Showing 174001 words to 177000 words out of 260160 words
Chapter 59 - SARAN BOYE Complete Document by Billyn Abdull .txt
ba'a bukata wuce gona da iri da yin almabazaranci da dukiya. (Wadda a yanzu hakan ne yafi yawa a bukukuwanmu. shiyyasa tun a filin bidi'oin ake zazzage daraja da albarkar auren atafi da gayyar sheɗanu😪🤦🏻).
Kansa ya ɗan jinjina da faɗin, “Tom shikenan. Amma bara na fara kiran Yaya (baba malam) na sanar masa tukunna”. Wannan ɗabi'ar tasu na birge Yoohan matuƙa.
Bayan Abbah daya koma gefe ya gama waya da Baba malam ya dawo yana faɗin, “Shikenan zasu zauna ɗin, amma yanzu su fito muje idan lokacin yayi sai a kaisu can. Idan mun koma sai ƴan uwanta suzo su tayata zama su yanzun”.
“Muna godiya Uncle, ALLAH ya ƙara girma”.
Murmushi kawai Abbah yayi, hakama Papa fuskarsa kamar gonar auduga.
★★★★★★
Tun bayan magriba mai kwalliya tazo yima Aymah. Amma saita tubure akan sai tayi sallar isha'i. Dole aka haƙura akan hakan, duk da su ƴan bikima harsun fara wucewa inda za'a gudanar da shagalin. Duk yanda taso su Amal su sanar mata wanene mijin sunƙi. Dan Amal da Yusrah da wasu ƙawayen Amal ɗin biyu maƙwaftansu suna nan tare da ita. Adawiya kam batazo ba wai kanta ke ciwo tasha magani sai anjima zata biyo su Aunty hibbah. Hakan bai wani damu Aymah ba, dan ita mantawa take ma da babin wata Adawiya yanzun.
Bayan an idar da sallar isha'i aka rangaɗama amarya Nu'aymah kwalliyar garari. Dan ko makaho ya taɓa saiya jinjina. Hakama su Amal an musu tasu. Momy daketa danne zuciyarta bisa shawarar ƙawartace da kanta ta kawoma Aymah rigar da zata saka wadda garariya garara har ƙasan amuruka akaje sayota daga aljihun papa da umarninsa.
Nu'aymah taso yin gaddamar sakawa. Amma yanda Momyn ke mata da lallashi ita da ƙawarta ya sakata amsa ta saka ganin rigar akwai hannu a jiki. Ammafa ta bala'i-bala'in haɗuwa sai ɗaukar ido takeyi. Farace tas sai kwalliyar furanni pitch color data ƙawata rigar. Hakan yasa dogon takalminta da shi kansa abin kallone ya kasance pitch. Sarƙa ɗankwali duk pitch. Humm lamarinfa ba'a cewa komai. Ita da kanta Aymah tasan ta haɗu, sai dai zuciyarta a raunane take, dan ta tabbatar ba Yah Ab ɗinta bane angonta. Musamman data san danginta basa irin wannan shirmen bidi'ar, kuma tasan ba Yah Naser bane shima, dan da ace shine katsina za'a kaita. ‘Ni Zainab wanene iyayena suka bama ni’ ta faɗa cikin zuciyarta tana kukan zuci, a fili kuwa idanunta sun cika da ƙwalla. Tayi jarumta sosai wajen ganin basu zubo ba.
Tare suka tafi dasu madam Chioma a mota ɗaya, dan shi ango yana acan hotel ɗin da za'ayi dinner ɗin, acan suke zaune da abokansa da baƙi da shi kansa wasu ma baisan da zuwan nasuba sai da sukazo ɗin. Dan ba ƙaramar gayya su Rich suka yo ba. Harda abokansu tunna secondary skull.
Lallai biki yayi biki kam, dan tun a ganin zuƙa-zuƙan motocin dake cike da harabar hotel ɗin har waje zaka san eh lallai manya ne ke lokacinsu. Ga ƴan jarida da ƴan sanda a wajen harda soji.
