Showing 162001 words to 165000 words out of 260160 words

Chapter 55 - SARAN BOYE Complete Document by Billyn Abdull .txt

29 Nov 2024

19591

Nu'aymah ta tashi. Wanka ta sakeyi da ruwa mai zafi tai salla. Ananah ta kaita falo da kanta ta bata abinci. Ta ɗanci kuwa babu laifi, dan abinda take so ne akai mata. A haka Naser ya shigo ya samesu. Cike da kulawa da tausayi yayta jera ma Nu'aymah sannu. Ita kuwa amsa masa take da ɗan murmushinta. Baifi zaman mintuna goma ba sai ga Abdallah ya shigo shima. Shima dai kulawar ya nuna a gareta sosai da jera mata addu'oin samun lafiya. Amsa masa tai shima, sai dai babu fara'a sosai kamar Nasir. Haka suka cigaba da zama a sashen suna harar juna har akai kiran sallar magriba. Nu'aymah dai tuni ma ta ɗauke kanta ta maida ga tv kamar ta manta da zamansu a falon.
Bata saka iyayenta a rai ba sai dare. Baba malam da Umm tare suka shigo suka dubata, zukatansu cike dajin daɗin sauƙi data samu. Tare da tausayin gudan jinin tasu mai tsanani. Sun ɗan jima anan sannan suka fita, ita kuma ta shiga ta kwanta cike da kewarsu. Badan karsu hajjo suka kamar ta raina musu ba da guduwa zatai wajen iyayenta, sai dai tasan koma taje can ɗin ba sakewa zata samu ba dan baƙine acan ɗinma. Musamman dangin Addah da duk biki acan suke sauka dama. Yanzu haka ɗakinta kansa tasan da baƙi a cikinsa.


________★★★★________


Haka aka cigaba da hidimar biki, baƙi nata sake cika gidan ta kowane sashi. Yayinda jikin Nu'aymah keta ƙara warwarewa. Bata fita ko ina, ko yaushe tana sashen hajjo. Sai dai taci ta ƙoshi tasha magani tayi barci. Wani lokacin Amal da Yusrah kan shiga su tayata hira. Adawiya ce dai tunda aka sallamota bata ganiba. Da dai ta gaji da haƙuri ta tambayi su Yusrah. Sune suke sanar mata ai Adawiya nacan gidan kakarsu da ta haifi Addah, wai bata da lafiya. Tun washe garin da aka kwantar da Nu'aymah a asibiti ita kuma ta koma can.
Hakan sosai ya bama Nu'aymah mamaki, dan tasan iyayensu sam basa barinsu matsawa ko nan da can. Duk ƙulafucin da Gwaggo kakarta ta keyi akan ta dinga ɗan zuwa mata hutu dole ta haƙura. Dan ba'a barinsu, sai dai taje ta wunar mata ta dawo. Ko kuma idan bikine suje su kwana da Umm. Amma yau sai gashi wai Adawiya ita an barta zama a gidan kakarta.

