Showing 48001 words to 51000 words out of 133697 words
Chapter 17 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt
"
"ok sai ka dawo" shazim ya faɗa haɗi da miƙewa ya nufi bedroom ɗinshi, toilet ya shiga bayan 5 minute sai gashi ya fito sanye da bath robe, dressing mirror ya nufa mai ya shafa ma jikin sannan ya fesa turare bakin bed ɗin shi ya dawo haɗi da ɗaukar wayar shi yayi dialing number ammy, tana fara ringing tayi picking, sallama yayi sannan ya gaishe da ita, on the other hand ta amsa mashi cikin kulawa haɗi da tambayar shi ya su innah da su uncle ahmad, amsa ya bata da suna nan lafiya lau, sannan ta tambaye shi sun faɗa mashi dalilin kiran shi da sukayi
amsa ya bata da "a'a basu yi faɗa man ba"
"to shikenan, ina auta da me babban suna? "
"auta na part ɗin uncle Ibrahim wurin sa'ada, mai babban suna kuma na part ɗin uncle ahmad wurin mahmud, ni ka ɗai suka bari "
"a'a kaima laifin ka ne, ai da sai ka sauka wurin mansoor "
"a'a nafi jin daɗin zama ni ka ɗai ne "
"to ai kaika sani " sun ɗanjima suna waya sannan sukayi sallama, malam ya kira suka gaisa har da ummy, shima malam sun ɗan jima suna tattaunawa sannan shima sukayi sallama, kwanciya yayi kan bed ɗin cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba dashi, hara sai da mansoor ya zo sannan ya tashe shi suka wuce masallaci saboda anfara kiran sallar magrib, sai da suka tsaya akayi har isha sannan suka fito, daga masallaci part ɗin uncle Ibrahim suka shiga, a part ɗinshi suka same shi, bayan sun gaisa ne yake tambayar sunyi maga da uncle ahmad, amsa shazim ya bashi da a'a
"amma mi yasa muke kiran ka ba mu samun ka?? " ɗan sunnar da kai yayi dan bai taɓa tunanin uncle Ibrahim zai mashi magana akan haka ba duk da yasan dole zasu tambaye shi, jin yayi shiru ne yasa uncle Ibrahim cewa "magana nake kayi shiru baka ce komi ba " amsa ya bashi da "bakomi kawai yana yin aiki ne" ɗan jin jina kai uncle Ibrahim yayi duk da ya san yana sane yasa ba'a samun shi a waya, amma a fili sai ya ce "to shikenan Allah ya kyauta gaba" da ameen suka amsa, chanza firar uncle Ibrahim yayi zuwa wata, sun ɗan jima awurin shi dan anan sukayi dinner tare da shi, sai wurin shaɗaya saura suka baro part ɗin,ra buwa suka yi da mansoor kowa ya nufi part ɗin su, shazim ko daya shiga part ɗin su bedroom ɗinshi ya nufa, laptop ɗinshi ya ciro daga cikin bag ɗin shi ya shiga aiki, ba shi bane ya kwanta ba sai ɗaya saura sannan ya kashe laptop ɗin ya nufi toilet ya ɗauro alwala, ya dawo ya kabbara sallah, ya jima yana nafilfilo sannan ya tashi ya nufi bed ɗin shi bayan ya kashe bulbs ɗin ɗakin, kwanta yayi haɗi da jan blanket ya rufe jikin shi, bai jima da kwanciya ba bacci yayi awan gaba dashi....
Episode 24_25
WASHE GARI
tun da safe suka fita shi da mansoor, sai da yamma liƙis suka dawo a gajiye, shazim part ɗin su ya nufa, wanka yayi ya ɗan kwanta, duk da ya san bacci a lokacin bai da amfani, amma haka nan ya kwanta saboda ba ƙarmar gajiya ya kwaso ba, cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba dashi, ba shine ya tashi ba sai gab da magrib, toilet ya shiga ya sake wani wankan da alwala, sannan ya shirya cikin wani farin yadi, ficewa yayi zuwa part ɗin uncle ahmad wurin mansoor, a parlor ya ci karo da mansoor, juyawa yayi suka wuce masallaci, sai da suka yi har sallar isha tukun suka fito daga masallacin, part ɗin uncle Ibrahim suka nufa, aliyu ka ɗai suka samu a parlor yana kallon cartoon, ya na jin sallamar su ya nufi shazim da gudu, ɗaukar shi shazim yayi yana faɗin "sai kai ka ɗai ina su momy "
"tana part ɗin dady "sauke shi shazim yayi yana faɗin "to yayi, tafi ka cigaba da kallon ka " to aliyu yace haɗi da komawa kan sofa ya zauna yan cigaba da kallon shi, mansoor yace"aliyu shazim ka ɗai ka sani ko"
"a'a, ai kai kullum muna tare " murmushi kawai mansoor yayi, haɗi da cewa "ok haka ne, ai shazim ɗin zai tafi zai barni da kai, babu ruwana da kai daga yanzu"
"sorry ya mansoor, wasa fa nake "
"ba wani nan"shazim yace "ƙyale shi kaji, idan zan tafi da kai zan tafi ai, kana zuwa lagos koh" ɗaga mashi kai aliyu yayi yana dariya, mansoor yace "zamu gani ai "aliyu sai tsalle yake zai bi shazim lagos.
sama suka wuce zuwa parlorn uncle Ibrahim, zaune yake shi da momy da alama suna tattaunawa ne, sallama suka yi haɗi da shiga ciki, amsa masu sallamar su kayi, wuri suka samu kan sofa suka zauna,gaishe da uncle Ibrahim da momy su kayi, amsa masu gaisuwar su kayi uncle Ibrahim na tambayar su ya aiki, da Alhmdllh suka amsa, ta shi momy tayi ta fice,fira suke jefi jefi, luqman ya shigo kamar wan da aka jeho yana faɗin dady! dady!! ,binshi suka yi da idanu, mansoor ne yace "lafiya kake luqman zaka shigo wuri ba sallama kamar wanda aka jeho"
"kullum faɗa nake masa saboda ɗabi'ar banza da ta wofi,ko kafiri bai shiga wuri ba sallama bare kai ɗan muslimi, kiran mi kake man haka?" duƙar da kan shi yayi ƙasa yana faɗin "ba komi" bai son yin maganar saboda su shazim daya gani,mansoor da shazim sun fahimci bai son yin maganar ne saboda ya gan su, fahimtar hakan ne yasa uncle Ibrahim cewa "fice to ka bani wuri" ba musu ya kama hanya ya fice,tsaki uncle Ibrahim yaja yana faɗin "lamarin luqman sai adu'a"
mansoor ya ce
"narasa mike damun shi uncle, tun da suka fita karatu waje ɗabi'un shi suka canza"
"hakane, Allah ya shirya"da ameen mansoor ya amsa, shazim dai na jinsu amma baice komi ba, sai da uncle Ibrahim yace" shazim kayi shiru kamar baka a wurin"
"uncle wai ni "
"a kwai wani shazim ɗin ne anan bayan kai "murmushi kawai yayi ba tare da yace komi ba, uncle Ibrahim yana lure da shazim duk wani abu idan ya shafi luqman da feenah to fah ba ruwanshi , ko kau mizai same su .
mansoor ya ce
"uncle bari mu wuce sai da safe, shazim tashi mu tafi" tashi shazim yayi yana cema uncle Ibrahim "sai da safe uncle "
"Allah ya tashe mu lafiya"da ameen suka amsa, haɗi da ficewa suka bar part ɗin, tashi uncle Ibrahim yayi ya fita daga parlorn shima,bedroom ɗin luqman ya nufa, tura ƙofar yayi ya shiga, samun shi yayi yana safa da marwa, sai kai kawo yake cikin ɗaki, a hanzarce ya juyo jin an buɗe kofa , ganin mahaifin shi ne yasa ya nufe shi da sauri yana faɗin "dady daman wannan cp dake bincike ne ya kira ni yace sun samu idan suke sai dai basu da tabbaci, amma suna nan suna bincike da sun tabbatar zasu kira ni, ya kira wayarka baka yi picking ba shi ne ya kirani, shi ne nazo faɗa maka ban san wannan ɗan rainin wayau yana nan ba shi da ya mansoor "
uncle Ibrahim yace "ok,wayar tana bedroom ɗina ne ban san ya kira ba, naji daɗin jin haka"
"dady yanzu zaka mai do man da motata da ka amsa ko"
"cewa nayi sai sun bayyana sannan"
"pls dady "
"kama bar bani haƙuri, dan ba baka zanyi ba har sai na gansu ido da ido tukunnan, kaga daga yau idan na saka ka abu ba zaka sake shashanci ba"
"dan Allah dady ka bani, insha Allah hakan ba zata sake faruwa "
uncle Ibrahim yace
"ni kaga tafiya ta , daga yau sai ka kiyaye " yana gama faɗa ya fice daga ɗaki.
