Showing 81001 words to 84000 words out of 133697 words
Chapter 28 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt
hannun shi Abba ya jawo
"zo mutafi ba abun da zai sake yi maka ai ina tare da kai "
"ni dai momy nake so ta duba ni"
"to shikenan zo mu tafi "
duk da yace haka ƙin binshi luqman yayi sai da dady yace "nima ina nan ba abun da zai maka kaji " sannan ya bi bayan su suna gaba yana baya sai zare ido yake har suka shigo main parlor ba kowa duk su mansoor sun fita sai momy dake zaune kan sofa ta buga uban tagumi, tana ganin su da sauri ta taso tana "luqman yanzu kaga irin ta ko "
da sauri ya nufe ya yayi hugging ɗinta " momy wallahi bazan sake ba Allah "
Abba ne yace "turai kiyi mashi dressing ɗin wannan ciwukan "sai a lokacin momy ta lura da ciwo kan da kae jikin shi,medical room ɗin su ta nufa da sauri zama su kayi kan sofa suna jiran ta fito, kamar daga sama suka ji ƙarar jiniyar motan ƴan sanda
Abba ne yace "Innalillahi ba dai usman sai da ya kira ƴan sandan nan ba, ya Allah "
da sauri luqman ya tashi yana zazzare ido " na shiga uku dady ni su kazo kama wa ya shazim ne ya kira su" dafe kai dady yayi
"shazim wai wane irin yaro ne yaya, yanzu duk wannan dukan da yayi mashi bai isa ba sai ya haɗa shi da ƴan sanda " shi dai Abba yayi shiru bai ce komi ba
"dady dan Allah kar ka bari su tafi da ni, dan Allah ba dan ni ba dady" duk ya bi ya ruɗe jikin shi sai rawa yake
dafa shi dady yayi "kwantar da hankalin ka ba abun da zasu yi maka kaji... "
ko rufe baki bai yi ba a ka turo ƙofar parlorn a shigo ƴan sanda ne su uku suka shigo, da gudu luqman ya boye bayan dady, Abba ne ya nufe su da sauri yana faɗin " yallaɓai lafiya?"
babban cikin su ne yace " munzo ne da sammacin kama luqman Ibrahim Nuraddeen "
Abba yace " wa ya baku izini ke nan?"
"nine ya ji an faɗa daga bayan su " matsawa yan san da sukayi a dai dai lokacin momy ta fito hannunta riƙe da first aid box
Abdallah ne tsaye bayan su ya harɗe hannuwa a ƙirji
da mugun mamaki su dady ke kallon shi Abba ne yayi ƙarfin halin cewa "a kan wane dalili kenan, duk dukan da shazim yayi mashi bai isa ba"
Abdallah yace "pls Abba kayi haƙuri" ya faɗa haɗi da kallon jami'an tsaron da ke tsayae yace " yallaɓai kuyi aikin da ya kawo ku "
matsowa dady yayi ganin ya matsa ne yasa luqman da sauri ya nufi sama
"dan Allah yallaɓai ku dakata dan Allah "
tsayawa su kayi suna sauraron mi dady zaice kamar daga sama suka ji ihun luqman yana kiran sunan dady a tamanin suka juya suna kallon sama, shazim ne su ka hango ya damƙi wuyan luqman ya nufo parlorn da shi ba wanda yaga san da ya shigo part ɗin, ya gaji da jiran police ɗin ne au fito da luqman ganin sun jima ne yasa shi ya shigo shine yaji dady nacewa su dakata ya kuma hangi luqman zau shige part ɗin dady, har wurin su ya ƙara so da luqman ya miƙama ɗaya daga cikin police yace "arrest him" kama hannun luqman police ɗin yayi ya sa mashi handcuff ya fice da shi,kan sofa dady ya zube, Abba ne yace " why shazim why, yanzu duk dukan da kayi mashi bai isa ba, shima fa ɗan uwan ka ne kamar fatimar " kallon Abba shazim yayi da idanun shi da suka kaɗa su kayi jawur tsantsanr ɓacin rai da masifa ce a cikin su hannu kawai ya haɗa ma Abba alamar haƙuri ba tare da yace komai ba ya fice daga part ɗin sai a lokacin momy ta fashe da kuka.
ciki mota su ka sa luqman suka tafi da shi sai ihu luqman yake yana kiran sunan dady..........
_Episode 42_43_
................ Sai ihu luqman yake yana kiran sunan dady.
