Showing 63001 words to 66000 words out of 260160 words

Chapter 22 - SARAN BOYE Complete Document by Billyn Abdull .txt

29 Nov 2024

19639

dan haka ya ɗauka wayarsa ya rubuta text ya turama Madam Chioma. Mintuna uku ba'ayi cikakkuba sai ga kiranta ya shigo wayar Yoohan.
Idanunsa ya ɗago daga abinda yakeyi ya kalli fuskar wayar. Duk da yaga sunan Mom ɓaro-ɓaro a jiki sai ya ɗauke kansa ya cigaba da abinda ya keyi. Kiran ya yanke wani ya sake shigowa. Yanzun kam maimakon kallon wanene sai ya lumshe idanunsa ma, sai da sukai kusan sakan goma a rufe sannan ya buɗesu akan su Solomon dake a gaba suna addu'a da fatan ya ɗaga wayar kafin su isa station ɗin.
Lip ɗinsa na ƙasa yaɗan lasa da harshe ya sake maida idanunsa ya lumshe bayan ya kife wayar alamar dai bazai ɗaga ɗinba..
“S...S sir ana kiran wayarka fa”. Solomon ya faɗa da rawar baki.
Tamkar yayi magana da dutse, dan Yoohan yi yay kamarma bai jisa ba, kuma sarai yaji miya faɗa ɗin.


A haka suka iso station ɗin, bai fitaba sai da yaja wasu mintuna, ta cikin motar ya gama ƙarema station ɗin kallo har su Solomon da suka fita suka buɗe masa. Solomon yay ƙasa da kansa ganin banzan kallon da Dr Yoohan ɗin ke masa. Batare da yace da shi uffanba ya zuro ƙafafunsa ƙasa ya fito. Gaba yay suka take masa baya kowanne zuciya babu daɗi.
Duk da ƴan sandan basusan wanene shi ɗinba shigarsa da waɗanda suka rufa masa baya ya sanar dasu ogan gayunne gaba ɗaya. Suda ya kamata ya fara gaidawa sai gasu suke masa tarba cikin tsantsar girmamawa kai kace wani babbane a cikinsu.
Ransa dake a ɓace da guards ɗinsa ya sakashi ɗaga musu hannu kawai batare da ya cire ko baƙin glasess ɗin idonsaba ya buƙaci a kaisa office ɗin d.p.o. Guards ɗinsa zasu magana da nuna masa sunada power ɗin shiga kai tsaye basai an nema masa isoba yay saurin ɗaga musu hannu suma cikin fushi. Tsitt sukayi kuwa kowa kai a ƙasa.
Maida dubansa yay ga ƴan sanda ya sake sanar musu su nema masa iso office ɗin d.p.o. Babu musu suka amsa masa cike da girmamawa, yayinda ɗaya a cikinsu ya nufi Office ɗin d.p.o ɗin domin sanar masa.
“Ranka ya daɗe yace ka shiga”. Ɗan sandan ya faɗa da harshen hausa yana ɗan risinawa. Ko motsi Yoohan baiyiba. bai kuma nuna yaji mi ɗan sandan ya ceba. Wani cikinsu dake acan gefe daya fahimci Yoohan baya jin hausa yay saurin sake maimaita abinda ɗan uwansu ya faɗa da turanci. Sai lokacin ne Yoohan ɗin ya motsa tare da ɗaga musu hannu.


Da sauri Solomon ya buɗe masa ƙofar office ɗin ya shiga. D.p.o yay azamar ajiye biron hannunsa yana mai miƙewa cike da tsagwaron mamakin ganin wanda baiyi zato ko tsammani ba. Shi kansa Yoohan ɗin tsaye yayi kawai yana kallonsa, a ransa yana raya ashe papa yayi amfani da wanda ya sanine shiyyasa ya nuna ƙarfin ikonsa.......
D.p.o ya katse tunaninsa da faɗin, “Oh God! Dr Yoohan!”. Hannu Yoohan ya saka ya zare glasess ɗin idonsa, batare da ya amsa d.p.o ba ya zuba masa idanu kawai kamar mai nazari. Har inda yake d.p.o ya ƙaraso shi, ya nuna masa kujera cike da girmamawa yana faɗin Please Sir ka zauna, ka taimakeni ka zauna”.
Kamar bazai zauna ɗinba, sai kuma miya tuna oho masa sai ya zauna a kujerar da d.p.o ya gyara masa tare da harɗe ƙafafu ya ɗora glasess ɗinsa saman table ɗin.
D.p.o daya koma tamkar ya mance da matsayinsa da kansa ya buɗe fridge ya ɗakko ruwa da lemo da kofi ya ajiye saman table ɗin. Abin mamaki duk ya wani rikice.

Nu'aymah na zaune a office ɗin ta cusa kanta cikin ƙafafunta dake mata wani irin ciwo taji takun shigowar mutum office ɗin. Yanda taji D.p.o na magana ba ƙaramin takaici ya bataba. A ranta rayawa take ‘Shin sai yaushene wai ƙasarnan tamu zata gyarune? Sai yaushene jami'an tsaronmu da duk wasu ma'aikatunmu zasu daina fifita masu hannu da shuni akan talaka? Ta taso gidan da Alhmdllh akwai arziƙi da wadatar zuci, akwai kuma kima da daraja na babban gidan. Dan haka duk inda suka tsinci kansu da wuya kiga ba'a girmamasu, sai dai idan ba'asan su ɗin su wanene ba. Ta tabbata wannan d.p.o ɗin inda ace bahaushene da babu yanda za'ai ya kasajin kunyar tura yaransa har gidansu ɗakkota, koda kuwa za'ace an basa kuɗin toshiyar baki. To amma yanda akema talaka na sosa mata zuciya da ruhi. A yanzu haka shigowarta station ɗin nan taga abubuwa kala-kala da suka sosa zuciyarta duk kuma an yisune akan talaka’. Batare data saniba tsaki ya kufce mata, cikin zafin zuciya da takaicin d.p.o ta ɗago dan taga wane shashasha ne yazo ake masa wannan tarbar tamkar wani IG ko gomnan kanon ma gaba ɗaya.
Akan bayansa ta sauke idanunta, dan ya juya mata bayane bata ganin fuskarsa, ta zuba ma bayan nasa harara duk da bawai ta gane wanene ba.


Yoohan da baisan Nu'aymah nayiba ya kalli d.p.o fuska babu walwala yace, “Inason ka saki yarinyar da papa yasa aka kawo nan”. “Sir amma.....” hannu Yoohan ya ɗaga ma d.p.o da sauri. “Emanuel! Haka kawai nake buƙatar ayi”.
“Za'ayi yanda kakeso sir, sai dai nima ka saurareni ko kaɗanne Please ”. Shiru Yoohan ɗin yayi alamar ya bashi dama. D.p.o daya fahimci hakan sai ya gyara zama, cikin kwantar da murya yace, “Ka taimakeni ka kira Pastor ka sanar masa kaine ka bada umarnin a saketa kar yaga kamar na saɓama umarninsa rayuwata ta shiga garari.
Lumshe idanu Yoohan yayi, wani irin takaici da ƙunci na daɗa faɗaɗa a cikin ransa. Yanajin zafi da matuƙar damuwa idan yaga yanda mutanensu ke masifar tsoron papa. Yakan rasa minene dalilin hakan? Dan kawai yana pastor ne ko me? Kodai akwai wani abu da bai saniba game da mahaifin nasa ne? K........’
“Please sir!”. Maganar d.p.o ta katse masa tunani. Maimakon ya amsa zai kira Papa, sai yace, “Ina yarinyar take?”. Da hannu D.p.o yay masa nuni da Nu'aymah dake bayansu ta sake duƙar da kanta saboda ƙafarta. Kafin Yoohan yace wani abu d.p.o ya bata umarni akan ta taso. Ko motsi bataiba dan abinda ya dameta shine matsalarta ba tsawarsa ba. Yunƙurawa ɗaya daga cikin yaransa yay a fusace zaije gareta Yoohan ya ɗaga masa hannu. Komawa yay ya tsaya inda yake cike da takaici.
Nu'aymah da duk tana jinsu bata motsaba, sai da ƙafarta ta lafa mata. Ƴar sandan da suka ɗakkota a gidace ta shigo bisa umarnin d.p.o ɗin ta taimaka mata ta miƙe. Miƙewar tata tayi dai-dai da ranƙwafawar Yoohan da ya miƙe yana faɗima d.p.o “Police ɗin da suka ɗakkota su maidata, su kuma bama iyayenta haƙuri da wanketa, inba hakaba Emanuel kaine zaka ɗauki laifin”. Da sauri d.p.o ya ɗaga masa kai zufa na keto masa. Yoohan ya ɗauki glasess ɗinsa ya juyo zai saka a ido. karaf suka sauka akan Nu'aymah dake tsaye tana binsa da wani shegen kallo na fusata, dan ko kaɗan batai tunanin shiɗinne yasa a kawota nan wajenba, saboda sam bata wani gane guards ɗinsa ba, hasalima ta manta da shi da abinda ya faru tsakaninsun.
Nunashi tai da ɗan yatsa babu alamar koda tsoro tattare da ita, “Kai ne dama kasa a kawoni nan wajen?” tai maganar fuskarta ɗauke da murmushin takaici, sai kuma ta haɗe fuska da maida dubanta ga d.p.o. “Yallaɓai ai bani na cancanci zuwa nanba wannan mai suffar ƴan damben ne, dan haka nima yanzu na kawo ƙararsa”.
Kafin d.p.o yace wani abu ta fisge hannunta daga na ƴar sandar ta fice a office ɗin da ɗan sauri duk da tana ɗingishi. Saurin bin bayanta d.p.o da ƴan sandan da ke office ɗin sukai, yayinda Yoohan ya lumshe idanu da saka glasess ɗinsa da ganinta ya hanashi sakawa ɗazun shima yabi bayansu.
Isowar su d.p.o yayi dai-dai da furucin Nu'aymah dake tsaye gaban ƴan sandan dake wajen kanta . “Yallaɓai na kawo ƙara”.
A tare suka kalleta, ɗaya a cikinsu yace, “ƙarar wa? A kanmi kuma?”. Juyawa tai inda su d.p.o ke tsaye cike da al'ajabi da mamakinta, dai-dai kuwa da fitowar Dr Yoohan daga lungun da office ɗin d.p.o yake ta nunasa da faɗin, “Ƙarar wannan mai siffar ƴan damben na kawo”............✍


😂Wagga ɗiya kina da tsaurin ido aradu😚🚶🏻.


Barka da juma'a😘😍🤗.


_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________


Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗


Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗


Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗


Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋


Duka akan farashi mai rahusar gaske.


Kamar haka👇🏻💃🏻


Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700


Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇


ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇


0903 234 5899


IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇


09033181070


💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.




*_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*


*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*


*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*


*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
*_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
*_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
*_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.


*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
*_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
*_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*


_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac


_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz


_NAMBAR TARHON MU_
08169380189


*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*


__________________________________
No. 17


.............Tsitt wajen yayi, dan kuwa kowa ya kasa koda tari dan al'ajabi wannan ƴar budurwa. Dalilai biyu suka hana kowa magana a tsakanin ƴan sandan da Guards ɗin Yoohan, sai kallon Nu'aymah da sukeyi.
Ƴan sandan ganin d.p.o ya fito da kansa yasa duk sukai tsit domin girmamawa a garesa. Guards ɗin Yoohan ɗin kuwa sanin ransa a ɓace yake da sune ya hanasu cewa komai suma duk da zukatansu zafi suke tamkar ana haɗa wuta a cikinsu. Ji suke da Yoohan ɗin zai basu wata dama akan Nu'aymah da wlhy ko buzunta bazasu bari ba saboda walmakalufatun da zasuyi mata.
Buɗe baki Nu'aymah tayi zata sake magana wanda batayi zato ko tsammanin ganiba taga ya shigo cikin station ɗin. Idanunsa a kanta suka fara sauka, kafin ya maida kan ƴan sandan da sauran mutanen da abinda Nu'aymah tayi ya sakasu tsayuwar sojan badakkare suga yanda wasan zai ƙare.
Sallama ya sake maimaitawa kafin ya bisu da sannu. D.p.o da bai amsa ko ɗaya a cikiba ya maida dubansa ga Yoohan dake jira su bashi hanya ya fice, dan ko kallon inda Nu'aymah take baiyiba balle ya nuna ya fahimci danshi takeyi ɗin. Kafin yace wani abu Barrister Atiku lauyan baba malam da shima ke kallon Nu'aymah yace, “Nu'aymah lafiya kuwa?”.
Fuska ta ɓata kamar zatai kuka, tace, “Uncle nima ƙarar wanda ya sa a kawoni nan ɗin zan shigar”. Sosai ya fiddo idanunsa waje na mamakinta, sai kuma yay saurin juyawa ya kalli ƴan sandan dake a kan kantar. “Officer idan bazaku damuba dan ALLAH inason ganin d.p.o ne, sunana Barrister Atiku Salis tofa”.
Kallon inda D.p.o ke tsaye suna magana da Yoohan sukai, kafin ɗaya a cikinsu yace, “To Barrister zaka iya faɗar mike tafe da kai sai a faɗa masa”. Ɗan murmushi Barrister Atiku yayi irin na kamilan mutane. Sai kuma ya kalli Nu'aymah da gaba ɗaya hankalinta na akan Yoohan, dan batason ya sulale ya fice bata saniba.
“Ba wani abu ya kawoniba, dama akan yarinyarnan ne” yay maganar yana nuna Nu'aymah ɗin.
Ɗaya a cikinsune yace, “Indai a kantane kakeson ganin Oga to ai an sallameta ma, ganinta da kai anan tsaye wai ta kawo ƙara ne”.
Da mamaki Barrister yake sake kallon Nu'aymah. Kafin yace wani abu d.p.o da suka gama magana da Dr Yoohan ya juyo garesu yana tambayar lafiya?. Cikin ƴan sandan wani ya sake cewa, “Oga wannan shine nake faɗa maka na gani zaune tun ɗazun a waje, harma nake sanar maka kamar ban yarda da shiba. To ashe lauya ne, yazone akan batunta”. ya ƙare maganar da nuna masa Nu'aymah da ganin Yoohan zai fita ya sakata raba hankalinta biyu. Batare da Barrister ya ankaraba tayi caraf tabar wajen tabi bayansa.

Ganin zasu tsere matane ya sakata saurin zuwa tasha gaban Yoohan da guards ɗinsa ke biye da shi fuska a murtuke da haushin kuɓutar Nu'aymah daga hannunsu.
A wani irin zafafe guards ɗin sukayo kanta kamar zasu cita ɗanya. Babu ko ɗar tattare da Nu'aymah ta zuba masu harara tana faɗin, “Dalla kukuma ku bani hanya marasa lokacin kansu, ba daku nakeyiba da oganku zanyi dan shine dai-dai da ni ba marasa aikiyi irinku ba”. Ta ƙare maganar da musu alamar su matsa a kanta da hannu tana wani tsume fuska da cije baki.
Lokaci guda duk suka sake kumbura da haushinta, sai dai kallon da Yoohan ɗin yay musu ya hanasu kowanne irin motsi suka zuba mata ido cike da tsagwaron takaici da tsana..
Yoohan dake ƙare mata kallo ta cikin google ɗinsa ya wani juya idanun tare da lumshesu a lokaci guda, so yake kawai yaga iya gudun ruwanta yau dai.
Fahimtar da Nu'aymah tai bayajin hausa a karon farko tai masa magana da turanci. “Ɗan dambe ban gama da kaiba ai, dan kaima na kawo ƙararka kuma na rantse har kotu sai munje”.
Koda wasa Dr Yoohan bai tunanin jin turanci a bakin Nu'aymah ba, turancinma mai ƙyau irin haka. Amma sai ya fiske a zahiri ya shanye mamakinsa a rai, ya koma mamakin tsaurin ido da rashin tsoron yarinyar.........
Tsawa Solomon da yazo wuya ya sake daka mata yana nufosu a fusace da nufin yima Nu'aymah dukan mutuwa kozata dawo hankalinta, inma oga zai kashesane ya kashesa ɗin. Jikinsa har wani irin rawa yake.
Saurin ɗaga masa hannu Yoohan ɗin yayi alamar ya dakata. Nu'aymah dake cike da haushin rashin yin maganar Yoohan ta kalli Solomon ɗin sheƙeƙe tana nunasa da yatsa, “Kai wlhy idan baka shiga hankalinka ba saika koma garinku da tsagen yarabawan farkon ƙarni, dan wlhy agaban d.p.o ɗin can zansa a maka tsatstsargiya a kumatu tunda taurin kaine da kai mtsooww”....
Duk yanda Barrister dake a bayansu yaso daurewa da lamarin yarinyar ya kasa daurewa, da ƙyar ya iya danne dariyarsa. Shi ba komaine ya burgesa da itaba sai yanda take masifarma cikin nutsuwa, babu wani rawan kai tattare da ita da zaisa kaimata fassarar bata da tarbiyya. Tsiwarce kawai a bakinta irin ta yaran nan ƴan gata da wahalar duniyarma basusan taba sai abinda baza'a rasaba. Yana mamakin yanda ta iya tsiwa, musamman idan yay dubi da irin gidan data fito. Dan shi kansa shaidane su baba malam tsaye suke a kan ƴaƴansu fiye da tunani, sannan ada da gaisuwa kawai ke haɗashi da Nu'aymah bai taɓa kawowa a ransa tana magana mai tsayibama balle akai ga wannan tsiwar.
Gyaran murya ya ɗanyi, hakanne ya saka Nu'aymah dake zubama Solomon harara ta ɗauke idonta ta maida ga Barrister.
“Kin sanshi ne?”. ɗaya daga cikin ƴan sandan da suka biyo Barrister ɗin zasuyima Nu'aymah rakkiya gida kamar yanda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login