Suna fita daga part ɗin uncle Ibrahim, part ɗin su shazim suka nufa, a parlor suka ya da zango, wayar mansoor dake cikin aljihun wandon shi ce ta fara ringing,ciro ta yayi yana kallon screen ɗin wayar baby shine sunan mai kiran shi , murmushi yayi haɗi da picking yana faɗin "sorry beb, yanzu nake shirin kiran ki" muryar mace ce tace "bawani nan, da ban kiraka yanzu ba da ba zaka kirani ba "
"haba dear ya zaki ce haka, kin san da ace na gama abun da nake da zan kira ki"
"uhmm dama haka zaka ce "
"haba dear, pls kiyi haƙuri "
tsaki shazim yaja yana faɗin"rainin wayau" hararar shi mansoor yayi yana nuna shi da ɗan yatsa, taɓe baki yayi haɗi da cewa "rainin wayau mana, ka zauna ƙaramar yarinya ta maida ka kamar wani wawa" harara kawai mansoor ya maka mashi ba tare da ya ce komi ba ya cigaba da wayar shi.
hannu yasa ya riƙe kunnan shi yana faɗin "afuwan na kama, bazan sake ba pls " ta shi shazim yayi ya fize wayar daga kunnan mansoor yayi rejecting,da kallon mansoor ya bi shi , rasa mi ma zai ce mashi yayi, gaba ɗaya ya kashe shi da mamaki sai kace shi akace ya kama kunne, komawa yayi mazaunin shi ya zauna yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya sai wani cin magani yake, matsowa kusa da shi mansoor yayi yana faɗin "ɗan rainin wayau bani wayata"
"wallahi bazan ba da ba"
"saboda wayar ka ce?"
"ko ba tau bace bazan ba da ba, tunda kai zubar ma kan ka aji ba komi bane a wurin ka ba"
"dallah ka bani wayata, ina ruwanka koma mi zanyi"
"wallahi kaji kunya, wai yarinya zata saka ka kama kunne, kamar wani teddyn wasan ta "
"ko ƴar tsana ta ɗauke ni ina ruwanka tunda ba kai ta ɗauka ba"
"Allah ma ya kiyaye, wane ita sai dai irinku da kuka raina kanku"
"wallahi ina tausayin ka shazim, duk randa so yayi maka mugun kamu, zaka gane baka da wayau"
"haba dai, ko zanyi so ba irin naka ba na rainin wayau "
"indai da rai zamu gani, zaka zo nan ne ka same kana kuka saboda mace"
"Allah ma ya kiyaye, nafi ƙarfin mace tasa na zubar da hawaye, sai dai kai, dan da alama har kuka kake mata"
"uhmmm shazim kenan, idan da rai da lafiya zamu gani ai"
"ba abun da zaka gani sai alkairi, dan Allah muma bar wannan zancen"
"za'a yi shine wata rana "
"naji koma yaushe za'ayi shi" kai kawai mansoor ya girgiza yana murmushi ba tare da yace komi ba, sun ɗan jima suna fira daga bisani mansoor yayi mashi sallam ya fice.
tashi shima yayi ya nufi bedroom ɗin sa, toilet ya shiga ya ɗauro alwala
yayi shafa'i da wutiri yana gamawa ya nufi bed ɗin sa bayan ya kashe bulbs ɗin ɗakin hada bedside lamp, wayar shi da ya ajiye kan bedside drawer ce ta fara ringing , hannu yasa ya jawo wayar yana duba mai kiran shi unknown number ce, tsaki yaja haɗi da rejecting,yana rejecting wani kiran ya sake shigowa "wai waye wannan zai ta kura man ne "ya faɗa haɗi da sake rejecting kiran, sai ga message ya shigo buɗe message ɗin yayi yana karanta wa, yana kammala karantawa , tsaki ya sake ja, kashe wayar yayi baki ɗaya, blanket yaja ya rufe jikinshi baki ɗaya har kai
washe gari weekend
Momy ce da su sa'ada a kitchen suna haɗa breakfast feenah ta shigo jikinta sanye da pajamas masu santsi white color, sun bi shape ɗin jinkata kanta sanye da black ɗin hula, hugging ɗin momy tayi ta baya "inakwan momy "
"lafiya lau, kin tashi kenan? "
fatima tace
"ina kwna aunty feenah "
banza tayi da fatima har sai da momy tace baki ji ana gaishe da ke ne
"naji "
"ok amsawar ce baki iyawa "
kallon fatima feenah tayi tana faɗin
"lafiya " tsaki momy ta ja haɗi da mai da kanta kan abun da take, fatima ma nunawa tayi ko ajikinta abun da feenah tayi mata, abu yayi matuƙar ɓata ran sa'ada kasa daurewa tayi har sai da tace "gaskiya aunty feenah abun da kike baki kyautawa "
"ni kike gaya ma haka"
momy tace "ai gskiya ta faɗi" jan hannun fatima sa'ada tayi sai hura hanci take tace " zu mu fita parlor "
"a'a bari mugama aikin "
"kizo kawai mu tafi " da hararar feenah ta raka sa'ada "zan kamaki ne yarin ya, zaki san wa kike hura ma hanci"
kallon momy tayi tana faɗin
"mi kike dafawa ne momy?"
"to acici bansani ba "
"momy dan Allah ki dai na ceman acici"
"bazan dai na ba " bubbuga ƙafa ta shiga yi cike da shagwaɓa, luqman shigowar shi kenan kitchen ɗi yaga feenah na momy shagwaɓa , daga shi sai boxer black color, mangare mata kai yayi yan faɗin"sakaryara banza ji kayan dake jikin ki, ko kunya ba kiji, ko aliyu bazai yi abun da kike ba "
"ina ruwan ka dani da zaka dake ni mugu kawai, kai bakaga kayan dake jikin ka ba sai ni azzalumi "
"ke dan ubanki ni kike faɗama haka"
"eh an faɗa maka "
duka yazo kai mata da gudu ta ɓoye bayan momy, ture ta momy tayi tana faɗin" matsa ki bani wuri mara kunyar banza, kai kuma fice ka bani wuri "
"haba momy yaza kice haka, rashin kunya take man fa kuma ji kayan dake jikinta "
"fice nace ka bani wuri kai bakaga kayan dake jikin na ka bane, ko kunya baka ji da ƙannan ka kake irin wannan shigar kana yawo cikin gida" gwalo feenah tayi mashi
"wallahi zan kama ki ne "yana faɗa ya wuce kamar zai tashi sama, kallon feenah momy tayi tana faɗin "kema wuce kije ki canza waɗannan kayan tun kafin ranki ya yi mummunan ɓaci"
"haba momy, miye aibun wannan kayan dan Allah "
"ki fice nace "
"dan Allah momy kiyi haƙuri "banza momy tayi da ita, kama ma momy tayi suka kammala breakfast ɗin,mai aikin momy ce ta shigo ta kwashe flaks ta kai dinning, dawo wa tayi tana faɗin"momy ina na yallabai shazim yake "
"gashinan " momy ta faɗa haɗi da miƙama mai aikin, charab feenah ta amshe flaks ɗin daga hannun momy tana faɗin "jeki kawai zan kai masa"
"A'a hajiya da kin kawo na kai masa"
"nace kije zan kai masa"da to mai aikin ta amsa haɗi da ficewa ta bar kitchen ɗin, fita itama feenah tayi tana faɗin "momy bari na kai masa na dawo" bata jira mi momy zatace ba kawai ta fice.
kwance yake a bedroom ɗin sa , cikin bacci yaji ana nocking ƙofar bedroom ɗin sa, farkawa yayi batare da ya motsa ba ya dai buɗe idon shi, sake nocking ɗin kofar aka yi, ta shi yayi ya nufi ƙofar ya buɗe, feenah ce tsaye , kallon sama da ƙasa ya sahiga binta da shi, ganin kallon da yake mata ne ya sata duƙar da kai "inakwan ya shazim "bai amsa mata gaisuwar ba sai cewa yayi"mi ya kawo ki part ɗi na?"
