Showing 72001 words to 75000 words out of 133697 words
Chapter 25 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt
to sai wasu da suka nuna ra'ayin yin aure yanzu duk da munfiso mu fara gamawa da manyan su amma tun da sun nuna ra'ayin su na son yin auren yanzu insha Allah za mu yi masu yanda su ke so, kafin nan ina so na sanar da hukuncin da muka yanke akan ga duk wanda bai gabatar da zaɓin shi ba "
Uncle Ahmad yace "shazim ina so ka sauraremu da kayau, tun da munce ka fitar da wacce kake so kaƙi, to mun yanke hukuncin haɗa ka aure da ƴar uwar ka hauwa'u "
tuna ni shazim ya shiga shin wai wacece hauwa'u cikin yaran dan bai ma san wacece mai wannan sunan ba
Uncle Ahmad ne ya katse mashi tunanin da yake ta hanyar cewa " kayi shiru banji kace komi ba " carab innah tace "yo mi zai ce, daga ma anyi mashi gata "
"duk da haka innah muna son jin ta bakin shi, ina jinka shazim " shiru kamar bazaice komi ba can dai yace
"Uncle bangane wacece kake magana a kanta ba "
riƙe haɓa innah tayi tana faɗin "lallai ɗan iskan gaye wato hauwa'un ce baka sani ba saboda ka raina ma mutane wayau ko, to ba kowa bace face takwara ta feenah ince ita ka santa " wani mumunnan faɗuwa gaban shazim yayi,a zuciyar shi yake faɗin " amma an raina mashi wayau arasa da wacce za'a haɗa shi sai wannan daƙiƙiyar yarinyar, lallai sun shiraya ganin ɓacin ranshi kenan" uncle ahmad ne yace "to ka dai ji ko wacece, mi kace a game da hukuncin " banza shazim yayi da shi kamar ma ba da shi yake magana ba, har sai da mansoor ya zungure shi yace "bro ana magana kayi shiru " ɗago da kanshi yayi idanun shi sun kaɗa sunyi jawur tsantsar ɓacin rai ne a cikin su ya wurga ma mansoor wata mummunanar harara wacce tasa mansoor kauda kai dan bai taɓa ganin ɓacin rai a fuskar shazim ba irin na yau, mai da kanshi yayi ya ɗuƙar, gwaggo Uwani tace "yau ga rainin wayau, yan isaka ka ɗauke mu ana magana kayi shiru "wani ɗan iskan kallo ya jefeta da shihar sai da gabanta ya faɗi innah tace " kayi fiye da haka ma mara mutunci, aure ne dai sai kayi " feenah dai sai zare ido take tsoron ta kar shazim yace bai son ta
ganin ya mai da su mahaukata ne yasa uncle Ahmad girgiza kai ya cigaba da faɗin"waɗan suka buƙaci a sa ranar da su "
ban da murmushi babu abun da ke fita daga fuskar luqman tun kafin ma a kira sunan shi
Uncle Ahmad yace "luqman da mahmud muna sauraron ku ku gabatar da zaɓin naku muna ji " jin uncle ya ambace su ne yasa farin cikin luqman ƙaruwa, sai da uncle ya sake magana tukunnan mahmud yace "Ilham itace zaɓin da na kawo maku "
"to masha Allah Ilham muna so muji daga bakin ki kinji abun da ɗan uwan ki yace " duƙar da kai Ilham tayi cike da kunya tace " uncle na amince "
"masha Allah, Allah ya nuna man lokaci " da ameen kowa ya amsa, sannan uncle ahmad yace "to kai luqman mauna sauraron ka " gyara zama luqman yayi yana kallon Innah da wani munafukin murmushi a fuskar shi yace " uncle ni ba kowa bace zaɓi na face fatima " kamar saukar aradu haka fatima taji maganar luqman, ita yau she harma su ka samu jituwa da zai ce wai yana sonta anya ba kunnuwanta bane suka jiyo mata ba dai dai ba, shazim mamaki abun ya bashi dan shi bai san da wani zacen soyayya ba tsakanin luqman da fatima ba kuma da ace ya sani da tuni yayi ma tufkar hanci amma ko yanzu bawai lokaci ya ƙure bane in dai da ranshi da lafiayar shi zai ga wanda zai masu auren dole, watau meeting ɗin nasu ne ma ke nan dan su aka tara wannan taron kenan maganar uncle Ahmad ce ta dawo da su cikin hayyacin su " to fatima kinji abun da yayan ki yace miye ra'ayin ki " kasa cewa komi fatima tayi sai ma kuka da ta fashe da shi " yau ga iskanci, daga tambaya sai kuka, zaki buɗe baki ki ba mutane amsar tambayar da aka yi maki ko kuwa " gwaggo Uwani ce ta faɗi haka cike da masifa, sake fashewa da kuka Fataim tayi " haba yaya kamata yayi kiji dalilin kukan ta bawai ki rufe ta da masifa ba, zo nan fatima " ta faɗa haɗi da miƙama fatima hannu ta zo kusa da ita, tashi fatima tayi ta nufe ta " yi shiru dai na kuka kinji, miyasa kikayi kuka baki son shi ne " carab innah tace " haba dai wane ita tace bata son shi, ta dai faɗi mi take ma kuka"
"dan Allah innah kiyi shiru, idan tace bata son shi ba wanda zai mata dole " acewar uncle ahmad
"idan tace bata son shi kenan biye mata zaku yi kenan, idan ba'ayi mata aure ba jiƙata za'ayi a sha " shazim dai na sauraron su dan yayi rantsuwa inda da ranshi babu wan da ya isa yayi mata auren dole kuma ma da wannan sakaran yaron
"shi nagani, wallahi ko tana so ko bata so sai ta aure shi tun ba jiƙata za'ayi ba... " katse ta uncle ahmad yayi yana faɗin
"ke uwani kar na sake jin bakin ki a nan, kinji na faɗa maki "
" a kan mi zaka ce haka amadu, idan ba'ayi mata auran ba mi zata yi ma mutane " tashi fatima tayi ta fita da gudu tana kuka kamar ranta zai fita, tashi luqman yayi ya bi bayan ta ba tare da kowa ya lura da shi ba
Shazim yace "idan bata da abun da zata yi maki ke, a kwai waɗan da suke da abun zata yima su, kuma wallahi da raina da lafiya ta babu wanda ya isa yayi mata auren dole " gaban innah ne ya faɗi jin abun da shazim yace,fashewa da kuka innah tayi tana faɗin "ni kake ci ma mutunci a gaban ƴaƴana da jikoki na, saboda baka ganin darajata dan bani na haifi ubanka ba " gwaggo Halima ce tace "kiyi haƙuri mama ki daina kuka, taya zaki ce bai ganin mutunci ki saboda ba ke kika haifi mahaifin shi ba,kin kasa fahimtar shi ne amma..... " bata ƙarasa ba innah tace " yi man shiru ai duk abun da yake aikatawa na lura akwai sa hannunki mara mutunci"
uncle Ahmad ne yace " dan Allah innha kiyi haƙuri kiyi shiru "
"taya zanyi shiru kuna ganin yaro na ci man mutunci a gaban ku kun kasa ɗaukar mata ki "
"Kiyi haƙuri dai dan Allah " ya faɗa haɗi da kallon shazim yace
"shazim mu kake faɗa ma haka koh, na lura ka raina innah ko, kenan ba mu isa mu yanke hukuncin ba a kan ku kenan ba"
"uncle ba da ku nake ba, amma tun da ta nuna bata son shi a ƙyale ta kawai tun da bawai tayi girman da za'ace ta isa aure ta ƙiyi ba "
"ok kai zaka nuna mana abun da ya dace kenan ko " a cewar gwaggo Uwani, banza shazim yayi da ita kamar ba da shi take magana ba, duk abun da ake uncle Ibrahim baice ƙala ba saboda a kan ƴaƴan shi ake magana,bazaka iya gane awane hali yake ciki ba jin su shazim sun nuna basu san ƴaƴan shi.
