Showing 96001 words to 99000 words out of 292821 words

Chapter 33 - NIHAAD COMPLETE DOCUMENT Complete by Khalisat Haidar .txt

25 Nov 2024

39443

manta wayar, idan ya so kamar yanda kika ce sai ki basa ya bani a gabanki sannan ki ja masa kunne sosai kar yace xai amshe" Umma tace "Kar ki damu sai dai na zo" Daga haka suka yi sallama, Nihal na kallon Nihad tace "kinsan Mumy bata da lafiya kuwa Nihad?" Nihad ta kalleta tace "Haba? To ai ni ba a gaya min ba" Nihal tace "Ai kam bata da lafiya, in kirata ku gaisa?" Nihad ta ษ—an yi shiru sai kuma tace "Ki bari anjima da daddare xan kirata" Nihal tace "Toh shkkn" Nihad tace "Idan xa ki ci abinci ga indomie can kitchen ki dafa fa" Nihal ta mike ta fita daga dakin, tana shiga kitchen taga kayan miya kawai tayi deciding ta dafa jollof rice, tana cikin grating kayan miyan taji muryar khalil yace "Sannu da aiki" Ta kalli kofar da sauri sai kuma tayi murmushi tace "Nagode" Yace "Yaushe xa ku kare hutun?" Tace "Nan da sati biyu" Yace "Ohk nan xaki gama hutun ko?" Tace "Aa ni da gobe xan tafi, i don't want to over stay my welcome" Murmushi yayi yace "Aa kiyi hutunki kawai a nan" Ita dai bata ce komai ba tana ci gaba da aikinta, juyawa yayi daga karshe ya bar kitchen din. Bayan Magriba yana xaune a parlor Nihal ta fito daga daki xata je kitchen ta xuba ma ita da Nihad abinci, ganin khalil zaune parlon ta koma daki wajen Nihad tace "Ki fito ki zuba masa abinci, ban fa xuba masa ba tun daxu" Da mamaki Nihad ke kallonta, sai kuma tace "A saboda me xan xo in xuba masa abinci? Dama da shi kika dafa abincin ne?" Nihal dai bata ce mata komai ba ta juya ta fita, Nihad ta rike ha6a tace "Ji wani iyayi wai in xuba masa abinci kamar wani mijina, ashe xai tsufa bai ci abincin ba" Tsaki ta ja ta jawo wayar Nihal for the 10th time ta sake kiran layin Aliyu amma a kashe, kwantar da kanta tayi saman pillow kamar xata yi kuka don har ta gaji da trying layin nasa, tun xuwan Nihal take abu daya, Nihal na komawa kitchen ta fara xuba masa abincin a plate sannan ta dauka ta fito parlor ta nufesa ta durkusa tace "Ga abinci" Yana kallonta yace "Thank you Nihal" Ta mike ta koma kitchen din ta xuba ma ita da Nihad a tare, kadan Nihad ta ci abinci duk hankalinta a tashe yake bata samu Aliyu ba, Nihal ta ci abinda xata ci ta bar mata ta koma saman gado ta dau wayarta tana dannawa, Daga karshe wajen karfe goma da taga Nihad ba ci xata yi ba ta dau plate din ta fita, Bayan ta kai kitchen ta fito khalil na kallonta yace "Wani level kike a makaranta?" Ta tsaya tace "Level daya muke da Nihad" Yace "But in tambayeki" Ta ษ—an tsaya sai kuma ta dawo parlon ta xauna tana kallonsa yace "Ke kika ce ma Abba Ahmadu Bello University kike so?" Nihal tayi murmushi tace "Aa, kawai cewa yayi can xan je ni" Yace "Ita kuma er uwarki fa?" Ta sunkuyar da kanta tace "He gave her option" Khalil dake ta kallonta yace "Ohk ke daga baya baki ce masa makaranta daya kike son xuwa da er uwar taki ba?" Nihal tace "Ya Usman da Mumy sun masa magana a lkcn, Mumy tace masa tunda har Nihad ta zaba Maryam Abatcha nima ya biya mun Maryam Abatcha din mu tafi tare ko kuma duk mu tafi ABU, amma sai yace Nihad kawai xata je ni in tafi ABU, he can't afford the fee of Maryam Abatcha for the two of us" Shiru Khalil yayi yana kallonta, can yace "Kuma Ummanku bata ce komai ba?" Nihal ta girgiza kai tace "Kawai ce min tayi inyi hakuri in tafi ABU din" Khalil ya gyada kai yace "Amma secondary daya ku ka yi ko?" Nihal ta girgiza kai tace "Shi ma ba daya muka yi ba, ita Nigerian Turkish tayi, ni kuma Yan dutse nayi" Khalil ya gyada kai yace "Ohk, yan dutsen kamar su Amina da Sudais nan suke xuwa ko?" Nihal tace "Har Aunty Kamila da Ya Usman da ya farooq ma can suka yi, Nihad kadai ce tayi Nigerian turkish" Khalil yace "Amma kamar er uwartaki tafi sabawa da Ummanki akan mamanta ko" Nihal tace "To ai a bangaren Umma take, ni kuma ina side din Mum dinta, though I don't know for her" Shiru Khalil yayi yana kallonta, can yace "Maa sha Allah, hakan yayi.... amma wani saurayinta da ya zo can gida ranan, sun dade tare ne?" Nihal tace "Wai Aliyu? Yea definitely shi, don ita bata kula wani saurayi idan ba shi ba, shekaran da ta shiga Maryam Abatcha suka hadu, shekara uku kenan" Yace "Ohk, kinsan saurayin sosai kenan?" Nihal ta bude ido tace "Nasan shi mana, he is the son of General Jikamshi..." Muryan Nihad dake labe jikin pillar din corridor tum daxu ya katse Nihal, cike da bacin rai Nihad tace "A gidan uwar wa kika san shi? Shi Aliyun kike tunani kinsani? Har da wani gaya masa sunan babansa salon yayi masa mugun abu irin nasu na kauye? To wallahi baki san shi ba kuma baxa ki ta6a saninsa ba, dama don ki zo ki hadu da wannan mutumin ku kafa munafurcina ya sa kika zo gidan nan ashe ban sani ba? To wallahi ni dai ki tashi ki tafi baxa ki kwanan min a gida ba, ai dai mun ga juna, har da wani ce masa ni kadai nayi Nigerian turkish, to wani yace kar kema kice ma Abba can kike so? Naga dai choice dina ne kuma Abba yayi accepting, sannan Maryam Abatcha ma wani yace kar ki sakar ma Abba kuka kice ke baxa ki je ABU ba sai dai Maryam Abatcha? Wallahi kin ban mamaki har xaki zauna da bare kuna cakalkalar namana ko tausayina baki ji ba, to Allah ya isa wannan gulman nawa da kika yi" Nihal dai bata ce mata komai ba, Banda kallon Nihad babu abinda khalil ke yi, tana huci tace "Shi kuma saboda gulma har da wani cewa nafi son Umma, dama ashe maza na gulma ban sani ba? Kuma ai Umma da Mumy duk daya suke a wajena babu wani bambanci, to tunda dai mun ga juna zo ki dau handbag dinki kiyi tafiyarki" Mikewa Nihal tayi ta nufi daki, