairah ta so muje mu kai masa wallahi ina tsoron abun da zai biyo baya "
"sai kin dawo, gaskiya ni yunwa nake ji"
"ok haka kika ce ko "
"eh" Aairah ta faɗa yayin da ta ke kai bread a bakin ta
hanyar kitchen Ameerah ta nufa tana faɗin
"wallahi idan baki zo mun tafi ba saina cema ya Abdallah ke akace kikawo masu ki kace baki zowa "
ɗan ɗaga murya Aairah tayi tana faɗin
"idan kin fasa uwar yan jan sharri " daga kitchen Ameerah tace
"wallahi zaki san ni kike cema uwar ƴan jan sharri "
"eh ɗin in sani, ai na san dalilin da yasa kike son jaman sharri kuma ko mi zakiyi bazan ba da ba ehe " ɗaga murya Ameerah tayi yan da Aairah zata jita sosai tace
" wannan kuma ke kika sani kar Allah yasa ki ba da ƴar rainin hankali " gwalo Aairah tayi mata sai kace tana gaban ta tace
"oho dai, ban ba dawa " Ameerah na jin ta amma tayi bazan da ita,
Aaimah dai na jin su bata ce ƙala ba sai zuba ma cikin ta abinci kawai take, Ameerah ce ta fito hannun ta ɗauke da trayn da ta shirya masu breakfast, zata wuce kenan Aaimah ta dakatar da ita tana faɗin
" kawo na ɗaukar maki naga kamar kayan sun yi maki yawa, ke kuma wallahi Aairah sai kin gane baki da wayau "
" dan Allah ku rabu da ni zuwa dai ne nace bazanyi ba koma mi zaki faɗa kin daɗe"
"ai dai haka kika ce " Aaimah ta faɗa, amsa Aairah ta bata da
" sosai ma kuwa, duk abun da zaku faɗa mashi kun daɗe " ta ƙarasa maganar tana murguɗa ma Aaimah baki
"haba yarinya kamar a gabansa kika yi haka"
"dan Allah ya isa haka, ke Aairah tashi ku tafi ko gaisawa ai kunyi da safwan"
"mom zanje idan na gama " Aairah ta faɗa, kallon su Aaimah mom tayi tana faɗin " to ke wuce ku tafi ba dole sai kunyi zuga ba ke da Ameerah ma ai ya isa "
"mom ai ta je ta gaishe da ya safwan ko "
"zataje ai tace idan ta gama, maza ku wuce ku" da to su ka amsa haɗi da nufar part ɗin, suna tafe suna surutun da suka saba amma fa acewar Abdallah, suna isowa bakin part ɗin Ameerah ce tayi nocking har ta ɗaga hannu zata sake wani nocking sai gashi an buɗe ƙofar, safwan ne tsaye jikin shi sanye da ɓakar jallabiya, da fara'a a fuskar Ameerah tace
" ya safwan ina kwana, fatan an tashi lafiya " fuskar shi shima da fara'a yace " lafiya lau, ina su ummah "
"suna main parlor suna breakfast, ga naku nan kai ma mun kawo maku kai da ya Abdallah " murmushi yayi a zuciyar shi yace " Ameerah ba dai surutu ba, Aaimah ce tayi gyaran murya tana faɗin
" to ni dai a bani wuri na wuce dan na gaji da tsuyuwa" girgiza kai safwan yayi da murmushi a fuskar shi yace
" Aairah uwayen ƙorafi, zo ki wuce kar ki faɗin ƙasa " ya faɗa haɗi da matsa mata hanya, ciki ta shige tana faɗin " wai dan Allah mi yasa ya safwan kake ce man Aairah ne, ba fa ita bace wannan Aaimah ce " ta faɗa yayin da take ajiye tray ɗin kan carpet, Ameerah ma bayan ta ta bi ita ma ta ajiye wanda yake hannun ta
"to naji ina ita Aairah take na ganku ku ka ɗai, ita bata zuwa a gaisa ba"
"tana parlor wurin su mom " Aaimah ta faɗa yayin da take nufar ƙofa
"to ki kira man ita " da to Aaimah ta amsa haɗi da nufar ƙofar fita su ka fice, tana zuwa wurin su mom tace " Aairah kije ya safwan yana kira " ɗagowa Aairah tayi tana faɗin ni kuma
"A'a ba ke ba ni " Aaimah ta faɗa yayin da take jan kujera ta zauna
"dallah daga tambaya zaki wani mai da man da baƙar magana "
"an mai da maki, dallah malam idan zaki tashi kije ki tashi idan kuma bazaki tashi ba kiyi ta zama ƴar rainin wayau wai ni A'a ni " Aaimah ta faɗa tana kwai kwayon yanda Aairah tayi magana,
Aairah tace " mom kina jinta ko daga maganar ariziƙi sai ta tsiya "
dafe kai mom tayi tana faɗin
" ya Allah, ke Aaimah kar na sake jin bakin ki ke kuma Aairah tashi kije kira da yake maki "
tashi Aairah tayi tana hararar Aaimah, taɓe baki Aaimah tayi tana faɗin
" inga sun zazzago ƙasa sannan zan san kina harara"tsaki Aairah taja haɗi da wuce wa ta nufi part ɗin Abdallah, girgiza kai ka wai mom tayi ba tare da tace ma su komai ba.
Nocking tayi, izinin shiga aka bata, tura ƙofar tayi ta shiga, zaune yake kan sofa kamar yanda su Aaimah su ka barshi hannun shi ruƙe da cup ɗin tea sai turiri yake,yayin da Abdallah ke zaune kan carpet yana haɗa breakfast fitowar shi kenan daga bedroom ya samu an kawo masu breakfast, safwan ɗago da fuskar shi yayi ya zuba mata ido haɗi da amsa mata sallamar da tayi, gaishe da su tayi tana faɗin " ya safwan gani Aaimah tace wai kana kira na " amasa mata gaisuwar yayi yana faɗin
" dama ba wani abu bane kawai naga baki zo bane shine na ce su kira man ke mu gaisa tunda ke baki zo ba "
" zan zo ya safwan breakfast nake ne shiyyasa "
" ok yayi kyau, kin tashi lafiya "
" lafiya lau "
" masha Allah "
" ina iya tafiya " ta faɗa dan duk ta gaji da tsayuwa da kuma kallon da yake mata
" eh kina iya tafiya dama kiran kenan "
"to sai anjima " ta faɗa haɗi da ju yawa zata wuce Abdallah ne yace " ki dawo anjima ki kwashe wannan kayan " ya faɗa yana nuna mata kayan breakfast ɗin da ke gaban sa, da to ta amsa haɗi da kama hanyar ficewa, idanu safwan zuba mata har sai da ta ɓace ma ganin sa tukun ya janye idon sa, karb su ka haɗa ido da Abdallah, hararar shi yayi yana faɗin
" lafiya da wannan kallon malam " taɓe baki Abdallah yayi yana faɗin
" aiki ya zo ga ma iya "
" ƴan sa ido ba " safwan ya faɗa
" mi zan sa ma ido a nan, Allah ya kiyaye " Abdallah ya faɗa yana mai da kanshi kan breakfast ɗin da yake yi
"Ohon maka kuma wannan " safwan ya faɗa shima yana kai cup ɗin tea dake hannun shi baki, babu wanda ya sake cewa komai cikin su.
_*✨LAGOS✨*_
Zaune yake a office ɗin shi yana aiki, files ne gaban shi na patient yana duba wa, wayar shi ce ta fara ringing, hannu ya sa ya ɗauko ta, du ba mai kiran shi yayi, privet number shine abun da ya gani, tsaki ya ja haɗi da yin rejecting kiran ya cigaba da abun da ke gaban shi, wani kiran ne ya sake shigowa, ko kallon inda wayar take bai yi ba haka taita ruri har ta gaji tayi shiru alamar mai kiran ya gaji
sai ga message ya shigo, ɗaukar wayar yayi dan ganin wanene ya turo mashi message, baƙuwar number ce ya gani kuma da alama bata nigeria ba ce, buɗe message ɗin yayi ya fara karan tawa kamar haka
_DR ABDULƘADIR ABUBAKAR NURADDEEN,manya yan aji bakwai ba'a ɗaukar baƙuwar number ganinka kuma sai an cika form,wow i like your style keep it up na san nan gaba zai yi maka amfani, ba komai bane ya sa nake neman ka ba face ina so na sanar da kai illar dake cikin yaƙin da kake son jefa kanka aciki,manyanka ma sunyi ba suci riba bare kai ƙaramin alhaki ko da yake hausawa na cewa barewa baza tai gudu ɗan ta yayi rarrafe ba malam Abdulƙadir o afuwan dr Abdulƙadir kar kace na mai da kai malamin makaranta 😊, ya ta kwaranka kuma kakan ka mun kwana biyu ba mu gaisa ba amma da alama yanzu na lura kana so mu dawo da zumunci dake tsakanin mu , fatan yana lafiya shi da hajiya zainab ina nufin ummy????,
Abdulƙadir ina mai baka shawara idan har kana son zamanka lafiya a duniyar nan to ka tsame hannuka daga abun da kake shirin aikatawa gudun aikata abun da zai jefa ka cikin matsala kai da iyalanka, fatan zaka ɗauki shawarata duk da na san kai mai taurin kai ne amma ina mai baka shawara._
Wani wawan tsaki shazim ya ja lokacin da ya kawo ƙarshen message ɗin yana faɗin " aikin banza matsora cin banza da wofi kawai, mu zuba mu gani ni da kai da duk wani mai hali irinka shege ka fasa " ya faɗa yana
maida kanshi yayi kan abun da yake, wani tsakin ya sake ja yana sake faɗin " aikin banza matsoracin banza da wofi kawai "
Ƙofar office ɗin yaji an turo an shigo, majeed ne ya shigo a uzirce kamar wanda aka jeho, wurin shazim ɗin ya matsa yana faɗin " amshi shazim ka gani " ya faɗa yana miƙa ma shazim wayar shi, amsar wayar shazim yayi yana duba abun da majeed ɗin ke nuna mashi, text message ne shima aka turo mashi da irin number da aka turo ma shazim yanzu, karanta message ɗin shazim ya shiga yi
_ABDULMAJEED MA'ARUF WAKILI,na san za kayi mamakin wanene ni da kuma sunan ka da na ambata, kar kayi mamaki yanyi ne yasa haka.
a taƙaice dai abun da ke tafe da ni, ba wani abu bane face ina so na ja maka kunne kai da abokinka, ku rufa ma kanku asiri ku fitar da kanku acikin yaƙin da iyayen ku su ka kasa,idan kuma ba haka ba zaku sa kan ku cikin bala'in da ba kuyi tsammani ba ku da iyalanku, shawara ce idan kun ɗauka ku zata yima amfani idan kuma kun ƙi to duk abun da ya biyo baya kuyi kuka da kanku._
Tsaki shazim yaja yana miƙa ma majeed wayar shi, amsa majeed yayi yana faɗin
" ni dai shazim a ganina mu fitar da kan mu a wannan matsalar ko dan su Ammy "
" tsoro kaji ne wai majeed?"
" dole naji tsoro shazim, barazana fa yake mana, ni abun da nake ganin zai fi shi ne kawai kayan nan mu miƙa ma hukuma su "
" to dan yana mana barazana sai mi, ya isa yayi mana abun da Allah bai nufa ba ne, sannan kaya da kake cewa mu miƙa ma hukuma su tamkar munji tsoron ne kuma Allah zai kama mu da laifi duk wanda ya cutu a kan kayan "
" bai isa ba shazim,kuma Allah bazai kama mu da lafin wani ba tunda hukuma muka ba kayan kuma muna kyautata zaton tayi adalci ne"
"majeed ina so ka fahimci wani abu a lamarin ƙasar nan cin hanci yayi yawa muna ba da kayan nan zai ba da cin hanci ne a bashi batare da tausayin bayain Allah ba da aka ɓata ma rayuwa ba, yau da ace ƴaƴansu zasu ba da bazan da mu amma inaji ina gani bazan bari a cuci al'ummah ba "
"haka ne shazim, amma duk da haka mu miƙama hukuma ko dan su Ammy dan gaskiya ina jin tsoron abun da zai biyo baya idan muka cigaba da riƙe waɗannan kayan "
" to idan kana jin tsoro ka kira shi kace kai ba ruwanka, Amma ni ba gudu ba ja da baya " shazim ya faɗa haɗi da miƙewa ya nufi wata ƙofa dake kallon in da yake zaune, tashi majeed yayi yana faɗin " miyasa zaka ce haka shazim, ko da naji tsoro ai bazan iya tsame hannu na ba na barka "
Shigewa ciki yayi ba tare da yace mashi komai ba, bin bayan shi majeed ɗin yayi, tura ƙofar ɗakin yayi ya shiga, ma daidai ci ɗaki ne mai kayan gaske harda ɗan madaidaici family bed a cikin sa da sofa masu kyau guda, tsaye ya hango shazim bakin wani ɗan ƙaramin fridge ya na ɗauko robar ruwa, sofa dake ɗakin ya nufa haɗi da samun wuri ya zauna, shima zama majeed yayi yana faɗin " Please shazim ina so ka fahimce ni ne, bana so mujefa wani daga cikin ahalin mu acikin matsala ne shiyyasa na ce haka" ajiye robar ruwan shazim yayi yana faɗin " majeed akwai wani ɗan adam daya isa yayi ma bawa abun da Allah bai ƙaddara ba "
"A'a shazim "
"to inaso ka fitar da wannan tsoron a ranka ka fuskanci gaskiya, duk wani barazana da zai yi mana yana yi ne dan muji tsoro "
"to shikenan, yanzu ya zamuyi "
"karka damu zanyi shawara komai na yanke zan sanar da kai "
"to shikenan bari na koma office na barshi ba kowa "
"to shikenan, ka ja man ƙofar idan ka fita" shazim ya faɗa, tashi majeed yayi ta fita haɗi da rufe mashi ƙofar kamar yan da yace.
Zamewa yayi ya kwanta kan sofar, idanuwan shi ya rufe kamar mai bacci.
Duk yinin ranar a wannan ɗakin yayi shi ko sallah a nan yayi ta, sai da yamma bayan sallar asr ya tashi ya koma cikin office ɗin kayan da ke kan table ɗinshi ya tattara ya zuba cikin locker sannan ya ɗauki briefcase ɗin shi da wayar shi ya fice zuwa parking lot in da ya ajiye motar shi, briefcase ɗin ya fara ajiye wa sannan ya zagaya ma zaunin driver ya zauna, key yayi motar haɗi da reverse ya nufi gate, da katar da shi mai gadi yayi ta hanyar ɗaga mashi hannu, parking yayi a bakin gate ɗin yana ce ma