Uncle Ahmad ne yace "to naji ba da mu kake ba,sai ka faɗa man da wanda kake " shiru yayi baice ƙala ba ganin bazai ce komai bane yasa uncle ahmad ɗin cewa " kace babu wanda ya ida yayi mata auren dole,mi kake nufi?" yanzu ma shiru yayi baice komi ba, ɗan nisawa uncle Ahmad yayi yace "to bari kaji hukuncin munriga da munyanke aure babu fashi "
"Uncle wannan yarinyar da kuka haɗa ni da ita bana son ta,a yana yin kukan da fatima keyi alama ce ta bata son shi, i dan kuka tursasa dole sai mun bi umarnin ku komai zai iya faruwa " yana gama faɗa ya tashi ya bar parlorn, da idanu kowa dake parlorn ya bishi,tashi feenah tayi zata bi bayan shi sai a lokacin uncle Ibrahim yasa baki tsawa ya daka ma feenah yana faɗin "dawo ki zauna, shashasha banza " innah ta nufa ta faɗa kan jikinta fashewa tayi da wani mahaukacin kuka sai ihu take kamar wacce uwarta ko ubanta ya mutu basu taɓa tunanin shazim zai iya shuka masu rashin mutunci ba irin wannan musamman uncle Ibrahim da ya kasance ƴaƴan shi ne na cikin shi, tashi uncle Ibrahim yayi ya nufi feenah dake jikin innah ya ɗauke ta da wani mumunnan mari haɗi da jan hannun ta ya bar parlorn, bin bayan su innah tayi tana mashi masifa dan mi zai mareta, yarinya na son shi yace bai son ta ya barta da baƙin cikin da ya ƙunsa mata..
gwaggo Uwani ce tace "yaya yanzu kenan haka za'a zuba ma wannan yaron ido yana cima ma mutane mutunci kuma baka ce komai ba "
gwaggo Halima tace " mi kike so yace, tunda yace bai sonta a ƙyale shi kowa Allah ya haɗa shi da rabon shi "
"dallah sadiya kiyi ma mutane shiru ke dama tuntuni nasan cewa baki tare da mu, hada ke cikin masu zuga wannan yaron "
"ni dai komi zakice kice,goyan bayan gaskiya nake, kuma tun da ya nun..... " bata ƙarasa ba uncle Ahmad yace" dan Allah ya isa haka, kowa zai iya tashi ya tafi na sallami kowa " ɗaya bayan ɗaya yaran suka fara ta shi suna fita wasu naji haushin shazim da fatima wasu kuma na ganin yana da gaskiya duba da rashin tarbiya da feenah ke da shi, uncle Ahmad ka ɗai aka bari a parlorn yayi shiru damuwa ƙarara a fuskar shi.
_*✨SHAZIM✨*_
Tun da ya bar parlorn part ɗin su ya nufa, bedroom ɗin shi ya shiga trollyn shi da ke bakin gadon shi ya jawo ya kai shi parlor wayar shi ya ciro ya kira noraiz bugu ɗaya noraiz ya ɗauka tunkafin yace wani abu shazim yace ka same ni a ɗaki ƙit ya kashe wayar, bayan kamar 10 seconds noraiz ya shigo da sallama, ko sallamar da yayi shazim bai amsa ba yace "wuce ka ɗauko kayan ka " kwata kwata babu sauƙi a fuskar shazim, da to noraiz ya amsa haɗi da ficewa ya nufi bedroom ɗin shi ya fito da trollyn shi zuwa parking lot da mansoor yaci karo zai shigo part ɗin, ba wanda yace ma ɗan uwan shi wani abu, ciki mansoor ya shiga zuwa ɗakin shazim yana shiga shazim na fitowa hannun shi riƙe da jakar laptop ɗin shi, kayan da ke jikin shi ne ɗazo a jikin shi sai p cap da yasa yanzu da baƙin glass, tsaye mansoor yayi yana kallon shi..........
_Episode 38_39_
...........Ƙarasa wa ciki mansoor yayi yana kallon shazim sama da ƙasa sanna ya fara magana
"shazim ka bani mamaki matuƙa, ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba "
"mamaki na baka ko?"
"tambayata kake ma "
"mansoor idan har baka ga laifin abun da akai man ba bai kamata ni kaga laifina ba "
"dole naga laifin ka, a gaban mu fa kake faɗa masu magan son ranka "
"sai dai kai ta ganin laifi na amma bazan zauna a tauye man haƙƙina inaji ina gani, mi fatima tayi da za'a yanke mata wannan hukuncin kuma su rasa dawa zasu haɗa ta sai wannan ɗan iskan "
"ko da yace yana sonta kaji sun ce zasu aura mata shi ne?"
"Koma dai mi ne ne, bazan taɓa bari a ci zalinta ba, kuma ni kaga tafiya ta "yana gama faɗa yaja trollyn shi ya bar mansoor tsaye yana kallon shi, bin bayan shi mansoor yayi a bakin ɗakin fatima shazim ya tsaya tura ƙofar ya shiga tsit ya samu ɗaki alamar ba mutum a ciki, tunani yayi ko ta fita tare da noraiz, fita yayi mansoor na tsaye "wai shazim fushi kake dani ko mi " banza shazim yayi da shi ya nufi stairs case janye da trollyn shi, sake magana mansoor "magana nake maka shazim "
"inajin ka, mikake so nace maka ne "
" ok haka kace " a taƙaice yace eh, fita su kayi zuwa parking lot aminu ne ya amshi trollyn da ke hannun shazim ya sa a booth, dawowa yayi ya buɗe mashi bayan motar ya shiga rufe ƙofar aminu yayi, mansoor na tsaye bakin part ɗin yana kallon su, noraiz ne ya ƙaraso parking lot ɗin shi da mahmud, tambayar shi shazim yayi ina fatima "tana ɗakin ta "
"bata can " noraiz yace " kila tana part ɗin uncle Ibrahim "
"mi take a can kuma?" shazim ya tambaya "nima ban sani ba "
"to kaje ka kira ta " da to noraiz ya amsa haɗi da juyawa ya nufi part ɗin uncle Ibrahim shi da mahmud,da sallama su ka shiga part tsit main parlorn babu kowa, bedroom ɗin sa'ada suka a bakin ƙofar ɗakin suka tsaya mahmud ne yayi nocking, zaune take bakin bed tana kuka taji ana nocking, tashi tayi ta nufi ƙofar ta buɗe mahmud ne yace " sa'ada kice ma fatima ta fito su tafi "
cikin muryar kuka sa'ada tace "ai bata nan, ina tunanin tana ɗakin ga " noraiz yace "bata can " maimaita maganar sa'ada tayi "bata can yaya, to ina ta tafi?"