Ɓangaren su Abdallah kam duk yanda sukaso keɓewa da Nu'aymah hakan yaci tura, iyakarsu zuwa su mata ya jiki kamar kowa shikenan. Ita kanta taƙi yarda ta sake dasu.
A daren yau da ya zama saura kwanaki biyu ɗaurin auren gidan da daddare su baba malam suka buƙaci ganin Nu'aymah da Abdallah sai Naseer. A sashen marigayi kakansu suka taru, dan canne kaɗai babu kowa a ciki.
Da hanzari Nu'aymah data fito wanka ta zura dogon hijjab akan zanin wanka ta fita kiran da Amal ta sake zuwa tai mata. Ta iske kowa ya hallara ita kawai ake jira, zuciyarta cike da mamakin taron ta ƙarasa garesu. Kusa da ƙafafun Ananah ta zauna tana gaishe da iyayen nata. Duk suka amsa mata da kulawa suna sake tambayarta ƙarfin jikinta.
Kanta a ƙasa tace, “Alhmdllh naji sauƙi sosai”. A kusan tare suma sukace Alhmdllhi.
Abban Adawiya ne ya buɗe taron da addu'a kamar yanda shari'a ta koyar da mu. Bayan sun kammala Ananah ta fara magana akan abinda ya tarasu.
“To da farko dai zan fara da tuna mana muhimmancin zuminci a addinance da kuma al'adance. mu dukanmu anan babu jahili, kowanne ALLAH yay masa nasibi da sani na ilimi dai-dai gwargwadon iko. Harma takai muna koyar da wasu ta hanyar baiwarsa. Dan haka inason mu nutsu, mu kuma fahimci junanmu. Mudai insha ALLAH ƴaƴa ko jikoki bazasu taɓa shiga tsakanin zumincinmu ni da ƴar uwata da muka rage ba. Sannan kuma ƴaƴan nasan ƴaƴa bazau zama silar ruguza naku zumincin ba. To haka nake fatan kuma su Abdullahi karku bari son zukata ya ruguza naku zumincin. Dan haka sakamakon halin da muka fuskanci kuna neman jefa kanku ne ya sakamu yin wani tunanin da ya kamata a kan matsalarku. muke kuma fatan kawo ƙarshenta a yau a kuma yanzun insha ALLAH. Sai ku nutsu kusa hankalinku jikinku dan ALLAH”.
Kansu duk suka ɗaga mata alamar gamsuwa da zancenta. Suka amsa kuma da cewar “Insha ALLAH”.
“Alhmdllh” ta faɗa tana maida dubanta ga Nu'aymah data jingina kanta jikin hannun kujerar da Ananah ke zaune tana kallon tattausan carpet ɗin dake tsakkiyar falon. “Zainabu!”.
“Na'am Ananah”. Nu'aymah ta amsa mata tana ɗagowa da ƙyau.
“Zainabu wannan zaman nakine. Dan haka inason ki nutsu waje guda ki tsai da hankalinki. Maganar abinda ya duk ya faru mu ajiyesa mu barsa. UBANGIJI yana kallon kowa yana kuma sane da komai. Duk da bamu gaskataba zukatanmu basu bar rawa da ciwo ba akan batun, amma muna nan akan bincike ainahin gaskiyar al'amarin dan bazamu bari ya wuce a banza ba saboda kiyaye gaba akan na baya. Shiyyasa muka yanke shawarar da mu kanmu muke da tabbacin zata sama mana nutsuwa da ke kanki. Ga Abdullahi nan, ga kuma Nasiru nan. Dukansu ƴan uwanki ne kuma masu sonki da fatan zama dake a matsayin matar aurensu. Kamar yanda a wancen karon bamu tauye haƙƙinki ba, a wannan karon ma bazamu tauye ba. Dan haka munason a yanzu basai anjimaba ki nuna mana wanda kike so tsakanin Abdullahi da Nasiru domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin zuri'ar mu”.
Wani irin faɗuwa gaban Nu'aymah yayi, ta dubi Nasir ta dubi Abdallah sai kuma ta maida idonta kan iyayen nasu. Muryarta naɗan rawa tace, “Ananah kuma a yanzu?”.
Hajjo tace, “Ƙwarai da gaske Zainabu, a yanzu zaki nuna mana zaɓinki, dan muna buƙatar salama da zaman lafiya”.
Zuciyarta na wani irin harbawa ta sake duban su Abdallah. Yanda duk suka zuba mata idanu cike da tashin hankali sai itama suka sake ɗaga nata hankali ƙololuwa. Saurin maida kanta ƙasa tai tanajin anya kuwa zata iya?. A take rauninta ya sake bayyana bisa fuska tamkar yanda suma duk suke a raunane zukatansu na rawa da barazanar son faso ƙirazansu su fito.........
Abbah Musbahu ne ya katseta da cewa, “Mamana ke muke saurare, ki daure ki faɗa mana abinda ke a ranki kinji, kinga dai bazaki auri maza biyu ba, dan haka karkiji komai ki zaɓi ɗaya a cikinsu mu zamu fahimceki suma haka. Zakuma mu saka muku albarka a cikin al'amarin”.
Kuka Nu'aymah ta fashe da shi, bakinta na sake rawa tace, “Ab...a... Abbah ni dukansu ai ina sonsu”.
Baba malam da tun ɗazun baice komaiba yace, “Zancen banza kenan. Ai munsan dukan kina sonsu, hakanne yasa mukace ki zaɓa tunda ai baki taɓa ganin ana auran maza biyu ba ko!”.
Bayan ta ɗan zabura kaɗan ta ƙara mannewa da jikin Ananah. Sai ɗan girgiza kanta take hawaye na zubo mata da sauri-sauri.
Cikin taushin murya Abban Abdallah yace, “A'a yaya ayi mata a hankali. Mamana ki kwantar da hankalinki kinji, ki faɗa mana a cikinsu dawa zaki iya zaman aure a yanzu? Dan bazamu bari a cuta ma rayuwarkiba insha ALLAH. idan ma dukansu basu miki ba falillahil-hamdu, mu a garemu ba komai bane, sai ki kawo wanda kike so koda ba'a cikin zuri'armu yake ba. Zamu duba nagartarsa idan ya cancanta zamu basa ke”.
Kanta ta jinjina masa tana share hawayenta. Ta ɗago a hankali ta zubama su Abdallah dake kallonta idanun. Kowannensu a kallo ɗaya zaka fahimci roƙonta sukeyi da idanu ta zaɓesa. Hakanne ya sake saka zuciyarta sake raunana. Cikin rawar hannu data jiki ta nunasu da ɗan yatsa.
Gaba ɗaya falon inda hannunta ya nuna sukabi da kallo..............✍


