Showing 27001 words to 30000 words out of 260160 words

Chapter 10 - SARAN BOYE Complete Document by Billyn Abdull .txt

29 Nov 2024

19630

kamar yanda ya saba a duk lokacin da ciwon nata ya motsa. Sai dai yau ta jima bata farfaɗo ba. Dan sai da sukaje sukai sallar magriba suka dawo sannan ya ƙarasa ƴan dabarunsa cikin amincin ALLAH ta farfaɗo.
Godiya yayma UBANGIJI tare da fita ya sanar musu ta farfaɗo. Dan yau ana idar da salla gaba ɗayansu suka baro massallaci, baba malam ne kawai yay zamansa. Matanma suna idar da sallar duk nan suka sake dawowa harda yaransu da dawowarsu islamiyya sukaji komai.


Bayan Doctor ya kammala komai ya buƙaci tattaunawa da su Abbah. Da ƙyar suka samu Baba malam ya baro massallaci yazo.
Doctor ya gyara zamansa cikin girmamawa a garesu yace, “Gaskiya wannan karon jikin Nu'aymah yayi tsamari. Kunsan matsalarta ba'aso abu yana firgitata da tsanani. tsawa da duhu suna gaba-gaba wajen girmama ciwonta da ƙarfafa shi”.
Hajjo ce tai saurin faɗin, “Hakane likita, duk munsan wannan, kuma ana ƙoƙarin kiyayewa. Yau ɗinma kuskure aka samu kasan ajizanci na ɗan adam. Yanzu minene mafita?”.
“To Hajjo ALLAH ya kiyaye gaba, amma kam yau abin yaso yin tsamari sosai a gareta, dan yanzu haka zancen da nake muku sam bata cikin hayyacinta, fatanmu dai ta dawo hayyacinta lafiya batare data manta komaiba ma bayan ta farka”.
Da matsanancin tsoro suke kallonsa, sai dai kowa ya kasa magana. Da sauri yace, “Bamu da tabbacin hakan, komai na ALLAH ne, mucigaba da mata addu'a insha ALLAHU zata farko cikin ƙoshin lafiya. Dama inada shawara ne, dan tun kwanaki naso zuwa da zancen sai nai tafiya kuma, yau kwanana shidda kenan da dawowa ma, zan kuma iya komawa a koda yaushe dan na samu gurbin ƙaro karatu a ƙasar Australia ne”.
A tare sukace, Masha ALLAH, ALLAH ya sanya albarka ya bada ikon karanto abu mai amfani”.
“Amin ya rabbi, nagode sosai”.
Abbah Musbahu yace, “Muna surarenka. Wane shawarace da kai?”.
“Dama akwai wani likita babba kuma ƙwararre, dan kam ALLAH ya hore masa baiwa ta fannoni da dama inhar a ɓangaren likitancine. To wani abokina ya tabbatar min har masu irin ciwon Nu'aymah yana basu taimako. Matsalar ɗaya ce, shine ganinsa. Ganinsa nada matuƙar wahala dan yana aikine a Nigeria da wajen Nigeria. Ko a yau zai iya shigowa kano ya duba marasa lafiya ya fice, zuwa dare kuma kaji bama ya ƙasar gaba ɗaya”.
“To ai mu Doctor ko biyansa ya kama muyi sai muyi dan yazo ya duba ta”. Cewar Abban Abdallah.
“Ai anan gizo ke saƙar Malam. Dan ko nawa za'a biyashi bazaizo gida duba mara lafiya ba. Dolene sai dai mutum yaje yay tanadin ganinsa kamar kowa, zai baka date ɗin da zaka gansa idan har ciwonka yakai shi zai dubaka, idan kuma yaga akwai mafita zai haɗaka da wani likitan da zakaje ka gani. Date ɗin da za'a rubuta maka kuma dole a sannan ne zaka gansa babu alfarma. Kwanaki yaron president ya samu wata babbar matsalar da sai shine ake fatan ya dubasa ko za'a dace. Har jirgi aka aika ya ɗakkosa daga wata ƙasar dan kawai yazo ya dubashi amma yace suje su sai kati subi layi kamar yanda kowa keyi shi bazaije ba. Kuma dole hakan akayi”.
Babu wanda bai jinjina wannan al'amari ba a cikinsu, sukai shiru kowa na tunanin mafita kuma. Ganin haka Ahmad yace, “To Doctor idan babu damuwa ai muma sai kai mana hanya mubi hanyar data dace ɗin na ganin nasa kawai, ko'a ina yake mu zamu bisa insha ALLAH. Fatanmu dai a dace”.
“Hakan shine dai-dai. Ga Number ɗaya daga ma'aikatansa zan baku sai ku nemesa, insha ALLAH zai muku ƙarin bayanima fiye da nawa ma, ga kuma ta abokina ma duk zan haɗa muku shima likitane zaku iya neman taimakonsa koda ni na wuce ne”.
Rubutawa yay ya miƙama Hajjo dake a kusa da shi, ita kuma saita miƙama Baba malan da tun shigowarsa baiyi ko tari ba. Bai musaba ya amsa ya ajiye gefensa da nufin idan ya tashi sai ya ɗauka yaje ya adana. Doctor ya tattare file ɗin bayanan ciwon Nu'aymah waje guda ya sake miƙama Hajjo yana faɗin, “Da wannan zaku gansa dole, dan ƙa'idarsa sai yaga bayanan ciwon mutum na baya inhar ya taɓa ganin likita akan hakan”.
Nanma godiya suka sake masa. Hajjo ta sake miƙama baba malam. Amsa yay ya saka Numbers ɗin da aka bashi a cikin file ɗin ya ajiye.
Kasancewar lokacin sallar isha'i yayi duk sai suka fice har Doctor. Bayan an idar da salla Doctor ya sake dawowa tare dasu Ahmad ya shiga ya ƙara duba Nu'aymah. Sai da ya sake tabbatar da komai ya zauna sannan ya fito yay musu sallama akan insha ALLAH da sassafe zai dawo yaga jikin nata. Idan kuma sunga da wata matsala komai dare su kirashi.
Sun masa fatan alkairi da godiya ya tafi.