Shazim ba irin haƙurin da su ya usman da su mahmud, faisal mama gwaggo halima, har da su Asma'u da kairiyya basu bashi ba amma ko kallon in da suke bai ma yi ba sai ma kama hanya da yayi ya bar part ɗin
tare shi mansoor yayi yana faɗin " haba shazim miyasa zaka yi haka duk haƙurin da ake baka yaci ace ka haƙura, dan Allah kar ka bari su tafi da shi, a nan ma zaka iya hukunta shi, please "
ya ƙara sa magana cikin sigar roƙo, amma ina ko kallon shi shazim bai yi ba sai ma bi ta gefan shi da yayi ya wuce, bin bayan shi mansoor yayi yana ci gaba da roƙon kwan shi amma kwata kwata babu alamar ma zai saurare shi, ko mawa yayi kan Abdallah yana faɗin " haba Abdallah miyasa zaka kira su tun da har shazim ya ɗauki doka a hannu ai da an barshi yaji da iya wannan "
"mansoor kafi kowa sanin halin luqman tun da kai ke tare da shi, ji irin abun da yayi ma fatima ace ma bai mata komai ba, halin ciwan da ya sata ya kyauta kenan "
"na san bai kyauta ba amma hukuncin zai mashi yawa "
"kai ka ga haka "
Shazim ne ya ce " ko da bai kira su ba ni sai na kira su, kuma wallahi na tabbatar da ya ci mutuncin fatima, wallahi kaji na rantse sai yayi daya sanin sani na a rayuwar shi, sai ya gommaci kiɗa da karatu daga shi har mahaifin na shi daya iya ƙoƙarin ɓoye ta dan kar wani ya sani " yana gama faɗar haka ya shige part ɗin su, mansoor yana ji yana gani ba shi da yanda zai yi haka police ɗin suka fice da liqman daga estate ɗin cikin dare, bin bayan su shazim yayi dan ya duba jikin fatima.
kusa da dady Abba ya matsa " Ibrahim kayi haƙuri kar ka sa kanka a damuwa insha Allah ba abun da zai faru da luqman zai dawo gobe da izinin Allah, ka kwantar da hankalin ka "
"amma yaya mi nayi ma shazim a rayuwa da zai saka man da irin wannan abu, ai ko darajar kasan cewa ta ƙanin mahaifin shi ya duba ya ƙyale luqman, amma saboda bai ɗauke ni a bakin komai ba bayan yayi mashi dukan mutuwa shine ya haɗa shi da jami'an tsaro, mi nayi mashi har haka "
"ka kwantar da hankalin ka ba abun da kayi mashi kawai ranshi ne ya ɓaci, amma nasan nan da zuwa wani lokaci zai huce kuma zai nemi afuwan abun da yayi maka "
"shikenan yaya, ya jikin feenah na manta tun ɗazu ban tambaye ka ba "
"jikinta da sauƙi gobe da safe za su ma dawo gida insha Allah"
"Allah ya kaimu " dady ya faɗa, da Ameen Abba ya amsa haɗi da tashi yana faɗin "ka tashi kaje ku kwanta, ka lallashi turai naga hankalin ta yayi matuƙar ta shi " da to dady ya amsa haɗi da tashi ya nufi ɗakin momy, ficewa Abba yayi zuwa part ɗin shi lokacin da ya shiga duk sun shige ɗakunan su hakan yasa ya nufi ɗakin shi ya kwanata
Zaune dady ya samu momy bakin gado tayi tagumi sai share hawaye take,abun zallah ban tausayi tana ji tana gani an kama mata ɗa bata yanda zata yi, zama dady yayi kusa da ita, ɗan shiru yayi na wani lokaci can ya dafa kafaɗar ta " dan Allah turai kiyi haƙuri, ko mai zai wuce da izinin ubangiji, insha Allah gobe luqman zai dawo kiyi haƙuri kinji "
fashewa tayi da kuka mai tsuma rai dady shima kukan ne yazo mashi amma sai ya danne shi bai yi ba, jawota yayi jikin shi yayi hugging ɗinta yana ɗan bubbuga bayan ta haƙuri ya cigaba da bata har sai da tayi shiru ta koma tana sauke ajiyar zuciya, a haka har bacci ya ɗauke ta, kwantar da ita yayi kan bed haɗi da jan blanket ya rufe mata jikin, sannan ya nufi toilet ɗinta bayan kamar ten seconds ya fito, switch ɗin ɗakin ya nufa ya kashe masu sannan ya nufi gadon ya hau sai da ya rufe jikin shi da blanket sannan jawo ta jikin shi yayi hugging, idanu ya rufe ba bacci yake ba tunani ya shiga na abun da ya faru ya daɗe yana tunani har shima bacci yayi awan gaba da shi.
