Showing 33001 words to 36000 words out of 133697 words

Chapter 12 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt

maganar da shazim akan zowan naso,to shine yake sanar man anyi mashi kiran gaggawa jos baza su samu zuwa ba sai sati na sama " katse ammy tayi da faɗin "dallah dakata man aisha kina nufin sai abun da shazim yace kenan, ko mi kike nufi"ammy ta ce "ba haka nake nufi ba innah" on the other hand "to mi kike nu, tun yau she muke magana sai dai kice man ranar kaza zasu zo amma kuma basu zo sai anyi magana ki kawo ma mutum wani uziri" shiru ammy tayi tana sauraran ta, da kaga fuskar ammy kasan cike take da damuwa " to bari kiji in gaya maki, baku isa ba daga ke har wannan mara kunyar, zumunci ne Allah ya riga da ya haɗa kuma dole ne ayi shi, bar ganin nayi shiru na barmaki yaran a hannun ki bawai hakan na nufin bazan iya ƙwatar su ba daga hannunki bane, saboda yara basu da wasu dangi a duniya bayan mu ɗinnan dai da kika gama rainawa kikasa ƴaƴanki suke ganin kamar bamu da amfani" sosai matar ta rufe ammy da masifa ammy na bata haƙuri tana gama faɗar abun da zata faɗa ko jiran mi ammy zata ce bata yiba ta kashe wayar, shiru ammy tayi ta ƙura ma wayar ido, chan kuma ta ɗaga hannun ta sama tana adu'a wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata, gefen hijabin ta ta sa ta goge tana faɗin "Allah sarki abubakar, Allah ya jiƙan ka ya haskaka kabarin ka " na ce ameen ammy, tashi tayi daga kan sallayar ta linke ta ta saka cikin wardrobe da hijabin da tayi sallah fita tayi daga ɗakin, fatima ta samu zaune kan sofa tana ta latsa sabuwar laptop ɗinta wacce shazim ya saya mata, ɗago da kanta tayi tana faɗin"barka da fitowa ammy "da yawwa ammy ta amsa mata haɗi da neman wurin zama ta zauna, fuskar ta duk a ya mutse, lura da hakan fatima tayi yasa ta cewa"lafiya dai ammy na ganki cikin da muwa " ce mata ammy tayi ba komai mikika gani "nagan ki duk wani iri ne ammy " amsa ammy ta bata da gajiya ce, "to ammy da kin kwanta kin ɗanyi bacci kafin la'asar tayi "to"shine kawai a bunda ammy ta ce mata.....


✨KATSINA✨


Sai bayan da a ka gama sallar asr ɗakin su Aairah ciki yake da ƙawa yen su na boko da islamiya , mai makeup ta fara tsara ma Aairah makeup mai kyan gaske, wayar Aairah ce ta fara ringing cema Aaimah tayi ta duba mata taga wake kira , Amsa ta bata da alaramma ne ( malamin su na Islamiyya ) haɗi da yin picking, tayi sallama, ba'a jin me na cikin wayar yake ce wa, kawai dai naji Aaimah ta ce to shikenan malam, sannan tayi rejecting tana ce ma Aairah "ya ce sun ƙara so, suna waje"
Aairah tace " to pls ki fita keda aeesha ku shigo da su, ko ki faɗa ma abie sai ayi ma su iso "
Aaimah ta ce " bari dai na faɗa ma abie ɗin kawai, dan na san babu hanyar wuce wa"
Aairah ta ce "to shikenan faɗa ma abie ɗin kawai"
dialing number abie Aaimah tayi, picking abie yayi yana cewa "lafiya Aairah , kun gama shirya wa ne"
"Aaimah ce abie "
"Ok kun gama ne"
"A'a abie dama su alaramma ne suka iso"
Abie ya ce " to bari na sa abdallah ya shigo da su, amma fa kuyi sauri bana son lokaci ya ƙure"
"to abie insha Allah mun kusa"
"to shikenan"abie ya faɗa haɗi da yin rejecting din call din
Aairah ta ce " sis ya abie ɗin ya ce "
Aaimah ta ce"gashi chan zai sa ya abdallah ya shigo da su"
Aairah ta ce "to kira su ki ce ga ya abdallah nan fi towa"
kiran su Aaimah tayi ta faɗa masu, sannan ta ajiye wayar, ana kammala ma Aairah ita ma aka yi mata, sanan najma, sai friend din su Aeesha, sosai suka yi kyau kamar ka sace su ka gudu mu samman ma su Aairah , dan ba ƙara min kyau suka yi ba, shiryawa su kayi cikin wata atamfa super ɗinkin riga da skirt, sosai ɗinkin ya amshi jikin su ba ƙara min kyau atamfar tayima fatar su ba, sannan su ka ɗaura farar alkyabba saman atamfar, faɗin kyan da alkyabbar tayi masu ɓata lokaci ne, kamar wasu ɗiyan sarakai, mom ce ta shigo ɗakin jikin ta sanye da wani haɗaɗɗen lace ɗinkin doguwar riga, wuyan ta da kunnan ta da hannu sanye da gold, mom ta ce "kai masha Allah kuce kun shirya, kai amma kunyi kyau sosai, kamar zan kai ku gidan miji"
dariya friend ɗin su da ke ɗakin suka yi suna ce wa"mom ai wannan ranar sai sun fi haka bada kala" su dai su Aaimah ban da murmushi babu abun da suke, "mom ta sake cewa "to kuzo ku fita ku ka ɗai ake jira " da to suka amsa mata, fice wa mom tayi daga ɗakin, suma tashi su kayi suda friend ɗin su suka fice chan compound, suna gaba friend ɗin nasu na baya, maƙil suka iske compoud ɗin da mutane, wurin da aka tana da domin su suka nufa suka zauna, ba ɓata lokaci aka shiga gaba tar da walima, alaramma yayi wa'azi, sannan su Aaimah suka yi karatu, sosai walimar tayi kyau ta kuma ba da ma'ana, su Aairah ba ƙara min burge mutane suka yi ba, sun kuwa sumu kyauta daga islamiyyar su, haka ma abie, mom, ya abdallah , dadi, granny, papi,aunty safiya, ƙannan abie duk sun basu kyauta, sosai suka tara kyaututtu ka daga wurare daban daban, su aunty rabi da aunty safiya suka yi rabon souvenirs, sai wurin karfe 6:40 ana shirin kiran sallar magrib sannan aka tashi, kowa ya tafi yana yaba hazaƙa irin ta su Aairah da kuma ganin nagartar islamiyar su .......


Episode 16_17


Sallah isha Aaimah ta kammala tana zaune kan sallaya Najma ta shigo hannunta ɗauke da wani madai dai cin kwali, Aaimah ce tace "ke kuma daga ina haka da wannan ƙaton kwalin" amsa najma ta bata da"saƙwan Aairah ne inji ya mus'af " ta faɗa yayin da take ajiye kwalin kan bed, ta sowa Aaimah tayi daga kan sallayar tana faɗin "ya mus'af dai, mugani" buɗe kwali suka shiga yi, Aairah ta fito daga bathroom jikinta ɗaure da towel tsayawa tayi tana kallon najma da Aaimah dake ko kuwar baɗe kwali, kayan da ke cikin kwalin suka shiga fitowa, qur'an ne da carpet sai watch na mata da turare, kwalin turaren su Aaimah suka buɗe suna ta fesa ma jikin su suna faɗin "ah lallai ya mus'af abun yar wariyar launin fata ce, to bari muji kalar ƙamshin turaren" ita dai Aairah ban da bin su da idanu babu abun da take, dan kwata kwata bata fahimci mi suke nufi ba, barin bakin ƙofar bathroom ɗin tayi ta nufi dressing mirror tana faɗin "wai ku lafiyar ku ƙalau kuwa, dare ne amma sai wani fesa ture kuke baji ba gani, wai ma ina kuka same shi ne" najma ce tace "naki ne inji ya mus'af, tun da mu bazai bamu ba shine muke fesawa" taso wa Aairah tayi daga gaban dressing mirror ɗin tana faɗin "kuji tsoron Allah, shine kawai za kuyita fesawa koma ku faɗa man" Aaimah ce tace to yan zu an faɗa maki shikenan ko, kayan Aairah ta shiga dubawa tana faɗin "kai amma nagode sosai ya mus'af, Allah ya bar ƙauna"da ameen su najma suka amsa, tashi Aairah tayi ta shirya cikin pajamas ɗin ta sannan suka shiga buɗe sauran kyaututtu kan da suka samu, sai da suka gama harma sun kwanta sannan ta ɗauki wayarta ta kira mus'af, sunjima sosai suna waya har su najma suka yi bacci, itama suna gama wa bacci ta kwanta....
Wannan kenan


✨lagos✨


Fatima da ammy ne a kan dinning suna dinner, fatima ce kawai ke cin abincin dan ammy bata wani ci sosai ba ta tashi tana faɗin "nizan shiga ciki, idan yan uwan ki sun shigo kice masu na kwanta sai da safe " fatima ce tace " to ammy, amma lafiya naga kin tashi ba tare da kinci komai ba"
"naƙoshi ne fatima, sai da safe "ammy ta faɗa, bedroom ɗin ta ta nufa, binta kawai da kallo fatima tayi, aranta tana faɗin "ko mike damun ammy ne yau"shiru tayi dan bata da mai bata amsar tambayar ta, ammy bata jima da tashi ba shazim suka shigo shi da noraiz bakin su ɗauke da sallama, amsa ma su sallamar fatima tayi, dinning ɗin suka nufo , warmars ɗin da ke kan dinning noraiz ya shiga buɗewa yana faɗin "mi aka dafa ne autar ammy " girgiza kai Shazim yayi yana faɗin "ina ammy ne naganki ke kaɗai? "
"ta shiga ɗaki "
"lafiya dai koh? "fatima ta ce "gaskiya yaya da sauƙi dai". shazim ya ce "mi kuma ya same ta yanzu"
"wallahi yaya har yanzu mood ɗin ta sai ahankali kuma na ƙara tambayar ta mike da munta, sai cewa tayi wai lafiya qlu, kuma fa yanzu bata ci komai ba wai ta ƙoshi" ɗan shiru Shazim yayi kamar me nazari chan kuma sai ya ce" ok shikenan sai da safen ku " ya wuce part ɗin sa, noraiz yace "nifa ina tunanin wani abu ke damun ammy wan da baza ta iya faɗa mana ba"fatima ta ce"abun da nake tunani ke nan ya noor"sun ɗan jima suna tattaunawa a kan chanza war mahaifiyar su, sannan suma suka tashi suka nemi wurin kwanciya su....


WASHE GARI...


Ammy na kan sofa a parlor, Shazim ya shigo da ga motsa jiki, wirin da ammy ta ke ya ƙara so, gaishe da ita yayi, amsa mashi tayi cikin kulawa, tashi yayi da nufin barin parlor ammy ce ta ce"ina zaka je? " Shazim ya ce "zanje ne na watsa ruwa nayi shirin ta fiya yau zan tafi jos " ammy ta ce " ok ashe yau zaka tafi? "
"eh ammy" ya bata amsa, ammy ce ta sake magana tana faɗin "to dawo ina son magana da kai " to kawai yace haɗi da dawowa ya samu wuri ya zauna, ammy ce ta fara magana tana faɗin "wai ni kam shazim mike da munka ne kai da ƙannan ka.? " ɗago da kansa yayi yana faɗin "bakomai ammy, mikika gani ne.? "
"ba komai, kawai dai naga nayi maku maganar zuwa abuja amma babu wanda ya sake ce man komai akan tafiyar, Noraiz ma da na tambayeta shi ceman yayi ya manta " ajiyar zuciya Shazim ya sauke sannan yace "ba komai ammy, ni aiki ne ya sha kaina shiyyasa " ammy tace "to yanzu bangane mikake nufi ba?" shazim ya ce "ammy ina ganin sai dai kawai fatima da noraiz su tafi, tun da ni jos zani kuma na faɗa maki, da ace zan iya zuwa ranar na dawo to da kawai sai na kai su ni sai na dawo " wani kallo ammy ta bishi da shi har ya gama faɗan abun da zai faɗa sannan ta ce "yanzu dai mi kake nufi ba zaka je ba ko kuma dai wani abun kake nufi??? "
"A'a ammy da na dawo zanje insha Allah " ammy ta ce "maganar sai ka dawo jos bama ta taso ba, yanda su fatima zasu je haka kaima zaka je,kai ka ɗai ne likita da baza su ne mi wani ba, in kuma maganar aikin ka kake nasan kafin kaje ka dawo hameed zai ji da komai na abnoor har ka dawo, in kuma eko ne da ka ɗauki permission nasan zasu baka, kuma duk abund a ya kamata ace kayi ai kabir na nan" kallon ammy kawai shazim yake, dan shifa har zuciyar shi baya son wannan tafiyar, shiyyasa ma ya kawo mata excuse ɗin zuwa jos dan kawai ta cire shi cikin masu tafiyar, amma daga ganin yanda take magana yama san bazata haƙura ba, katse mashi tuna nin ammy tayi da cewa "sai wani kallona kake kana tunani, tafiya ce dai dole kayita shazim" ajiyar zuciya ya sake saukewa yana faɗin "ammy bawai bana son zuwa bane,a kullum ke kike faɗaman ka taimaki mai ne man tai mako da gwar gwadan abun da Allah ya hure maka, ammy yau ke kike cewa su ne mi wani, dan Allah ki bari naje in dai abuja ne zanje idan ma kikace na wuce daga jos ɗin sai na wuce amma dan Allah karki hanani yin wannan taimakon"
"babu wani excuse fa da zaka kawo man, nariga da nagama magana, garama kawai kayi shiru dan bazan saurari excuse ɗin ka ba"
"shikenan ammy kwana nawa kike so muyi"
"sati biyu nake son kuyi sannan ku dawo" ɗago kai shazim yayi da sauri yana kallon ammy jin tace sati biyu zasu yi"haba ammy ina laifin kwana biyar"
"sati biyu fa zaku yi kaji na faɗa maka"
"dan Allah ammy kiyi haƙuri, ki maida shi kwana biyar"
"to naji sai dai kai kayi biyar ɗin, ammy fatima da noraiz sai sunyi sati biyu cif sannan su dawo" ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ce "ammy ina dai laifin ita fatima tayi sati biyun"
"bangane ba shifa noraiz mizai sa bazai sati biyun ba? "
"Ammy kinga nace shi zai cigaba da kula da business ɗina ai kinga bai kamata ace yayi sati biyu ba"
"ban amince ba to, ina masu kula da business ɗin time ɗin da yake makaranta"
"suna nan ammy"
"to su cigaba da kula da shi kafin su dawo"miƙewa shazim yayi yana faɗin "to shikenan ammy, nizan shiga na shirya time yana ƙurewa" da to ammy ta bisa har zai wuce, tace "idan kaje jos ɗin kwana nawa za kayi?" murmushi yayi dan dama ya san bazata taɓa hana shi taimako ba,ba tare da ya juyo ba yace "dama kwana biyar zanyi, amma tun da kince ba sai naje ba zan tura majeed yaje kawai"
"to na fasa kaje ka dawo sai ku tafi" murmushi yayi yana cewa
"A'a ammy ki bari kawai majeed ɗin yaje"
"kaci gidan ku nace kaje zaka wani ce man majeed yaje bayan nasan kana son zuwa"murmushi yayi mai ɗan sauti yana faɗin"to shikenan "haɗi da wai go wa ya dawo kusa da ammyn yana ƙara faɗin "nagode sosai ammy na "dun gure mashi kai tayi tana faɗin"ni kake ma dariya ko, dan kasan dama bazan taɓa hanaka zuwa ba ko"
"a'a ammy ba da ke nake ba"
"to shikenan, tashi kaje ka shirya kar lokaci ya ƙure"da to ya amsa haɗi da miƙewa ya haye sama , fitowa fatima tayi daga bedroom ɗin ammy, wurin da ammy take kan sofa ta zauna tana faɗin "na kammala jera kayan ammy" ammy ta ce "masha Allah, Allah ya biyaki"
"Ameen ammy" fatima ta ce, innah asabe ce ta shigo parlorn gaisawa suka yi ita da ammy sannan take cewa "hajiya an kammala karin kumallon "
"Masha Allah sannu da ƙoƙari, Allah ya saka "
"Ameen hajiya "innah asabe ta amsa sun nan suna ɗan taɓa fira shazim ya sauko shi da noraiz, gaishe da ammy noraiz yayi danshi shazim sun gaisa tun ɗazu,sannan suka gaishe da innah asabe, sannan suka tashi suka nufi dinning, shazim da norai basu wani jima ba suka miƙe shazim na ma su ammy ban kwana sai ya dawo sai sun dawo, adawo lafiya ammy da fatima suka yi mashi, suna fita parking lot suka nufa, mota suka shiga noraiz ke driving, suna tafe suna fira har suka kawo airport, sai da jirgin shazim ya ta shi noraiz yabar airport ɗin ya wuce abnoor wurin majeed, acan ya wuni sai da yamma ya koma gida.
kamar yan da shazim yace kwanan shi biyar ya dawo daga jos, san da ya dawo har ammy tasa fatima ta shirya kayan ta.


