Showing 105001 words to 108000 words out of 260160 words
Chapter 36 - SARAN BOYE Complete Document by Billyn Abdull .txt
ɗin dake a gabansu tare da naɗe towel ɗin hannunsa saman kansa ya jingina bayansa da kujerar ya lumshe idanu.
Shi dai Solomon na tsaye yana cigaba da kallonsa cike da damuwa. A can ƙasan ransa kuwa zargine fal ciki akan su baba malam. Gani yake kamar yau rashin bin Yoohan cikin gidan yasa aka cutar da shi........
“Ina buƙatar coffee”. Ya katsema Solomon tunaninsa cikin yin magana a daƙile.
Da sauri Solo ya dawo hankalinsa. Ya amsa da “Okay sir” yana matsawa inda telephone ɗin ɗakin take yay kira domin yin order ɗin coffee ɗin da Yoohan ya buƙata.
Ba'afi mintuna uku zuwa huɗu ba kuwa sai ga cikin ma'aikatan yay knocking. Solomon ne ya je ya buɗe ya amso. Ya dawo inda Yoohan ɗin ke zaune ido a lumshe ya ajiye tray ɗin ƙasa dan ya ɗaura ƙafarsa akan table ɗin. Saida ya tsiyaya masa, tare da saka sukari ƙwara ɗaya kamar yanda yasan Yoohan na buƙata sannan ya miƙa masa.
“Gashi Sir” ya faɗa da yarensu.
Buɗe ido Yoohan yay a hankali. Sunyi jajur alamar baya cikin nutsuwarsa. Baice komaiba ya amsa tare da yima Solomon alamar yaje. Badan Solo yaso hakanba ya fito yana waigensa. A falo ya maƙale dan bazai iya zuwa ko inaba yabar Yoohan ɗin a haka, kodan gudun ɓacin rai mai tsanani da zai iya fuskanta a gurin madam Chioma da Papa.
Yoohan da baisan Solomon bai fitaba ya fara shan coffee ɗin a hankali zuciyarsa na cigaba da kai kawo akan abubuwa masu yawan gaske. A haka ya shanye ya sake zubama kansa. Yanzu kam ko sugan ma bai sakaba a haka ya sha kayansa. Koda ya gama kuma nan ya cigaba da zama har tsahon lokaci.
Zuwa can kuma tamkar wanda aka mintsina sai ya miƙe, duk da rigar wanka ce a jikinsa bai damu ba, a haka ya buɗe ƙofar ya fice bayan ya zura Slippers. Tsaye yayi yana kallon Solo dake gyangyaɗi a falo, kansa ya ɗan girgiza ya nufi ƙofa batare da yayi magana ba.
Can ya fita harabar hotel ɗin da ko ina ke ƙwanyar da haske, mutane nata kai kawo tamkar ba dare ba. Mafi yawansu mazane dake shigowa da mata. Wasu kuma matan su kaɗai ke shigowa alamar masu jiran nasu suna ciki su. Wasu mazan kuma su kaɗai ne suma, dan wasu matafiyane ba sheɗancin ne ya shigo dasu ba.
Watsar da komai yay dan shi baya matsama kansa shiga hurumin da banasa ba. Can wajen kujerun da aka tanada dan hutawa ya nufa. Babu mutane sosai a wajen, dan haka ya samu ɗaya ya zauna, tare da sake tsunduma cikin abinda ke masa kai kawo a zuciya da ruhi tun ɗazun.
A cikin tunanin nasa ne hankalinsa ya fara karkata ga abinda na kusa da shi ke saurare a wayarsa. Duk da ya saka ƙarar can ƙasa sosai hakan bai hana Yoohan ji ba saboda dare ya fara nisa. Wajen da suke kuma wajene da sam babu hayaniya, dan hotel ɗin dama bana ku bayi bane, na manya ne masu ji da ƴan canji, inda aka ginasa ma kawai ya isa baka amsa.
Lecture ce da ga bakin Sheikh Fantami yake saurara. Kasancewar da turanci ne sai komai yake shiga kunnen Yoohan raɗam. Buɗe idanu yay a hankali ya kai dubansa ga mai sauraren wa'azin. Matashin saurayine tamkarsa, sai dai kallo ɗaya zakai masa kasan kaga ustaz. yayi shiru a wajen tamkar baisan da motsin kowaba yanata sauraren wa'azin sa.
Tsintar kansa yay shima da sake nutsuwa sosai yana saurare. ya shagala sosai da sauraren wa'azin nan mutumin ya miƙe, batare da yayi tunanin wani na tayasa ji ba ya kashe tare da barin wajen ya koma ciki dan ya kwanta ya huta.
Ko kaɗan Yoohan baiso hakan ba, dan anzo wata gaɓa da duk mai sauraren wa'azin zai so jin ƙarshensa. Bin mutumin yayi da kallo harya ɓacema ganinsa. Ji yay tamkar ya bisa ya roƙe ya basa ya ƙarasa ji. Dan jikinsa wani irin tsuma ya keyi, gashi duk ya mimmiƙe masa. Komai ya sake birkice masa, duk yanda yake tunanin tasirin mafarkinsa da maganganun Nu'aymah sai lecture ɗin nan daya saurara ta sake faɗaɗa rauninsa zuwa ƙololuwar rikicewar tunani da gushewar wani duhu daya fahimci ya jima a cikinsa. Tunanin bin bayan mutumin ya sakashi kallon agogon hannunsa, ya ɗan waro idanu waje dan bai ankaraba sai yaga agogo ya nuna ƙarfe ɗaya saura.
Sake maida idanunsa yay ya lumshe tamkar baiga mi agogon ya nuna masa ba. Sai ajiyar zuciya daya dinga saukewa a jajjere.
A haka Solomon daya sake shiga ɗakin nemansa bai gansaba ya fito a rikice nemansa ya iske sa. Duk da wayar dake a hannunsa da alama ta nuna wanine akan layin sai da ya sauke ajiyar zuciya .
“Ashe kana anan sir?!”. Solo yay maganar yana sake sauke numfashin ruɗanin da yake ciki na rashin ganin nasa da farko.
Yoohan da tun isowar Solomon wajen yana kallonsa ta ƙasan ido ya buɗe idanunsa ya watsa masa wani shegen kallo mai cike da gargaɗi.....
“I'm sorry sir. Madam ce”.
Kafesa da ido sosai yayi, duk da kuwa yasan Momy Solomon ɗin ke nufi. Bai amshi wayarba, bai kumace komaiba ya miƙe yabar wajen. Solo dake binsa da kallo yay saurin bin bayansa hankali a tashe.
Koda suka koma ɗakin bai gajiya ba sai da ya sake maimaita masa maganar amsar wayar sannan ya miƙa masa hannu alamar ya bashi. Yana amsar wayar ya nunama Solo toilet da hannu.
Duk da bai fahimcesa ba haka ya nufi toilet ɗin dan ya duba. Shi kuma ya ɗora wayar saman kunnensa muryarsa mai amo da kauri ɗin nan ta fara fidda sauti. “Hello Mom”.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi madam Chioma ta sauke da ga can, kafin cikin ƙasa da murya sosai tace, “My boy!”.
“Humyim”.
Ya faɗa a hankali cikin maƙoshi.
Murmushi mai sauti ta sake da ga can tana mai ƙanƙame filo a ƙirjinta da lumshe idanu. Cikin sake narke murya tace, “Mike damunka?”.
Shiru yay na wasu sakanni. kafin ya furzar da ɗan huci yana sauke idanunsa da ga table ɗin. “Ba komai Mom, bakiyi barci ba?”.
Sake narke murya tayi kamar zatai kuka. Tace, “My Boy tunaninka ya hanani barci. Kai kasan muna tsananin buƙatar ganinka tare da mu ni da papan ku dama ƙannenka gaba ɗaya. Amma duk da ɗokin dawowarka da mukeyi wannan karon, bayan tsahon sati biyu da ka ɗauka bakanan shine kai wucewarka wani gari batare da ka fara sauka Abuja mun ganka ba”.
“Am so sorry Mom”. Ya faɗa a taƙaice kawai.
Matse filo ta sakeyi sosai a ƙirjinta. Dan ji take jininta na wani masifar yamutsawa tamkar zaiyi tsartuwa ya fito. Kafin ta samu damar sake magana ta sake tsinkayar muryar Yoohan na faɗin, “Mom goodnight, zan kwanta”. Ƙitt ya yanke wayar.
“My b......” tai yunƙurin faɗa sai kuma taji ƙitt. Da sauri ta ciro wayar daga kunnenta ta kalla. A take fuskarta tai masifar tsukewa hawaye na taruwa mata cikin idanu. Filo ta sake jawowa zata ƙanƙame papa ya shigo ɗakin nata.
“Wai lafiya kika maƙale anan bayan inata jiranki a can?”.
Wani irin takaici da baƙin ciki ne ya kumeta a zuciya. Ta ɗan hararesa a kaikaice tana maijin wani irin zafinsa da ɗaci a ranta. Amma a zahiri sai tai ɗan murmushi da cewa, “Ka bari kawai. Solomon ne ya kirani wai yaga kamar John a damuwa. Shine fa nasa ya haɗamu dan wayoyinsa duk basa tafiya. Amma yaron nan sai ya amsa ni sama-sama. daga ƙarshe ma ya yanke wayar”.
Ƴar dariya Papa dake hawowa gadon yayi. ya jata jikinsa ya rungume yana faɗin, “Kema kinsan halin yaronki ai. Minene zai ɓata miki rai a ciki. Maybe yana buƙatar hutawa ne shiyyasa ya kashe”.
Kafin ta samu damar basa amsa ya haɗe bakinsu waje guda. Duk yanda taso ta ƙwace kanta ya hanata wannan damar. Dan dama inhar ALLAH ya bashi sa'a a kanta baya wasa da damarsa. Saboda duk lokacin da zai buƙaci kasancewa da ita sai sunsha uwar rigima, wani lokacinma ƙarfi yake nuna mata ya samu nutsuwa. Yakan rasa miyasa take masa hakan tunda shi dai yasan auren soyayysa sukayi. ada can kuma sam bata masa wannan halin sai a shekarun nan da bazasu gaza goma zuwa sha ɗaya ba.
To komadai minene yau ya moreta da ƙyau. Daga ƙarshe ya koma lallashinta sabida kuka da take masa tamkar wanda yay mata fyaɗe. Da ƙyar ya samu kuwa tai shiru sukai barci duk da shi ya rigatayi kafin itama ya sacetan.
Yoohan kam koda ya yanke wayar sai yay jifa da ita saman kujerar dake gefensa. ya sake maida kansa jikin kujerar ya lumshe idanunsa tamkar ɗazun.
A haka Solomon da ya kammala tattare kayan da Yoohan ɗin ya baza a toilet ya fito ya samesa. Baiyi magana ba, ya lallaɓa kawai ya ɗauki wayarsa ya fice da ga ɗakin. Duk da Yoohan najinsa bai motsaba, haka ya cigaba da zama a wajen har tsahon lokacin da shima kansa baisan ya kai ba, dan barci ne mai nauyi ya kwashesa a wajen, tare da faɗawa cikin nannauyan mafarki maiban tsoro da al'ajabi a garesa.
Gabannin asuba ya farka a firgice, da ƙyar ya iya motsa wuyansa da ya ƙage, cikin dauriya da jarumta ya shiga jujjuyasa yana matse fuska saboda zafi. Sai da yaji ya ɗan sake masa sannan ya miƙe tsaye yana sauke tagwayen ajiyar zuya. Duk da a zuciyarsa yayi mamakin barcin da yay a zaune na kusan awa huɗu sai baiyi magana ba ya taka a hankali zuwa gaban Window. Idanu ya rufe zai fara addu'a kamar yanda sukeyi a addininsu sai kuma yay saurin buɗewa. Hannu ya saka ya buɗe Window ɗin. Sassanyar iskar asubahi ta feso masa, tare da ƙwala kiran sallar farko da ga wani massallaci da alamu suka nuna yana gab da hotel ɗine ko kuma a cikin hotel ɗinma yake . Wani wawan numfashi ya sauke tare da lumshe idanunsa. Haka kawai sai ya tsinci kansa a wani irin nishaɗa na musamman..............✍
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 28
............Sake buɗe idanun yay ya saukesu bisa giza-gizai dake yawo cikin hasken sararin samaniya na yanayin asubahi. Karan farko a rayuwarsa da zuciyarsa ta tafi wajen tunanin da girmama UBANGIJI da ya halicci sammai, gata dai babu icce ko ɗaya daga kowacce kusurwa ta duniya da zakai zaton ta riƙeta. Sannan babu wata sarƙa ko ƙarfe da suma suke amsa sunan ginshiƙi a gareta. Da rana hasken *_Rana_* ya mamayeta. Da dare hasken *_Wata_* ya ƙawata ta da adon taurari. da *_Damuna_* na _Giza-gizai_. Lokacin asubahi takan canja kala zuwa sky blue da wasu ado masu ban mamaki da al'ajabi. Hakama da yammaci lokacin faɗuwar rana takan ƙawatu da kalar sky blue da na yanayin faɗuwar rana. Duk wannan hikima da rahamar akan azurtamu da sune babu ko naira ɗaya. Babu kuɗin haraji babu na ƙarshen wata. To miyasa wanda ya azurtamu da ita bai taɓa jiran mu biyasa da ko taro ba? ‘saboda shi ɗin *_(SARKI NE GAGARA MISALI DA BAUTA KAWAI AKE KAƊAICE SA)’_*
Wani yanki na zuciyarsa ya bashi wannan amsar.
Samun kansa yay da sake lumshe idanu ya sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya saboda wata kalma data faɗo cikin kunnensa daga massallacin da aka kira salla dan sun saka tafsir ne.. (Kana son sanin ni'imar dake cikin addinin musulinci?). Furicin ya fito daga bakin Sheikh Sooraj Hashim jibiya (Baba malam) dan sun saka tafsir ɗin nasa ne.
‘Tabbas ina son sanin ni'imar dake cikin addinin musulinci?’. Ya amsa tamkar shi ɗin akeyima tambayar kai tsaye. yana mai cigaba da kallon yanda wata keyin ƙasa cikin giza-gizai alamar lokacin faɗuwarsa yayi, zai bama rana guri itama tazo ta cika umarnin ALLAH (S.W.A) akan aikinta.
Tabbas wannan tambaya ta tsayama Yoohan a zuciya. Dan da ita ya ƙarasa sauran daren daya rage masa. Akan kunnensa har aka kira assalatu akai salloli a massalatai. Sai da gari yay haske sosai sannan ya iya barin jikin Window ɗin zuwa toilet.
Ji yake a ransa bazai taɓa samun nutsuwa ba sai ya dangane da gidan baba malam a safiyar nan. Dan tabbas yana buƙatar sanin (Hanyar fahimtar ni'imomin dake cikin addinin musulinci? A yau).
A gaggauce ya gudanar da komai. Kamar ko yaushe yay shirinsa cikin ƙananun kaya. Blue jeans da farar shirt mai gajeren hannu. Sai ya ɗora suit jacket fara tas itama. Yau dai bai saka necktie ba, maɓallin shirt ɗinma ba duka aka rufe ba. Cikin ƙamshinsa ya baro cikin hotel ɗin batare daya nema inda su Solomon suke ba.
Safiya ce sosai a garin, hakan yasa da ƙyar ya samu keke napep, shima da mutum ɗaya a ciki. Bai damu ba, duk da kuwa wannan shine karan farko a tarihin rayuwarsa da zai shiga napep ɗin. Lokacin da mai napep ya tambayesa ina zasa? Da ƙyar ya iya haɗa hausan ya bashi amsa da sunan baba malam kawai. Dan dama bawai ya iya hausan bane yana dai jin abubuwa sosai saboda mu'amula da mutane marasa lafiya akan aikinsa. Sai dai bai iya maidawa, bayan gaisuwa sai abubuwan da baza'a rasaba suma ɗai-ɗai ne.
Sai da aka fara ajiye wanda ya tarar a ciki kafin shi a kaisa. Kusan dubu uku ya miƙama mai napep ɗin. Da mamaki shiko yake kallonsa, yama rasa mizai ce masa dan ya fahimci hausa ba isarsa tayi ba. Sake miƙo masan da yayne ya saka mai napep ƙoƙarin haɗa ɗan turancinsa ya sanar masa naira ɗari da hamsin ne kuɗinsa. Duk da dai turancin bai haɗu da ƙyau ba Yoohan ɗin ya fahimci mi ya faɗa. Dan haka ya ajiye masa kuɗin a jiki yana faɗin, “Na baka ne duka”. Yanda yay maganar da hausa abin dariya, harma mai napep ya kasa haƙuri sai da ya dara.
Yoohan baibi takansa ba ya nufi ƙofar gate ɗin su baba malam kansa tsaye, kai kace gidansa yazo.
Sau uku yay Knocking sannan maigadi ya buɗe ƙaramar ƙofar ya leƙo yana tambayar “Wai wanene haka da farar safiyar nan?” dan yasan su Baba malam ta ƙaramin gate sukaje massallaci yau.
Bai gane Yoohan ba. Dan duk zuwan da yay har sau biyu bashi kaɗai ya shiga ba sai da jagorancin masu gidan. Sai da ya gama ƙare masa kallo sama da ƙasa kafin yace, “Samari lafiya kuwa? Mikake nema ko buƙata anan?”.
Sam Yoohan bai fahimta ba, bayan kalmar (lafiya da wasu ɗai-ɗai) babu abinda ya gane a zancen maigadi. Sai yay shiru yana kallonsa cike da nazarin miya kamata ya ce da shi. Maigadi da haushi ya kama ya sake maimaita masa tambayar?. Nan ɗinma dai ba fahimtar yayi ba. Sai ma ya jefa masa tambaya da turanci shima.
“To bakajin hausa kenan?”. Maigadi ya faɗa a hankali. Sai kuma ya kalli Yoohan yay masa alama da hannu (wai yana zuwa). Kafin Yoohan ɗin yace wani abu maigadi ya koma ciki. Saurin yunƙurowa Yoohan ɗin yayi zai tsaidashi sai dai tuni ya rufe ƙofar.
Cike da damuwa ya dafe kansa. Sai kuma ya juya yana kallon titin anguwar. babu mutane sosai, sai tsilli-tsilli dake fitowa cikin massallacin. Sai