Fitowar shi kenan daga toilet ta farka a firgice tana kiran sunan shi da Ammy da malam har noraiz sai bige bige take tana ƙoƙarin cire drip ɗin da aka sa mata da sauri ya ƙarasa wurin ta yana sa hannu ya riƙe hannuwanta da take bige bige yana kiran sunnan ta da cewa " dai na kuka gani nan a kusa da ke " jin muryar mutum ne a kusa da ita yasa ta ƙoƙarin fisge hannun ta tana kiran sunan shazim a ruɗe " ya shazim ka zo ka taimake ni kashe ni ya luqman zai yi dan Allah ka taimake ni " gaba ɗaya a firgice take ta dai ji muryar shazim amma bata san yana ina ba dan bata san shine a kusa da ita ba duk a tunanin ta luqman ne, sai ko kawa take zata ƙwace hannun ta da shazim ya riƙe jawo ta yayi jikin shi da sauri yana faɗin " kwantar da hankalin ki ni ne a kusa da ke ba luqman ba " duk da haka bata daina yunƙurin fisgewa daga riƙowan da yayi mata ba, ganin dai da gaske a tsorace take bazata tsaya ba ne yasa shi jawo ledar magungunan da yasa aka siyo mata allurar da ke ciki ya ciro dama ya haɗata, hakan yasa bai tsaya wata wata ba ya yayi mata allurar a damtsen hannun ta,dan danan allurar ta fara aikin ta cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya ɗauke ta, jin jikinta yayi sanyi ne yasa shi fahimtar tayi bacci, kwantar da ita yayi kan gadon ya ja mata blanket, ya daɗe zaune yana kallon ta saƙawa da kwan cewa kawai yake , muddun gwajin da ya tura asibiti sakamakon ya fito, abun da yake zargi ya tabbata , ya rantse babu abun da zai hana shi yin shari'a da luqman har da mahaifin shi, ya jima yana saƙawa da kwancewa daga bisani ya tashi ya nufi parlor wurin Abdallah da mansoor, zaune ya same su kan sofa kowa yayi shiru yana tattaunawa da zuciyar shi, wuri shima ya samu kan sofar ya zauna
Abdallah ne yace " har yanzu bata farka ba " ɗaga mshi kai kawai shazim yayi, yan da suka ga rana haka suka ga dare kowannen su a zaune ya kwana, har luqman da ke station a tsaye ya kwana har gari ya waye
_*WASHE GARI*_
Haka su ka tashi da jiki su ku ku ba bu walwala, har lokacin kuma fatima bata farka ba, kowa da ke estate ɗin ya shigo ya duba jikinta har da dady,sa'ada ke zaune kusa da fatima ta zuba mata idanu.
da safen ma ba irin haƙurin da su ya usman basu ba shazim ba akan ya haƙura a saki luqman, amma fir yace bai san wannan zancen ba dole sai anyima fatima gwaji ya tabbatar da luqman bai mata komai ba sannan, har station ɗin suka je ko za'a basu bail shi amma ina saboda shazim ya hana ba yanda su ka iya haka suka dawo estate suka zuba ma sarautar Allah ido, ba wanda ranshi bai ɓaci ba da shazim, shi kuwa abun da ke gabansa kawai yake, har estate ɗin ummah matar uncle ahmad ta zo domin duba fatima kuma duk wani gwaji da shazim ke so ayi ma fatima ita tayi mata da yake likita ce tafiya tayi zuwa hospital dan ta bicika awan da tayi ma fatima,kowa zaman jiran dawowar ta yake da saka makon da zata zo da shi dan shazim yace dole sai sai yaga sakamakon ko da zai yarda aba da bail luqman, shiyyasa suka zauna zaman jiran tsammani kowa adu'ar shi Allah yasa luqman bai mata komai ba kamar yanda yake faɗi, kafin ummah ta dawo su
Innah su ka dawo daga asibiti da feenah, ta ji sauƙi kamar ba ita ba sai dai damuwa da take ciki, kwata kwata bata da walwala,har ƴar rama tayi duk a kan shazim, part ɗin innah su ka nufa gwaggo halima da mama ne suka shigo su kayi ma feenah ya jiki, feenah na kwance kan sofa tayi matashi da cinyar innah , su ya usman ma sun zo gaishe ta ganin noraiz ne yasa innah cewa " ai ku nayi tunanin kun tsufa da tafiya ashe kuna nan, kenan zuciyar da uban naku hau ba wata bace" shiru noraiz yayi bai ce mata ƙala ba gwaggo halima ce tace "dan Allah mama kiyi haƙuri daga dawowar ki " tsaki kawai innah ta ja ba tace komai ba,can kuma tace " ina su Ahmad ne "
gwaggo Uwani tace " nima dai naga ban gan su ba, kuma wai mike damun ku ne nagan ku duk sai a hankali "
"nima abun da zance kenan, sai kace kunyi zaman makoki" innah ta faɗa tana tsare gwaggo halima da idanu
"ba komai innah kawai saboda jikin feenah ne, amma tun gashi kun dawo Alhmdllh " shiru kawai su innah su kayi bawai dan sun yarda da abun gwaggo halima ta faɗi ba, feenah ce ta tashi tana cema innah zataje part ɗin su dan ta watsa ruwa, da to innah ta amsa mata, tashi tayi Ilham ta bi bayan ta, a bayan part ɗin innah su ka tsaya feenah tace " dan Allah Ilham ki faɗaman mike faruwa ne na ganku duk sai a hanli " ɗan nisa wa Ilham tayi sannan ta faɗa mata duk abun da ya faru da basu nan, kuka feenah ta fashe da shi tana faɗin "wai dan Allah mi yasa ya luqman bai gudun abun magana ne wani lokacin mi zai sa yayi ma fatima haka laifin mi tayi mashi har haka "
Ilham tace "gaskiya kam bai kyauta ba, amma baki ga irin na damar da yayi ba, yayi daya sanin yimata haka "
"ba abun da dady yayi a kan ya luqman ɗin "
"ba abun da yayi, domin ya shazim ya hana a bada bail shi wai har sai ya tabbatar da bai mata komai ba "
"shikenan " feenah ta faɗa part ɗin su suka nufa, tsit suka same shi ba motsin kowa, bedroom ɗin momy su ka nufa zaune su ka same ta bakin bed ta zuba uban tagumi gaba ɗaya damuwa tayi mata da bai bayi, sai sallama suke bata ma san suna yi ba tayi zurfi cikin tunani har sai da feenah ta dafa ta sannan ta san da shigowar su, ajiyar zuciya ta sauke haɗi da wai gowa tana kallon su, shafa kan feenah tayi tana faɗin " kun dawo kenan " ɗaga mata kai feenah tayi " to ya jikin " da sauki feenah ta faɗa " momy ina dady yake "
"yana ɗakin shi "
"ok, momy abun da ya luqman yayi kenan " ta faɗa idonta na tara ƙwalla shiru momy tayi batace komai ba
"momy wai miyasa ya luqman bai jin magana, yanzu yana ganin ta kyauta, duk ya saku a cikin damuwa "
"feenah dan Allah ki bar maganar nan abun da ya faru yariga da ya faru "
" amma momy..... " da katar da ita momy tayi
" daga dawowarki ki feenah, kar ki dawo man da abun da yariga ya wuce, insha Allah ba abun da zai faru "
"shikenan momy, bari naje ɗakin dady " ɗaga mata kai kawai momy tayi, hannun Ilham taja zuwa ɗakin dady basu same shi a parlor ba hakan yasa feenah ta nufi bedroom ɗin shi Ilham kuma ta zauna kan sofa, a bakin ƙofar ta tsaya haɗi da yin nocking, izinin shiga dady ya bata a hankali ta tura ƙofar ta shiga tsaye ta same shi sai kai kawo yake, sallama tayi haɗi da maida ƙofar ta rufe, juyowa dady yana kallon har ta ƙaraso kusa da shi tayi hugging ɗin shi, shafar sumar kanta yayi " ya jikin naki "
"da sauki "
"Allah ya ƙara sauki " da Ameen ta amsa sannan tace " dady yaushe za'a bada bail ya luqman "
"daga dawowar ki waya faɗa maki abun da ke faruwa, nima ban sani ba feenah, amma insha Allah na san zuwa anjima za'a sake shi "
" to Allah ya kaimu " da Ameen dady ya amsa, ta ɗan jima a part ɗin dady daga baya ta fita ita da Ilham , duk abun da ke faruwa har lokacin innah da gwaggo Uwani basu sani ba har sai da ummah tazo da sakamakon gwajin da tayi ma fatima, sanna su innah suka san abun da ke faruwa, innah tasha kuka zagi kuwa na duniyar nan ba irin wanda bata yima shazim ba, har papah dake kwance cikin kabarin sa bata bari ba sai da ta zage shi tasa da maifiyar shi kakar su shazim, har part ɗin su taje ta samu shazim, zaune ta same shi a part ɗin su ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, su Abdallah da ummah har da Ameerah duk suna zaune kan sofa, kowa ya zuba ma shazim ido, jira kawai su ke ya gama karanta takar dar suji minene sakamakon gwajin fatima , kamar daga sama suka ji muryar innah tana faɗin
" dama ubanka ko da ya bar duniya sai daya tozar ta man ɗana, wallahi duk abun da ya samu luqman bazan