Showing 198001 words to 201000 words out of 292821 words

Chapter 67 - NIHAAD COMPLETE DOCUMENT Complete by Khalisat Haidar .txt

25 Nov 2024

39504

couldn't say a word, Noor na ganin yanayinta ta ɗan yi jim, don daga lips dinta har idonta sunyi ja sosai, and she looks so sick, can tace "Are you okay?" Nihad bata ce mata komai ba, Noor na kai hannunta jikinta tayi saurin janye hannun, bata taɓa sanin temperature din mutum na irin wannan zafin ba, ta koma baya tana kallonta, sai ga Mami ta sake kiran wayarta, Noor ta daga daga daya bangaren cikin fada Mami tace "Uban me kike yi a dakin ne? Baxa ku fito a kulle gidan ba" Noor ta kasa cewa komai da farko ita duk tunaninta Mami tasan Nihad ce a kwance, Mami tace "Hello, baki ji na ne..." A hankali Noor tace "Mami she is very sick fa" Mami taji wani sabon faduwar gaba, tace "Sick? Toh baxata fito ba kenan?" Noor dai ta kasa cewa komai, Mami ta katse wayarta, Noor ta karasa saman gadon ta kamo hannun Nihad tace "Ki daure ki tashi, za a kulle gidan as instructed by our father" Nihad ta girgiza mata kai amma ta kasa cewa komai, Noor ta cire duvet din gaba daya wanda shi ma duk ya dauki zafi, dai dai nan Mami ta bude kofar dakin, and she met the shock of her life, don sai da numfashinta ya dauke na yan dakikai saboda bugun da zuciyarta yayi, ta dinga kallon Nihad da idanuwanta kamar zasu fito bata ko kiftawa, lokaci daya taji komai ya tsaya mata cak, at yhe same time kanta ya kulle, zuciyarta ya canza bugun da yake yi, wait.... raina mata hankali Khalil zai yi?? wannan din ce zai ce ma matarsa saboda ya fara shan wiwi, dama gidansa ya kawota all this while, shine yake kokarin covering up yace matarsa ce tunda yasan babban laifi yayi, a fili tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me zan gani haka?" Nihad dai ta kasa ci gaba da kallon Mami, Mami ta daka mata wani tsawa tace "Me kike yi a nan? Amma dai babu tantama daga sama kika fado babu iyaye...." Noor ta kalli Mami, sannan ta kalli Nihad, sai a sannan ta fahimci Mami bata ma san ita ce a dakin ba, da sauri Noor ta nufi Mami tace "Mami she is very sick" ko sauraronta Mami bata yi ba cikin bacin rai tana kallon Nihad tace "To zo ki fita...." Duk da Nihad na jin ko tashi zaune bazata iya ba, haka tayi karfin hali ta yunkura zata sauka daga saman gadon, abu biyu taji a lokaci daya, wani mugun jiri sannan kuma taji kamar ta taka allurai a kasan kafarta har zuwa laps dinta, bata san sanda ta fasa kara ba, sai kuma ta tafi luuu ta fadi kasan dakin, Mami dai sai kallonta take, controlling temper dinta kawai take kada ta fadi abu da zai yi affecting ɗan nata taje tayi masa baki, bata taɓa jin ɓacin rai irin na yau ba, Noor ta durkusa gaban Nihad sai taga kamar bata motsi, ta kalli Mami da sauri tace "Mami kamar fa suma tayi" a fusace Mami tace "Dauki Hijab dinta ki bata ta fitar min daga nan, idan taje waje sai ta suma...." Noor ta mike ta kalli Hijab din Nihad dake saman gado ta dauka, kallon bedsheet ta dinga yi sai kuma ta kalli Mami dake kallon saman gadon ita ma, Mami ta karaso dakin tana kara kallon zanin gadon, Noor dai sai kallon Mami take, bayan few seconds Mami tace "Ajiye Hijab din kije ki ce ma sojojin nan they should be patient muna fitowa" Noor ta nufi kofa ta fita, Mami ta sake kallon saman gadon sannan ta kalli Nihad dake kasa, dukawa tayi gabanta cike da karfin hali tace "Me ya sameki?" Nihad ta bude idonta da yayi ja a hankali tana kallonta amma ta kasa cewa komai, Mami ta dake tace "Tashi zaune" Hawaye ya fara gangarowa idonta ta girgiza mata kai kawai, Mami ta kai hannu jikinta taji sa kamar wuta, ta dagota tace "Hau saman gadon" Nihad ta girgiza kai da sauri cikin muryarta da baya fitowa tace "Baxan iya tashi ba...." Mami ta kasa hada ido da ita, sai da ta fara cire zanin gadon sannan ta taimaketa zuwa saman gadon, kamar warce aka zare ma laka ta fita daga dakin ta sauka kasa tana kallon Noor dake zaune parlon tace "Kina da number Dr Rukayya?" Noor tace "Eh ina da shi" Mami tace "Kira min ita" Noor ta shiga neman number bayan tayi dialing yana fara ring ta mika ma Mami, Mami ta amsa ta kai kunne Dr Rukayya na dagawa suka gaisa Mami tace "Hajiya Fatima ce ke magana Dr" Dr Rukayya tace "Na gane Hajiya, ya yaran?" Mami tace "Alhamdulillah, pls za ki zo ki duba mara lafiya ne amma ba can gida ba, will send u the address right away" Dr Rukayya tace "Ohk Ma" Mami ta katse wayar ta tura mata address din gidan Khalil, daga haka ta mika ma Noor wayarta ta koma sama duk jikinta ya mutu, tsaye tayi corridor tunani kala kala na yawo a ranta, she is confuse, meye hakan ke nufi kenan? Tana safa da marwa a corridor din for almost 20 minutes don hakan kadai ke sata jin relieve din abubuwan da suka tunkushe a zuciyarta, har dai likitan ta iso gidan, Noor ta kai ta sama ganin Mami na corridor ta sauko kasa ta bar su, Mami suka kara gaisawa da Likitan sannan suka shiga dakin tare, likitan na kallon Nihad tace "Me yake damun ki yan mata?" Nihad dai kallonta kawai take ba bakin magana, duk gaba daya tayi laushi, Likitan tayi considering haka ta kalli Mami dake tsaye tace "Hajiya what's wrong with her, and for how long is she sick, naga ta jikata da yawa..." Mami ta hadiye wani abu da kyar tace "I don't know precisely Dr, amma dai ki dubata ki ga" Likitan na kallon Nihad cikin kwantar da murya tace "Just indicate duk inda kike jin ciwo...." Nihad ta nuna mata kanta sai kuma kafarta, Likitan ta dinga kallon kafar tace "Daga ina zuwa ina?" Nihad ta nuna mata daga lap dinta har kasa, Mami dai ta jingina da bango don tsayuwar taji yana neman ya gagaranta, Likitan tayi shiru tana kallonta, can ta kalli Mami tace "Is she a new bride?" Rasa abun cewa Mami tayi lokaci daya taji kamar ta fashe da kuka, Likitan ta na kallon kayan baccin jikin Nihad da kyau sai ta lura da few blood stain, Kallon Mami likitan tayi, kawai sai Mami ta juya ta fita daga dakin hawaye na zuba a idonta, hakan ya daure ma likitan kai ta kalli Nihad tace "Are you married??" Nihad tayi karfin halin gyada mata kai, Tashi likitan tayi ta shiga bandaki, tana ganin zanin gadon dake bandakin ta tabbatar da zarginta, ruwan zafi kawai ta hada a bathtub, ta fita xuwa wajen Mami tana kallonta tace "Za a samu gishiri Hajiya?" Mami tayi karfin halin girgiza mata kai kawai, Likitan ta koma ciki, dole ta ɗan ɗiga disinfectant dake bandakin sannan ta fito, sosai taji tausayin Nihad kafin su karasa bandakin, she is in so much pain, sai ta fara imagining where is the husband that is this heartless, wannan ma yana da imani kuwa, duk yanda tayi da Nihad ta shiga ruwan kin shiga tayi tana kuka kamar yanda tayi ma khalil jiya, bata mance wahalan jiya ba, Sun bata minti kusan biyar a haka likitan na fama ta shiga ta ki, likitan ta kara ruwan zafi a bathtub din ta fita daga bandakin taje ta samu Mami, tana kallon Mami tace "Tana bukatar ta shiga ruwan zafi, ban san ko zaki mata magana taji ba, she isnt co-operating" Mami was lost of words, kawai ta gyada ma Likitan kai, likitan tace "Zan fita yanzu in siyo mata drugs da allura" A hankali Mami tace "Toh" Daga haka Likitan ta sauka downstairs, Mami ta shiga dakin sannan ta karasa bandakin, ta fi minti daya tsaye kafin ta tura kofan, Nihad tayi da ta sanin da bata hakura duk azaban da zata ji ta shiga a haka ba, bata yi zaton Mami likitan ta tafi ta kira ba, ga kunyan yanda Mami ta shigo ta ganta, ta kasa yi ma Mami musu banda hawaye babu abinda take, haka nan ta shiga ruwan, bata san daga inda dauriya ya zo mata ba a wannan lokacin, Mami ta canza mata ruwan ya kai sau uku, daga karshe ta tara mata ruwan wanka, duk wannan abun karfin hali kawai Mami take amma her heart is so heavy, bata yarda su hada ido da Nihad all through ba, kamar yanda ita ma Nihad din bata iya ta hada ido da ita ba saboda kunya, Nihad na wanka Mami ta wanke bedsheet din ta fita daga bandakin, zaunawa Mami tayi gefen gado ta rike kanta, ita Khalil yayi deceiving haka? Tunanin abinda zata masa taji sanyi a ranta kawai take, ta ina za a fara wannan babban lamarin? Hawaye ya hau sauka fuskarta tana girgiza kai, she wish all this is nothing but a dream, daga karshe ta mike ta fice daga dakin ta shiga wani dakin daban, Nihad na fitowa bathtub din taji dama daman abinda take ji, amma har sannan zazzabin na jikinta, tana dingishi cike da karfin hali ta fito daga bandakin daure da towel ta kwanta saman gado ta takure waje daya tana jin sanyi.
Bayan wani ɗan lokaci Mami ta goge idonta ta sauka downstairs tana kallon Noor tace "Ki duba ko akwai yanda zaki dafa mata shayi a kitchen, idan babu kuma ki fita ko restaurant ne ki siyo mata abinci kafin likitan ta dawo" Noor tace "Toh" Mami ta juya ta koma sama tana jin jikinta babu dadi kwata kwata, kofar dakin da Nihad ke ciki ta bude ta ganta kwance har ta fara bacci, Mami ta karasa cikin dakin tana kallonta tunani iri iri na yawo a zuciyarta, press din dakin ta nufa ta bude taga babu kaya a ciki, ta kalli akwatinta dake dakin tana tafiya a hankali ta nufi gun akwatin ta bude tana duba kaya a ciki, wata doguwar riga ta fiddo mata da underwear sannan ta mike ta karasa kan gadon, bude akwatin da Mami tayi ya tada Nihad, Mami ta ajiye mata kayan a gefen gado ba tare da ta kalli idonta ba tace "Tashi ki sa" Nihad ta mike zaune, Mami ta fita daga dakin, hawaye kawai Nihad take, all her thought was that Khalil left her upon the condition she is in, bai duba halin da take ciki ba yayi tafiyarsa ya kyaleta haka, rabon da taji haushinsa yanda take ji yanzu tun farkon zuwansa gidansu.....
Har kusan azahar Nihad bacci take tun bayan da Dr Rukayya tayi mata allurai ta bata magani, ita ma Mamin maganin bacci ta sha don truly bata jin dadin jikinta, tasan da kyar idan jininta bai hau ba, nan spare room dake gidan tayi bacci har kusan azahar din ita ma, har a lokacin kuma Noor na gidan, ana idar da azahar Mami ta sauko downstairs tana kallon Noor tace "Zan kiraki zuwa anjima, xan je gida yanzu" Noor tace "Toh Mami, Allah ya kiyaye" Daga haka Mami ta fita tare da sojoji biyu suka maida ta gida, tana sauka compound direct Guard room ta nufa wani soja yayi saurin bin bayanta yace "Hajiya Oga ya dawo ai an fito da shi" Mami da gabanta ya fadi don sai da yayi magana taga motar Janar a gidan, ta juya tana kallonsa cikin karfin hali tace "Yana ina?" Sojan yace "Yana ciki" Mami ta karasa cikin gidan da sauri, tana shiga main parlor Aunty Hassana na kyabe baki tace "Plan din naku yayi aiki...." Mami ta kalleta sai kuma kawai ta tafi part din Khalil, bata gansa a dakinsa ba, ta fito kenan sai ga Mimi ta biyota, Mimi tace "Mami yana part din Abba, he is very sick" Mami tace "Me yake yi a can?" Bata jira abinda Mimi xata ce ba ta nufi bangaren Janar, bude kofar parlon tayi, taga Aliyu a tsaye Janar dake zaga Parlon yana ma Aliyun magana, don shi bai iya tsayuwa waje