Momy da ƙawarta ne kawai suka fita. Aymah kam zata jira angonta. Su Yusrah ma dake motar bayansu duk sun fito suna tsaye. Ba'a rufa mintuna biyarba sai ga Doctor Yoohan mai zamani ya fito tare da gayyar abokansa. Tab, lallai kam ita ranar aure ta musamman ce ga kowa. Duk da shigar suit ɗabi'arsa ce sai yau tafi ta kullum. A kallo ɗaya zaka gane cewa kuɗaɗe masu nauyi aka zuba wajen sayen kayan. Fararene tas shima sai shirt ɗin ciki ce kaɗai ta kasance pitch. Gashin kan nan nasa da saje sunsha gyara sai walƙiya da ɗaukar idanu sukeyi. Duk da fuskar babu murmushi a sake take bai ɗaure ta ba. Hakan ya saka ƙyawunsa sake fita da ƙyau, ga wani irin kwarjini na angwanci dana ruwan alwala daya fara bin ƙofofin gashinsa na ɗawainiya da shi. Duk da ƙyawun da abokansa sukayi suma duk sai ya damasu ya shanye saboda darajar hasken musilinci.
Solomon yay saurin buɗe masa motar da Aymah ke a ciki zaune tanata haɗiyar zuciya. Baice komai ba sai matsawa da yayi jikin motar. Ya ɗan ranƙwafa kaɗan yanda zai iya ganinta da ƙyau. A tare hancinansu suka shaƙar musu ƙamshin turaren juna. Kowanne zuciyarsa ta harba kaɗan, musamman ma Yoohan da ƙyawun da Aymah tayi ya nema zarar da shi a tsaye. Amma a fili sai ya fuske abinsa ya miƙa mata tattausan tafin hannunsa, cikin harshensa da baya fita da ƙyau yace, “Bismillah”.
Wani irin harbawa da ƙarfi ƙirjin Nu'aymah yayi a karo na biyu, duk da kuwa dama ta tsargu tun jin ƙamshin turarensa. Amma sai bata kawoma ranta shiɗinne ba..... Kafin ta fahimci ruɗanin da take neman afkawa taji ya saƙala hannun nasa cikin nata.
Da sauri taja zata fisge jikinta na wani irin tsuma. Riƙesa yayi da ƙyau tare da matso fuskarsa gab da tata. A cikin kunnenta yace, “Wlhy kina min tsiwankin nan sai wannan ya shiga jikinki, garama ki nutsu mubar wajen nan lafiya”. Yay maganar yana nuna mata syringe da batasan daga ina ya cirosa ba.
‘Innalillahi....’ Aymah kawai ke iya maimaitawa a cikin zuciyarta. Kanta ya sake shigewa a ruɗani har batasan lokacin daya fiddota waje ba, ta dai ganta akan ƙafafuntane kawai dake sanye da dogon takalmi. Sauƙinta ma ta iya tafiya dasu dama can, amma da ansha kunya yau.
Gaba ɗaya ta zame masa mutum-mutumi, binsa kawai take duk yanda ya juyata. Ƴan jarida da abokansa da duk suka rikice sai zuba musu hotuna suke tako ina. Hasken camaras kawai kake gani babu ƙaƙƙautawa.
Duk da a cikin abokansa wasu na ganin Nu'aymah tayi kanƙanta hakan bai hanasu taya abokin nasu murna ba da mamakin inda ya samo wannan ƴar shilar. Yoohan dai ya fuske abinsa, dan bayason yayi wani ɗan sakaci da Aymah zata birkice masa a wajen nan. A haka suka shiga cikin hall ɗin daya haɗu harya gaji, decoration ɗin wajen ma komai fari ne da kwalliyar pitch kaɗan-kaɗan. Gashi komai a tsare babu wani hayaniya ko shirme, ga uban haske tako ina tamkar rana. Ko allura ka yadda zaka ɗauka abarka. Kowa yana zaune a inda ya dace da shi. Ita dai kanta na a ƙasa ne bata yarda ta kalli kowa ba duk da uban tafi da ake musu, ga wata waƙar na tashi a hankali cikin hall ɗin. Bayan an musu rakkiya inda ya dace su zauna kowa ya nema wajen zama. Papa ya gudanar da addu'a a wajen da kansa, shidai Yoohan yayi tasa a cikin rai. Nu'aymah ma sunayi tanayin tata cike da takaici. Ita abinda yafi birkitata shine su baba malam basu san Yoohan arne bane suka aura mata kenan? (Kusanfa ita batasan Yoohan ya musulinta ba) wannan bahagon tunanin ne yake neman zauta mata ƙwalwar kai. Shiyyasa tai shiru bata sake koda wani ƙwaƙwƙwaran motsi ba har aka fara gudanar da abinda ya tara mutane. Ita dai komai a shirme ma take kallonsa, sai dai ta ɗanji sanyi a ranta lokacin data ɗaga kai idonta ya sauka akan ahalinta su aunty hibbah da sukazo wajen daga baya. Amma saboda girmamawa a garesu sai aka kawosu gaba inda aka tanadar musu tebiri biyu dama. A yanzunma bataga Adawiya ba tare da su.
Lokacin da akace su yanka cake tasha uban takaici. Dan ƙin basa tayi. Idanunsa yaɗan lumshe ya buɗe a kanta ganin yanda hall ɗin yay tsit kowa ya zuba musu idanu. “Kinason muji kunya wajen waɗan nan ɗunbin mutanen da suka taru saboda mu ko? To idanfa kinƙi yin yanda akace ALLAH saina miki abinda sai kin kasa fita hall ɗinnan da kafafunkin nan”.
Gabantane ya faɗi. dan tasan zai iya aikatawar. Tunda har baiji nauyi ko shakkar mata kiss a gidansu ba. Sai da taɗan hararesa ta gefen ido sannan ta ciri cake ɗin da suka yanka ɗin, batare da ta yarda ta kallesa ba takai hannunta bakinsa. Hannun ya kama da nasa hannun ya ƙarasa da cake ɗin cikin bakinsa. Ɗan kaɗan ma ya gutsira ya juya hannun nata dake riƙe a cikin nasa wajen nata bakin. Badan ta so ba ta buɗe kaɗan itama danta ɗan gutsirar sai ya tura mata shi gaba ɗaya tsabar neman rigima. Saurin ɗagowa tai a ɗan zabure, hakan yasata gullewa tai gefe zata faɗi yay azamar riƙo ƙugunta ta dawo kan ƙirjinsa. Tuni tsiwar mutuniyar taku ta motsa, ta ɗago birkitattun idanun nan nata da suka sake girma ruwan hawayen da suka taru a ciki suka sasu wani kala ta musamman. Cikin nasa manyan idanun suka shige caraf, ya sarƙeta da su yanda ya hanata koda motsi suka cigaba da tsaiwa a haka tana a jikinsa idanunsu sarƙe cikin na juna. Gaba ɗaya tama rasa wane kalar bore zatai masa yasan halin da take ciki akan ganinsa matsayin wai miji a gareta. A hankali ta motsa laɓɓanta zatai magana. Yatsansa ya ɗaura saman laɓɓansa. a hankali yace, “Shiiii!!!”. Kasa yin maganar kuwa tayi batare da tasan dalilin hakan ba. Sai ma wata iriyar kasala data saukar mata da bala'in kwarjininsa da bata taɓa ganiba cikin idanunsa.
Kusan a tare hall ɗin ya ɗauki dariya, sai uban hasken camaras kake gani nata walwala su. Dan yanda suke a tsayen dolene su birge mai kallo, musamman ma'abota son soyayya.
Saurin yin ƙasa da kai Madam Chioma tayi tare da saka handkerchief ta share hawayen da suka cika mata idanu, badan shirin da suka ƙulla akan yarinyar nan ba ita da ƙawarta da tun a wajen nan saita halakata ta huta akan yaronta da takejin tsananin kishi. Miracle ma tsaki tayi ta miƙe ta fice daga cikin hall ɗin tana kuka, daga nan sai gidan barasa, dan tana buƙatar sheƙe wasu kwalabe ko zata sami nutsuwa. Hakama sauran ƴammatansa da baisan da zamansu ba abun yamusu takaici, ko joy da take ƙanwarsa sai da ranta ya sosu duk da kuwa sun birgeta itama.
