Showing 105001 words to 108000 words out of 133697 words
Chapter 36 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt
daga baya mansoor ya ce mizai hana su dunga tafiya tare, amincewa shazim yayi suna tafiya tare, ta dalilin haka shaƙuwa sosai ta shiga tsakanin su kowane lokaci suna tare da juna ko a school ko a gida, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma uncle's ɗin shi ba dan dama burin su yaran su haɗe kan su, innah ce kwata kwata hakan bai mata daɗi ba dan ba haka taso ba, har kiran mansoor tayi tana mashi faɗa dan mi zai shige ma shazim, shazim ɗin ba ba son su yake ba san da suna yara, shikuma ya ce mata ko ada laifin su ne , su suka nuna ba su son shi shiyyasa shima ya nuna bai son su, ba ƙaramin haushi maganar mansoor ta ba innah ba hakan yasa ta ƙara jin ta tsani shazim musamman ma yan da yayi fatali da ita a estate ɗin, dan sai ayi sati bata sa shi a ido ba kuma kullum sai mansoor ya zo gaishe da ita da safe amma bata taɓa ganin shazim ba, ƙarar shi ta kai wurin uncle ahmad akan bai zuwa yana gai she ta, kiran shi uncle ahmad yayi yayi mashi faɗa da nuna mashi hakan bai dace ba, haƙuri ya bashi ya kuma yi alƙawarin gyarawa, tun daga ranar kullum da safe idan mansoor zai je gaishe da ita tare suke zuwa, kullum kuma yaje gaishe da ita ta rinƙa faɗa mashi baƙaƙen maganganu, in tana yi yi yake kamar ma bai san mitake yi ba, hakan kuwa ba ƙaramin haushi yake bata ba, sai daga baya daya lura abun nata ba mai ƙarewa bane yasa intace mashi a to sai ya kai mata har z, bata yi mamaki ba tun da daman tasan halin shi tun yana yaro ba ragamata yake ba, wata rana suna dawowa daga makaranta mansoor ya ce suje su gaishe da ita ko da suka je gaishe da ita basu same ta ba tana part ɗin uncle Ibrahim sai su feenah da kairiyya suka samu a part ɗin suna kallo, gaishe da su kairiyya tayi amma feenah mansoor ka ɗai ta gai da, dama tun da shazim ya zo kowa na gaishe shi amma ban da ita, lura da bata gaishe da shi bane yasa mansoor rufe ta da faɗa maimakon ta gaishe shi sai tashi tayi tafice tana ƙunƙunai, a kwai wata rana da uncle Ibrahim ya kira shazim part ɗin shi daya je part ɗin ba kowa a parlor sai ita kaɗai da yayi sallama ta ƙi amsawa sai ma ɗago da kai tayi ta kalle shi ta kauda kai tana jan tsaki , abun yayi matuƙar bata ran shi ya tsani rainin wayau da rashin kunya hakan yasa ya ɗauke ta da mari har sau biyu har sai da ta duƙe saboda zafin da taji ai kuwa ba shiri ta nufi ɗakin momyn ta tana kuka, da ta shiga ko da ta sanar da momyn ta taso ƙeyarta tayi har parlorn ta bashi haƙuri, dole ta bashi haƙuri tun da ga ranar kuwa ta dai na yi mashi koda kallon banza bare aje ga tsaki.
Lokacin da su shazim su kayi hutu da zai tafi lagos tare suka tafi da mansoor har hutun su ya ƙare suka dawo, haka rayuwa ta cigaba da tafiya shaƙuwa ce sosai tsakanin shazim da A hashim dan A hashim yana yawan zuwa lagos wurin shazim hakan ne yasa kowa ya sanshi tare da shazim musamman fatima ba ƙaramin son a hashim take ba idan ya zo lagos to tana nan maƙale da shi, tun wata rana da noraiz ya ji ciwo yayi mashi alura shine ta tambaye shi daman ya iya alura kamar ya shazim sai yace mata eh ai su dr ne tunga ranar ne ta sa mashi suna ya dr.
Cikin ikwan Allah sun kammala degree zasu joining masters,maganar aure su uncle ahmad suka yi masu amma sai suka ce su ba yanzu ba sai sun kammala masters sun fara aiki tukunnan, ko da suka ce haka su uncle ahmad sunyi na'am da hakan, tunga time ɗin basu sake masu maganar auren ba sun barashi a sai sun fara aikin,business malam yace shazim ya fara kafin su fara masters, da zai fara malam ya bashi jali, cikin ikwan Allah san da zasu tafi business ya haɓaka Allah ya sa ma abun albarka,da zasu tafi malam ya samo wani yaro mai gaskiya da ruƙwan amana ya ɗaura shi akan business ɗin kafin shazim ɗin ya kammala karatu,cikin ƙanƙanin lokaci business ɗin ya ƙara haɓaka,saboda yaron na kula da business ɗin shazim cikin aminci ga gaskiya da ruƙwan amana,
lokacin da suka kammala master business ɗin shazim ya haɓaka sosai dan malam na kula da komai ga kuma hameed hakan yasa business ɗin haɓaka.
lokacin da suka kammala masters lokacin su noraiz shi da mahmud da luqman suna aji biyu a jami'a.
Basu jima da kammala masters ba suka samu aiki su duka,har da a hashim, uncle Ibrahim ya so shazim yayi aiki a abuja amma yace ya fi son lagos saboda business ɗin daya ke hakan yasa uncle Ibrahim haƙura,shazim yana aiki awata babbar asibiti dake garin lagos, haka rayuwa ta cigaba da tafiya shazim yana aiki hameed na kula mashi da business,yanke shawarar yin phd yayi, ko da ya sanar da uncles ɗin shi da malam goya mashi baya su kayi ,amma sai malam ya bashi shawarar yin phd ɗin ta online, sosai hakan yayi mashi daɗi ko ba komi zai samu ya dunga zuwa aiki wani lokacin yana kuma kula da business ɗin shi,cikin ikwan Allah yana kula da aikin shi da business ɗin shi ya kammala phd,ƙarin girma ya samu a wurin aikin shi bayan nan kuma yana visiting wasu hospital ɗin,ganin komai na tafiyar mashi dai dai yasa ya yanke shawarar buɗe privet hopital, daya samu malam da maganar , goya mashi baya malam yayi ya kuma tai maka mashi da wani abun wurin gina hospital ɗin, cikin ikwan Allah aka gama gina hospital ɗin , ammy ma ta tai maka mashi da wani abun da zai zuba kayan aiki, sosai yaji daɗi ya kuma yi ma ammy godiya,kayan aiki masu inganci ya zuba, sai da komi ya kammala sannan ya ɗauki ma'ikata,ya kuma ɗaura wani abokin shi mai suna majeed wan da su kayi islamiya ɗaya,da yake iyayen shi talakawa ne masu rufin asiri, kuma da man yayi karatu a harkar lafiya hakan yasa shazim ya ɗauke shi aiki ya kuma ɗaura shi a matsiyin babba mai kula da harkokin Hospital ɗin idan baya nan ko yana wurin aiki...........
_Episode 54_55_
........ Uncle Ibrahim da uncle ahmad tasa shazim da mansoor gaba suka yi akan su fito da mata suyi aure, amma sai su kace ba yan zu ba, faɗa suka yi masu sosai suka kuma ce sun basu nan da wata huɗu ko dai su fito da mata ko kuma su zaɓa masu da kansu
ganin haka ne yasa mansoor ya gabatar da wacce yake so amma shazim shiru ta business ɗin shi kawai yake dan ya ma manta da wata magana ta aure,ganin mansoor ya gabatar da wacce yake so amma shazim shiru yasa uncle Ibrahim shiryawa yaje har lagos ya samu malam da batun, ya kuma sanar da shi sun yanke shawara kodai ya fito da mata yayi aure ko kuma su aura mashi duk wacce suka ga dama, malam bai ba da goyan baya ba akan hukuncin da suka yanke yace su bar shi da shazim ɗin shi da kansa zai sa ya fito da matar , kwata kwata ba haka uncle Ibrahim ya so ba yaso ace malam ya goyi da bayan su, ba dan ya so ba ya amince ya koma abuja, koda ya koma ya sanar da uncle ahmad yan da suka yi da malam faɗa ya kama yana cewa kenan malam ke goya mashi baya shiyyasa da suka yi mashi magana yayi kunnen uwarshegu da su, ya kuma yanke hukuncin dole tare za su yi mashi aure shi da mansoor da su feenah dake shirin kammala makaranta, {su noraiz sun gama masters kawai suke jira} ko yana so ko baya so, sosai uncle Ibrahim da innah suka amince da hukuncin da uncle ahmad ya yanke, uncle ahmad da kan shi yakira malam ya sanar da shi cewa sun ƙarama shazim ɗin wata biyu kacal ko dai ya fito da mata kokuma su aura mashi duk wacce ransu ya so,abun yayi matuƙar ba malam mamaki yan da suka ɗau abun da zafi sosai har haka, shima yana so yaga shazim ɗin yayi aure amma ya fiso abi komi a sannu gudun dana sani.
Ammy da ummy malam ya kira ya sanar da su abun da uncle ahmad ya ce, suma basu ji daɗin hukuncin da suka yanke da zafi haka ba,suma babu abun da suke buri sama da shazim ɗin yayi aure.
Kiran shazim malam yayi ya sanar da shi hukuncin da uncle ahmad ya yanke,sannan yace mashi komi yake ya fito da mata suma sun fi son yayi auren tunda dai dai dai gwargwado Allah ya bashi rufin asiri, to sai ya gode ma Allah shima yayi aure ya tara iyali, cewa yayi insha zaiyi ƙoƙari ganin ya fitar da mata yayi auren, malam yaji daɗi da ya amince zai yi auren ya kuma yi mashi adu'a Allah ya zaɓa mashi mata tagari.
Tun ranar da su kayi magana da malam har tsawan wata biyu shazim bai kawo matar ba bai kuma sake maganar ba, tun su uncle ahmad nasa idon ya zo yace ga wacce yake so har suka gaji,su kai fushin har suka gaji ganin wanda suke yi dan shi yayi kamar ma bai san suna yi ba,gajiya malam yayi da shirun nashi ya sake mashi maganar, ko da yayi mashi maganar sai cewa yayi gini yake yanzu so yake sai ya kammala tukunnan,malam yace to ya kamata ya kira su uncle ahmad ya sanar da su, da to ya amsa, ya kuma kira su ya sanar da su, balbale shi da faɗa uncle ahmad yayi dan mi bazai sanar da su ba tuntuni sai yan zu da lokacin da suka bashi ya ƙare, haƙuri ya bashi ya kuma sanar da shi ya kusa kammala gini ai saura ka ɗan , jin yace hakane yasa uncle ahmad haƙura ya ƙara mashi wasu wata uku, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma shazim ba dan shi kwata kwata bai shirya yin aure yan zu ba neman kuɗi kawai yasa a gaban shi,tun da uncle ahmad ya amince da maganar gini daya ce yana yi yasa ya fake da ginin har akayi shekara ɗaya bai kammala ba bai ce ga mata ba, sai da malam ya tasa shi gaba da faɗa sannan ya kammala,gida ne mai girman gaske kusan part uku ne gidan, kuma yana kammalawa yace su koma gidan da zama, malam cewa yayi sai dai shi da ammy da fatima su koma(da yake noraiz na makaranta shi da su mahmud) amma shi ba yanzu ba sai yayi aure sannan zasu dawo shi da ummy, ba yan da bai yi da malam ba amma ya ƙi amincewa dole tasa shazim haƙura suka koma shida su ammy duk da da farko da malam yace bazai koma ba ammy cewa itama tayi bazata koma ba sai tare da su malam amma sai malam yace ta koma suma sunan za su dawo.
_*CIGABAN LABARI*_
........ Aunty safiya ce tsaye bakin ƙofar parlorn mus'af tana nocking amma ba'a buɗe ba , ba kuma a bata izinin shiga ba, da dai ta gaji da tsayuwa ne yasa ta fara kiran sunan mus'af ɗin tana faɗin " wai lafiya kake ne? , ana nocking amma kayi shiru ka kuwa san ƙarfe nawa yanzu kowa na waje kai ka ɗai ake jira "
daga ciki mus'af yace " gani nan zuwa, ina gama shirya wasu kayan ne "
"amma kai ko anyi shiriritacce, yanzu da baka gama shirin ba kenan, yayi maka kyau, to kayi sauri ina nan ina jiran ka "
zaune yake bakin gado sai dialing number Aairah yake amma bata ɗaga wa ga umma dake bakin ƙofa tana faɗa mashi shi kaɗai su ke jira, ganin dai da gaske ba ɗagawa zata yi bane ya sa shi haƙura da kiran ya miƙe trollyn shi da ke bakin gadon ya ja haɗi da sanya wayar cikin aljihu, da kaga fuskar shi zaka tabbatar da cewa yana cikin damuwa kwata kwata ba walwala a fuskar shi duk dan saboda kiran Aairah da yayi bata picking, da ya fita tsaye ya samu ummah tana jiran shi ya fito, da kallo Aunty safiya ta bishi " wai mus'af mike damun ka ne, tafiyar ce baka son yi ko mi"
"a'a ummah "
"idan ba ita bace ba ka sonyi ba, ace tun last month kasan da wannan tafiyar amma ace har yau baka gama shirin da zaka yi ba "
"kiyi haƙuri na gama yanzu "
gaba tayi tana faɗin "ka taho mu wuce kowa na waje yana jiran ka "
bin bayan ta yayi, a compound su ka samu abba da su najma su kawai su ke jira, suna isowa wurin su ba ɓata lokaci kowa ya shiga mota su ka fice faga gidan zuwa airport, mus'af duk a takure Aairah ta ƙikiran shi, bini bini ya duba waya amma shiru har su ka kawo airport tun yana sa ran ganin kiran ta har ya fidda, parking su kayi a parking lot ɗin airport ɗin, fitowa su kayi su ka ɗunguma zuwa ciki, saura 25 minutes jirgin su ya tashi, zama su kayi kan chair's ɗin da aka tana da domin zama, mus'af gaba ɗaya ya kasa su kuni sai zuba idon ganin Aairah yake amma shiru har dai Abba da ummah su ka lura da halin da yake ciki, Abba yace " lafiya dai ko mus'af"
"lafiya lau Abba "
"A'a ba dai lau ba, ko a kwai wanda ka ke jiran zuwan shi ne " girgiza ma Abba kai yayi alamar a'a, har lokaci ya rage saura 15 minutes jirgin su ya tashi Aairah bata kira shi ba ba kuma ta zo ba, sai da ana saura 8 minutes sai ga su sun zo ita da Aaimah harda mom ya Abdallah ya kawo su, sunje gidan mai gadi yake sanar da su ai sun tafi airport ɗin tun ɗazu, shine fa su ka biyo bayan su, mus'af har wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke da yaga Aairah,da sauri ya nufe ta ganin mom da ya Abdallah ne yasa shi waskewa ya nufi mom ɗin, murmushi Aairah tayi dan ta san wurin ta ya nufo sai so yake su ƙeɓe domin suyi ban kwana amma Abdallah ya kasa ya tsare,sai dai kowannan su ya ƙura ɗan uwan shi ido ba yanda su ka iya dole su kai ban kwana kamar kowa,kowa da kewar ɗan uwan shi, jirin su na ta shi kowa ya nufi mota, mom bin su Aunty safiya tayi zata je gidan granny, da mom zata tafi Aaimah ba yan da bata yi ba akan tana son su bi mom gidan granny amma ya Abdallah ga hana, Aairah da man bata tanka ba dan ta mafi so su tafi gida,suna isa gida parking yayi a parking lot,yana gama parking ko kashe motar bai yi ba Aairah ta buɗe ta fice, bedroom ɗin su direct ta nufa,tana shiga ta faɗa kan bed fashewa tayi da wani kuka mai tsuma zuciya sai kace wacce akayi ma wani abu, a haka Aaimah ta shigo ta same ta, kallo ɗaya Aaimah tayi mata haɗi da taɓe baki tace " amma wallahi kin haɗa kanki da aiki, da man wannan cika da batsewar da kike yi a mota kuka ne kike ɓoyewa ashe, ah lallai sannun ki " banza Aairah tayi da ita sai ma ƙara sautin kukan ta da tayi, tun Aaimah nayi mata iya shege har dai ta koma lallashin ta " dan Allah Aairah kiyi haƙuri in dai ya mus'af ne zai dawo ki kwantar da hankalin ki, karatu kawai fa yaje ba wani abu ba " haka Aaimah tai ta lallashin ta har ta sa mu ta ɗan yi shiru sai sauke ajiyar zuciya take.
"ni banga abun da zai sa ki tashi hankalin ki ba Aairah, in dai ya mus'af ne zai dawo karatu ne ya tafi ba wani abu ba "
magana Aairah ta fara cikin muryar kuka
" ni fa ba tafiyar da yayi bace ta sani kuka ba "
"idan ba ita bace to minene ya saki kuka ana zaman lafiya?"
"ya Abdallah fa shi ya hana mu muyi ban kwana, ya tsare mu da idanuwa ni na rasa mi yasa baya son soyayyar mu ni da ya mus'af, shima abie baya goyan baya"
dafa kafaɗar ta Aaimah tayi "sister ba wai baya son soyayyar ku bane, kawai dai abun da nake tunani ya na ganin ƙanƙantar ku ne ku duka "
"amma idan haka ne miyasa mom da Aunty safiya da Abba basa gani sai shi da Abie kawai "
"to Allah ka ɗai ya san dalilin su, amma tabbas na san ba wani abu bane "
"Allah yasa haka, amma wallahi ina matuƙar ƙaunar ya mus'af ban san ya zanyi ba idan su abie su ka ƙi goya mam baya ba, ina son shi sosai "
"ki kwantar da hankalin ki insha Allah za su amince,amma kiyi ta adu'a Allah ya zaɓa maki abun da yafi zama alkairi, nima zan taya ki da adu'a "
Kwantar da kanta tayi saman kafaɗar Aaimah tace "Ameen sister nagode"
mangare mata kai Aaimah tayi haɗi da cewa tace" dama a kwai godiya tsaka nin mu "
murmushi Aairah tayi tana shafa inda Aaimah ta mangare ta " sorry my lovely twiny"
Aaimah tace " sister ni fa ko na ƙagara mu samu addimisson mutafi makaranta na gaji da