Showing 147001 words to 150000 words out of 292821 words
Chapter 50 - NIHAAD COMPLETE DOCUMENT Complete by Khalisat Haidar .txt
su Sudais, daga haka yace "Bari in ba Aunt dina ku gaisa" Mumy tace "Toh..." daga haka ya mike ya kai ma Aunty Maryam wayar, suka gaisa, nan Mumy tayi mata godiya sosai kamar tasan issue din da ake kai, Aunty Maryam tace "Ahh ba komai Hajiya ai ɗa na kowa ne, ke dai ki kwantar da hankalinki in sha Allah komai xai daidaita, kawai kiyi ta bin ta da addu'a domin kuwa addu'an ki gareta baxai ta6a faduwa kasa ba, Allah Ubangiji ya rufa mana asiri ya kara daura mu akan makiyyanmu" Mumy taji dadin wannan furucin na Aunty Maryam, nan kuma ta kara jin hankalinta ya kwanta ta samu relieve, suka yi sallama Aunty Maryam ta mika masa wayar, ya amsa Aunty Maryam tace "Ka ba Murja ta kai mata wayar su gaisa ko yau tayi trying kiranta da wayana bai shiga ba" Khalil ya mike ya nufi dakin da Nihad take, ko kwankwasa kofar bai yi ba ya bude, ta juya da sauri don ko Aunty Maryam kafin ta shigo tana mata Knocking haka ma Mus'ab ko mai aikin gidan, ta ci gaba da game din da take a Ipad din Mus'ab, ya karaso cikin dakin ya sake dialing number Mumy yana fara ring ya mika mata wayar, ta amsa tana kallon screen din ganin Number Mumy ta kai kunne da sauri, you can tell how happy she is da take magana da Mumy, Mumy ma ta kara samun nutsuwa jin how lively her daughters voice is, Nan dai Mumy ta kara mata nasiha a kan ta bi mijinta, Nihad dai tayi shiru har Mumy ta gama, sannan tace "Toh nagode Mumy, Allah ya saka da Alkhairi" Mumy tace "Yauwa ki gaida yan gidan gaba daya" Nihad tace "Toh Mumy a gaida min da su Sudais" Daga haka ta katse wayar ta mika masa without looking at him, ya rungume hannunsa bai amshi wayar ba yana kallonta da kyau yace "Wato kin dawo da rashin kunya da fitsaran da kika saba yi ma mutane ko?? Kuma i am hoping kin dai tabbatar ni ba sa'anki bane yanzu in all aspect" Ta juya ido tace "To dama ai ba dainawa nayi ba" Sake baki yayi yana kallonta, Ta jefa masa wani kallo tace "Kuma da kake wani daddaga min shoulder 2 days back naga dai babanka ne mai kudi ba kai ba, kuma gidan babanka ne ba naka ba, duk motocin gidan nan na babanka ne not urs, all those securities are for ur father not you, don haka ka jira sai kayi naka kudin kafin ka dinga daga min shoulder kana forming, thinking u are not my mate in all aspect...." Kallonta ya dinga yi da mamaki, ya dake yace "Ke me yasa baki jira kinyi naki kudin ba kike daddaga naki shoulders din da kudin babanki a gidanku" Ta turo masa baki tace "Toh ai ni macece, kuma ni yarinya ce yar karama ban san abinda nake ba" ya kai hannu xai yi squeezing bakinta yace "Sha'awar gado ce ba yar yarinya ba" Ta koma baya da sauri tana kallonsa, ya hade rai yace "Na maki iya abinda xan iya maki albarkacin mahaifiyarki da mahaifinki amma ba don halinki ba domin baki cancanta ba, it's now left for u ki zauna gidan mutane kisan ba gidanku kike ba yanzu, ki kwantar da kanki, ki gane you are now a NOBODY, kina gida ne wanda level dinki bai kai nasu ba, baki wuce kiyi wanke wanke a gidan ba a biyaki, shi ma by luck xaki samu don mu masu degree muke dauka suyi mana aiki a gida.... Dai dai nan aka bude kofar dakin, Aunty Maryam na tsaye bakin kofa tace "Basu gama wayar bane?" Nihad ta mika masa wayarsa tana kallonsa, ya amsa shi ma yana kallonta, dauke kai tayi ta nufi kofa, Aunty Maryam tace "Pls ki yi feeding din Mus'ab, ko na basa ni ba ci xai yi ba" a hankali Nihad tace "Toh" Sannan ta fita, Aunty Maryam ta juya ta bi bayanta, sai a sannan shi ma ya fito parlor, Aunty Maryam tace "Ji Ayman da nake maka magana dazu ina buda WhatsApp yanzu naga message dinsa wallahi" Khalil dai kallonta kawai yayi ya zauna, sai kuma yace "Toh Allah ya baku nasara" Aunty Maryam tace "Ameen" Yace "Xan je gidansu Nadeeyah, sai da safe Aunty" ta gefen ido Nihad dake ba Mus'ab indomie ta kallesa, Aunty Maryam tace "To a gaisheta" Ya mike yace "Xata ji" Daga haka ya nufi kofa ya fita. Har Khalil ya koma Kasar Tanzania ranan lahadi bai koma gidan Aunty Maryam ba, ya dai mata forwarding admission letter da komai na Nihad ta e-mail dinta ranan lahadin kafin ya tafi, Aunty Maryam tayi murna sosai ganin Nile din ya samar mata kuma ta samu, Aunty Maryam ta fito parlor tana kallon Nihad looking so happy for her tace "Congratulations Dear, ga admission letter dinki...." Nihad ta amshi wayar da Aunty Maryam ke nuna mata, ta dinga kallon sunan makarantar as if she wants to be sure, wannan ai Nile take gani, can ta kalli Aunty Maryam tace "Aunty wani makaranta ne?" Aunty Maryam tace "Nile University my dear" Sai da Nihad tayi shock jin da gaske sunan da take gani jikin screen din wayar ne, Nihad tayi karfin halin cewa "Aunty na ina?" Aunty Maryam tace "Wanda dai kika sani" Nihad ta zaro ido tace "Aunty waye ya biya min makarantar?" Aunty Maryam na Murmushi tace "Khalil, he paid the tuition fees and everything, don haka it is good to be good, as a result of the goodness ur father did to him, he is also doing u good by sponsoring you to one of the costliest university...." Lokaci daya Nihad taji bata son zuwa makarantar kuma baxata je ba, amma bata ce ma Aunty Maryam komai ba, Aunty Maryam tace "Anjima xan kirasa in baki waya kiyi masa godiya" A hankali Nihad tace "Toh" Da daddare kuwa Aunty Maryam ta zo har daki ta kawo mata wayar, Nihad ta amsa Aunty maryam ta juya ta fita, ko sallama bata yi masa ba a takaice yace "Bana bukatar godiyarki ba don ki gode min na maki ba, sannan ba don kinyi deserving nayi maki ba...." Nihad tace "Toh ai ba godiyar xan yi ba dama, da ka kwantar da hankalinka kaji abinda xan ce maka kafin ka yanke hukunci.... If you are lucky xa su maka refunding ka sanar masu suyi maka, don baxan je ba"
Abba ne xaune parlonsa da Umma dake yanka masa lemo, yace "Kamila ta zo gida ne?" Umma ta kallesa tace "Aa bata zo ba, rabonta da gidan nan ai xai yi sati daya" Abba yace "Ohk na fito masallaci yanzu mijinta ya kirani" Umma ta ajiye wukar hannunta tace "Lafiya dai ko?" Abba zai yi magana aka doka sallama bakin kofa, duk suka kalli kofar, Umma ta amsa ta mike, Inna ta shigo parlon Umma na mata sannu da zuwa da fara'a tace "Saukan yaushe Inna?" Inna ta saki baki tana kallonta, can tace "Da naje ina?" Sai kuma ta ja tsaki bata kara sauraronta ba tana kallon Abba tace "kai Ibrahim kira sabon drebanka maza ya taso ya kai ni wajen jikata ba kashe mutum tayi ba da xan yanke alaka da ita haka kawai, balle babu laifin tsaye balle na zaune sharri ne aka mata, abinda wasu haka zaka ga an masu bedion da mamansu saɓaɓar saɓaɓar a titi, sannan babu dan kamfai a jikinsu mazaunansu mala mala, matancinsu duk a titi, sai ita da idan ba ido mutum yasa sosai ba baxai san babu kaya a jikinta ba, wallahi wani ma tunani xai yi yar shekara shidda ce a bedion indai bedion da aka nuna min ne, bashi da wani aibu da har za a kullace yarinya a banzatar da lamarinta haka, bayan an aura mata gansameme da bamu san isilinsa ba ko ɗan yankan kai ne, ko ɗan kinnafin ne, ko ɗan fashi, oho duk dai bamu sani ba, duk da haka kuma mu fita harkarta? to na dawo hayyacina maza maza a kai ni gidan jikata in ga halin da take ciki yanzun nan"
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
07087865788
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: 💖💖 NIHAAD 💖💖
44
Mikewa Nihad tayi bayan ta tuna wayar da Aunty Maryam ta bata, ta sauko daga kan gadon ta tafi inda empty bags din suke ta duba wanda wayar ke ciki bata gani ba, mamaki ne ya cikata ta dinga kallon jakar, ta duba second bag din nan ma taga babu wayar babu alamarsa, Knocking aka yi a kofar dakin ta mike tsaye da sauri tana kallon kofar, can ta karasa ta bude taga Mimi a tsaye, Mimi tace "Ki fito mu ci abinci" Nihad tace "Toh" Mimi tace "At Mami's parlor" Nihad ta gyada mata kai, Mimi ta bar bakin kofar, komawa dakin Nihad tayi ta dau mayafinta tana kallon agogo, karfe sha biyu saura ake cin abincin rana kenan a gidan, ta dai nufi kofa ta fita zuwa parlon Mami tana tafiya a hankali, Mimi na zaune with 3 different foods a gabanta, Nihad ta karasa tana kallon abincin, Mimi ta nuna mata wajen da zata zauna, Nihad ta zauna, Sai ga mai aikin Mami ta shigo da ruwa me sanyi da drinks a hannunta ta ajiye masu tana kallon Mimi tace "Za a kawo fruit Salad din ne?" Mimi ta kalli Nihad tace "Will you take fruit Salad?" Nihad ta girgiza kai alamar a'a, Mimi ta kalli Bilkisu tace "No need" Bilkisu ta juya ta fita, Mimi ta zuba abinda xata ci a abincin gabansu, tayi ma Nihad alamar ta diba, Nihad ta dau plate ta debi shinkafa da miya, daga Nihad har Mimi cakalkala abincin kawai suke yi, ita Mimi sae danna wayarta take, daga karshe ta mike tana kallon Nihad dake mamakin wai har ta gama cin abincin kenan, Mimi tace "Let me go and brush My teeth" Nihad ta gyada mata kai kawai, Mimi ta fita daga parlon, ba a dau lokaci ba Noor ta shigo parlon kallo daya tayi ma Nihad ta dauke kai ta nufi dakin Mami ganin Mami bata nan ta juya ta nufi kofa zata fita, Nihad ta bi ta da ido har ta fita, Mimi na dawowa parlon ta kira Bilkisu ta waya ta zo ta fitar da sauran abincin daga parlon.... Har yamma Nihad na parlon Mami, wayar da bata gani ba yayi mugun tsaya mata a rai, kuma ta ma san wa zai dau wayar, Lokaci lokaci Mimi ke shigowa wajenta a parlon, seems basa wani zama nan bangaren sae Mami ta kirasu ko kuma sun shigo gaisheta, shigowar Mimi na karshe tace "Pls mu je ki rakani saloon xan yi gyaran gashi" Nihad tace "Toh" Mimi ta jirata har ta dauko Hijab dinta sannan suka fito Main parlor din gidan, Nihad sai estimating uban tafiyar da suka yi kafin su shigo ainahin parlon gidan wanda girmansa ya wuce misali take, the house is really huge, Tun da suka shigo parlon Aunty Hassana dake waya ta bi su da ido, can ta katse wayar da take tace "Ke Mardiyya zo nan" Mimi ta dawo tana kallonta, ko kadan Nihad wasn't comfortable at the way the woman was looking at her, Aunty Hassana tace "Wacece wannan?" Mimi ta kalli Nihad da tayi tsuru tsuru tace "Aunty bakuwa ce" Aunty Hassana tace "Bakuwar wa?" Mimi ta buda hannu tace "Bakuwar Mami" Nihad tayi karfin halin cewa "Ina yini" Aunty Hassana na kallonta daga sama har kasa tace "Lafiya" Mimi ta jawo hannun Nihad suka bar parlon, Sajida da shigowarta parlon kenan ta kalli Aunty Hassana tace "Wallahi Mama she is the one" Aunty Hassana tace "Anya kuwa? Naga wannan fara ce sosai fa" Sajida tace "I am telling you the fact, ita ce, bari in dauko wayata ki gani" Daga haka ta tashi da sauri ta tafi ta dauko wayarta ta shiga video tayi playing ta mika ma Mamarta wayar, Aunty Hassana tace "Toh ba cewa ku ka yi tare da wannan ɗan iskan suke ba? Kun ce shi ya kawota gidan" Sajida tace "We are not sure, kawai muna shiga parlon Mami muka ganta a zaune, kilan er uwarsu ce saboda yau da Aunty Maryam xata tafi ne ta sake dawowa gidan nan, all those while tana gidanta" Aunty Hassana tace "Kaiii, da yar uwarsu ce xan santa, da kyar dai in ba shi ya kawota gidan nan ba, idan kuwa ba shi bane ya aka yi sai da ya dawo ita ma muka ganta a gidan, amma ba komai xan samu yaya anjima idan ya dawo, ae dai baxa a kawo masa yarinya gidansa bai sani ba, xai min bayanin ko wacece" Nihad ta dinga kallon motar da wani mutumi sanye da camouflage yayi parking dai dai inda Mimi ke tsaye, ya sauka ya bude masu back seat, kana ganin shigar da Mimi tayi na English wear ga baƙin shade dinta a ido sannan ga wani jaka da ta rataye xaka san ba karya, she looks so cute and beautiful, Nihad bata ta6a jin da akwai wanda xata ji ya fita komai a rayuwa ba sai yanzu, ita da ganin kanta take babu ya ita, har University da take zuwa ma kallon kasa kasa take masu ba kowa take ma magana ba ko da kuwa an mata, don tana ganin ba class dinta bane su, sai gashi yanzu kawai taji ta raina kanta, Mimi na kallon Nihad ganin yanda ta ja gefe ta tsaya tace "Shigo" Nihad ta shiga motar ta kulle a hankali, mutumin ya ja motar aka bude gate suka fita daga gidan, Mimi ta ajiye wayarta da take dannawa tana kallon Nihad tace "Here is a question for you Nihad" Nihad ta dinga kallonta ba ko kiftawa, Mimi tace "How did u come to know my broda?" A hankali Nihad tace "Wanne?" Mimi ta ɗan yi jim tace "Yayana fa nake nufi, wanda ku ka dawo tare da shi dazu da safe" Nihad tace "Ohk, Yayanki ne?" Mimi ta buda ido tace "Yea he is my senior brother, we are having same father and same mother, Mami is our Mum, Noor is my senior sister, she is his immediate but ya girmeta sosai, ya bata 12 years, xan nuna maki ita idan mun koma gida kilan baku hadu ba har yanzu" Nihad sai kallonta take don truly Mimi na nugun kama da shi, both the nose and eyes, a hankali Nihad tace "Pls ki gaya min gaskiya gidansu ne wannan gidan da muka fito?" Mimi ta wara manyan Idonta tace "That's funny, he is the first and only male child of our father, did he tell you ba gidansu bane?" kallonta kawai Nihad take tana jin ita fa yanzu da ta ga ainahin cikin gidan da irin girmansa da kyau ta kasa yarda gidansu Khalil ne, ita kawai yanxu gani take kamar rikonsa ake a gidan ko kuma gidan ɗan uwan babansa ne, abinda ta saka a ranta kenan don she is beginning to get confuse ta yaya ma xa ace wannan gidan nasu ne, mutumin da yaje gidansu yake driving ana biyansa for almost a year, sannan har kauyensu ya kai ta, to me yasa xai kawota irin wannan gidan yanzu ta yarda nasu ne, Mimi da ke ta kallonta ta katse mata tunaninta tace "What are u thinking about?" A takaice Nihad tace "I am finding it hard to believe, and I don't think i will believe" Mimi tayi murmushi tace "Now i understand, he acted like he is a nobody right?" Nihad tayi shiru tana kallonta, Mimi ta shiga gallery dinta taje inda take ajiye hotunan yayan nata, wanda sun fi dari ta shiga ta mika ma Nihad tana kallonta, farkon hotonsa da Nihad ta gani ta dinga kallo babu ko kiftawa, sanye yake da farin labcoat with stethoscope round his neck, ta tafi next hoton, ta gansa cikin private jet an masa unaware picture, yayi crossing kafa yana danna waya with a serious face, ga tsadadden non-alcoholic wines a gabansa, designers ne kayan jikinsa, irin kyan da yayi kuwa a hoton ba ace wa komai, Nihad ta dinga kallon hoton don karya ne mutum ya kalli hoton bai sake kallo ba, bata san sanda tayi zooming ba still wanting to confirm and be sure shi din ne dai, taga wallahi shi ne, da zaka shiga zuciyarta kaga mamaki da shock da ya cika sa, a hankali ta tafi next picture din ta gansa a Newyork, then another in Los Angeles, Paris and another in United kingdom, infact duk yawanci hotunan a kasashen waje ne, wasu hotunan da turawa, wasu larabawa, she is really shock at all what she is seeing, sai kuma ta fara ganin hotunansa da Nadeeyah, a hotonsu na uku tare ta ki ci gaba da kallon, ta ɗan kalli Mimi dake danna second phone dinta giving it all her attention, tayi tapping dinta ta mika mata wayarta, Mimi tace "Are you done?" Nihad ta gyada mata kai, amsar wayar Mimi tayi ta mayar cikin jaka ta ci gaba da abinda take da dayar wayarta, har suka isa saloon din Nihad bata sani ba don tayi nisa tunanin da take, Mimi ta kamo hannunta tace "Dear" Firgit Nihad ta dawo, Mimi tayi murmushi tace "Mun iso" Nihad ta kalli mutumin da ya bude masu motar yana jiran su sauko, ta sauka daga cikin motar, sannan Mimi ma ta sauka, kallon wajen Nihad ta dinga yi tana imagining duk nan saloon ne? How big and beautiful, ganin yanda ta tsaya Mimi tace "Mu je" Nihad ta bi bayanta ta kasa daina kallon saloon din har suka shiga ciki, nan taga fararen mata ne masu gashi har gadon baya ke zuwa gyaran gashi wajen, har turawa da larabawa, kana ganin cikin saloon din kasan ba karya, Mimi tace "Ke ma kiyi gyaran gashinki" Nihad dai bata ce komai ba, da Mimi ta sake mata magana tace "Ohk" sai da suka 6ata kusan awa daya