Da sauri Nu'aymah data dawo hayyacinta saboda maganar mc tai saurin saka hannayenta ta ɗan turasa. Sakinta yay badan yaji turawar datai masa ba, sai dan kawai muguntar da tazo masa a cikin rai. Baya ta sakeyi zata faɗi ya riƙo hannunta da sauri ta kuma dawowa jikin nasa. Ya ɗan tsuke fuska kaɗan yana faɗin, “Silly girl”. Sannan ya saketa a hankali. Baki ta murguɗa masa kaɗan tana gyara tsaiwarta zuciyarta na wani irin harbawa da sauri-sauri. Kallo ɗaya taima sashen dasu Ananah suke ta maida idonta ƙasa ta duƙar saboda tsananin jin kunyarsu data lulluɓe ta.
Haka dai taro ya tashi lafiya bayan anci an sha kamar ba'asan ciwon kuɗi ba. liƙi kam sai kace basu sa zafin nema ba. Dan ƴan dubu-dubu ne sabbi ƙal keta farfar a ƙasa. Musamman lokacin da ango da amarya suka fito filin rawa. Sai dai sunyi tsayene babu wanda ya motsa, dama can kowa yasan Yoohan baya rawa, to bare Aymah da basa samun wannan sakewar a nasu gidan dama.
Su Osin abokan ango dai dasu Gebrail ƙannen ango an cashe gwargwadon iko. Mawaƙan da sukayi wasa a wajen sun kwashi kuɗi kam gwargwadon iko. Ƙarfe ɗaya dai-dai aka tashi.
Wasu sun nufi gidajensu ne, wasu kuma anan hotel ɗin, sai masu komawa gidansu Yoohan da amarya. Su Amal dai binsu Aunty Ananah sukayi suka koma gidan Abbah kamar yanda Omar ya tasasu a gaba............✍
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[6/10, 11:24 AM] +234 903 585 9738: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 46
__________
_INA MA’ABOTA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA? WANDA ZAI NISHADANTAR DAKU, YA FADAKAR, YA KUMA TSUNDUMA KU A KOGIN LOBAYYAR KAUNA? TO KU MATSO KUSA... DOMIN MUNZO MUKU DA ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI.. DAYA NE TAMKAR DA DUBU.. YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH.._
_LITTAFIN *UNCLE NE...* LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021. AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE.._
_”Wait... Dakata hafsat Rano, Kina nufin NIMCYLUV, dai shararriyar murubuciyar nan itace tazo da wani salon rubutun..?..”_
_”Kede bari Billyn Abdul.. Tsaya kiji kanun labarin a tak’aice..*NIMCYLUV* Tace book din a ta’kaice labarin *UNCLE NE* ne yana tafe:_
_Da farko yana mata kallon uwa wacce ta haife shi kuma jigon rayuwarsa, ashe itace silar rushewar rayuwarsa😢yarinyar da yakewa kallon ƙanwa uwa ɗaya Uba ɗaya ita aka wayi gari ta zama MATAR SA🙆🏻♀️ ƙaddara ta haɗashi da (Ahlil kitab) kiristan ya bata farin ciki, kulawa, soyayya, harya samu ta musulunta, Dalilinta sbd al'ƙawarin aure da yyi mata,ashe ba sonta yake ba🤔yaje birnin NUFAR domin kai masu tayin Muslunci, sun amince da hakan amma sharaɗin dole ya kwanta da ƴarsu,🤦🏼♀️gashi bashi da cikakkiyar lfy mazantakarsa bata aiki😫 ashe mahaukaciya ce ta haife shi.._
“_Kai lalle akwai runguntsumi acikin wannan littafi.. Ba za’ayi babu ni ba, Domin Za’a sha lagwadar romon dadi. shin tayaya ake biya Hansatu?_”
_”Ai ta Abdul..LITTAFIN *UNCLE NE* Naira 300 ne, Idan kuma kana son vip inda za'a ake posting sau biyu a rana kuma za'a baku littafan data rubuta na kuɗi sai ka bada 600 mai ma kon 1k.. number asusu wato bank account details: 0116886423 : account name sulaiman Na’ima S. Bank name: unioun bank: Sai a tura shedar biya ta 08119237616... A nuna mata ƙauna ta hanyar turowa ta account🤲🏻kamar yadda Za’a faranta maku a littafin UNCLE NE_
_(Best romantic love story of the year//Had’adden labarin kauna na shekarar 2021)_
____________
No. 46
.............Washe gari ƴan biki duk suka kama gabansu. Ciki kuwa harda ƴan kano su aunty hibba. Dan cikin sa'a sun sami jirgin safe. Sun tafi kuma da ɗunbin alkairi daga Yoohan. Sai dai kuma zukatansu cike da tausayin Nu'aymah da ƙaddarar aure ta kawo tsakkiyar waɗan nan mutane. Amma zasu cigaba da tayata da addu'ar zama mai nasara a cikinsu.
