Showing 159001 words to 162000 words out of 260160 words
Chapter 54 - SARAN BOYE Complete Document by Billyn Abdull .txt
mana mi yake cewa”. Ananah ta faɗa da iya gaskiyarta.
Gaba ɗaya su baba malam murmushi sukayi dajin zancen Ananah. Umm ma saita nufi ƙofar fita ita dai tana nata murmushin. Cike da ƴar tsokana Ahmad yace, “Gaskiya Abba kubani kwangilar maida Hajjo da Ananah makaranta, dolene su fara jin turanci kwanan nan”.
Daƙuwa Abban Adawiya yay masa. Yayinda Hajjo ta talle masa ƙeya tana faɗin, “Kaci gidanku Ahmadu. Yo turancin banza turanci wofi. tunda munajin yaren da ALLAH yayimu a cikinsa muna kumajin yaren dayafi kowanne daraja, yaran MANZON ALLAH larabci ai mungama nasara. Kune kuka ɗauki amanar kanku kuka miƙama masu jan kunne shiyyasa gashinan kullum sai hanyoyin wajiga rayuwarmu suke ƙara ƙirƙirowa. Shima Yahaya ɗin kwanan nan dan gidansu sai ya fara iya hausar”.
Duk da Yoohan bajin abinda ta faɗa yay ba, baisan sanda murmushi ya kufce masa ba ganin yanda take masifa akan Ahmad tana duddungure masa kai hularsa har tana matsawa baya. Su Baba malan kuwa sai zuba murmushi sukeyi. Sosai abin nasu sai ya birgesa, musamman daya tuna nasa kakannin da kullum babu abinda sukafi ƙwarewa sai masifa da faɗa kamar kajinaye.......
Hannunsa da Nu'aymah ta riƙo ne ya sakashi saurin juyawa gareta. Cikin yanayin ciwo ta sake matse lallausan tafin hanun nasa cikin nata tare da ɗorasa bisa kanta, “Abbah ka riƙemin zai fashe”.
A hankali Yoohan ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. Baiyi magana ba, bai kuma janye hannunsa data ɗora akanta ba ta danne da hannunta kuma.
“Inaga mu bara mu barka kayi aikinka”. Ya tsinkayi maganar Abban Abdallah a cikin kunnensa. Janye idanunsa yay daga kallon da yakema Aymah, sai dai kafin ma ya ɗago su duk sun fice. Hajjo da Ananah da Ahmad kawai aka bari.
Baice komaiba sai hannunsa da yay ƙoƙarin janyewa daga kanta. Amma sai ta sake riƙesa da ƙyau tana faɗin, “Abbah Please karka tafi ka barni, kaimin addu'a kaji Abbana”.
Sosai tausayinta ya sake lulluɓe su Hajjo. Yoohan ya ɗan matsar da kansa kusa da nata kaɗan, a hankali yace, “Ki daina magana zan baki magani yanzu zai daina insha ALLAH”.
Tabbas taji muryar ba Abbahn ta bane, amma halin da take ciki bai bata damar banbance wanene ɗinba sam.
Kallon Ahmad Yoohan yayi, yay masa nuni da box ɗin da suka shigo yana faɗin, “Brother Please ko zaka iya haɗamin allurar nan?”. “Yes! Doctor babu damuwa”. Ahmad ya bashi amsa yana jawo box ɗin.
Wata irin zabura Nu'aymah da zancen ya shigarma kunne tayi, batare da sun fargaba suka ganta tsaye bisa ƙafafunta jikinta na rawa. “Bana son allura, Abbah! Abbah! banason allura...” ta faɗa a wahale tana riƙe kanta da hannu biyu duka tai baya luuuu zata zube.
Cikin zafin nama Yoohan ya miƙe tsayen shima, hakan yasa Nu'aymah faɗawa jikinsa nata jikin na wani irin karkarwa. Saurin riƙota yayi shima yana faɗin, “Relax, Please calm dawn!”
Ina batama san yana faɗa ba, kanta kawai take jujjuyawa a ƙirjinsa da faɗin, “Banason allura, Abbah banaso”.
“Okay shike nan, kinga baza'ai mikiba, ya isa ki daina magana, tana sa miki ciwo kai”. Yay maganar da ɗaukarta gaba ɗayanta ya maida a kujerar zai kwantar. Sake ruƙunƙumesa tai, sautin muryarta na ƙara fita da ƙarfi wajen faɗin, “Abbah karka bari sumin allura dan ALLAH ” ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
Su dai su Hajjo duk wannan drama dake faruwa suna tsaye ne suna kallonsu, Ahmad dake murmushi yace, “Hajjo kumuje kawai mu barsa da ita, nasan zaiyi duk dabarar data dace yay mata insha ALLAH ”.
Cike da gamsuwa suka amsa masa. Allurar ya matsa ya miƙama Yoohan da Aymah ta kanannaɗema jiki kamar mage ta samu katifar audiga. “Gashi, bara mu baka waje kai aikinka Doctor ”.
Yoohan zaiyi magana Ahmad ya ajiye syringe ɗin da sauri yabi bayan su Hajjo da har sun fice abinsu............✍
Likita bokan turai😉😜.
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.
*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 41
.............Tunda su papa suka koma Abuja Suka kasa zaune suka kasa tsaye shida ƙannensa da aminansa. Sunyi zaman mitin kuwa yafi sau goma.
A kuma kowanne zama babu abinda suke tisawa da tirzawa sai kalaman baba malam masu cin zuciya da farin ciki.
A yanzun ma dai suna zaune ne su duka bakwai da suka kasance aminan juna kuma shakiƙai. Papa daketa kai kawo hannunsa goye a baya ya girgiza kansa idanunsa tamkar zasuyi aman wuta saboda jaa. “Bazai yuwuba. Dolene sai mun cimma burinmu akan Hausa man ɗin nan. Dan abinda ya shuɗe tsakanina da shi shekaru kusan ashirin da takwas yana a ransa daram babu abinda ya manta. Idan kuwa har ya tabbata bai manta ɗinba tofa ku sani, ni da ku duk muna cikin........”
Da sauri Uncle Mike ya ɗaga ma papa hannu. Muryarsa cike da barazana yace, “Karma kace komai Pastor. Ba'a haifi mahalukin daya isa hanamu cimma burinmu ba bayan wahalar da mukai ta tsahon shekaru. Duk da kuɗin da kuke tunanin hausa man ɗin nan nada shi wannan ba komai bane. Ni inada hanyar da zamuyi amfani wajen cinsa da yaƙi batare da shi kansa yasani ba. Zamu ruguzashi shi da duk zuri'arsa ta hanyar SARAN ƁOYE. Ni dai fatana shine ku bani haɗin kai kawai na nuna muku hanya mafi sauƙin ɓullewa”.
A take duk suka dubesa zukatansu na samun nutsuwa kaɗan. Ba komai yasa hakanba sai sanin da sukaima Mike wajan iya ƙulla talalar rufta duk wanda suka sakama kahon zuƙa a rayuwarsu. Dan haka babu wani kace na ce duk suka shiga sauke ajiyar zukata.
Hannunsa ya ɗaura saman tebirin gabansu yana dubansu. Papa ne ya fara aza nashi akan na Mike ɗin. Sai Godwin. Sauranma duk sai suka shiga ɗorawa ɗaya bayan ɗaya alamar tabbatar da mubayi'arsu akan idea ɗin da Mike zai kawo musu wadda suke fatan ta zama hanyar da zasu ɓulle akan baba malam.
Wannan zama shine ya samawa papa ƴar nutsuwa, duk da a kallo ɗaya zaka fahimci yana tare da fushi har zuwa yanzun. Wayarsa ya ɗauka yay kiran Yoohan da a yau ya wuce birnin Lagos. Bai ɗaga ba harta tsinke. Hakan ya sashi tunanin ko baya kusa. Dan haka bai sake kiraba ya ajiye wayar gefe ya cigaba da kora giyarsa.
Kusan mintuna goma sai ga kiran Yoohan ɗin ya shigo masa. Ɗauka yay fuskarsa cike da fara'a, dan har cikin ransa yana ƙaunar ɗan nasa. A duk irin fushin da yake ciki inhar ya kasance da Yoohan sai yaji ya samu nutsuwa ta musamman.
Yanda Yoohan ɗin ke gaishesa cike da shagwaɓa ne ya sakashi sakin murmushi. Cikin muryar ɗan mayen daya fara tasiri a kansa yace, “My sweet John yaya dai?!”.
Cike da ƴar shagwaɓa Yoohan dake zaune a office tare da Richard yace, “Papa na gaji ne, barci nakeji. Kaga tunda nazo Rich bai barni na hutaba sai laftamin aiki yakeyi kamar wani jakki”.
Ƴar dariya papa yayi yana kurɓar giyarsa. “Oh my Darling kaifa gwarzon namiji ne. karka karaya da sauri haka mana a gaban Richard”.
“Papa kai masa magana to ya tayani”.
“Hhhh to babu damuwa zan masa. Kasan miyasa na kiraka?”.
A nutse Yoohan daya gyara zama yace, “A'a papa, sai ka faɗa”.
“Humm” papa ya faɗa yana miƙewa. Ya kurɓa giyarsa saboda ɓacin ran baba malam na sake dawo masa sabo a zuciya. muryarsa cike da kaushi yace, “Jiya mukaje kano wajen wancan hausa man ɗin”.
Sosai gaban Yoohan ya faɗi. Ya ɗan ture files ɗin gabansa yana faɗin, “Kana nufin Sheikh Sooraj jibiya”.
“Yes! My son”.
Miƙewa Yoohan yayi da sauri. Ya tura kujerarsa ta zama baya ya bar gaban tebirin Richard na binsa da kallo. A wani irin yanayi yace, “Papa mi kukaje yi wajensa?”.
Batare da papa ya ɓoyema Yoohan ɗin komaiba ya sanar masa cewar sunje nema masa auren Nu'aymah ne. shine dan wulaƙanci baba malam yake sanar musu wai shi yarinyarsa bata isa aure ba. Idanma ta isa bai shirya aurar da ita ba........”
“Oh my GOD papaa! Miyasa baku sanar dani ba kafin kuje?. Nifa koda nace muku zan aura ƴarsa bawai ina nufin yanzu ba. Da gaske yarinyarfa ƙaramace. Shekararta sha bakwai ne kacal fa.......”
“My son! kai kake ganinta a ƙaramar, sufa sunama yaransu aure suna shekara goma ko sha biyu. Kawai dai ya shirya wulaƙanta mune saboda.......” sai kuma yay shiru bai ƙarisa ba
Yoohan da ransa ke a dagule yace, “Saboda mi papa? Ko dai ba neman auren ne ya kaiku ba dama?!. Papa kuna son ku ɓatamin aiki nane kawai kudai. Idan ba hakaba tayaya zaku tafi nema min aure batare da shawarata ba. Inada tabbacin kuma su Uncle Godwin ka kwasa kukaje sukaita masa gadaran da sukema mutane. Shifa wannan ya wuce duk yanda kuke zato, yanada iliminsa yasan mi yake yi. Sannan baya ɗaukar wulaƙanci ga kowa shiyyasa nakeyi komai cikin taku da taka tsantsan a kansa. Idan kuɗi kuke taƙama da shi shima ya tara su. Idan mabiya ne shima yana dasu bama a Najeriya kawai ba. Kaga kuwa tunkararsa sai an shirya”.
Jikin papa ne yay sanyi. Dan haka murya a sanyaye yace, “Tabbas na sake tafka kuskure na biyu Yoohan. Gaba ɗaya farin cikinka ne ya rufe min idanu na kasa fahimtar zuwa dasu zai iya haifar da matsala. Yanzu dai kayi haƙuri mu nemo mafita zan sake gyarawa da kaina. Kuma zan kiyaye”.
Duk da ran Yoohan a jagule yake har yanzun sai ya sauke ajiyar zuciya yana gyara tsaiwarsa. “Karka damu zamuyi magana. Yanzu ina kan aiki ne. Amma papa Please ka daina biyema su Uncle Mike suna sakaka zubar da mutuncinka gaskiya”.
“Karka damu zan kiyaye my son”.
Daga haka sukai sallama.
Yoohan da zuciyarsa ke masa zafi da ƙuna ko sauraren Richard dake jera masa tambayoyi baiyi ba ya tattara kayansa yace masa zai je gida nanda awa biyu zai dawo ya cigaba da duba marasa lafiyan....
*_KANO_*
Alhmdllhi, kamar yanda sukai fata an dace. Dan kuwa Nu'aymah ta farfaɗo cikin hankalinta, sai dai ramar da tayi dolene ta baka tausayi, hancin nan ya sake tsaho. Haka ma ta ƙara haske idanun sun fita da ƙyau masha ALLAH. Ramarma sai ta sake fiddo mata da ƙyawun nata.
Ba ƙaramin farin ciki ahalinta suka tsinci kansu ba. Dan tunda farar safiya aka fara tururuwar zuwa ganinta. Ga ƴan biki dama sun fara cika gidan musamman dangi na nesa. Ganin za'ayi yawa a asibitin Baba malam ya dakatar da zuwan. Ya sanar musu likitocin sun sanar masa a yau ma zasu sallameta insha ALLAH. Daɗine ya ƙara lulluɓe kowa, musamman ma Abdallah da Naser da farfaɗowan Nu'aymah ta sakasu komawa kamar an musu albishir da gidan aljanna.
Duk a yanayin da Nu'aymah ke a ciki su Dr Aysha na sanarma Yoohan. Shi da kansa ma ya basu umarnin sallamar Nu'aymah ɗin, dan insha ALLAHU ya tabbatar ta dawo cikin hayyacinta. Zata kuma lallaɓa jikin har lokacin da za'a fita da ita ai mata aiki a ƙwaƙwalwarta ɗin. Kasancewar yayi niyyar zuwa ɗaurin auren gidan nasu sai ya bari kawai sai ranar juma'ar ya iso kanon da safe, dan a ranar ta kama za'a ƙarama Nu'aymah allura ɗaya daga cikin allurorinta.
Sai wajen sha biyu na rana aka basu sallamar, daga Abdallah har Naseer suna a asibitin. hakama Omar malam ƙarami Yah Ahmad. Sai Abbah Musbahu. Kai tsaye motar Abba Musbahu Yah Ahmad daya kamota ya sakata. Dan ya kula akan tafiyar babu makawa su Abdallah sai sun nuna hali, shiyyasa ya raba gardamar ma tunkan a fara.
Murmushi kawai Abba Musbahu yayi yana jin daɗin abinda Ahmad ɗin yayi. Sukuwa duk sai suka ja guntayen tsoki kowa ya nufi motar da yazo ciki. A jere suka bar asibitin kamar wasu ƴan kai amarya.
Gidan bawani cika yay sosai ba. Dan dangine kawai irin na nesa sosai wasu daga cikinsu suka iso. Amma duk da haka daka shigo zaka fahimci bayan jama'ar gidan akwai baƙi a ciki. Da yake duk ba'ai tsamanin sallamar yanzu ba sai babu wanda yaji har suka gama fakin. Abbah Musbahu ya kamo Nu'aymah dake kwance a jikin kujera ya fiddota a hankali yana mata sannu.
Kanta kawai take ɗaga masa a hankali. Kai tsaye sashen Hajjo ya nufa da ita. Su Abdallah suka take musu baya gaba ɗaya. Sun iske sashen ba mutane sosai. Dan Umm ce ke cin-cin dasu dibulan, nakiya, alkaki da dai sauran kayan gara na fulawa da akeyi. Hakan yasa duk ƙannenta da ƙannen Adda da wasu daga cikin ƙawayensu dama matan gidan da yaran manya na ma'auri duk suna can anata aikin a can sashen.
Cikin farin ciki Hajjo da Ananah duk suka shiga musu sannu, idanunsu akan Nu'aymah dake langaɓe jikin Abba Musbahu (dama yaya lafiyar kura😂). Har cikin ɗakin Hajjo Abba Musbahu ya kai Nu'aymah. Nan Hajjo da Ananah suka biyosa. Sake yimata dannu sukayi cike da kulawa da tausayi, sunata jera mata addu'oin samun lafiya mai ɗorewa. Itako idanunta akan Ananah dake riƙe da hannunta tanata ɗan murmushi. Dan duk zuwan da sukeyi dubata sai yau ne ta ganta. Suna shiri sosai da Ananah, itaɗin ƴar gaban goshintace saboda sunan hajjo da taci.
Abbah Musbahu dake kallonsu shima cike dajin daɗi yace, “Ananah tayi wanka sai a bata abinci taci, dan likitocin sunce ta fara cin abinci da gaggawa”.
“Ba laifi auta. Dan wannan ramar da tayi gara taɗan cicciko, koni tsohuwa na fita ƙyan gani ai”. Baki Nu'aymah ta turo gaba tana janye hannunta daga cikin na Ananah datai maganar. Abbah Musbahu dake musu dariya yace, “Karki damu mamana, yanzu zanje na haɗo miki kayan daɗi kema zaki zama ƙatuwa ki fisu. Kuma karki basu ko ɗan cinguli kinji”.
Murmushi tai tana jinjina masa kai da kallon su hajjo irin bazaku cisa ɗin nanba ko.
Jama'ar gidan da labari ya kai musu ta hanyar yara sunta zuwa yima Nu'aymah sannu. Sai da kowa ya gama shigowa sannan hajjo ta sakata ta shiga wanka da ruwan data haɗa mata mai ɗumi. Yanda take jin jikinta wani irine yasata nutsuwa sosai tai wanka mai ƙyau, dan ta kwashe tsahon lokaci a ciki kafin ta fito. Taji daɗin ganin jakar kayanta, duk da tana kewar Umm ɗinta tanaso ta ganta. Dan kowa ya shigo dubata a agidan banda Umm........ Shigowar Addah, Amal biye da ita da tire a hannu ya katse mata tunani.
Duk sannu suka sakeyi mata. Addah ta zauna gefenta tana jawo akwatin da faɗin, “Daughter tashi kisa kaya ga abinci kici kinji, idan naga ramar nan taki hankalina sake tashi yake yi”. Cike da shagwaɓa Nu'aymah tace, “Addah nafi yin ƙyau a haka fa, dan ALLAH Amal banfi ƙyau haka ba?”.
Amal dake zuba mata abinci tace, “A'a mudai munfi sonki da ɗan jikinki Aymah. Gara ki ciko kafin nanda kwana uku. Yanzu ƴan biki kowa ya ganki sai ya tambaya”.
“Barta Amal, ɗura zan dinga mata ai”. Addah ta faɗa tana ajiyema Nu'aymah kayan da zata saka. Dariya Amal tayi da yima Aymah gwalo. Addah kuma ta taimaka mata ta saka kayan. Da taimakonta taci abincin. Ta bata maganganun ta tasha ta kwanta a gadon Hajjo dan ta ɗan huta. Babu jimawa kuwa barci yay ayon gaba da ita.
Sai bayan la'asar