_★__★_


Baba malam bai shigo gidan ba sai kusan goma saura, dan ya tsaya sunyi karatu ne. Sashen Hajjo ya fara shiga ya duba Nu'aymahn. Har sannan barci take, dan haka ya ɗauka file ɗin nata ya fice da shi zuwa sashensu.
Duk abinda Umm take masa bata fasaba. Yanda kuma bai mata magana akan Nu'aymahr ba itama batace da shi ƙala ba har suka kwanta.


______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.


Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇


ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇


0903 234 5899


IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇


09033181070


_______________________
WASHE GARI
_______________


Alhmdllh Nu'aymah ta tashi jikinta da sauƙi, kuma kamar yanda kowa yay fata bata manta da komai ba kamar yanda Doctor yayta jin tsoro. Hajjo ce ta taimaka mata tayi wanka. Yusrah ta kawo mata abinci tama zauna da kanta ta ringa bata. Ta ɗanci babu laifi, dan Yusrah lallaɓata ta dingayi ita da Hajjo.
Kamar yanda kowa na gidan yazo ya dubata da safen haka Baba Malam da Umm ma sukazo suka dubatan. Sunji nutsuwa sosai a zukatansu ganin jikin nata Alhmdllh. Sai dai kowansu bai nunaba a fuska, sunma haɗe mata gabas da yamma.
Hakan ba ƙaramin sake ɗaga hankalin Nu'aymah yay ba, harta kasa haƙuri ta shiga tambayar Yusrah ko wani abu ya faru bayan barinta gida ne? Dan ita tayi zaton idan ta dawo zataga kowa na murnar dawowar tata. Amma saita samu saɓanin hakan, sai ma kalaman baba malam na jiya keta mata kaikawo a cikin rai.
Ƙasa Yusrah tayi da kanta hawaye na cika mata idanu, haka kawai ta tsinci kanta da jin kunyar Nu'aymah ɗin mai tsanani. “Yusrah dan ALLAH kimin bayani mana? Ina Yah Ab da Adawiya duk bamma gansu ba”. Nu'aymah tai maganar cikin sanyin murya na alamun rashin jin daɗin jiki.
Saurin miƙewa Yusrah tayi ta juya mata baya zata bar ɗakin. Nu'aymah ta riƙe hannunta itama da sauri. Hannu Yusrah tasa ta goge hawayen dake rige-rigen sakko mata a kumatu batare data juya ta kalli Nu'aymah ba.
Dai-dai nan Hajjo ta shigo tare da Doctor da yazo sake zuwa ganin jikin nata.
“Kai lafiyarku?”.
Hajjo ta faɗa ganin Nu'aymah da Yusrah duk suna hawaye.
“Ba komai Hajjo”. Yusrah ta bama Hajjo amsa tana zare hannunta daga cikin na Nu'aymah. Kamar hajjo zata sake magana sai kuma tayi shiru suka bama Doctor damar duba Nu'aymahn. Yaji daɗin ganin jikin nata normal, sai dai yanason mata allura yana tsoron rikicinta da zasu kwasa. Nu'aymah ta mugun tsanar allura a rayuwarta, indai akace za'ai mata allura to lallai an taro match kuwa. Dan sai kowa yaji a gidan harma makwafta.
Kallon hajjo yay murya ƙasa-ƙasa yace, “Hajjo ko za'a kira mana su Ahmad ne kusa. Allura zan mata kinsan kuma sai ansha yaƙi”.
Sosai hajjo ta waro idanu waje. Taɗan kalli Nu'aymah data kwanta idonta na kallon fanka dake juyawa a hankali. Sake kallon Doctor tayi, itama a hankali tace, “bara dai a dubamin cikin iyayen nasu tunda duk basu fita ba”.
Kansa ya ɗaga mata ya tashi ya fita falon dan ya haɗa allurar. Itama Hajjo biyosa tayi.


Kusan mintuna biyar da fitar tasu duk suka dawo harda Baba malam dake cikin shirin fita. Batare da yayi maganaba ya kama Nu'aymah da kansa ya tayar zaune. Kallonsa take cike da so da ƙaunar mahaifin nata. Amma yanda yay kicin-kicin da fuska sai yake ƙara tsoratata. Ganin yanda ya jata jikinsa ya rungumene ya saka ƙirjinta bugawa. Dan tun tana yarinya inhar taga ya mata irin wannan rungumar to lallai allura za'a mata. Saurin ɗagowa tai ta kalli Doctor daya ɓoye hannunsa a baya. Jikinta ne ya fara tsuma, zatai magana Baba malam ya balla mata hararar da ta sakata maida kanta jikinsa ta kwantar.
Rikici sosai akasha kafin Doctor ya mata allurar, ba ita kanta ba har baba malam da hajjo masu riƙetan saida ta tarama gajiya. Doctor kam har ƴar zufar wahala yakeyi a goshi, a ransa yana sake jinjina daru irin na Nu'aymah.
Tunda baba malam ya maidata ya kwantar ajiyar zuciya kawai taketa faman saukewa hawaye na zirarar mata da gudu. Hajjo ta zauna inda baba malam ya tashi ta ɗago kan Nu'aymah ta aza bisa ƙafarta tana shafa mata dogon gashinta.
Sauran magungunanta Doctor ya ajiye yayma hajjo sallama suka fice shi da Baba malam.
Hajjo ta jima tana lallashin Nu'aymah kafin ta samu tayi shiru barci ya saceta. Amma har cikin barcin tsabar rikicinta ajiyar zuciya taketa faman saukewa a jajjere. Haka dai hajjo ta lallaɓa ta kwantar da ita da gyara mata kwanciya ta tashi ta fice.


______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.


Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇


ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇


0903 234 5899


IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇


09033181070


_______________________
______________
DUBAI
________


Amarya Adawiya da ango Abdallah sun isa ƙasar dubai lafiya, sai dai gaba ɗaya ya canja tsarin daya shiryama kansa da Nu'aymah. Ya dai kama musu babban hotel kuma a ɗaki ɗaya. A randa suka isan kuma ya sace wayar Adawiya ya ɓoye batare data saniba.
Ita dai duk abinda yake mata bai ɓata mata rai, haɗe fuska da ƙin mata magana tunda suka taho baisa taji haushinsaba balle sonsa ya ragu mata a zuciya. Saima ƙaruwa da ya sakeyi tanajin kamar ta haɗiyesa.
Gadon ya bata ta kwanta shi kuma yasa bargo a ƙasa yay kwanciyarsa. Da asuba ya rigata tashi, yay wankansa yay shiri tsaf. Sai da ya kammala komai sannan ya tadata. Mamaki ya kamata matuƙa ganinsa cikin shirin fita, sai dai kuma babu fuskar tambayarsa.
Murya a shaƙe yace, “Duk abinda kike buƙata ki kira zasu kawo miki”. Daga haka bai sake tofa komaiba yay ficewarsa daga ɗakin yaja mata ƙofar. Ta jima zaune a wajen tamkar wata gunki har gari yay haske sosai kafin ta sakko jiki a sanyaye taje tayo alwala. Duk da hakan da yay mata babu daɗi sai bataji haushinsaba. Haushin Nu'aymah nema ya kamata, dan a ganinta zaman dataine cikin zuciyarsa yasa baya ganin kowa da gashin mutunci sai ita. Aiko ta ɗauki alwashin sai ya manta wata banza Nu'aymah a zuciyar tasa har abada balle kuma wata Yusrah da tasan bata a gabansa.


“Hajiya Adawiya, ke dai kike kiɗanki kike kuma rawarki🤣😏”.


Haka ta yini ita kaɗai, daga kallo sai cin abinci da kwanciya. Gashi ta nema wayarta ta rasa, sai kawai tunaninta ya bata kota barta a gidane kokuma ta yaddata a jirgi Yah Abdallah ya ɗauke mata. Ta barsa akan idan ya dawo zata tambayesa.
Abdallah bai dawo hotel ɗinba sai kusan 11 na dare, harkokin kasuwancinsa ya yini yi hankalinsa kwance. Baiyi zaton iske Adawiya ido biyu ba. Amma a mamakinsa sai ya sameta zaune dirshen tana kallo. Sannu da zuwan data masa kawai ya amsa ya ɗauke kansa. Ya ɗauka kayan barci ya nufi bathroom. Tana nan zaune ya fito tsaf da shi. Nanma bata ishesa ko kalloba ya zauna a ɗaya daga rukunin kujerun ɗakin yay kira a kawo masa tea. Babu jimawa akai knocking ƙofar. Adawiya ta miƙe jiki na ɓari zataje ta buɗe ya ɗaga mata hannu. Da kansa ya tashi yaje ya amso ya dawo yay zaman sha bayan ya kunna laptop.
Sunja tsahon lokaci zaune, Adawiya nata faman kallonsa kamar ta samu television, shiko aikinsa yakeyi tamkarma ya manta da ita a cikin ɗakin.
“Uhhm Yah Ab dan ALLAH ko kaga wayata?”. Cak ya tsaya daga aikin da yake yana sake tsuke fuska batare da ya kalleta ba. Ba komai ya jawo hakanba sai Yah Ab datai kiransa da shi. Dan Nu'aymah itace ta fara kiransa da suna har kowama ya ɗauka. itace kuma ke kiransa hakan a koda yaushe. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya girgiza mata kansa kawai ya cigaba da abinda yakeyi.


★★★★


Haka suka cigaba da tafiya a kwanakin da duk suka gabata na barinsu ƙasarsu. Adawiya duk a takure take, dan Abdallah kullum da sassafe yake fita, bazai dawoba kuma sai sha ɗaya. amma soyayya ta rufe mata idanu ta kasa jin zafin hakan da yake mata.
Shiko gaba ɗaya ya ɗauketa yasa a kwandon shara ya maida hankalinsa ga kasuwancinsa kawai, dan a maimakon kwana goma da ya shirya yi a ƙasar ya maidashi kwana shida zasu wuce.


Tun a randa Nu'aymah ta dawo gida yay mafarkin hakan da daddare, aiko tunda asuba yay kiran Number Ahmad. Cike da farin ciki Ahmad ɗin ya sanar masa komai, dan dama shima yana da shirin kiran nasa, so yake kawai jikin Nu'aymah aga yanda zai kasance a washe garin.
Karan farko da tun faruwar al'amarin nan Abdallah yay sassanyan murmushi hawayen farin ciki na cika masa ido. Jiyake tamkar an tsundumasa aljanna yau. Yana katse kiran ya kira Momy itama. A lokacin dawowarta kenan daga sashen hajjo taje ta duba Nu'aymah itama.


Bayan sun gaisa cike da so da ƙaunar juna irin ta ɗa da uwa, ya tambayi lafiyar kowa a gidan sannan cike da zumuɗi yace, “Momy ashe Nu'aymah ta dawo?”.
Jimm tayi kamar bazata amsa masaba, sai kuma tace, “Uhmm! ta dawo jiya”.
“Kai Alhmdllhi Momy, yanzu zanje na saya mana tickets kuwa mu dawo, in ALLAH ya yarda wannan karon bazan sake ta sake kuɓuce minba Momy, a yau ɗin nan ina durowa koda magriba ne sai an ɗaura mana aur......”
“Kai! Shashasha dakata min. To idanma mafarki kake maza ka farka ka dawo hayyacinka. Wai kai Abdallah wane irin sakaran banzane halan? Ka fita idanuna tunkan na rufesu da kai a ciki wlhy. Bara makaji na maka mai kankat. Wlhy tallahi idan naga ƙafarka a ƙasarnan batare da ni nace kazoba ALLAH ya isa ban yafe maka ba.....”
“Momy!!” ya faɗa cikin tsananin tashin hankali.
“Yes! Abinda kaji shi na faɗa. Idan zakai haƙuri da waɗanda aka baka kayi. Hauka akeyi da za'a manna maka mata har uku ƴan family ɗaya uban ƴan son zuminci? Itama Yusrahn ina nan ina nema maka hanyar barinta wlhy. Adawiyar dai ta tsira tunda ALLAH ya sota ka baro ƙasar da ita da wuri. Idan suma sunada nasu zaɓin nima inada nawa ai, amma aka nunamin fin ƙarfi da ƴan uwantaka. Kai kuma shashasha da yake baka kishina hakan ko damunka bayayi. To wlhy kama cire wannan tunanin a ranka. Kuma ko a waya ka kira wani cikin iyayenku kace a ɗaura maka aure da Nu'aymah shima ban yafe makaba. Idan wannan maganar tasa ka kirani karka sake kirana”.
Ta katse wayar batare da ta jira cewarsa ba.



Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login