Showing 6001 words to 9000 words out of 133697 words

Chapter 3 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt

hidaya ta tare maki a hospital ɗinnan,ai ko bakomi ƴar uwarki ce tawurin aiki, amma ace kullum baki da abokiyar faɗa sai Ita"
karka faɗa man mgnr banza mana Joseph ina ruwanka"
"sorry shawara ce" barin wurin yayi wanda akakira da Joseph
"mike faruwa ne anan cewar destiny wacce isowarta kenan, a'a hidaya Victoria bata faɗa maki dr nakira ba nagan ki zaune ko har kin dawo daga wurin shi
"A'a destiny yanzu zanje, ok destiny ta faɗa haɗi dacewa kefa Victoria naga kinyi tsaye kutafi mana bin bayan hidaya destiny da Victoria sukayi suna ɗan yin nisa da sauran nurse's ɗin destiny ta ɗan taba Victoria alamar ta roki hidaya akan ta taya ta ba dr haƙuri ganin baza tayi ba yasa destiny dakatar da hidaya haɗi da cewa "kiyi hakuri hidaya akan abun da Victoria tayi maki haushin dariyar da kuka yi matane ɗazu, amma kiyi hakuri" "shikenan bakomi, ni da man bawani riƙe taba" "shikenan amma ki taya ta ba ma dr hakuri pls karya cireta daga cikin nurses ɗin dake tura mashi patient pls, a ranta take faɗan"ok shiyyasa kenan tazo ta ciman mutun ci"amma a zahiri sai tace "bkm yawuce insha Allah zan taya ta" thanks Victoria ta faɗa yayin da suka kawo office ɗin shiga ciki sukayi sallama hidaya tayi yayin da Victoria ke bayan ta, dr gani hidaya ta faɗa, ok a saka patient a layi amma mutum 15 kawai zan duba sauran kiturasu office ɗin DR KABIR, sorry sir ni ina iya tura su a cewar Victoria data ga yayi kamar bai san tana wurin ba, as from today this is the last time dazaki Kara zuwa office ɗin na I hope you understand, a fuwan sir kayi mata haƙuri bazata ƙara ba hidaya ta faɗa gaban ta na faɗuwa tsoron kar itama ya koreta, nagama magana get out
ƙasa Victoria tayi akan gwiwo winta tana ci gaba da bashi haƙuri harda kuka, I said get out from my office ya faɗa da tsawa yana nuna mata hanyar fita, fita tayi tana kuka kamar ranta zai fita ,kema zaki iya tafiya" Ok sir hidaya ta faɗa fita itama tayi " wajen office ɗin ta samu Victoria da destiny suna ganin ta suka nufe ta rokonta suka shigayi a kan ta taya victoria ba ma dr haƙuri " shikenan insha Allah zan taya ta kar ku damu hidaya ta faɗa hadi da sharema Victoria hawayen dake fuskarta ta cigaba da kwantar mata da hankali godiya sukayi mata sannan suka koma office ɗin da suke zama ita kuma ta wuce wurin patient domin tura ma dr su .
haka ya cigaba da ganin patient shikuma wannan dattijon ruwan da aka sa mashi na ƙarewa yasa driver ya mai dashi ABNOOR aka bashi gado , bashi ne ya bar EKO ba sai wurin 12:30 sannan ya wuce ABNOOR nan ma yaga patient dayawa saboda da nan yafi jimawa a nan a kan eko , abnoor hospital ɗin sane halak malak Ita kuma eko aiki yake a chan, sau biyu yake zuwa eko a sati idan yana lagos saboda yana visiting wasu Hospital ɗin , kuma in yaje 2 to 3 hours yake yi yaje abnoor , amma standard in da yafi zama abnoor ne saboda chan har ranar Saturday yana zuwa in yana lagos ,sai wurin 6:00 ya tashi daga aiki dan har an fara kiraye kirayen sallar magrib masallacin hospital ɗin ya nufa domin gabatar da sallah sai bayan angama tukkun nan yanu fi gida,


horn yayi a bakin wani katafaren gida naji da faɗa dake Victorian Ice land , gida ne har gida wanda daga gani ba sai an faɗa maka ba kasan cewa an narkar da kuɗi, me gadine ya bude masa gate, ciki ya shiga ya nufi parking lot da ke chan cikin gidan,ɗakin mai gadine farko daka shigo gidan sai boys quarters daga chan gaba sai kayi ƴar tafiya sannan zaka iso part ɗin masu gidan sai parking lot dake gefe sai wani katon garden dake bayan part ɗin masu gidan hade da Wani katon swimming pool me kyen gaske,ride's ne gasunan kala kala a kallah zasu kai 6 a parking lot ɗin , parking yayi cikin gidan ya nufa tura ƙofar shiga part ɗin yayi bakinsa ɗauke da sallama,parlor ne me kyan gaske komai na cikin sa ya kasan ce golden and white color ne royal sofas ne masu kyan gaske set biyu sai wani ƙaton dining table mai chairs kusan guda 10 , sai wasu bedroom guda 3 dake hannun dama sai kitchen da store atare, wani corridor ya nufa inda yana shiga nan ma wani madaidaicin parlorn me dauke da sofa a set 1 komai na cikin sa golden color ne sai dining mai dauke da chairs guda 5 sai two bedroom, daya daga cikin su ya nufa bakinsa ɗauke da sallama, wata kyakyawar mace ce zaune a kan sallaya itama farace sosai suna Kama da dr banbanchi Ita mace ce shikuma namiji zata yi kimanin shekara 50 , sanye take da hijab hannun ta reke da chasbaha tana ja , da a lama sallah ta gama, sallamar da yayi ta amsa mashi yayin da yake ƙarasa wa inda take zaune wuri ya nema ya zauna "an wuni lafiya ammy, ya gida"ya faɗa , amsa mashi tayi da" lafiya qlu Alhmdllh ya aiki ya fama da patient, alhmdllh ammy, Masha Allah ta faɗa haɗi da cewa katashi ka shiga ciki domin kasamu ka huta zansa fatima ta kawo maka dinner ɗinka , dama shi ba ma'a bocin cin abinci a dinning bane, to shikenan ammy bari na wuce ciki, fito wa yayi daga bedroom ɗin yanu stairs dake parlor wani part ya shiga wanda da alama nasa ne tura ƙofar yayi haɗi dayin sallama, ya kutsa kai ciki parlor ne shima ma dai dai ci me kyan gaske komai nacikin sa ash and black ne bedroom ya nufa wanda shima bedroom ɗin kayan cikin sa ash ne hattada furnitures ɗin ciki ash ne ɗan corridor ya nufa cloth set ne sai gefe laundry basket, kayan jikin sa ya shiga ragewa ya koma daga shi sai boxer bathroom yanu fa domin watsa ruwa after 15 minutes ya fito jikin sa sanye da bathrobe wurin clothes set ɗinsa ya nufa jallabiya ya saka ajikin sa bathroom yakoma domin ɗauro alwallah sbd time ɗin sallah isha yayi masallachin gidan ya nufa dan gabatarda sallah anagama sallah part ɗin sa ya koma a parlor ya zauna kan sofa bai jima da zama ba yaji ana nocking tambaya yayi waye ne " fatima " ce Yaya ok shigo ya faɗa , turo ƙofar tayi tashigo bakinta ɗauke da sallama kyakyawar matashiya ce akalla zatayi kima nin shekara 18_19 fara ce itama tana kamada ammyn su amma ba sosaiba dr dai shine ke kama da Ita sosai " ina wuni Yaya andawo lafiya, lafiya qlu , dama ammy ce tace nakawo maka dinner ɗin ka, ok ajiye kan table, ajiye mashi tayi haɗi dafita jawo table din yayi , serving ɗin kanshi yashiga yi, yana kammala cin abincin bedroom ɗinsa ya koma laptop dinsa ya jawo dake kan bedside aiki yashiga yi.....


KATSINA....


Su Aaimah ne zaune a falon mom suna kallo, sanye suke da pajamas sky blue, mom ce tafito daga bedroom ɗin ta, ita ma sanye take da pajamas purple color, waya ce a kunnan ta da alama waya take wuri tasamu kan sofa ta zauna tana cigaba da wayar " mom abie ne Aaimah ta faɗa yayin da take matsowa kusa da mom, daga mata kai mom tayi alamar eh" mom dan Allah kice muna gaishe shi munkira shi bai ɗauka ba, to kaji Wai twins ɗinka nagaishe da kai wai sunkiraka baka ɗauka ba mom ta faɗa , mika ma Aaimah wayar tayi da a lama cewa yayi a basu wayar, amsa tayi haɗi da cewa" inawuni abie ya Abuja, ya kuma aiki " on the other hand abie yace" lafiya qlu Alhmdllh ya gida ya kuma school " Alhmdllh abie ta bashi amsa, abie ko kace ina nake Aaimah ka ɗai kasani" Aairah ce ke mgn wacce ƙara sowarta kenan "afuwan yanzu zance kina ina sai kuma gaki ya gida ya schll" Alhmdllh abie yaushe zaka dawo, jibi insha Allah zan dawo " to Allah ya kaimu abie , ameen ya faɗa sun jima suna waya sannan suka yi sallam, bedroom ɗinsu suka nufa domin bacci dan mom ta daɗe dashige wa nata bedroom ɗin ....


Episode 5_6


_FRIDAY......._


sauko wa yake daga stairs jikin sa sanye da baƙaƙen coat hannun sa riƙe da briefcase , ammy ce zaune kan sofa ƙaraso wa yayi kusa da ita " Ina kwana Ammy ina fatan kintashi lafiya " ya fada yayin da yake samu wuri kusa da Ammy ya zauna " lafiya lau Shazim har kafito," eh ammy ya bata amsa," ga breakfast din ka nan kan dinning" "to,ammy kinkuwa yi waya da NORAIZ "( kanin sa mai bimasa yayan fatima dayake baya nan yana kasar portland yana masters akan business ) ya fada yayin da yake nufar dinning "eh naji yace yana nan zuwa ranar sunday ( lahadi ) , ammy ta fada " eh ammy haka yake fada man jiya, "to Allah ya kaimu lafiya" Jiya uncle ɗin ku ya kirani, yace kai ka ɗai suke jira" shiru yayi baice komai ba sai da ammy ta sake cewa "da kai fa nake magana, ni ban san mikake nufi ba , da anyi magana sai kayi shiru, tun yaushe ake abu ɗaya sai yawo kake ma mutane da hankali"
"kiyi haƙuri ammy, wlh ban gama abun da nake ba, kuma nifa bani da wata wacce zance ina so, nafi son su barin harsai na samu wacce nake so"
"to bari kaji na faɗa maka ni ba ruwana daga yanzu bazan sake shiga maganar ba duk hukuncin da suka yanke akan ka babu ruwana "shazim yace "dan Allah ammy karkice haka idan kika zare hannunki innah zata iya zuga su su yanke man hukuncin da duk sukaga dama"
"to idan har baka son haka tafaru to dole sai ka nema ma kanka masalaha" "insha Allah ammy"
"to Allah ya yarda, ameen ammy ".


fatima ce ta fito daga bedroom dinta dake kusa da na Ammy jikinta sanye da uniform , dinning ta nufo Ita ma domin breakfast
" Ina kwana Yaya dafatan antashi lafiya " lafiya qlu ya bata Amsa, yana gama breakfast ya mike hadi da daukar briefcase din shi " Ammy ni zan wuce, to a dawo lafiya Allah ya bada sa'a, ameen Ammy fita yayi zuwa parking lot, gaisawa ya tsaya yi da masu aikin gidan tun daga kan maibama flower ruwa Har izuwa kan maigadi sannan ya fuce daga gidan, ABNOOR ya nufa domin yau baya zuwa EKO.


ABDULƘADIR ABUBAKAR NURADDEEN PRIVATE HOSPITAL ( ABNOOR ).


Direct office din sa ya nufa briefcase din sa ya aje akan table zama yayi hadi da bude laptop dinsa Aiki yafara kafin time din daya ke duba patient yayi. sallama a kayi hadi da turo kofar wani matashin saurayi ne wanda zasu yi sa'anni da shazim din.


Amsa mashi sallama yayi, shigowa yayi daga ciki hadi da mikama shazim din hannu suka yi musa baha , sannan ya zauna kan kujerar dake gaban table din " shazim amma yanzu ka shigo ko dan nazo baka nan, eh shigowata kenan nakama aiki , ai ku manya ne agogo sarkin aiki, haka dai kake gani majeed karfin haline kawai, wlh kuwa ai kana kokari, to ya za'ayi, dole a nema"
"hakane dama maganar kayan da suka kusa ƙarewa ne"
"kai ai kuwa gara daka tuna man dan har na manta, zanyi magana da su yau insha Allah "
"to shikenan nibari nakoma office"
"to shikenan nima yanzu zanje duba patient insha Allah sbd da time din sallah nayi zan tashi sai kuma gobe Idan Allah ya kaimu, ameen majeed ya fada hadi da barin office din shima baijima ba ya fita dakin marasa lafiya nufa sai 12:10 sannan ya dawo office yana shiga bawani jimawa yayi ba ya hada kan kayansa ya fito direct gida ya nufa bedroom din ammy ya fara zuwa gaisawa kawai sukayi ya nufi part din sa bedroom din sa ya nufa kayan jikin sa ya shiga ragewa ya nufi bathroom after 10 minutes ya fito kugunsa daure da towel dressin mirror ya nufa mai ya shafa mai dankaran kamshi, comb yasa ya shiga combing din kansa sannan ya shafesa da man aloe da hair spray clothes set dinsa ya nufa shaf shaf ya shirya cikin wata shadda ƴar ubansu milk color ba karamin b
kyau yayi ba sannan ya dauko hula ya daura brown color, feshe jikin sa yayi da turare mai ƙamshi,sannan ya nufi shoe rag dinsa takalmi ya dauko me kyan gaske shima brown color. masha ALLAH kawai zamuce dan ba karamin kyau yayi ba wayoyin sa dake bedside ya dauka fita yayi daga bedroom din yana zuba kamshi, ya nufi down stairs parlorn ammy zaune ya sameta tana karatun Al'qur'an tana kai aya tace " sai masallaci kenan, eh ammy ya bata amsa , to shikenan a dawo lpy nima zanje gida domin na ƙasa duba jikin baba , to saikin dawo Allah ya bashi lfy nima insha Allah yanzu daga masallachi zan biya na gaishe shi saina dawo ya fada hadi da kama hanyar fita Ammy nacewa a dawo lpy , da innah asabe ya cikaro ( mai Aikin su) zata shiga wurin Ammy, gaishe da Ita yayi ta amsa mashi da " Lafiya lau Shazim har za'a tafi masallachi kenan, eh ya bata amsa hadida fice wa daga falon ya nufi parking lot mota yashiga mai gadi ya bude masa gate ya fuce.........


_KATSINA......._


AIRAH
Zaune take bakin gado jikinta daure da towel da alama wanka zatayi .
"sister gaskiya kiyi sauri kifito nima nayi wanka kinsan yau abie zai dawo kuma mom tace muje gidan granny mu gaishe ta har so nake muje gidan aunty safiya ( kanwar MOm wacce suke uwa daya uba daya) mun kwana biyu ba muje ba "Aairah ta fada.
fitowa Aaimah tayi daga bathroom jikinta daure da towel " bawani sis zaki ziyara ne kodai zakije ganin ya MUS'AF dan nasan halinki sarai, Amma wlh Aaimah kin bani da sharri yau she nace maki saboda shi zanje gidan ni dai ziyara zani bawai saboda ya mus'af , dan wlh ki bari karki jaman ya usman yaji wannan maganar , ai kuwa saina fada masa ince bakiji gargadin da yayi maki ba, ni wlh har mamaki kike bani kirasa dawa zakiyi soyayya sai ya mus'af harka duk ta yarin ta, eh naji matar babban mutum sai mi koda ace na girmi ya mus'af ina ruwan ki Aairah ta fada tana huro hanchi, Allah ya baki hakuri Aairah ni nayi nan Aaimah ta fada hadi da nufar dressing mirror bathroom Aairah ta nufa shaf shaf Aaimah ta shirya cikin atamfa super Red color ɗinkin riga da skirt tana nan tsaye tana fesa turare Aairah ta fito sai bata rai take shiryawa itama tayi cikin atamfa color daya data Aaimah tana gamawa ba tai ma Aaimah magana ba taka ma hanyar fita daga bedroom din, murmushi Aaimah tayi hadi dacewa " ki nafa iya cewa kinji haushi, bata bata amsa ba sai tsaki data ja, haba twin sis kiyi hakuri bazan sake ba kinji ta ya mus'af sorry pls Aaimah tafada hadi da matsowa kusa da Aairah sake bata hakuri tayi tare da cewa haba abun gidan ya mus'af kiyi dariya mana dan Allah tafa da yayin da take langwabar da kai, murmushi kawai tayi hadi da cewa wallahi Aaimah ki daina kushe man ya mus'af Indai kina so mu zauna lafiya da ke, kaina bisa wuya na daina insha Allah Aaimah ta fada hadi dajan hannun Aairah suka fita bedroom din mom suka nufa samun ta sukayi zaune gaban dressing mirror tana saka sarka a wuyan ta sanye take da wani hadaden less brown color ta sha daurin ture kaga tsiya hannunta ya sha dan hannu da zobe na gold kalar sarkarta, har suna hada baki wurin fadin masha Allah , Aaimah ce ta ce "kice yau an tashi rikita mana abie kenan , wannan kwaliyya haka mom ai sai ya ka sa gane ki yayi tuna nin sabuwar amarya aka kawo masa, Aairah tayi charab tace ba kiga harda ture kaga tsiya ba, lallai duk wanda ya ture ya taro match ba yan ball, murmushi kawai mom tayi hadi da cewa kun rainani ko, na lura ni kuka maida granny da dadi, Aa wane mu kawai dai munga kin hadu kar abie ya riki ce, ALLAH ya shirya ku mom ta fada ameen suka amsa, Aairah tace daman mom daga gidan granny zamu wuce gidan aunty safiya dan Allah, shikenan Idan kunje kuce ina gaishe ta , to shikenan mom zataji Insha Allah amma sai abie ya shigo sannan zamu tafi , to shikenan mom ta fada..


Ya usman ne ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login