Showing 291001 words to 292821 words out of 292821 words
Chapter 98 - NIHAAD COMPLETE DOCUMENT Complete by Khalisat Haidar .txt
har rashin mutunci kike mana a kansa, Umma tace to mu bi maki ta karkashin kasa mana, da so tayi ma mu bi ta zuwa gidan Malamai amma ko wacce xata kawo ɗan abinda za a ba ma malam don tace bata da kudi ita a lokacin, shine Husnah ta tuna wannan video dinki dake wayanta wanda tayi maki sanda kika koma hostel da zama, ranan mun je zaria mun sauka wani hotel za ayi Birthday din wata kawar Naf, gaba dayanmu sai muka sa maki kwaya a drink dinki kin fita kiyi waya da Abbanki, mu ma duk mun saka a namu tunda mun saba sha, wllh wllh ba don video dinki ya tafi viral aka yi ba Nihad, mun yi sa kawai saboda nishadi, we did it da wayar Husnah just for fun saboda yanda kika dinga reacting very drunk after taking the juice, Da Umma ta kawo mana batun zaki yi aure ki bar mu and we are doing nothing about it kuma ta nemi mu kawo kudi ta kai mu gidan malami sai Husnah ta tuno da video din da tayi maki, wallahi Umma ce cause din sakin wannan video din a social media, da mun bi ta Naf ma baza a saki Video din ba don she was against that amma saboda son zuciya ni da Husnah sai da muka bi bloggers muka tura masu video din duk don Aliyu yace ya fasa aurenki, don girman Allah ki yafe min Nihad, ita dai Husnah ta rasu, ni ma dai kinga ga yanda rayuwa ta mayar da ni a yau, bani da sauran gata a duniya mahaifiyata ma cewa tayi in koma inda na fito kar in kashe mata aure da naje wajenta a kauyen da take, duk samarin sun gama amfani da mu sun gujemu ga cuta mun kwaso ma kan mu, duk inda muka yi gudunmu ake yanzu, karatun ma Naf kadai ce ta gama a cikin mu ita din ma dai da pass, tana gamawa kuma babanta ya aura ma abokinsa me mata biyu ita..." Kuka Zully take sosai kamar ranta zai fita kana ganinta kasan tayi nadama ainun, Khalil ya dinga kallonta fuskarsa daure yana jin zuciyarsa na tafarfasa, Nihad ta kasa cewa komai banda hawaye babu abinda ke sauka idonta abubuwa masu yawa na dawo mata, no wonder ta kasa gane inda aka yi video din don in da a hotel dake garin kano ne dole zata sani, har kasa Zully ta durkusa tace "Kiyi ma girman Allah ki yafe min Nihad, ya kai ya kawo sai ina bin eatry da manyan malls ina baran abinda zan kai baki, duniya ta juya min baya ga ciwo ina fama da shi kuma bazan boye maki ba wallahi nima HIV din gareni Nihad, yanzu haka karfin hali kawai nake, da kinga inda nake kwana ma zaki san ta kare min a rayuwa Nihad" Khalil ya kalli Nihad yace "Shigo mu tafi Baby" ta kallesa hawaye na sauka idonta tace "Pls let help...." Wani tsawa ya daka mata wanda bai taɓa mata irinsa ba, ba shiri tayi shiru, ya wani hade rai yace "Shigo mota nace" Zagawa tayi ta bude motar a hankali ta shiga, Zully ta biyota da gudu tana kuka tace "Don Allah ki ɗan taimaka min ko da kudin magani ne Nihad...." Khalil ya kulle motar ya sauke glass yana kallonta da kyau yace "This should serve as a lesson to people with the kind of ur heart" Yana fadin haka ya ja motarsa ya bar wajen Zully na kuka sosai tana bin motar da kallo, Nihad dai sai share hawayen da yaki tsaya mata take, bayan sun isa gida Nihad ta shiga dakinta duk jikinta a sanyaye maganganun Zully na dawo mata, dama su suka yi mata video din nan har suka ba Bloggers suka baza shi a duniya they cause all her pain in life, tunanin hakan yasa ta fashe da kuka sosai, a haka Khalil ya shigo dakin ya sameta, ya rungume hannunsa yana kallonta a hankali yace "Duk abinda ya faru ya faru ne in ur favor Nihad, and kin yarda cewa every disappointment is a blessing in disguise?? Ur disappoinment was nothing but a blessing to you Baby, da basu maki hakan ba u will end up marrying Aliyu, who is a bloody liar and a gangster, his wicked mum will become ur mother inlaw, abinda baki sani ba Aliyu ko 5 daily sallah baya yi, ba shi da aiki sai shaye shaye da neman mata daga wannan kasar zuwa wancan kasar duk da kudin Abbana, we grew up together na fi kowa sanin waye shi nasan mugayen halayyansa, babu kalan giyar da baya sha, ya saukar maki da kai ne saboda ya gama cin duniyarsa yana neman mace warce yasan ba a lalata ba ya aura yayi settle down, da ace kin auri Aliyu sai kin fi regretting akan abun da ya sameki a baya, mahaifiyarsa bata san Allah ba, bata kuma kadaita Allah ba, she is a devil in human form, amma kin ga da yake zuciyar Mum dinki is clean and pure shi yasa Allah ya sauya maki jarabawan auren Aliyu zuwa wani daban...." Nihad na goge hawayen da suka ki tsaya mata tace "Haka ne" Ya karaso ya zauna kusa da ita ya jawota jikinsa, murya can kasa yace "Da duk abinda suka faru basu faru ba, da ba mu yi aure har mun samu Aaryaan ba" Ta lumshe ido tana shaƙar daddadan kamshin jikinsa cikin sanyin murya tace "Ina alfahari da kasancewar ka mijina, Allah Ubangiji ya bani ikon yi maka biyayya in bi ka sau da kafa har karshen rayuwata, Allah ya tsare min kai da tsarewarsa ya kara maka arzikin da zae amfani al'umma mijina...." Ya rungumeta sosai yace "Ameen my wife, Allah ya sa ki haifo min yan biyu sau biyu" Ta lumshe ido tana murmushi a hankali tace "Ameen my world" ya dago kanta yace "Aryaan na cika 3 months zaki yi resuming school, and in sha Allah har masters sae kinyi Baby...." Nihad ta kasa ce masa komai tana jin sabon sonsa na shigarta, cikin sanyin murya tace "Promise me duk sanda mu ka kara ganin Zully zaka taimaka mata da duk abinda Allah ya hore maka kaga tace magani zata siya" Yayi shiru sai kuma yace "I promise u my love" Tayi kissing dinsa tace "Thank you Abuu Aryaan" kissing her also yace "U are welcome Ummu Aryaan, some other time xan baki labarin encounter dina da Husnah when she came to spend the night at our place back in kano" Daga kai tayi ta kallesa da sauri, taga yana murmushi.... lumshe ido yayi ya fara kissing dinta passionately.
Mumy ta samu kwanciyar hankali fiye da yanda tayi zato a gidan Janar Ahmad, so na hakikanin gaskiya bawan Allahn ke mata, taga yana da wasu dabi'u in common da marigayi Abba, he is such a caring husband, and bai rageta da su Fadil da komai ba a gidan, Ga er sa Maryam warce hankali har yayi mata yawa, Mumy ta dauketa kamar ita ta durkusa ta haifeta, Mumy bata yanke alaqarta da Umma ba don suna yawan gaisawa ta waya duk bayan wani lokaci, har ma Amina kan zo gun Mumy ta mata kwana biyu a Abuja sannan ta koma, ba a cikakken sati biyu sai Nihad ta je gidan mahaifiyarta, don wannan satin in taje gun Mami, to wani satin gun Mumy zata je, lokaci lokaci kuma tana zuwa gidan Hajiya Safeenah, at times kuma saboda Nadeeyah take zuwa gidan wanda suka zama very best of frnds yanzu.....
And every one of them lived happily ever after!!!😊
_Kar ki manta er uwa idan kinsan baki sauke hakkina na dari biyar dake kanki ba ina me maki tunatarwar karshe ki sauke don na zo karshen littafin, idan kuma baki biyani a nan ba to ban san inda za mu hadu ki biyani ba, and lastly ɗan abinda ka raina might definitely be ur doom one day, i neva sold the copywrite of Nihad balle kice ai wani ya siya ya baki, but no p we shall meet somewhere one time in sha Allah_ Masu zagina without me knowing them kuma za mu hadu a inda ya kamata 🤗
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah.
07087865788...
Gaisuwa ta musamman zuwa ga Hajiya Asabe Hassan, ina maki fatan alkhairi Aunty, Allah ya jibanci lamarinki ya raya maki zuri'arki Ameen.
*Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! a nan na sauke littafina me suna NIHAAD* darussukan dake ciki Allah ya sa mu amfana da su, kurakuren dake ciki kuma Allah Ubangiji nake rokon ya yafe min.... *Na kuma sadaukar da littafin nan zuwa ga Mijina Barrister Ibrahim Khalil, ina alfahari da kai ina kuma godiya da ara min some of ur time to do what makes me happy... Allah ya saka maka da gidan Aljanna ya daura ka kan makiyanka, Allah ya kara maka arziki da zai amfani al'umma, thanks for the encouragement and support from the beginning of the book Nihad till the end, u were always by my side all through the long journey, i appreciate you so much dear, Allah ya kara mana zaman lafiya da kwanciyar hankali.....*
My *Mother* Hajiya Hajarah and my sweet *Dad* Alhaji Bello Ahmad.. Allah ya kara maku lafiya da kwanciyar hankali, Allah ya saka maku da gidan aljanna, Allah ya kara maku arziki da wadata ta inda baku zato, ina alfahari da kasantuwarku iyayena. My siblings Allah ya raya min ku gaba daya, Maryam Bello ga gaisuwarki a kyauta!!! My cousins ina kewanku gaba daya, Allah ya raya min ku....
Aunty Zahrah mai gari, Deejah, Chamo, Aisha Bela, Aunty Amzaj, Mom twins, Aunty Maryam, Maman Farida, Aisha Abdul, Sis Safiyya, Aunty Inna, Damsel, Aneesah, Mrs Bello, Rabi'ah, da duk members din Khaleesat palace da ya kamata in ambaci sunansu a nan ina alfahari da ku wllh, ina kuma yi maku fatan Alkhairi duniya da lahira, Allah ya raya maku zuri'a, kafin wasu su yi patronizing dina ku ne farko as usual, Allah ya kara maku budi Ameen. Scentmania, KMZ, Albaita-Al-sahal, Sapna borno incense Allah ya karo maku kasuwa ta yanda ba kwa zato.
And finally my lovely fans that patronized me, ku ne farko ku ne karshe as usual, wallahi ina yin ku, without u all they won't be Khaleesat Haiydar, Allah ya jibanci lamarinku, ya kara maku arziki from every angle, ya kara ma iyayenku lafiya da wadata... Ameeen, Nagode Nagode Nagode ina alfahari da ku.
*I need 10 concrete lessons from this book, kuma duk wanda ya rubuto lessons din ya turo min i will check the best and i promise 3000 recharge card to the person with the best write up, idan kuwa wanda bai siya littafin bane na yafe masa karantawar da yayi a kyauta sannan in kara masa da recharge card na 1500* Idan kuma mutum bai son katin sai inyi masa transfer.... Goodluck😊
07087865788
Taku har ko da yaushe Hauwa Bello Jiddah AKA _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