"shine ba mu sani ba, mun ma yi tunanin kuna tare "
"ai tun da ta fita a parlor na biyo bayan ta ban san ina ta shiga ba da na zo ɗaki banganta ba sai nayi tunanin ko tana ɗakin ta , to ko dai tana tare da Aunty kairiyya " sa'ada ta faɗa, fita su kayi zuwa part ɗin uncle Ahmad mahmud da sa'ada ne suka shiga part noraiz wurin shazim ya nufa, yana isowa shazim yace "wai ina fatimar ne kasan ƙarfe nawa yanzu "
"yaya gata nan zuwa, bata tare da sa'ada ne " ok kawai yace, gaba kusa da driver noraiz ya buɗe ya shiga, mahmud ne ya fito shi da sa'ada wurin su suka nufo tun kafin su ƙara so noraiz yace "tana ina "
sa'ada ce tace "can ma bata nan " shazim yace "bata nan" ɗaga mashi kai sa'ada tayi alamar eh, wayar shi ya ciro ya shiga dialing number ta tana ringing amma ba'a ɗauka ba, tsaki shazim yaja yana faɗin "amma sai na ci mutuncin yarinyar nan" sai da yayi mata kusan 5 missed call bata ɗauka ba, ganin dai da gaske fatima ba ɗaga wayar zata yi ba ne yasa shazim cewa "noraiz ku shiga ciki ku duba ta ko tana ɗakin ammy, ko ina dai ku duba ta " da to suka amsa noraiz ya fito su ka nufi part ɗin su, ba inda basu duba har bedroom ɗin shazim dana noraiz ɗin amma ba fatima ba dalilin ta,ne man fatima har part ɗin innah da na su Aunty zainab,su da zasu bi jirgin ƙarfe biyar na yamma sune har aka yi sallar magrib ba su tafi ba suna ne man fatima,abun da ya ɗaga masu hankali ganin wayar ta da suke ta faman kira a main parlorn part ɗin uncle Ibrahim kan sofa sa'ada har ta fara kuka, hankalin shazim yayi ƙololuwar tashi, ina fatima taje.
duk wannan bidir da suke na ne manta babu wanda su ka faɗa ma suna ne manta, zaune suka yi a main parlorn part ɗin su shazim kowa yayi ta gumi tunanin kawai suke ina fatima ta shiga, sa'ada kuwa sai kuka take mahmud na lallashin ta,har aka yi sallar isha basu san in da ta shiga ba, tashi sukayi su ka nufi masallaci, sa'ada kuwa part ɗin su ta nufa wurin momy , ko da ta shiga samun momy tayi zaune bakin gado tayi tagumi, damuwa ce ƙarara a fuskar ta, da gudu fatima ta faɗa saman jikin ta tana kuka, ɗago da ita momy tayi tana faɗin "lafiya ke kuma daga ina haka, mi kike ma kuka kuma " cikin shashekar kuka tace "momy ba'aga fatima ba " da sauri momy ta ɗago da fuskar ta tana faɗin "ban gane ba, ina ta je "
"momy tun ɗazu muke nemanta ni da su ya shazim ba mu gan ta ba, muna ta kiran wayar ta ashe tana a nan parlor ta barta " dafe kai momy tayi tana faɗin "ya salam, ina taje , kun du ba har part ɗin su innah da na su Auntyn ku?"
"eh momy babu inda bamu duba ba amma bata nan"
"har ɗakin feenah kin duba "
"a'a momy ban duba ba "
"to ta shi muje mu duba " ta shi su kayi zuwa ɗakin feenah babu in da basu duba har cikin toilet sai da su ka duba babu almun ta,ɗaya bayan ɗaya duk wani ɗaki da ke part ɗin sai da suka duba amma bata ba alamar ta, date kai momy tayi kamar mai tunanin girgiza kai ta shiga yi tana faɗin " ba gaskiya bane , hakan ma bazata taɓa faruwa ba, idan ko haka ne na shiga uku ni turai "
"momy miya faru, miye kuma ba gaskiya ba?" sa'ada ta jefa mata tambayar haɗi da tsare ta da idanu
"bakomi sa'ada,kije part ɗin su Kairiyya ku sake duba ta " momy ta faɗa tana nufar part ɗin dady,fita tayi zuwa part ɗin su shazim yan da ta bar su ɗazu zazzaune kan sofa yanzu ma haka ta same su amma ban da shazim
"ya noraiz an ganta " girgiza mata kai kawai yayi, fashewa tayi da kuka sai kace ƙaramar yarinya, mahmud ne yace" dan Allah sa'ada kiyi mana shiru, ba ɓacewa tayi ba za'a ganta"
ficewa tayi daga part ɗin.
Su Asma'u ne zaune a main parlorn part ɗin uncle Ahmad, fira su ke duk a kan meeting ɗin ɗazu