Showing 90001 words to 93000 words out of 260160 words
Chapter 31 - SARAN BOYE Complete Document by Billyn Abdull .txt
raɓashi zata wuce. Sake shan gabanta yayi yana mazurai, “Nabaki izinin tafiya ne?”.
Idanunta cike da ƙwalla tace, “To idan na zauna mizan maka? Kodan kaga nazo na zauna a gidanka kakeson ƙuntata rayuwata?”. Hannu ya ɗaga tamkar zai ƙwaɗa mata mari sai kuma ya fasa ya dunƙulesa yana taune lip ɗinsa jikinsa na tsuma. Yace, “Uban wanene Ameer?”.
Cike da takaici Nu'aymah ta kallesa ta watsar, kamar karta bashi amsa sai kuma mamakin abin nasa yasa ta kallesa da ƙyau. “Ban gane mikake faɗa ba Yah Ab?”. A hasale yace tayaya zaki gane mara mutunci. Nu'aymah wai harni zaki iya gudammawa a daren aurenmu saboda wani jaki? Kinsan baƙya sona miyyasa kika yarda aka saka mana ranar aure?”.
Sallamar Adawiya da batai zato ko tsammanin Abdallah zai dawo gidan a wannan lokacinba ya hana Nu'aymah da mamaki ya kume bashi amsa. Turus Adawiyan tayi tana kallonsu, dan wanda bai saniba zai ɗauka ne wata maganar arziƙi sukeyi da juna.
Binsu take da kallo tamkar idanunta zasu zubo ƙasa, Abdallah yay ƙaramin tsaki yana barin wajen ya nufi ɗakinsa. Har Nu'aymah ta cira ƙafa itama zata bar wajen Adawiya ta dakatar da ita ta hanyar riƙo mata hannu. Juyawa tai tana kallonta fuska a haɗe sosai, “Malama sakeni”. Nu'aymah ta faɗa a hasale.
“Anƙi a sakekin, idan kin isa kiyi duk abinda zakiyi. miya haɗaki da mijina?”. Kallon tsantsar mamaki Nu'aymah kema Adawiya, sai dai kuma a fili saita saki lallausan murmushi da har ya bayyana haƙoranta. Tace, “Tunda kinsan mijinkine mizai hana shi kije ki tambayesa miya haɗashi dani? Inaga kamar hakan zaifi birgewa a gareki shashasha kawai”. Ta ƙare maganar da fisge hannunta tai gaba tabar Adawiya da huci.
Hajjo data hango tahowar Nu'aymah saita saki labulen cikin ɗakin ta zauna a bakin gado. A haka Nu'aymah ta shigo ta sameta. “Hajjaju kin tashi ashe?”. Nu'aymah ta faɗa tamkar babu wani abu daya faru. Murmushi Hajjo tayi tana kallonta, “Ba dole na tashiba tunda kin gaza zuwa ki tadani mu wuce massallaci”.
Kusa da ita ta zauna tana dariya, “Ho hajjonmu, yanzu kuma dana tadakin cazaki ban barki kin rintsa ba, gara mu maidake da ƙwarinki karsu Abba suga kin sake rugurgujewa”.
Duka Hajjo ta kaima Nu'aymah da filo. Hakanne ya sakata tashi ta shige bayi da gudu tana dariya. Cike da tausayinta Hajjo ta sauke ajiyar zuciya, a ranta kuma tana ƙulla abubuwa da dama game da rayuwar Nu'aymahr
A falo kam Nu'aymah na shigewa Adawiya ta nufi ɗakin Abdallah a fusace, babu ko sallama ta tura ƙofar ta shiga. Sai dai ganinta yay kawai a kansa kamar an jehota. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. Hakan ne ya sake hasala mata zuciya, sai ta fashe masa da kuka. “Yanzu Yah Ab abinda kakemin kana ganin adalcine? Ni dake matarka baka da lokacina amma kanada lokacin dawowa gida da wuri dan ka kasance da Aymah? Badan ALLAH yasa yau na shigo gidan da wuri ba bama zansan hakan na faruwaba tsakaninku. Shin wai da mi Nu'aymah ta fini ne? Wlhy sai ALLAH ya sakamin duk cin amanata da akeyi, kuma ni na gaji zan kira baba malam na faɗa masa komai tunda naga ita hajjo goyon baya take baku ma, ƙilama wataran a gabanta zaku shiga ɗaki ku rufo bazata tankaba saboda tana tsoronku......”
Wani wawan mari ya sauke mata a fuska da saida taga stars na mata kaikawo, balle dama ga azumi. A take ta zube ƙasa da sakin wata ƙarar kuka data kai har kunnen Hajjo.
“Kai Abdillahi lafiya kuwa? Mike faruwa hakane nakejin kukan Adawiya?”. Ta ƙare maganar tata dai-dai lokacin da take ƙarasowa cikin ɗakin. Ganin Adawiya kwance ƙasa dafe da kunatu ya saka hajjo zaro idanu, “Mikai mata Abdullahi?”.
Cikin ɓacin rai yace, “Hajjo barni da ƴar iskar nan kawai, wlhy tai wasa wataran saina karya ƙasusuwanta a gidan nan tunda ita kamar dabba take”.
“Ya isa haka”. Hajjo ta faɗa tana ɗago Adawiya dake ƙasa tana cigaba da sakin gunjin kuka. Saida ta zaunar da ita saman kujera sannan ta sake tambayar Abdallah miya faru?. Faɗa mata komai yayi amma banda tsayuwarsu da Nu'aymah, baisanma ita taji komaiba.
Cikin ɓacin rai Hajjo tace, “Adawiya dama baki da wayo haka? Ita ƴar uwar takice kuma tazama abar kishi a gareki? Har kike jifansu da wannan mummunan lafazin ita da mijinki? Adawiya yaushe kika bari ƙawayen banza suka canja miki tarbiyya ne? Har haka. To wlhy ki shiga hankalinki, idan kuma ba hakaba ni bazan ɗauki wannan banzan halayen a cikin zuri'ata ba, saina ɓatama kowa rai a cikinku har iyayen naku ni babu ruwana. Bandama iya shege kowa na fama da ibadar ALLAH a baki ke kina biyema sheɗan yana ɗoraki akan dokin zuciya. To idan na sakejin makamancin wannan zancen lallai sai kinyi nadama shashasha kawai. Banda ƙaddara da yanzu ita wadda kike cin zarafin ba itace matsayin matar tasa ba”.
Haka Hajjo taima Adawiya tas sannan ta fito ta barsu. Duk abinda akeyi Nu'aymah najinsu, sai dai ko tari bataiba balle a fahimci ta sani ɗin. Daga ƙarshema sukai shiri suka wuce massallaci, suda gidan kuwa sai anyi sallar asuba kuma.
Tun daga wanan ranar Adawiya ta shiga fishi da kowa a gidan. Daga gaisuwa bata sake tankama wani. Ahmad yamata nasiha harya gaji ya watsar da ita shima. Bayan kwana biyu da yay dai-dai da cikarsu kwanaki biyar da zuwa, ashirin kuma ga watan azumi Nu'aymah ta tattara inata-inata ta koma massallaci zaman ittiqafin.
Abdallah yaso hanata, sai dai Hajjo tace ya barta tai ibadarta yamafi zaman nata a gidan aita fitina. Badan yasoba ya haƙura, dan yaso a wannan zaman suyi magana ta fahimta da Nu'aymahr ya samu ya lallaɓa hajjo dasun koma a ɗaura musu aure.
Bayan barin Nu'aymah gidan sai ga Adawiya ta saki jikinta, ashe dama Nu'aymahr ce natsalar rayuwarta. Babu wanda yace mata komai. Saima hajjo ce taima Abdallah magana akan su shirya shi da Adawiyan dan tare zasu wuce Najeriya ayi bikin salla. Kai tsaye Abdallah ya nuna cewar bazaije ba, sai dai Adawiya, dan shi bai manta ALLAH ya isan da mahaifiyarsa tai masa akan zuwan nasaba.
Balbalesa da masifa sosai hajjo tai dan ita batasan dalilinsa na bijirewarba. da taga dai ya tirje ɗin saita kira baba malam ta faɗa masa komai. Shine ya kira Abdallahn cikin bada umarni ya sanar masa ya shirya suzo salla gida tunda suna samun hutu a wannan lokacin.
Abdallah ya shiga tsaka mai wuya sosai akan hakan, dan yasan dai umarnin mahaifiyarsa dana baba malam babu wanda yake da damar tsallakewa a ciki, dan duk sunada daraja da kima a idanunsa da rayuwarsa.
_________________________
*_NIGERIA_*
A kwanaki biyun nan abubuwa sun sake tsamari akan Yoohan, gaba ɗaya neman birkicewa yake saboda rashin samun barci, tun daga jiya zuwa yau yaƙi magana da kowa a gidan, yama kulle kansa a ɗaki ya hanama kowa ganinsa. Momy tayi kukan tayi roƙon amma yaƙi buɗewa. Hakama su Gebrail sunyi nasu ƙoƙarin ya sharesu.
Amma saboda ƙarfin hali da burinsa nason cika alƙawari sai gashi a safiyar yau talata yayi shirin tafiya kano. Tunda safe ya bama Solomon umarnin faɗama guards ɗinsa su tafi kano. Su kuma ya nema musu ticket guda uku. Solomon nason tambaya akan hakan yanajin tsoro, dan haka yaja bakinsa yay shiru yaje dai ya cika umarninsa
Kusan ƙarfe huɗu na yamma sai gashi ya sauka ƙasa cikin shigarsa ta suit blue mai haske. sun masa bala'in ƙyau duk da yana a yanayin da a kallo ɗaya zaka fahimci akwai damuwa tattare da shi.
Momy ce kawai zaune a falon sai Victoria da Abraham. Cikin girmamawa a garesa yaran suka shiga gaishesa. Hannu ya ɗaga musu kawai tare da ƙarasowa inda suke duk ya shafa kansu batare da yayi magana ba..
Ya maida dubansa ga Momy da idanunta suka kumbura saboda kuka, ɗauke kanta tayi ita a dole fushi take da shi. Baice komaiba ya ƙaraso inda take ya tsaya a gabanta tare da riƙe kunnuwansa da hannayensa alamar ban haƙuri.
Bata iya dogon fushi da Yoohan ɗinta. Dan haka tai murmushi tare da miƙewa ta rungumesa. Yau dai ya daure bai tureta ba, sai da ta gaji dan kanta ta sakesa sannan, ta amshi tie ɗin hannunsa ta ɗaura masa tana faɗin, “My Boy nikam yaushe zaka fara saka necktie da kanka?”.
Bai bata amsaba, sai dai ya sake ɓata fuska alamar shagwaɓa. Da ƴar dariyarta ta shafa masa kwantaccen sajensa da yasha gyara yau, ya kama hannun nata ya sumbata kaɗan.
“Ina zakaje ma wai?”. Ta tambaya tana tsatstsaresa da idanunta manya. Da ƙyar ya buɗe baki wajen bata amsa da “Kano”. “Kano!! kuma Yoohan? Mizakayo a kano kaida kake cikin wannan halin? Badai aiki ba?”. Kansa ya girgiza mata, batare daya bata wani ƙarin bayani ba yace mata, “Bye” yana nufar ƙofa.
Saurin binsa tai tana kira, amma sai yaƙi tsayawa, saida ta haɗa daɗan gudu ta cimmasa, duk da kuwa tafiyarma ba wani sauri yakeba saboda rashin ƙwarin jikinsa. Yanda ta riƙosanne ya sakashi waigawa ya kalleta. Tace, “Ina tambayarka mizakayo acan amma ka taho baka kulaniba Yoohan”.
Kansa dake faman masa ciwo ya dafe kaɗan, kafin cike da ƙosawa yace, “An gayyaceni ne” danshi baison yin ƙarya a rayuwarsa, kamar yanda ya tsani kuma saɓa alƙawari. Yana gama faɗa ya zare hannunsa zai juya ta kuma riƙewa. Yanzunkam bai juyoba sai da yaja wasu sakanni. Muryarta da damuwa ta zagayo gabansa tana magana. Amma maimakon ya bata amsa sai ya saka yatsansa akan baki yace “Shiii!!!”.
Shirun kuwa tayi tana kallonsa, ya ɗaura yatsunsa saman baki yay mata alamar *_Smile_* kamar yanda ya saba mata aduk sanda ya ganta a damuwa tun yana yaro. Duk da batason yin hakan saita murmusa. Yay mata jinjina yana ɗan lumshe idanunsa dake a kumbure sosai.
Tanaji tana gani ya shiga mota driver ya jasu shi da Solomon suka bar gidan, gashi Papa bayama ƙasar jiya sukai tafiya shi da Uncle Zamani.
★★★★★
Airport driver ya kaisu. inda acan suka haɗu da Manager Hamza Ibrahim yana jiransu. Sun gaisa cikin mutunta juna Hamza na mamakin ganin Yoohan ɗin a ƙunci fiye da waccan ranar. Ga idanunsa da fatarsu tai jajur hakama farar fuskarsa. Haka kawai yaji a ransa akwai abinda ke damun Yoohan ɗin. amma sai baiyi magana ba suka nufi ciki.
Ƙarfe biyar da rabi jirginsu yabar Abuja zuwa birnin dabo kodami kazo mun fika🤗😜.
Kamar yanda Yoohan ya iske Guards ɗinsa na jiransa haka suka iske motoci biyu na tarbarsu kuma. Hakan ya sai ya sake birge Yoohan matuƙa, dan haka bai shiga tasa motarba ya shiga wadda aka aiko musu, Guards ɗinsa kuma suka bisu a baya.............✍
No. 24
...............Baba malam daketa kaikawo na ƙoƙarin ganin komai ya kammala yanda yake buƙata ya nufi sashen nasa a karo na babu adadi. Yanda ya hana kansa sakat akan tarbar baƙonsa haka ya hana Umm sakat itama, dan baiwar ALLAH nan tun ƙarfe biyun ran take a kan ƙafafunta tana hidima. Sauƙinta ma Addah ta shigo tana taimaka mata, ga kuma mai aikinta.
Omar ne biye da shi, dama yafi shaƙuwa da shi a samarin yaran gidan fiye da kowa, duk da dai ada kam sunfi shaƙuwa da Abdallah, amma daga baya da Omar ɗin yafi Abdallah zaman kano sai shaƙuwarsu ta zarce ta tsakaninsa da Abdallah ma. Dan shi Omar yarone mai tsananin ƙwazo da biyya ga iyayen nasa, sannan baba malam shine babban malaminsa na addini fiye da kowa, shiyyasa koda yaushe yana kano bai cika son zaman Abuja ba shi.
Kai tsaye kitchen suka nufa, inda suka iske Umm da Addah suma dai kamar su tsinke nasu ran, dan tare suke aikin daya rage ɗin. Bayan Baba malam yay sallama baima bari an amsa masaba yace, “Umm Muhammad yaya kun kammala?”.
Ɗagowa Umm tai taɗan kalli mijin nata, sai kuma ta maida akan aikin gabanta tana cewa, “Abban Nu'aymah wlhy nikam dai zakama sake rikitamu gaba ɗaya, insha ALLAH muna gab da kammalawar, dama zuwa kai kayi wanka dan magrib ta gabato”.
Murmushi shimfiɗe a fuskarsa ya ƙaraso yana amsar abinda take tace lemon mangwaron daya rage su haɗa. “Ke dai kawo na taimaka miki ki kammala kawai, dan yanzu haka an wuce ɗakkosu fa”.
Dariya Umm da Addah da Omar sukai, ya ƙaraso wajen baba malam ɗin yana faɗin, “Abba kawo ni nayi basai kayi da kanka ba. Dan nikam yau namafi kowa zumiɗin son ganin wannan baƙo mai daraja a wajenku Abba, dan naga gaba ɗaya hankalinku na kan son ganin an ƙyautata masa, yau kota abincin buɗa bakinmu bakwayi sai na baƙo”.
“Kace ido ka saka mana? Hakama malam ƙarami (baban yaron Addah) sai da ya gama ƙorafi kafin ya wuce airport ɗakkosu”. Ita dai Umm da Addah dariya sukayi musu kawai, ta matso suka ƙarasa haɗa komai ita da baba malam ɗin. yayinda Omar da Addah kuma suke ɗorawa tray. Omar ne ya ƙarasa kwashewa ya kai komai can sashen kakansu inda za'a sauke baƙon. Hakan kawai ya isa kasan an daratta baƙon sosai, dan duk baƙon da su Baba malam zasu kai da shigo dashi cikin gidansu to lallai ya isa kuwa.
Sai da yaga an fita da komai sannan ya sauke ajiyar zuciya, tare da ficewa domin aiki da shawarar Umm ta farko. Cike da gulma irin ta aminai Umm da Addah suka kalli juna, sai sukai murmushi kawai dan Baba malam ɗinne ya basu dariya.
Ficewa sukai a tare suma zuwa sashen da aka shirya abincin, suka ƙara gyara komai tare da saka turaren wuta da kuma Air Fresheners masu ƙamshi. Kamar Umm ta sani har zasu fito saita yanke shawarar fita da kaskon turaren, acewarta kar ko a baƙin asamu mai Asthma ya cutu. Ta ɗan ɗaga labulen Windows ɗin kaɗan hayaƙin turaren ya ragu sosai. Cikin sa'a ma sai gashi Omar yaje ya tada Genretor. Ac suka kunna tare da sake duba komai suka tabbatar yayi dai-dai sannan kowa ya nufi part ɗinsa Umm nama Addah godiya.
Dan tasan badan itaba da aikin baiyi sauriba sam. Mama amaryar Abba Musbahu kuwa dama ita sai a hankali ce, San jikinta bai bari tama kula da sashenta ba balle taimakon wani kuma, komai ƴan aikine keyi, kodan taga mijin ba mazauni bane oho.
Motocin na shigowa anguwar ana fara kiraye-kirayen sallar magriba. Yoohan na kwance shiru a jikin kujera idanunsa a lumshe. Baisan inda ake shiga da fita ba har saida motocin suka tsaya a ƙofar katafaren gate ɗin. Hakan sai yayi dai-dai da fitowar baba malam da Abban su Adawiya, sai Malam ƙarami da Omar da sauran samarin gidan da yara amma iya mazan kawai.
Duk da yanda guards ɗin Yoohan suka firfito suka zagaye motar da yake a ciki hakan bai saka fuskokin su baba malam sauyawa daga fara'ar dake tattare da suba. Akan idonsu Hamza Ibrahim ya fita. Kafin Yoohan da Solomon ya buɗemawa shima.
Shima a gaban idanun nasu ya fito, bayan ƙafarsa kuma da sarƙar Cross ɗinsa suka fara cin karo kafin cinkusashshiyar fuskarsa. Abinda zai baka mamaki a tare su baba malam sukayo caa a kansu. Cikin ƙyaƙyƙyawan tsari na masu ilimi da baiwar hikima suka tarbesu. Wani iri Yoohan yaji a ransa shima duk da kuwa dama ya fahimci masu gayyatar tasa musulmai ne, amma sai ya dake ya basar.
Duk yanda yaketa faman musu shan ƙamshi da cika da batsewa babu wanda ya canja yanayin nasa, saima sannu da zuwa da suka shiga jera musu tare da basu hannaye suna musabaha har guards ɗin. Kafin baba malam ya bama Malam ƙarami da Omar damar shiga da Yoohan ɗin ciki. Danshi Hamza Ibrahim ya buƙaci a inda zaiyi alwalane kai tsaye.
Yoohan dai baiyi musu ba yabi bayan su Omar, sai dai idonsa da zuciyarsa nakan hasaso masa a inda ya taɓa sanin fuskar baba malam a rayuwarsa. Guards ɗinma bin bayansu sukai. Omar zaiyi magana baba malam ya girgiza masa kai alamar ya barsu.
Tun a farkon shigowa gidan Yoohan yasan masu gidan sun wuce raini, dan babu abinda nasu gidan zai nuna masa sai dai kayan ƙawa da ƙyale-ƙyale, nasu baba malam ma yafi nadu girma sosai. A haka su Omar suka kaisa har falon, guards ɗinsa biye da dasu