Nu'aymah kam bama tasan wainar da ake toyawaba a cikin gidan. Babu wanda ya nemeta a jama'ar gidan, itama kuma bata damu da son ganin kowa ba ma. Dan kukan data raba dare tanayi jiya ne ya ja mata komawa barci mai nauyi yau da safe. Bata farka ba sai wajen sha ɗaya. Haka ta tashi jikinta zau da zazzaɓi. Cikin dauriya tai wanka da ruwa mai zafin gaske. Tana fitowa anayin knocking ƙofar. Sai da ƙirjinta ya ɗan harba kaɗan, dan zatonta ko Yoohan ɗin ne. Jin an sake knocking ɗin ya sakata rumtse idanunta da sukai mata nauyi, hijjab ta ɗauka ta zira, sannan tazo ta buɗe ƙofar tana faman cin magani.
Victoria ce tsaye da tray a hannu, Destiny a bayanta ɗauke da flask ɗin shayi madaidaici. Ganin yanda yaran keta washe mata fuska ya sata sassauta fuskarta data ɗaure. Baki suka haɗa wajen faɗin, “Good morning Aunty!”.
A taƙaice Nu'aymah tace musu, “How are you?”.
“Fine Aunty, dama Aunty Blessing ce tace mu kawo miki breakfast”. (Kukun gidan).
Matsa musu tayi suka shiga cikin ɗakin batare data sake cewa komai ba. Ɗakin sukebi da kallo cike da sha'awar yanda ya haɗu. Bayan sun ajiye Destiny da bakinta baya iya yin shiru tace, “Aunty ɗakinki yayi ƙyau”.
“Thanks you”. Aymah ta sake faɗa a taƙaice. Dan ta kula shegen surutu yaran zasu dameta da shi idan ta basu fuska. Ilai kuwa sai Victoria ma ta buɗe baki zatai magana aka turo ƙofar ɗakin. Basai an faɗa ba, ƙamshin turarensa ma kawai ya isa amsa garesu. Da sauri suka miƙe daga zaman da sukayi akan sofa. Cikin ɗan rawar baki suke gaishesa. Janye idanunsa yayi akan Nu'aymah data ɗauke kanta bayan ta masa kallo ɗaya ya maida garesu. A taƙaice ya amsa musu yana cigaba da takowa cikin ɗakin. Saurin nufar ƙofa sukai suka fice.
Duk abinda sukeyi Nu'aymah na kallonsu ta cikin mirror, sai dai ta basar tanata shafa mai a ƙafarta kamar batasan da zamasu ba. Sai dai a ranta ji take kamar taje ta shaƙesa. Amma zata daure taga iya gudun ruwansa na yinin yau kawai......
Yanda bata tanka masa ba shima bai tanka matanba. Wayar dake a hannunsa yana latsawa ya matsa ya ajiye mata saman mirror ɗin, batare da yace komaiba ya juya zai fice. Cike da jin haushi Aymah ta bisa da kallo, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta