Showing 96001 words to 99000 words out of 133697 words

Chapter 33 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt

gama zaman makokin iya sadiq ya koma gidan mahaifin shi da zama, sadiq ya ga rayuwa, wahalar maijidda yake ci sosai ba kaɗan ba ita da uwani, saboda magaji tun da ya girma ya watsar da huɗubar mahaifiyar shi ya kama ɗan uwan shi ganin magaji yana son sadiq yanzu yasa halimatu ita ma take janshi a jiki dama shi Ibrahim baya da matsala tuna farko, uwani ce dai dama can ita bata da mutunci sak halin maijidda gare ta, sosai sadiq ke shan wahalar ta kai sai ayi rabon abinci a manta da shi sai dai halimatu da Ibrahim su bashi nasu a ɓoye dan idan maijidda ta sani dukan tsiya take masu shi daman magaji baya gidan yana kasuwa tare da mahaifin shi, haka rayuwar sadiq ta cigaba da tafiya kamar mara galihu mara gata, shi da gidan mahaifin shi amma bashi da sakewa sai in mahaifin shi da yayan shi magaji na gida, wata rana wani aminin nuraddeen alhaji abdulƙadir wanda suka taso tun ƙuruciya,lagos yake tun bayan rasuwar iyayen shi ya koma wurin ƙanin baban shi da zama acan yayi karatun shi ko da ƙanin mahaifin nashi ya rasu bai dawo kurfi ba a lagos ya cigaba da zama , du da yana lagos nuraddeen na kurfi tare suke harkar kasuwanci , sai dai shi alhaji abdulƙadir yana zuwa har ƙasashen waje ,alhaji abdulƙadir yafi nuraddeen ƙuɗi nesa ba kusa ba, matar shi ɗaya hajiya zainab balarabiyar ƙasar Morocco ce, sun haɗu ne a chan ƙasar har Allah yasa suka yi aure, shekarar su kusan goma amma basu da ɗa ko ɗaya, zainab tana haihuwa amma ƴaƴan basu zuwa da rai, ko da ya kawo ma nuraddeen ziyara bai nufi kasuwa ba gidan shi ya nufa direct , nan ya ci karo da sadiq bakin ƙofar gida yana kuka,dafa kafaɗar sadiq alhaji abdulƙadir yayi yana cewa "yaro yaya sunan ka? " cikin shashekar kuka sadiq yace "sunana sadiq "
"masha Allah, amma miyasa kake kuka, ina mahaifin ka? "sadiq ya ce
"bakomi, babana yana kasuwa"
"to ko zaka iya rakani wurin shi? " da to sadiq ya amsa mashi, har kasuwa ya raka shi wurin nuraddeen, sosai nuraddeen yayi farin ciki da ganin alhaji abdulƙadir dan sun ɗan dade basu haɗu ba, gida suka koma, nan suka shiga firar yaushe gamo, anan alhaji abdulƙadir ya nuna yana son ya tafi da sadiq logas ,ƙin amincewa nuraddeen yayi, saboda ba ƙaramin son sadiq yake ba baiso ko kaɗan yayi nesa dashi, ko da ya shiga gida fuskar shi da ɗan damuwa, tambayar shi maijidda tayi akan mike da munshi, nan yake faɗa mata "wallahi wani aminina ne yazo, to shine ya buƙaci da na bashi sadiq, to gaskiya gani nake kamar zai ƙara ma kan shi wahala ne, dan nafi shi rufin asiri ne sa ba kusa ba, to abunda ya sa ki gannin ciki da muwa ban so yaga kamar na hanashi sadiq ne saboda ni Allah ya bani , da yake shi bai da ɗa ko ɗaya " wani da ɗi ne ya rufe maijidda tana ganin wannan ce hanya mafi sauƙi da zata raba sadiq da nuraddeen, kuma da taji mutumin talaka ne abun ya ƙara mata daɗi sai dai bata ji daɗin ƙin amincewa da nuraddeen yayi ba , ta so ace ya ba da sadiq ɗin ko dan ta huta da ganin shi, kuma tana ganin idan sadiq ya tafi daga nan nuraddeen bashi da wanda zai so sai ƴaƴanta, haka ta shiga zuga nuraddeen akan ya ba abdulƙadir sadiq, ita duk a tuna nin ta da gaske abdulƙadir talaka ne bai da komi,dan bai faɗa mata Abdulƙadir bane dan ta san Abdulƙadir sosai rashin faɗa mata ko waye yasa tai ta zuga nuraddeen,kallon ta kawai nuraddeen yake, dama yace mata aminin shi ne kuma talaka ne dan yaga mizatayi yayi ne daman dan ya gwada ta, sai kuma yaga farin cikin ta, hakan ya ƙara tabbatar mashi da cewa da gaske maijidda bata son sadiq ko ƙaɗan, ko da magaji yaji labari shima haɗa mahaifin shi da Allah yayi akan ya bari a tafi da sadiq ko ba komai zai samu kwanciyar hankali, sai daga baya shima nuraddeen da yayi tunani yaga da cewar ya ba abdulƙadir sadiq, ko dan shima sadiq ɗin ya huta da tsangwamar da maijidda keyi mashi , dan abdulƙadir mutumne mai mutunci, yana da kirki sosai kuma zai ruƙe sadiq kamar ɗan daya haifa,ya san kuma rayuwar sadiq zata chanza, har ma sauki ya samu abdulƙadir ya faɗa mashi ya amince zai bashi sadiq, ba ƙaramin daɗi abdulƙadir yaji ba ya kuma yima nuraddeen godiya sosai, sannan yace ya shirya sadiq ɗin gobe da man zai koma lagos da safe , sunjima suna fira har kusan yamma sannan nuraddeen yayi mashi sallama, yana komawa gida yasa halimatu ta haɗa kayan sadiq cikin jaka, Ibrahim sai kuka yake za'a tai mashi da ɗan uwan shi wani wuri, lalla shin shi sadiq yake amma ya ƙi haƙura, ita kuwa maijidda sai jin daɗi take sadiq zai shiga cikin wahala.


Washe gari da safe wurin ƙarfe takwas abdulƙadir yazo domin tafiya da sadiq, halimatu ce ta fito da kayan sadiq har ƙofar gida, amsar jakar drivern abdulƙadir yayi da ga hannun halimatu ya sa a bayan mota , nuraddeen ne da abdulƙadir suka fito magaji na riƙe da hannun sadiq, ban kwana abdulƙadir yayi ma nuraddeen sannan ya ja hannun sadiq suka shiga mota, sadiq na ta ɗaga ma magaji da Ibrahim da halimatu hannu, suma suna ɗaga mashi hannun har motar ta bar anguwar,kasuwa nuraddeen da magaji suka wuce halimatu da Ibrahim kuma suka koma gida, abdulƙadir koda ya kai ma matar shi sadiq, sosai tayi murna kuma ta karɓi sadiq hannu bi biyu, gata da kulawa sadiq ke samu wurin abdulƙadir da hajiya zainab, abdulƙadir ya saka sadiq makaranta,sai dai makarantar basu sa shi ajin daya tsaya ba ya fara ne daga primary 4, kuma kamar yan da ya faɗa duk akayi hutu sadiq na zuwa kurfi, zuwan shi na farko kurfi maijidda kamar tayi huaka dan baƙin ciki ganin yanda sadiq ya koma, yayi kyau yayi fresh hasken shi ya ƙara fitowa, tayi data sannin sa baki nuraddeen ya bada sadiq, nan ta nace akan idan sadiq zai koma lagos sai ya tafi da Ibrahim, sosai nuraddeen ya ci mata mutunci ya kuma ce shi ba mutum banza bane, sadiq abdulƙadir yace yana so to dan haka bazai tura Ibrahim ba, bala'i sosai maijidda tai ta yi akan wai nuraddeen ya nuna ya fi son sadiq shiyyasa da abdulƙadir yace ya bashi shi ya ɗauka ya bashi,kullum cikin ɗaga ma nuraddeen hankali maijidda take har sadiq ya gama hutun shi ya koma, shekarar sadiq ɗaya a lagos Allah ya azurta zainab da samun ciki, zo kaga murna da farin ciki wurin zainab da abdulƙadir sadiq ma sai murna yake za'a haifa mashi ƙani ko ƙanwa, daya dawo daga school zai tasa zainab gaba yana faɗin ummy yaushe zaki haifa man ƙani, wani lokacin idan yayi mata tambayar sai dai tayi dariya, cikin zainab na shiga watan haihuwa, ta matsa ma abdulƙadir akan dole sai ya kaita Morocco ta haihu acan, ba dan ya so ba ya kaita, sadiq ma yasa rigima akan dole sai ya bita, haka abdulƙadir yayi masu visa yakai su shi kuma ya dawo, satin zainab ɗaya a morocco ta haifi ɗiyar ta kyakyawa mai kama da ita,ba'ayi suna a morocco ba suka dawo nigeria, da sati ya zagayo yarinya ta ci sunan mahaifiyar zainab watau Aisha, har lagos nuraddeen yazo ranar sunan aisha, sosai sadiq yayi murna da ganin mahaifin shi, da nuraddeen ya tashi tafiya maƙale mashi sadiq yayi akan sai ya bishi, zainab tasa ƙanwarta wacce suka zo tare da ga morocco ta haɗa ma sadiq kayan shi da zai bi nuraddeen.........






_Episode 50_51_


............. Koda nuraddeen ya koma da sadiq kurfi, bala'i maijidda ta tada akan dole sai sadiq ya dawo kurfi da zama tun da daman dan abdulƙadir bai da ɗa ko ƴa yasa aka bashi sadiq to tun da yan zu matar sh ta haihu sai sadiq ya dawo gida, sai da nuraddeen ya biyo mata ta bayan gida sannan ta kama kanta, sadiq bai gama hutun ba nuraddeen ya haɗa mashi kayan shi ya mai da shi lagos , a kwana a tashi asarar rai sadiq ya kammala secondry school lokacin aisha na da shekara bakwai a duniya,a lokacin tana primary 4, daya ke tun tana 4 year alhaji abdulƙadir ya sata makaranta, akwai soyayya da shaƙuwa tsakanin sadiq da aisha bacci kawai ke raba su, ko wane lokaci zaka same su suna tare da juna, musamman da yanzu sadiq yake zaune a gida yana hutu kafin ya fara zuwa jami'a, da sadiq zai tafi kurfi kuka aisha ta sa a dole sai ta bishi hajiya zainab da sadiq su kaita lallashinta sadiq yayi mata alƙawarin idan zai koma bikin su halimatu zai tafi da ita sannan ta haƙura,ko da sadiq yaje kurfi anan yake samun labarin rasuwar kakar shi wacce ta haifi ruma, yayi kuka sosai dan ba ƙaramin son tsohuwar ya ke ba saboda ita ma tana son shi,hutu na ƙarewa ya koma lagos , bai wani jima da dawowa ba ya fara zuwa school, kullum kafin ya tafi school sai ya fara ajiye aisha a school sannan yake wuce wa , saboda da zai fara zuwa jami'a mota abdulƙadir ya siya mashi, idan an tashe su kuwa driver ke ɗauko ta ranar da bashi da lectures kuwa shi ke kaita ya ɗauko ta, haka rayuwa taci gaba da tafiya an tsai da ranar bikin su uwani ita da halimatu, bikin su na saura sati ɗaya sadiq ya shirya zai tafi kurfi maƙalewa aisha tayi sai ta bi shi, shirya mata kayanta hajiya zainab tayi suka tafi,suna isa kurfi da Ibrahim suka ci karo zaune ƙofar gida shida abokan shi, yana ganin su ya taso da fara'a a fuskar shi yana ma sadiq barka da zuwa yayin da yake amsar jakar kayan da ke hannun shi, gaishe da shi aisha tayi, ya amsa mata da fara'a yana ce ma sadiq su shiga ciki, gidan suka nufa, suna shiga halimatu na zaune kan kujera yar tsugunno tana wanke wanke, ta so wa tayi da sauri tana ma su barka da zuwa suna nan tsaye maijidda ta fito daga kitchen hannun ta riƙe da kwano, wurin su ta ƙaraso tana bin aisha da ido, sadiq ya ce "ina wuni innah, mun same ku lafiya " daga mashi kai kawai tayi tana tambayar wannan fah, sadiq ya bata amsa da aisha ce ƙanwa ta, fuska a ya mutse tana kallon aisha ta ce"ba shakka, sannu ko " duƙara da kai aisha tayi tana cewa ina wuni da lafiya lau maijidda ta amsa sai kuma tace" yasu mamar ki kun baro su lafiya" da fara'a aisha tace" lafiya lau suke suna gaishe da ku"
"muna amsawa "maijidda ta faɗa sannan tace ma halimatu " ki kaita ɗakin ku, kunyi tsaye "tana gama faɗa ta juya ta nufi ɗakin ta, da kallo suka bita fuskar su da mamaki dan ba su taɓa tuna nin zata yima aisha ko kallon arziƙi, kayan ta da ke hannun sadiq halimatu ta amsa haɗi da jan hannun ta suka nufi ɗakin su, sadiq ma ɗakin su suka nufa shida Ibrahim yana tambayar shi ina su baba da magaji
sai da yamma magaji suka dawo daga kasuwa shida nuraddeen, sosai magaji yaji daɗin ganin sadiq hakama nuraddeen yayi farin ciki sosai musamman da yaga aisha, kulawa sosai aisha ke samu wurin dangin sadiq mu samman halimatu dan ta ɗauki aisha kamar ƙanwarta, uwani ce kawai ba ruwan ta da aisha amma har maijidda na jan ta a jiki, abun ba ƙaramin daɗi yayi mata ba, ana gobe ɗaurin aure gida ya cika da baƙi alhaji abdulƙadir yazo shida hajiya zainab, tarba mai kyau suka samu wurin nuraddeen da maijidda, washe gari aka ɗaura aure aka kai amare gidajen mazajen su aisha gidan halimatu ta kwana, sai washe gari ta dawo gidan su sadiq saboda ranar zasu koma lagos harda sadiq, da zasu tafi kiran sadiq maijidda tayi ɗakin ta akan mizai hana su tafi tare da Ibrahim tun da ya kusa gama makaranta, haƙuri sadiq ya bata yana cewa ko jiya yayi ma baban su maganar yana so su tafi tare da Ibrahim amma yace bai amince ba, haushi kamar ya kashe maijidda, gani take nuraddeen baya son ƴaƴan ta sadiq kaɗai yake so, kwantar da murya tayi tana cewa "kana jina sadiq ka rabu da maganr baban ku, da kace ma alhaji abdulƙadir kana son tafiya da ɗan uwanka nasan zai amince "maganar nuraddeen suka ji daga bayan su yana cewa "to wallahi ban amince ba , idan har kana son zaman lafiya da ni kar na sake naji kayima abdulƙadir wannan maganar kaji na faɗa maka "maijidda ta ce" wai miyasa kake haka ne, yaro na son tafiya da ɗan uwan shi amma ka hana haba dan Allah "ko kallon inda take bai yi ba yace ma sadiq "kama hanya ka wuce suna waje suna jiran ka "da to sadiq ya amsa yana ma maijidda ban kwana, Allah ya tsare kawai tace tana bin nuraddeen da kallo da zai fita, har ƙofar gida nuraddeen ya samu su sadiq yayi ma abdulƙadir ban kwana dayi mashi godiya, da motar su zata bar anguwar Ibrahim harda kukan shi, sannu sannu bata hana kaiwa sai dai ajima ba'a kai ba magaji ma yayi aure lokacin halimatu da uwani na da ƴaƴa ɗai ɗai uwani na da namiji mai suna usman halimatu kuma mace sunan ta zainab.


soyayya ce ta ƙullu tsakanin sadiq da aisha hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma abdulƙadir da nuraddeen ba, dama basu da wani buri daya wuce haka zainab abun yayi mata daɗi dan baƙaramin so take yima sadiq ba tamkar ɗan cikin ta haka ta ɗauke shi , da
sadiq ya kammala degree ɗinshi,kullum suna tare da aisha dan har binta yake makaranta, alhaji abdulƙadir ya ɗaura sadiq kan kasuwanci kafin ya fara aiki, sai da sadiq yayi kusan shekara ɗaya da rabi yana gudanar da kasuwanci sannan alhaji abdulƙadir ya sama mashi aiki a Abuja duk da sadiq ɗin yaso yayi a lagos saboda kwata kwata baya son abun da zai sa yayi nisa da aisha, da zai tafi kuwa aisha har da kuka abun ma mamaki ya ba ma hajiya zainab,sadiq bai daɗe da fara aiki ba nuraddeen da abdulƙadir suka tsai da rana auren su da aisha akan da ta kammala makaranta za'a yi bikin, hakan ce ta faru aisha na kammala makaranta aka fara shirye shiryen biki,ana saura wata ɗaya ƙanwar zainab tazo daga Morocco ta tafi da aisha, chan zasuyi mata gyaran jiki sai ana saura sati za su dawo da ita, ana saura sati ɗaya bikin Aisha ta dawo daga Morocco ita da yan uwan hajiya zainab , gida ya cika da baƙi aka fara shirye shirye an je anyi ma aisha jere gidan sadiq, shagali sosai alhaji abdulƙadir ya shirya haka ma nuraddeen ba'a barshi a baya ba, ana saura kwana uku yan kurfi suka zo part guda alhaji Abdulƙadir ya ware ma Nuraddeen ya ajiye duk wani baƙo daya zo mashi da yan uwan shi, maijidda kuwa ita da su uwani da yaran su suna part ɗin hajiya zainab , ranar juma'a aka ɗaura auren Abubakar Nuraddeen Ahamad Sharani da amaryar shi Aisha Abdulƙadir murna wurin ango da amarya ba'a cewa komai da yamma Alhaji abdulƙadir da nuraddeen suka haɗa aisha da sadiq su kayi masu nasiha,sannan suka je wurin hajiya zainab,nasiha sosai tayi masu da fatan alkairi, aisha na kuka ƙannan hajiya zainab suka yi mata rakiya gidan mijinta, ranar lahadi yan uwa da abokan arziƙi suka fara tafiya , ƴan kurfi kuma washe gari zasu tafi litinin kenan , da yamma maijidda tasa aka kira mata sadiq ta sake mashi maganar Ibrahim, cemata sadiq yayi "innah baba ya hana, ina kuma tsoron abun da zai biyo baya idan nace dole sai Ibrahim ya tsaya"bal bale shi da masifa maijidda tayi, wai bai son zumunci dan yaga Allah ya ɗaukaka shi shine zai fara ƙyamar ɗan uwan shi,abun yayi mugun bama sadiq mamaki, bai taɓa tuna nin maijidda zata ce mashi haka ba arayuwa, haƙuri kawai ya bata, washe gari da safe sadiq yaje gidan alhaji abdulƙadir domin gaisawa da su ya kuma yima su nuraddeen rakiya saboda da safen zasu tafi, koda ya gaishe da nuraddeen bai san miya faru kawai nuraddeen ya rufe shi da faɗa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba yana cewa "kenan ni ban isa na hana ka abu ka hanu ba ko "
haƙuri sadiq ya shiga bashi batare da yasan miya aikata ma mahaifin nashi ba, sai da zasu tafi halimatu ke bashi haƙuri haɗi da faɗa mashi abun da ya faru, wai ashe lokacin da ya bar ɗakin da maijidda ta sauka, fita tayi daga ɗakin taje har ɗakin hajiya zainab ta roƙe ta akan dan Allah tunda sadiq da aisha basu gidan yanzu za su ji duk ba daɗi mizai hana Ibrahim ya dawo gidan da zama, to shine hajiya zainab ta sami alhaji abdulƙadir da maganar shiku ya samu nuraddeen akan dan Allah ya bar mashi Ibrahim ɗin, to shine nuraddeen yayi tuna nin sadiq ne ya faɗama abdulƙadir ɗin shine ya rufe shi da faɗa, koda halimatu tagama faɗama sadiq bai ji daɗin abunda maijidda tayi ba yaso ace ta bari ya lallaɓa baban nasu harya amince, amma ta ɓata mashi komai gashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login