😱Munga Idi Aymah wa?! 🤔?.




ZAFAFA BIYAR 2021


Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗


Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗


Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗


Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋


Duka akan farashi mai rahusar gaske.


Kamar haka👇🏻💃🏻


Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700


Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇


ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇


0903 234 5899


IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇


09033181070


💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.




*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.




No. 43


............Ajiyar zuciya ya sauke a hankali jin yanda Aymah take sake tura kanta cikin ƙirjinsa. Ya ɗan lumshe idanu ya buɗe akan dogon gashinta dake ta uban ƙamshi ga ƙyallin mai daya sha masha ALLAH. “Silly girl!” ya faɗa a hankali yana kai bakinsa dai-dai kunnenta. Batare da ya jira amsarta ba ya sake miƙewa da ita ɗauke a hannunsa. Zama ya farayi saman kujerar sannan ita kuma ta koma saman cinyarsa da ƙyau batare da tasan mi takeyi ba. Syringe ɗin da Ahmad ya ajiye ya ɗauka, ɗan guntun ruwan allurar dake ciki ya kalla, ya ɗan yamutsa fuska kaɗan da zare hular kansa ya ajiye gefe. Ya sake kallon Aymah ya girgiza kansa, cikin ƙwarewa da sanin makamar aiki ya kuma turata jikinsa da ƙyau tare da ranƙwafowa ya ɗaura bakinsa akan kunnenta. Wata irin sassanyar iska ya shiga hura mata cikin kunne a hankali, yayinda can kuma hannunsa ke saita inda zai mata allurar batare da ta saniba.
A hankali ta saki wani irin nannauyan ajiyar zuciya da sake shigewa jikinsa, saboda ƙamshinsa na sake jan hankalinta. Hakane ya bashi dama tsira mata allurar dai-dai inda ya dace. Da masifar ƙarfi ta zabura tare da fasa ƙara ta sake damƙesa da ƙyau jikinta na wani irin karkarwa.
Zare allurar yay yana sakin wani lallausan murmushi daya sake fidda annurin fuskarsa. “I am sorry”. ya faɗa a hankali cikin kunnen nata.


Ihun Nu'aymah duk sai da ya shiga cikin kunnen su baba malam. Duk rumtse idanu sukayi tausayinta na tsargama zukatansu. Sai dai babu wanda yay yunƙurin shiga cikin falon.
A ɓangaren Yoohan kuwa idanunsa ƙyam akan Aymah dake ta juyi a jikinsa tamkar wata macijiya, sai zufa dake ta faman tsatstsafo mata a goshi. Handkerchief ɗinsa fari ƙal ya fiddo cikin aljihun gaban rigarsa ya shiga share mata zufar, tsahon mintuna biyar suna a haka kafin ta shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere, a hankali kuma sai jikinta ya fara saki alamar barci. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sauke numfashi. Kwanciyar ya gyara mata a cinyarsa yanda zataji daɗi sosai, sai kuma ya kai hannu saman gashinta daya barbaje ya tattaresa cikin hannunsa. Ribbon ɗin ya ɗauka ya ɗaure mata shi a tsakkiya ya nannaɗesa da ƙyau yanda bazai takura mata ba. Baya yayi ya kwanta jikin kujerar shima, ya lumshe idanunsa da sakin sassanyar ajiyar zuciya.
Shirun da su baba malam sukaji babu motsinsu har tsahon wasu mintuna ne ya saka Ahmad faɗin, “ALLAH yasa dai lafiya naji shiru”. Ɗan murmushi baba malam yayi, ya kalli Ahmad ɗin yana faɗin, “Ai tunda kaji mamana tabar kwakwazo na tabbatar anyi alluran”.
Kusan a tare duk suka murmusa. Hajjo tace, “Raguwar amarya ba, sai tsiwa a baki amma cikinta fal tsoro, gashi kuma ta zama matar likita sai su ƙarata ai”. Yanzun kam duk dariya suka ɗanyi. Ananah tace, “Ai irinsu dama hakane, zakiga akwai tsiwa amma matsoratane a bugun farko. Ahmadu leƙa kagani”.
Da to Ahmad ya amsa yana nufar falon. Sallama kusan uku yayi baiji an amsa masa ba. Hakane ya sakashi tura ƙofar a hankali ya shiga. Sai dai daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallonsu. A take murmushinsa ya sake faɗaɗa.
Buɗe idanu Yoohan yayi a hankali tare da ɗagowa zaune sosai yana kallon Ahmad ɗin. Sai kuma ya yunƙura ya ɗaga Aymah cak daga cinyarsa zai miƙe.
Da sauri Ahmad yace, “No Doctor, kayi zamanka dama na leƙone kawai naga idan komai lafiya. To ashema har tayi barci”. Yoohan daya ƙarasa miƙewa baice komaiba, sai da ya shimfiɗe Nu'aymah a kujerar da ƙyau ya gyara mata kwanciya sannan ya ɗauki hularsa ya maida bisa kai yana bama Ahmad ɗin amsa. “Barrister wannan ƙanwar taka ta cika raki da ragwantaka, saboda allura kawai duk ta jigatani tamin Squeezing ɗin kaya”.
Ƴar dariya Ahmad yayi yana ƙoƙarin tattare syringe ɗin da komai da sukai amfani dashi. Yace, “A'a Doctor karmuyi haka da kai. Ni na tabbatar maka sai kazo wataran ka sanarmin Aymah jarumace, ballema itama likita zata zama insha ALLAH ”.
Idanu Yoohan yaɗan waro yana gyara zaman rigarsa, yace, “A hakanne zata zama likita tana tsoron allura tamkar bindiga ɗin? Tab za'aga likitoci kam”.

Da haka suka fito Ahmad na dariyar zancen Yoohan, shiko Yoohan ya fiske abinsa tamkar ba shine yay maganar ba.
Kusan duk a tare su Abbah ke tambayar jikin Nu'aymahn. Ahmad yace, “Ku kwantar da hankalinku ita harma ta tafi duniyar barci. Dama ihun na allura ne”.
Duk kallon Yoohan sukai cike da farin ciki, suka shiga jera masa sannu da godiya. Shi dai kansa a ƙasa yake faɗin, “Uncle karku damu aikina ne ai. Insha ALLAH zata tashi kamarma komai bai faruba dan amfanin allurar kenan. Sai dai a dinga kula dan abu kaɗan ita yanzu zai iya birkita ta, ruɗanin kuma shine ba'a so dan zai maida cigaban da ake murnar samu bayane. komai a ringa mata shi da lallashi”.
“Insha ALLAHU za'a kiyaye. ALLAH ya saka maka da alkairi, ita kuma ALLAH ya bata lafiya yasa kaffara ne”.
A tare suka amsa da amin, harsu hajjo da Ahmad ya fassara musu abinda Yoohan ɗin ya faɗa.


A cikin gida kuwa dai hidimar bikinsu suke tayi, babu wanda yasan abinda ke faruwa da Nu'aymah sai shaƙiƙan Umm da suke a bedroom ɗinta kawai. Suma kuma tunda Umm taje ta sanar musu likitan da zai duba Aymah yazo duk sai suka samu kwanciyar hankali.
Bayan wucewar Yoohan duk suka shiga har falon baba malam suka ganta. Hakan ya ƙara musu nutsuwa sosai, dan haka suka dawo ɗakin Umm suka cigaba da hirarsu ta zuminci tare da tattaunawa akan auren na Aymah.
Koda suka koma can baba malam da kansa ya ɗauki Nu'aymah dake barci hankali kwance ya maida bedroom ɗinsa. Sannan ya fito shi da ƴan uwansa suka fice massallaci gabatar da sallar magriba.

Biki yayi biki masha ALLAH, dan Addah ta samu alkairi sosai daga wajen abokan arziƙinta. Hakama sauran matan gidan bisa al'adar biki da kowa ya sani suma sun samu rabonsu ga abokan arziƙansu. Harma da Umm da kowa sai yanzu yasan harda gudan jininta. Ana idar da sallar isha'i kuma aka shiga shirya amare. Hajarah da Kubrah. Nu'aymah dai babu wanda yay magana maybe ba yau ba kenan.
Kamar yanda kowa ya sani baba malam shike raka duk ƴaƴansu gidan aure. Babu wani gayyar ƴan kai amarya. Duk wanda yake da buƙatar ganin ɗaki yakanje da rana bayan ɗaurin aure ko washe gari idan amarya ta kwana a gidanta. To gasu Hajarah ma tsarin bai canja ba. Dan ana idar da sallar isha'i su baba malam duk suka shigo gida. Sashen Hajjo aka kai amaren, Hajarah nata kuka kamar zata shiɗe. Kubrah kam idanunta ƙyar cikin lifayar da aka naɗa musu. Sai uban ƙamshi suke kamar gidan turare.
Duka iyayensu da shaƙiƙan ƴan uwa suka taru a sashen Hajjo aka shiga musu nasiha. A yanzunma dai Hajarah kuka take, Kubrah kam kanta dai a ƙasa tana saurarensu. Bayan nasihar da akai musu da gargaɗi mai ratsa jiki akai musu doguwar addu'a da fatan alkairi sannan aka fito dasu. Da motoci uku kacal za'a kai amaren. Motar farko amaren ne a baya sai baba malam da Omar da zaiyi driving. Mota ta biyu iyayene mata na ɓangaren Addah su huɗu, sai yayun Umm biyu, su kuma Malam ƙarami ne zai jasu. Sai motar ƙarshe da Yah Ahmad zai ja ita kuma tsoffin iyaye ne dangin su baba malam a ciki su biyu, sai Umm da momy da amaryar Abba Musbahu. Motar ƙarshe, Abban Abdallah, Abba Musbahu, Abubakar da zai jasu, Uncle Kabeer mahaifin Nasir, sai Uncle Babangida shima dai shaƙiƙinsu ne.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login