Showing 84001 words to 87000 words out of 133697 words
Chapter 29 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt
bar ka ba daga kai har uwar taka, mara mutunci kawai" masifa iri iri sai da innah ta sauke ma shazim, zagi kuwa ba wanda innah bata sauke ma shazim ba duk masifar da take mashi ko kallon in da take bai yi ba,takardun dake hannun shi kawai yake aikin dubawa, gwaggo halima ce ta shigo tana bama innahr haƙuri amma ina masifa ta rufe ma innah ido har su dady sai da suka sa baki amma taƙiyin shiru, shazim yana gama karanta takar dar gawajin , sallama yayi ma ummah da godiya, ba tare da yace ma kowa ƙala ba ya tashi ya nufi bedroom ɗin sa inda ya kwantar da fatima,sai magana su mansoor suke mashi akan ya faɗa masu sakamakon amma yayi banza da su ya nufi ɗakin shi , ummah su ka tambaya ce masu tayi itama bata karanta ba, shikenan kawai su kace, rakata parking lot mansoor da Abdallah su kayi, sai da ta tafi sannan au ka dawo parlorn,
Kamar dai yanda take jiya yauma haka take kwance,goshinta da bandage jikinta duk a bushe yake,
sa'ada na nan zaune kusa da ita ta zuba uban tagumi, ɗagowa tayi jin shigowar mutum da kallo ta bi shazim daya shigo,ce mata yayi taje bedroom ɗin fatima ta ɗauko mashi trollyn ta, da to ta amsa mashi haɗi da ficewa ta nufi ɗakin fatima, noraiz ne ya taso ya nufe ta yana faɗin" ya akayi naga kin fito "
"kaya yace na ɗauko ma fatima da trollyn ta "
Ok kawai noraiz yace haɗi da nufar bedroom ɗin shazim ɗin samun shi yayi a bakin wardrobe ɗin shi, sallama noraiz yayi mashi haɗi da faɗin " yaya minene sakamakon, hankalin kowa a tsahe yake kai kawai su ke jira ka faɗa masu sakamakon ka kuma taso ka shigo ɗaki.... "
"dakata man dan Allah noraiz, ka wuce ka fita yanzu zamu wuce "
"amma yay.... "
"bana son jin komai daga gare ka, kayi abun da nace kawai " da to kawai noraiz ya amsa haɗi da nufar bedroom ɗin shi laptop ɗin shi ya ɗauka haɗi da kashe duk wani abu wuta a ɗakin sannan ya fito dama trollys ɗin su suna cikin mota tun jiya
bedroom ɗin shazim sa'ada ta koma da trollyn fatima da ta ɗauko, lokacin da ta shiga shazim harya canza kayan jikin shi zuwa baƙar t_shirt da cargo trouser shima baƙi da p_cap sak shigar da yayice jiya sai dai ba kayan bane wasu ne yasa irin su, a tsakiyar ɗakin ta tsaya da trollyn
"boɗe ki ciro mata doguwar riga mara nauyi " shazim ya faɗa, da to sa'ada ta amasa haɗi da ɗora trollyn bakin gadon, buɗe shi tayi doguwar rigar abaya mara ɗauyi ta ɗauko mata ajiye ta tayi gefe ta rufe trollyn , kallon shi tayi tana faɗin "yaya gashi "
"ok,kina iya samata?"
"eh " ta bashi amsa, jinjina kai yayi haɗi da jan trollyn fatimar ya fice.
da ya fito wata takarda ya ciro daga cikin aljihun trouser ɗin shi ya miƙama mansoor, amsa mansoor yayi yana faɗin " thank you,zan same ku kuwa kafin na dawo " ɗaga mashi kai shazim yayi, hugging ɗin shi mansoor yayi " shikenan sai na dawo bro " ok shazim yace, a tare su ka fita shi ya sa trollyn fatima a booth mansoor kuma ya shiga motar shi ya fice daga estate ɗin.
Mansoor na ficewa AMBULANCE ɗin asibitin su ummah na shigowa, ita ta turo da ambulance ɗin dan su samu sauƙin zuwa airport da fatima,tsayawa shazim yayi har sai da tayi parking sannan ya gaisa da drivern ambulance ɗin sannan ya shiga ciki yana faɗi inazuwa da to drivern ya amsa, ha zai shiga ciki wayar shi dake aljihu tafa ringing, tsayawa yayi yana amsa kiran
✨SA'ADA ✨
Rigar ta shiga kiciniyar sanya ma fatima, tasha wahala kafin ta sama ta rigar saboda jikinta duk a sake yake kamar wacce ta mutu babu inda ke motsi a jikinta,bayan ta sa mata rigar ne ta nufi dressing mirror ɗin shazim main shafawa ta ɗauko ta ɗan shafa mata a hannuwan ta da ƙafafuwan ta saboda jikin ta duk ya bushe tana gama shafa mata ta fice zuwa waje lokacin da ta fita Abdallah da noraiz ka ɗai ta samu su Abba duk sun fita, fita tayi itama zuwa parking lot inda anan ta samu shazim tsaye yana waya jira tayi har ya gama wayar sannan tace " ya shazim idan tafiya za kuyi, dan Allah ka tafi da ni "
" ki bari idan mansoor zai zo sai kuzo tare "
"dan Allah ya shazim, wallahi hankalina bazai kwanta ba,dan Allah ya shazim " kai kawai ya ɗaga mata alamar to shikenan
"nagode sosai ya shazim ta faɗa " haɗi da nufar part ɗin su da sauri, zazzaune ta samu su Abba da su gwaggo halima harda innah,sallama kawai tayi masu bata jira sun amsa ba ta nufi ɗakin ta da sauri, shaf shaf ta canza kaya ita ma doguwar riga ta sa, gyalen ta kawai ta ya fa sai side bag ɗinta da wayar ta da ta ɗauka, da sauri ta fice kowa dake parlorn da idanu ya bita, gwaggo uwani ce tace " ke kuma ina zaki "
"lagos zan bi su ya shazim"
kawai tace haɗi da juyawa ta fice,da sauri feenah ta tashi jin wai shazim zai tafi, gwaggo Uwani ce ta jawo tana faɗin "dawo nan " dawowa tayi ta zauna sai turo baki take, innah tace " amma wannan ɗiya anyi ƴar banza, kenan waɗannan marasa mutuncin zata bi " Abba ne yace " ai ba komi innah dan ta bi su, nasan tana son zama da ƴar uwarta ne har ta samu sauƙi "
"amma kuma bata ga abun da yayan yarinyar yayi ma yayan ta ba da zata wani bisu kamar wasu ƙannan uwar ta "
"kiyi haƙuri innah,shima luqman ɗin yana da laifi "
"dama nasan bayan shi zaku bi"
gwaggo Uwani ce tace
" bansan mi yake nufi ba tafiya zai yi ba tare da yasa an saki luqman ɗin ba komi "
"ke bari kiga naje na samu wannan mara mutuncin "
innah ta faɗa haɗi da miƙewa ta fice bayan ta su gwaggo Uwani suka bi har da su Abba, tana fita shazim na fitowa ɗauke da fatima a kafaɗar shi kamar wata gawa, noraiz da Abdallah na bayan shi sai sa'ada data fito hannun ta ɗauke da jakarta da jakar laptop ɗin fatima,drivern Ambulance ɗinne ya buɗe mashi ƙofa ya saka fatima, zama yayi kan wata ƴar chair dake cikin ambulance ɗin,ledar magungunan fatima ya amsa a hannun sa'ada haɗi da maida ƙofar ya rufe,wani drip ɗin ya sake sama fatima sai da ya komai na tafiya yan da yaso sannan ya fito, motar mansoor ce ta shigo estate ɗin, gaba ɗaya hankalin su kan motar ya koma har yazo parking lot yayi parking buɗe motar yayi ya fito nufo su yayi luqman ne ya fito jikin shi duk a sanyaye har ya ɗan faɗa dare ɗaya kawai, da sauri innah ta tare shi yana ganin ta shima da sauri yayi hugging ɗinta hawaye na bin idanuwan shi , su dady ma nufo su su kayi binsu yayi tayi ɗaya bayan ɗaya yana hugging ɗin sai kuka yake, dady ne yayi hugging ɗin shi yana lallashin shi,sa'ada ƙin zuwa tayi wurin luqman haushin shi take ji, mansoor ne ya ƙaraso wurin su shazim, hugging ɗin shazim yayi "tnxs bro " ɗago da shi shazim yayi yana faɗin " godiyar ta isa haka, yaushe zaka zo "
"Insha Allah next week zan zo "
"to Allah ya kaimu " da ameen mansoor ya amsa, raba jikin su su kayi,
"ku kuzo mu wuce " shazim ya faɗa haɗi da nufar Ambulance ɗin da fatima ke ciki zai shiga, gwaggo halima ce ta ƙaraso kusa da shi " shazim baza ka bari ko breakfast kuyi ba sannan ku tafi "
"ba komai Aunty, idan mun isa cana za muyi "
"shikenan, Allah ya kai ku lafiya, ina gaishe da Ammyn ku sai nazo "
"zataji insha Allah, sai kinzo "
"to shikenan " ta faɗa haɗi da ko mawa wurin su innah,mama Allah ya sauke su lafiya tayi masu,dady ma da Abba sai da suka yi masu Allah ya kiyaye haɗi da adu'ar Allah ya ba fatima lafiya, ƙin amsa masu shazim yayi dan duk haushin su yake ji musamman dady kowa sai da yayi masu Allah tsare ban da mutum uku innah, gwaggo Uwani,sai momy dake part ɗin ta bata fito ba dan bama ta san luqman ya dawo ba, sai luqman ɗin dake tsoron yazo wurin saboda shazim, amma yaso ya ga ya jikin fatima yake,mota su ka shi ga, shazim na cikin ambulance da fatima sai mansoor da noraiz Abdallah da sa'ada a motar mansoor , kairiyya taso ta bi su amma Abba yace ta bari sai zasu je sai su tafi tare, feenah taci kuka kamar ranta zai fita haukace masu tayi ita a dole sai tabi shazim tun ana lallashin ta kan ta bari sai su dady zasu har ta kai ga ba mutane haushi dady ya wanke mata fuska da mari, Allah ya ƙara kowa ke mata. Luqman ya so ya raka su airport amma dady yace a'a.
Suna nan tsaye har motocin su suka bar estate ɗin, sai da suka ga fitar su sannan kowa ya koma part ɗin shi
Suna zuwa airport ba daɗewa lokacin tashin su yayi,har filin in da jirgi yake Ambulance ɗin ta shiga , shazim ne ya turo ɗan gadon da take kwance, da sauri mansoor da Abdallah suka fito daga cikin mota suka shigar da ita cikin jirgin.
. Allah sarki fatima ta zo da ƙafar ta cikin ɗoki da nisha ɗi amma zata koma cikin halin jinya, dama haka rayuwa ta gada in yau kai ne gobe ba kai bane, Allah ya baki lafiya mai amfani Ameen.
sa'ada da noraiz ma fitowa su kayi su ka shiga.
Sallama mansoor yayi masu, da yake harda Abdallah zasu tafi.
Sai da jirgin su ya tashi sannan mansoor ya koma cikin motar ya bar airport shi ka ɗai cike da kewar su.
Sai da suka kusa isa lagos sannan shazim ya kira malam ya sanar da shi suna hanya sun ma kusa isowa , faɗa sosai malam yayi mashi saboda ƙin ɗaukar wayar su da baiyi ba,duk ya bi ya tayar masu da hankali,haƙuri ya shiga bashi ,ƙin haƙura malam yayi sai ma kashe wayar da yayi yana faɗin "zaka dawo ka same ni ne ai "
number majeed ya lalubo ya kira shi ya sanar da shi suna hanya ya turo mashi da Ambulance suna tare da patient ne, bai jira mi majeed zai ce ba yayi rejecting kiran yasan dole majeed zai tambaye shi waye bai da lafiya.
✨LAGOS✨
Kiran Ammy malam yayi ya sanar da ita su shazim na hanya
"amma shazim bai da hankali baba, yanzu da lafiyar su lau amma mu kai ta kiran shi baya ɗaga wa"
"Allah dai ka ɗan yasan dalilin da yasa bai ɗauka ba"
"amma ko ma minene, ai ya ɗauki kiran mu idan baza su dawo a jiyan ba "
"yanzu dai sai sun shigo, kisa ilya yaje ya ɗauko su dan yace sun kusa isowa " da to Ammy ta amsa haɗi da yin rejecting, kiran ilya tayi ta sanar da shi su shazim na hanya yaje ya ɗauko su.
Suna gama waya da Ammy bai jira komai ba ya shirya ya nufi airport shi da ɗayan drivern gidan mai suna ɗan Auta, shi ba kasa fai ya cika driving ba yafi yawan zaman gida.
Ko da suka isa airport ɗin su majeed sun daɗe da zuwa da Ambulance tun da shazim yace mashi suna tafe da patient hankalin shi yaƙi kwaciya sai da ya zo dan yaga waye ba lafiya, basu wani jima ba jirgin su shazim ya ƙaraso.
hankalin majeed yayi matuƙar tashi da yaga fatima,bawan Allah ilya har da ƴar ƙwallar shi, shigar da ita su kayi cikin Ambulance ɗin , bai ma lura da Abdallah ba hankalin shi naga fatima, har sai da shazim yace" wai lafiya Abdallah na maka magana hankalin ka na wani wajen baka ji " sai a lokacin ya lura da Abdallah dake mashi magana, gaisawa su kayi da shi.
Mota kowannan su ya shiga, yanzu ma shazim Ambulance ya shiga shi da Abdallah sai majeed daman a nan yazo,majeed na gaba shida driver yayin da Abdallah ke kusa da fatima shi da shazim, ganin duk sun shige nan yasa noraiz da sa'ada nufar motar da ilya yazo ɗaukar su, ɗan auta kuwa empty ya koma ba kowa a motar da ya zo da ita, Ambulance ɗin ke gaba su ilya na binsu a baya.
Kasa haƙuri majeed yayi har sai da ya tambayi shazim mike damun fatima, duk ya bi ya damu, abun har so yayi ya ba Abdallah haushi ganin yanda majeed ya ruɗe kan ciwan fatima, amsa shazim ya bashi da ciwan ta ne ya tashi, tambayar shi majeed yayi miye dalilin
"majeed ka kwantar da hankalin ka, da sauƙi jikin ta "
tsaki Abdallah yaja,shi kuwa majeed hankalin shi naga fatima bai ma san Abdallah nayi ba, shazim kawai ya lura da shi, girgiza kai kawai yayi ba tare da ya ce ma kowa komi ba
"to amma hospital za'a nufa da ita " majeed ya faɗa, tsaki Abdallah ya sake ja yana faɗin "wai lafiya majeed ka bi duk ka tashi hankalin ka, ance maka jikin ta da sauƙi, amma sai tambaya kake "
"daga tambayar lafiyar ta zaka wani ce na damu mutane jiman ƙarfin hali"
" dan Allah ya isa haka, gida za'a kaita duk wani abu da ya dace ayi mata zan iya yi mata shi a can ba dole sai a hospital ba " shazim ya faɗa
Majeed yace "to shikenan , Allah ya bata lafiya "
"Ameen ya Allah " shazim ya amsa, babu wanda ya ƙara cewa komai cikin su har suka ƙara so gida, horn su kayi da sauri mai gadi ya buɗe masu, ciki su ka shiga, a compound drivern yayi parking da Ambulance ɗin, jin jiniyar Ambulance ne yasa Ammy dake parlor zaune fitowa da sauri gaban ta na faɗuwa, tana fitowa su shazim na fito da fatima, da sauri ta ƙara so kusa da su dan taga waye kuma ba lafiya, ai ko da tayi arba da fatima kwance kamar matacciya,wani mummunan faɗuwa gaban ta yayi, jiri ne ya fara kwasarta ta tafi luuu zata faɗi babu wanda yalura da ita sai noraiz,da wani masifafen gudu ya ƙaraso wurin ta yana kiran sunan ta cikin ƙaraji ya ganin ta tafi luuu zata faɗi,ririƙeta yayi,ƙasa suka nufa shi da ita dan tuni har ta sume, gaba ɗaya hankalin su shazim ya dawo kanta, shazim a tamanin ya ƙaraso wurin su saura kaɗan ya faɗi......
_Episode _44_45_
_..........Gaba ɗaya hankalin su shazim ya dawo kanta, shazim a tamanin ya ƙara so wurin su saura kaɗan ya faɗi, tallabo kanta yayi yana kiran sunan ta
"Ammy! Ammy!! pls ki tashi dan Allah " sai ro ƙwan ta yake da ta tashi duk ya bi ya firgice sai jijjiga ta yake, noraiz ban da kuka babu abun da yake, ilya ne ya shiga ciki da sauri, ruwa ga ɗauko a kitchen da sauri ya fito ya dawo wurin su, Abdallah ne ya amsa ya nufi ammy da ke kwance a jikin shazim, da sauri ya kwance marfin robar ruwan ya shiga yayyafa mata sai da ya yayyafa mata kusan sau ukku sannan ta ja wani dogon numfashi, Alhmdllh su ka shiga furtawa, hawaye ne suka taru idanuwan ta
" mi ya faru da fatima??, kar ka saki kace man ta mutu " tana faɗa hawayen da suka taru a idanuwan ta na zuba, abun tausayi su Abdallah ma sai da zuciyoyun su suka karaya ganin yanda Ammy ke zubar da ƙwalla
"ki kwantar da hankalin ki Ammy, ba wani abu bane ya same ta lafiyar ta lau "
"taya zaka ce man tana lafiya bayan na ganta a haka "
"da gaske nake Ammy, ki kwantar da hankalin ki " ya faɗa haɗi da kallon su majeed yace " majeed ku shiga ciki da ita " da to majeed ya amsa, shi da Abdallah su ka shiga da fatima, da sauri Ammy ta tashi ta bi bayan su, bin bayan ta noraiz yayi ya na share hawaye , shazim kallon sa'ada da ke gefe rakuɓe gefe sai hawaye take yayi yace " shiga ciki mana " da to ta amsa haɗi da bin bayan su noraiz ta shiga ciki,komawa yayi cikin Ambulance ɗin ledar magungunan fatima ya ɗauka sannan yayi ma drivern sallama, bai shiga ciki ba waya ya ciro daga aljihun wandon shi, dialing ɗin wata number yayi,wanda ya kira na ɗagawa bai ko amsa mashi sallamar da yake yi ba yace " kayi sauri ka kawo man na dawo " yana gama faɗa yayi rejecting kiran, ciki ya nufa, bai same su a main parlor ba hakan yasa shi nufar medical room ɗin su dake kusa da part ɗin shi, tura ƙofar yayi ya shiga ciki, tsai tsaye ya same su fatima kuma na kwance kan gadon marasa lafiya gaban gadon ya ƙarasa haɗi da ajiye ledar da ke hannun shi kan ɗan table ɗin dake gefan gadon wani drip ya sake fiddowa daga cikin ledar haɗa shi yayi duk su Ammy na nan sun zuba mashi ido harya gama haɗa shi ya sama fatima, sai da ya gama dai data komai sannan ya kalle su yace " mu fita mu bata wuri "
ficewa su kayi zuwa waje,