daya, Ta dinga bin parlon da kallo bata ga Khalil ba, Aliyu yayi kasa da kai yace "Ina yini" Mami tace "Where is Khalil" Wani kallo Janar yayi mata ya ci gaba da gaya ma Aliyu abinda yake gaya masa na zuwa Germany da zai yi akan wani business, Aliyu ya nuna mata inda Khalil yake, ta karasa ta bude kofar da sauri, kwance ta gansa saman gado yana bacci, ga allurai da drugs a kan bedside drawer, sai kuma drip da aka sa masa, har sannan kuma hannunsa daya akwai handcuff, ya bude ido a hankali jin an bude kofar dakin don baccin nasa sama sama ne, ganin Mami sai da gabansa ya fadi, ya mike zaune da sauri kusan a firgice, Mami ta dinga kallonsa kafin ta karasa cikin dakin ta tura kofar tana girgiza kai cike da takaici tace "Wato ni zaka raina ma hankali Khalil? Ni ka maida yar iska tsohuwar banza, ni zaka raina ma wayo kamar kai ka haifeni, ka ban mamaki wallahi, ka ban mamaki, dama kuma tun farko ni ce ban tsaya nayi nazari ba, amma da na tsaya nayi nazari da na gano cewar babu iyayen arziki da za su hada 'yar su da namiji wai ya kai ta karatu, a da ina alfahari da tarbiyan da na maka amma banda yanzu, i can't count on you now, ban taɓa tunanin akwai ranan da zaka saɓa ma Allah ta hanyar zina ba" Khalil ya katseta da sauri yana girgiza kai, zuciyarsa na bugawa yace "Keep on counting on me Mami, i am not a fornicator, ban taɓa ba, kuma baxan fara ba, i am sorry ban san ta yanda zan billo ma lamarin bane, amma Nihad matata ce ta sunna... Da aurenmu na kawota gidan nan, kamar yanda kika fada da ba don aure ba babu abinda zai sa iyayenta su bari in taho masu da yar su daga ni sai ita...." Mami kallonsa take babu ko kiftawa with new shock, lokaci daya ta fashe da matsanancin kukan takaici tana girgiza kai ranta na mata zafi tace "Sai dai in bayan raina zaka zauna da ita a matsayin matarka... amma matukar da raina a doron kasa to wllh babu aure tsakaninka da yarinyar nan, wallahi baza ka zauna da ita ba...." Tura kofar dakin aka yi Mami ta juya da sauri tana share Idonta, Janar na kallon Khalil with the expression of soldiers yace "Wacece matar taka???" Mami ta fashe da kuka sosai tana girgiza kai tace "Ban taɓa dana sanin haifanka ba sai yau Khalil, kuma ina me tabbatar maka sai dai ka zaɓi ko ni ko yarinyar, baxan taɓa hada zuri'a da ita ba wallahi tallahi, this time around duk abinda ubanka zai maka yayi maka sannan nima ka jiraye nawa hukuncin, sai na nuna maka ni na haifeka ba kai ka haifeni ba" Daga haka ta fice daga dakin, zufa ya dinga keto masa yaji kansa yayi masa mugun nauyi, lokaci daya zazzabinsa ya dawo masa sabo, Janar dake ta kallonsa yace "Wace yarinya kenan take magana a kai??" Lokaci daya hawaye ya kawo idon Khalil idan Mami tayi masa haka waye kuma zai tsaya masa, yana kallon Abbansa ya kasa cewa komai saboda shock, Abba ya masa tsawa yace "I am talking to somebody" Khalil ya rike kansa with shaky voice yace "A gidan da na zauna a kano suka bani aurenta, ni kuma na amsa saboda sun amsheni a lokacin da aka nuna ba a bukatata a gidanmu, i can't tell them no" Janar na ta kallonsa yace "So now, where is the girl?" Khalil ya kasa dagowa yace "Tana gidana" Janar ya hau safa da marwa a dakin kamar me pareti, can yace "Sai suka ce kuma ka boye mana ko?" Khalil ya dago a hankali yana kallon Abbansa with tears in his eyes, Janar na gyada kai yace "Zaka kai ni har kanon gidan iyayen yarinyar to make confirmation, and if i should find out u are lying sai na karya maka kafa i promise, idan kuma din da gaske matarka ce that's fine...." Daga haka ya juya ya nufi kofa Khalil ya bi sa da kallo zuciyarsa na bugawa.......






Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah




Ur evidence via 07087865788


https://instagram.com/ruuscollections?igshid=MzNlNGNkZWQ4Mg==
Ruuscollections turaren wuta and more we got you everything scent,long lasting fragrance at very affordable price, change or complete refund if you don't like any of our product in Sha Allah
Arabian,Traditional,English,Khumra ,Oil perfumes,Koleccha,Morphingmist,Roomfreshener,
Armpit powder, Mouth freshener,Laces ,Shoes,
Bags,Atamfa, 07025393114
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: 💖 NIHAAD 💖


57




*This page is dedicated to my one and Only Deejah me lamurje, she is a sister from another Mother, ina kuma sonta har cikin raina, Allah ya bar xumuncinmu har aljanna*🥰😍
Hajiya Zahrah Me gari naji labarin Najar Jikamshi ya siya maki sabon kasuwar cikin garin dutse, to su kuma yan dutse su yi yaya? Ko da yake ga dai kasuwar Hakimi. 🤔






Khalil na zaune gefenta ya jinginar da kansa jikin gado yana kallonta ko kiftawan kirki bai yi, gaba daya a sanyaye yake kamar ba shi ba, bai taɓa jin haushin kansa irin yau ba, he know she will ever trust him again because he never fulfilled the promise he made to her, he can't tell what came over him that way, he didn't take it easy on her, and all this is making him feel so bad, duk motsin da Nihad zata yi idonsa na kanta, even in sleep she doesn't look alright, baccin karfin hali kawai take, duk tayi laushi saboda wahala, wani mugun tausayinta yake ji har ransa, a karo na farko kuma yaji yana son sanin ta yanda video dinta ya fita, yaji yana son yasan who is behind the leakage of that video of her, da kuma a inda aka yi sa, this he is going to find out by all means.... Bacci


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login