Showing 15001 words to 18000 words out of 260160 words

Chapter 6 - SARAN BOYE Complete Document by Billyn Abdull .txt

29 Nov 2024

19664

na daban har cikin raina😘😘🤝🏻_.




*_Masu buƙatar mu saka musu tallar kayan sana'arsu zasu iya zuwa suyi magana damu domin tayasu tallata hajojinsu a yanar gizo😘🤝🏻_*.




No. 5


.................“Indai har a yau dole sai an ɗaura auren Abdallah da wata kamar yanda Yaya Malam ya faɗa, to kuwa sai dai a ɗaura masa da ɗiyar ƴar uwata Nusaiba!!”.
Abban Abdallah dake shirin fita wajen ɗaurin aure ya tsaya cak daga ƙoƙarin saka maɓallin rigar farar shaddarsa ƴar ciki yana kallon Momy ta mirror. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya cigaba da abinda ya keyi.
Ƙarasa shigowa cikin ɗakin tayi ta tsaya a bayansa cike da damuwa. Sai da ya gama saka maɓallin guda uku sannan ya ɗauki babbar rigar itama ya warware zai saka. Saurin riƙe rigar Momy tayi hawaye na zubo mata saman fuska. Yanzu kam kallonta yayi da ƙyau yana ƙoƙarin haɗiye damuwarsa. “Na zata mun gama wannan maganar tun shekaru uku da suka shuɗe Khadija”.
Sosai ta fashe masa da kuka yanzun kam tana kallonsa cikin ido, “Abban Abdallah dan ALLAH ka fahimcen......”. “Anƙi a fahimcekin Khadijah!!”. Ya faɗa a tsananin tsawace jikinsa har yana rawa. Ya fisge rigarsa dake a hannunta tare da nuna mata hanya alamar ta fice masa a ɗaki.
“Abban Abdal.......” “Khadija!!!”. Ya kira sunanta da tsawa fiye dana farko. Baya taja a firgice ta manne da bango, sai kuma ta fashe da kuka bakinta na rawa alamar tanason yin magana amma tana shakka.
Tsaki Abba yay ya jefa babbar rigar saman gado yay ficewarsa ya barta a ɗakin. Can bayan ɗakunansu ya zagaya yanata huci. (nace, “Ashe ba Baba malam bane kawai mai zuciya a gidan😂).


Zubewa ƙasa Momy tayi tana kuka abin tausayi, kusan mintuna huɗu da fitar Abba akai Knocking ƙofar dayin sallama. Saurin share hawayenta tayi ta miƙe tsaye jin muryar Abdallah. Sai da ta kalla kanta a mirror ta sake cirar tissue ta gyara fuskar da ƙyau sannan ta amsa masa sallamar da bashi izinin shigowa.
Jikinsa a sanyaye ya shigo, ya ƙaraso cikin ɗakin sosai idanunsa akan mahaifiyarsa da itama kallonsa take cike da tausayawa. Matsowa tai da sauri kafin ya ƙaraso, ta kama hannunsa ta zaunar a bakin gadon tana faɗin, “Abdallah kana lafiya dai ko?”.
“Momy bana a lafiya wlhy”. Ya faɗa tamkar zai fashe da kuka. Murmushin ƙarfin hali Momy tayi, kusa da shi ta zauna tana ƙoƙarin haɗiye tata damuwar. Ta kamo hanunsa cikin nata ta rumtse. “Abdallah nasan dole ka tsinta kanka a cikin ruɗani game da wannan al'amarin, sai dai dan ALLAH ka kwantar da hankalinka kaji, kasa a ranka haka shine mafi alkairi shiyyasa ALLAH ya ƙaddara hakan. Nu'aymah ba ita bace autar mata, bakuma dama an halicceka domin ita kawai bane ba........”
“Momy karkice haka, wlhy ina son Nu'aymah sosai, da sonta na rayu tun ban gama sanin ciwon kaina ba. Amma dan ALLAH Momy ki faɗamin inada wani haline mara ƙyau da zaisa Nu'aymah ta ƙini?”.
Murmushi Momy tayi, takai hannu saman kumatunsa ta shafa. “Baka da wani aibu Abdallah na, babu wata mace da zaka tunkara da kalmar so ace ta gujeka. Itama ƙuruciya ce da rashin sanin ciwon kai ke ɗawainiya da ita. Shawara ɗaya zan baka shine ka kwantar da hankalinka, ka cigaba da addu'a kuma, inhar Nu'aymah alkairi ce a gareka, ALLAH kuma ya ƙaddara zata kasance cikin matanka ALLAH ya dawo da hankalinta gareka. Idan kuma ba alkairi bane aurenta ALLAH ya cire maka ita a zuciyarka kaji. Zan tayaka da addu'ar nan nima insha ALLAH”.
Kansa ya ɗaga mata hawaye na sulalo masa a ido ɗaya. Momy ta saka babban yatsanta ta ɗauke masa shi tana murmushi. “Banason ganin wannan hawayen Sweetheart kaji”. Nanma kai kawai ya jinjina mata yana haɗiye tsantsar damuwarsa.
“To amma Momy ni banason a auramin kowa, a bari kawai zan jira Nu'aymah. Na roƙi Baba Malam hakan amma yaƙi saurarena, nasa Abba ma bazai saurareniba tunda basa tsallake maganar Baba malam”.
Shiru Momy tai kamar wadda ta tafi tunani, sai da Abdallah ya ɗan taɓata da kiran sunanta sannan ta sauke gajeren numfashi da kallonsa. “Abdallah kaima ka sani babu wanda ya isa canja abinda Yaya Malam ya faɗa a gidan nan, ko Hajjo goyama duk abinda ya sharɗanta baya takeyi. Babbar damuwata kar ace za'a aura maka cikin ƙananun yarannan Yusrah ko Adawiya, dan kaga dai Hajarah da Kubrah duk sunada samarinsu kuma kowa yasani a gidan nan, tunda har an tsaida magana, jira kawai ake su kammala karatunsu a ɗaura musu aure. Abdallah kullum shekaru kake ƙarawa ba ƙuruciya ba, ka kai minzalin da ya kamata ace ka ajiye iyali tuni, da ace baka zauna jiran gawon shanu ba da yanzu ɗanka ko ƴarka zai kai shekara biyar koma fiye da haka Abdallah. Abdallah dubeni tsufa fa nakeyi, ina buƙatar jikokina kamar yanda nasan kaima kana buƙatar mace tare da kai. Ya kamata ace ka auri yarinyar da zata iya kula da duka ɗawainiyarka ba wadda zakai tunanin zaman raino ba Abdallah. Kayi nazari akan maganata ka ɗaurata a mizanin fahimta. Aysha, Sumayya, Badariyya, Maryam duk ƙannanka ne a gidan nan, amma ka duba shekarunsu nawa da yin aure?, dukansu sunada ƴaƴansu abin sha'awa, duk da matane ba kamar kai namiji ba”.
“Momy duka na fahimci maganarki, to amma kinga nima ai bansan wadda zasu aura mani ɗinba, amma nasan Abbah ya sani, ki tambayesa kozai sanar miki?”.
“Bazai sanar mini ba Abdallah, sai dai kaine nakeson ka kawoma kanka mafita”. “Mafita kuma Momy? Tami?”.
Numfashi ta sauke tana sake kallonsa da ƙyau. “Abdallah kaje ka samu Baba malam ka sanar masa ka yarda su aura maka duk wadda sukaga ta dace, amma su haɗa maka da Nusaiban Fatima {Gwaggonka}”.
“Momy Nusaiba kuma? Momy baki haƙura da zancen nanba dama? ALLAH ni bantaɓa jin Nusaiba a rainaba Momy, ina mata sone na ƙanwa kamar yanda nakema su Aysha”.
“Abdallah basai kaso Nusaiba ba yanzun, idan kukai aure tana gidanka a hankali zaka fara sonta. Yarinyarnan ƙyaƙyƙyawa ce itama, sannan tanada tarbiyya da hankali kaima ka sani ai”.
Shiru Abdallah yay kawai yana kallon Momy, a cikin ransa sai faman faɗin, ‘Nu'aymah kina inane? Dan ALLAH ki dawo gareni, ki taimakeni ki ceci zuciyar da bata taɓa fashi a ƙaunarki ba, ki taimaki numfashin da ke burin rayuwa da naki har abada. Nu'aymah miyasa kika kasancemin mai SARAN ƁOYE ne.........?’
“Abdallah!”. Momy ta faɗa tana girgiza shi. Kallonta yay da sauri dan baiji mitace ba. Zaiyi magana Abba ya shigo ɗakin. Duk da ya gansu sai ya ɗauke kansa kamar baisan da suba, rigarsa ya nufa ya ɗauka yana ƙoƙarin sakawa. Tashi Abdallah yay ya tako zuwa gabansa, taimaka masa yay ya saka rigar sannan ya kallesa. Zaiyi magana Abbah ya ɗaga masa hannu. “Banason jin komai Abdallah, kaje ka shirya ka fita massallaci, dan da an idar da sallar Juma'a za'a ɗaura maka aure kamar yanda Yayah ya faɗa”.
Ƙasa Abdallah yay da kansa yana haɗiye zuciya da sauri-sauri, baice komaiba ya juya ya fita idanunsa cike da ƙwalla.
Ɗauke kai Abba yay ya maida ga mirror inda yake hidimar cigaba da shiryawa. Momy kuwa tabi ɗan nata da kallo tamkar zata fasa kuka.


__________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
______________________


Masu posting a facebook dan ALLAH wannan roƙonane a gareku dama na WhatsApp da ko ina.. Nasan duk masoyin ƙwarai nason cigaban masoyinsa. Tabbas soyayyace ta sakaku kai littafina can, kuma inajin daɗin hakan da alfahari da wannan soyayya. To amma dan ALLAH ina roƙonku ku tausaya mana banda littatafan mu na ƙuɗi. Kamar wannan SARAN ƁOYE na kuɗi ne, yana cikin ZAFAFA BIYAR 2021. daga yau kuma free pages sun ƙare, gamai buƙata yazo ya biya naira 300 kacal sai ya cigaba da samu dan girman ALLAH Masoya amana adalci🤓😥🙏🏻.


Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇


ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇


0903 234 5899


IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇


09033181070


____________________________


Hankalin Umm a tashe yake matuƙa gaya, taƙi yarda ta fita wajen ƴan uwanta balle ta sanar musu halin da ake ciki. Tunda Baba Malam da yaƙi saurarenta itama ya fita bayan yayi shiri taketa kai kawo a ɗakinsa. Lokaci zuwa lokaci tana share ƙwallar dake ziraro mata.
Sam zuciyarta ta kasa yarda Nu'aymah guduwa tayi da kanta. Tasan wacece ƴarta, tasan tarbiyyar data bata. To amma a yanda al'amarin ya zone babu ta inda ita kanta zata iya bama Nu'aymah kariya koda a wajen mahaifinta ne. Balle kuma sauran jama'ar gidan. ‘Shin miya samu yarinyarta ne? Ta yaya tabar gida?’ tai maganar a fili tana fashewa da kuka maiban tausayi.

“ALLAH sarki Umm kiyi haƙuri ALLAH na nan😭🚶🏻”.


___________________________________


Gaba ɗaya yanayin shagalin bikin a cikin gida ya canja, mazane kawai a waje da basusan mike faruwaba keta walwalarsu. Hakama abokan Abdallah sai faman fantamawa suke cikin farar shadda datai bala'in musu ƙyau.
Sai da aka fara gabatar da sallar juma'a kafin a ɗora da ɗaura auren da yazoma mutane da saɓanin abinda suka gani a jikin invitation card.
Ba mutanen waje kawai ba, hatta ƙannen Baba Malam su Abba sai da sukasha mamaki matuƙa da yanda ɗaurin auren yazo. Dan kuwa ɗaurin auren yazo musu ne a yanda basuyi tunani ko tsammani ba.
An ɗaura auren Abdallah Rudwan Hashim Jibiya da Yusrah Musbahu Hashim Jibiya akan sadaki naira dubu ɗari. Sai aka sake ɗaurawa da Adawiya Mustapha Hashim jibiya, da Abdallah Rudwan Hashim Jibiya shima akan sadaki naira dubu ɗari. Aka ɗora da doguwar addu'ar fatan zaman lafiya ga ma'auratan daga ƙarshe.


Babu wanda ya iya magana a cikin su Abbah, dan kuwa su duk abinda Baba Malam ya zartar akansu bama ƴaƴansu ba basu da ja. Sun gama bashi darajar Uba tun tuni, sunsan bazai cutar da suba balle kuma ƴaƴansu. Fatansu kawai ALLAH yasa hakan shine mafi alkairi, ALLAH ya basu zaman lafiya kuma. Itama Nu'aymah ALLAH ya dawo musu da ita gida lafiya.


Kan Abdallah neman kwancewa yay dajin wannan al'amari, ko kammala ɗaura auren ba'ayiba ya sulale ya koma cikin gida kansa na wani kalar mahaukacin sara masa, ɗakin Abubakar cikin ƙannensa samarin gidan ya shige ya kulle kansa batare da kowa ya saniba.


Abokansa kansu cikin ruɗani da mamaki suke, sai dai kafin su sami damar tambayarsa suka nemesa suka rasa a wajen. Dole sai tambayar juna lafiya? suka komayi. Amma babu mai bada amsa.


★★★★★★★


Hakama cikin gidan tunda sakamakon ɗaurin aure ya iso kunnuwansu kowa ya kasa motsi, sai kallon kallo kawai akeyi da idanu baki ya gaza furta komai.
Momyn Abdallah jitai kamar an ɗaura mata dutsen dala bisa kai. Tayayama za'a aurama Abdallah aure da yara ƙanana irin waɗan nan har guda biyu?.
Haka taketa ayyanawa a zuciyarta, a fili kam sai laɓɓanta ke motsi maganar ta kasa furtuwa. Sai danginta ne keta ƙananun magana musamman ma Umman Nusaiba.


Yusrah ma tunda zancen ya isa garesu ta yanke jiki ta faɗi a sume, sai da aka yayyafa mata ruwa ta farfaɗo. Kuka take tamkar ranta zai fita. Ta yayama zata auri Yah Abdallah da tasan duk duniya babu wadda yake so sama da Nu'aymah. Sannan Nu'aymah ma na bala'in sonsa da ƙaunarsa. Tunda aka wayi gari da ɓatan Nu'aymah sam bata yarda guduwa tayiba, dan kuwa a daren jiya ana wajen walima ta dawo gida tanason shiga toilet. Motsin mutum taji a ɗakin, amma tana shigowa aka ɓuya bataga ko waneneba. Kashin daya matseta ne yasa batabi takan sanin wanene ba ta shige toilet. Bayan ta shiga ta fito taji motsin fitar koma wanene daga ɗakin. Bataga kowayeba, hakan yasata fita da sauri ta zagaya ta bayan Windows ɗin saboda ƙarar jan akwati da taji kamar anayi tacan. Dan ko ina na gidan Interlock ne. Tana ɓullowa ana barin wajen, sai dai zuciyarta ta zargi mutum ɗaya a lokacin, amma bata da tabbas ɗin da zata fito tace ga abinda ta gani kokuma ga wanda ta gani. Dan babu wata ƙwaƙwaran shaida a hannunta.
Abu na biyu Nu'aymah abokiyar firartace sosai, dan ko suna Lagos takanyi dogon Charting da Nu'aymah fiye da Amal da Adawiya, sannan kusan kullum sai sunyi waya, mafi yawan hirar da Nu'aymah ke mata kuma akan Yah Abdallah ne, dan komai na Nu'aymah da sunan Abdallah a ciki.
Ta sake fashewa da kuka tana ƙanƙame Aminta da itama cikin ruɗanin take. Bawai auren ƴarta da Abdallah ne matsalarta ba, matsalarta yanda al'amarin yazo. Tana ganin kamar Mazansu sunyi gaggawa akan yanke wannan hukuncin. Kamar ya dace ace sun zauna sunyi dogon nazari da bincike akan al'amarin Nu'aymah. To amma ita bata da wani ƙarfin iko akan sakawa ko hanawa a gidan, sai dai kawai ta shiga jerin shiga sahun masu addu'ar ALLAH ya warware al'amarin cikin sauƙi, duk inda Nu'aymah take kuma ALLAH ya kareta ya tsareta, ALLAH ya maido hankalinta gida.


★★★★


Adawiya da ko wanka ta kasayi saboda fargabar wadda za'a mayema Abdallah gurbin Nu'aymah da ita ta miƙe zumbur sanda labarin ya iso kunnenta. Dama a sashensu take tun bayan gama dambarwar guduwar Nu'aymah. Ta daka wani uban tsalle zata ƙwala ihun farin ciki Hajarah yayarta wadda takebi data shigo yanzun tai azamar rufe mata baki.
“Innalillahi, Adawiya minene haka kikeyi? Kefa nagama tamkar murna kikeyi ne ko mi?”.
Janye hanun Aunty Hajarah Adawiya tai daga kan bakinta tana hura hanci, kamar zatai magana cikin masifa kuma saita fasa. Canja yanayinta tayi zuwa damuwa ƙwalla na taruwar mata a idanu. “Aunty Hajarah ki barni nayi ihu ko zanji sanyi a raina, ta yaya za'ace ni Adawiya nice matar Yah Abdallah yau?”. A mamakin Hajarah sai taga Adawiya kuma ta fashe da dariya.
Baki Hajarah ta saki tana kallonta dan al'ajabi. Zatai magana sai ga Addah ta shigo ɗakin.
“K! Wane kalar iskancine wannan?!!”. Ta faɗa da matsananciyar tsawa tana kallon Adawiya data fara taka rawa. Daɓar ta zauna a bakin gado tana ɓata fuska.
Addah ta ƙaraso cikin ɗakin jikinta har rawa yakeyi, jikake “Tasss!!” ta ɗauke fuskar Adawiya da wani bahagon mari haggu da damanta. Kifff Adawiya ta kifo ƙasa dan azaba da gushewar numfashi na wucin gadi.
Cikin tsananin firgici da tashin hankali Hajarah tai tsalle gefe jikinta itama na rawa, tai masifar ware idanu akan mahaifiyar tasu da akan daɗe ba'aga fushintaba a gidan.
Addah tasa hannu ta ɗago Adawiya ta cigaba da bata maruka, sai da tai mata shidda ƙwarara sannan ta hankaɗata kan hado. Sosai wahala ma ta hana Adawiya kuka, sai sauke numfarfashi take tamkar zata shiɗe. Kallon Hajarah Addah tayi, batare da tayi magana na ta nuna mata hanyar fita.
Zabira Hajarah tai ta nufi ƙofar da bala'in sassarfa, sai da taje gab da fita sannan ta tsaya cak saboda tsawar da Addah ta daka mata. “Idan kin fita ki sanar da kowa kinji ko?”. Saurin haɗiye kukan dake neman kufce mata Hajarah tayi, ta kalli mahaifiyar tasu tana mai girgiza kanta. “K....k...kiyi haƙuri dan ALLAH Addah”. Hanya ta sake nuna mata alamar ta wuce. Hajarah bata sake magana ba tabi umarnin Addah ta fice.


______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.


Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇


ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇


0903 234 5899


IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇


09033181070


____________________________


Juyawa Addah ta sakeyi ga Adawiya dake kwance tamkar wadda shaƙar iskar numfashi taima ƙaranci. “Tashi dan Ubanki!!”. Da sauri Adawiya ta tashi tanaja baya daga farkon gadon zuwa ƙarshe, jikinta sai rawa yake tana kallon Addah, amma tsabar bushewar zuciya ajiyar zuciya kawai take saukewa taƙi tai kuka.
Addah ta kalleta babu ko ɗigon rahama a fuskarta. “Waye ya taimaka miki a gidan nan wajen ɗauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login