"yaya dama momyce tace na kawo maka breakfast " juyawa yayi yana faɗin
"ok kina iya ajiyewa kan dinning "
"haba ya shazim, dan Allah wai mi nayi maka a rayuwa ne kake wulaƙan ta ni, ko gaisuwa ta baka amsawa"
shigewa yayi cikin bedroom ɗin batare da ya bata amsa tambayar da tayi mashi ba, kamar ta fashe da kuka saboda tsabar baƙinci, tarasa mi tayi ma shazim ya tsane ta a duniyar nan kwata kwata baya ƙaunar ta ya tsane ta, parlor ta koma kan dinning ta ajiye mashi haɗi da ficewa tana sharar ƙwalla, tana shiga part ɗin su ɗakinta ta nufa, kan bed ta faɗa, sai a lokacin ta fashe da kuka.
wanka yayi sannan ya fice ba tare da ya zuwa part ɗin uncle ahmad,sai da ya gaishe da mama sannan ya wuce sama wurin uncle ahmad,gaisawa suka gaisa ya nufi bedroom ɗin mansoor,tura ƙofar yayi bakin shi ɗauke da sallama, zaune yake yana aiki cikin laptop , ɗago da kan shi yana kallon shi "ai nayi tunanin sai na zo tuk zaka tashi? "
"ai da kazo ɗin "
"kunyi waya da a hashim kuwa? "girgiza mashi kai shazim yayi alamar a'a "ya kirani ɗazu yake ce man ya kira ka bai samu ba"
"na kashe wayata ne da zanyi bacci may be ya kira ya ji akashe"
"to ba mamki, sai ka kira shi"
ok kawai yace, wayar shi ya jawo yayi dialing number kairiyya, tana picking yace "ki kawo man breakfast part ɗin mansoor "yana gama faɗa yayi rejecting ba tare da ya tsaya yaji mi kairiyya zata ce ba, kallon shi mansoor yayi yana faɗin "ɗazu fa da su fatima suka shigo mama tace su zo su kaimaka breakfast suka ce sun baro feenah zata kai maka, bata kai maka ba? "
"ta kai"
"to mi yasa ba ka ci ba?"
"saboda bana jin yunwa lokacin "
"ba ka jin yunwa ko ko dai bazaka ci ba saboda ita ta kawo, wai mi yasa kake haka ne shazim "
"dan Allah ka rabu dani, bana ji yunwa ne lokacin, yanzu kuma ina ji shine kawai"
girgiza kai kawai mansoor yayi ba tare da yace komi ba ya mai da kan shi kan aikin da yake, nocking ɗin kofar aka yi, ba da izinin shiga mansoor yayi, kairiyya ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama hannun ta riƙe da tray, amsa mata sallama suka yi, ƙasa ta ajiye tray ta jawo center table ta ajiye gaban shazim tana faɗin "ina kwana ya shazim " da lafiya lau ya amsa mata, tray ta ɗaura kan table ɗin tayi serving ɗin shi,thanks yace haɗi da ɗaukar spoon ya fara cin abincin, ficewa tayi daga ɗakin, a hankali yake cin soyayen arish kamar baya son ci,sai da yaja time kafin ya kammala, wayar shi dake gefan shi ce ta fara ringing, ɗaukar wayar yayi yana duba mai kiran, ammy ce, picking yayi haɗi da sallama yace,om the other hand ammy ta amsa mashi sallamar tana faɗin "mutanen abuja "
shafa sumar kanshi yayi yana faɗin "ina kwana ammy"
"lafiya lau, ya uncles ɗinka da innah "
"suna nan lafiya "
"ina gaishe da su, ina auta ta na kira wayar ta bata ɗauka ba "
"yanzu haka ta jefata wani wuri "
"to idan ka ganta kace ta kirani"da to ya amsa yana faɗin "ammy ga mansoor zaku gaisa "ya faɗa haɗi da