Wannan kenan.


sauko wa yake jikinsa sanye da jeans da t_shirt, wurin ammy ya nufo dake zaune kan sofa, gaishe da ita yayi, cikin kulawa ta amsa mashi tana tambayar "yau batare zasu fita da noraiz ne ba "
"tare zamu fita yana shiryawa ne "ko rufe baki bai yi ba sai ga noraiz ɗin ya sauko cikin sauri yana faɗin"yaya na shirya, ina kwana ammy"
"lafiya lau "ammy ta amsa, tashi suka yi suka fice suna cewa sai mun dawo, adawo lafiya ammy tayi masu,fi cewa su ka yi zuwa parking lot,
wata sabuwar mota suka nufa suka shiga, shazim na driving, noraiz na kusa da shi,buɗe masu gate mai gadi yayi suka fice,
sai da suka kawo kwanar da zata kaisu eko shazim ya cema noraiz "yaushe zaka fara kula da business ɗin" Noraiz ya ce "yaya duk sanda kace na fara, sai na fara " shazim ya ce "to shikenan, idan nagama kammala tsara komai zanyi maka magana sai ka fara"
"to shikenan yaya, Allah ya kaimu " da ameen shazim ya amsa yayin da ya ke shiga cikin eko ɗin, parking lot ya nufa, yayi parking,sannan ya fito suka shiga ciki, yana gaba Noraiz na biye da shi, har suka kawo office ɗin Shazim bu ɗewa yayi suka shiga ciki, wuri noraiz ya sumu kan sofa a office ɗin ya zauna, shi kuwa Shazim wurin zaman shi ya nufa ya zauna, ba ɓata lokaci ya fara aiki, nocking ɗin kofar office ɗin aka yi , izini shazim ya bada , hidaya ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama, amsa mata sallamar suka yi, gaishe da su ta yi sannan ta ɗaura da cewa "doctor patient zasu iya fara shigowa kai kawai shazim ya ɗaga mata alamar eh yayin da ya ke mayar da kansa kan laptop ɗinsa dake gaban sa ya cigaba da aikin da yake yi , ok ta ce haɗi da ficewa daga office ɗin....

KATSINA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login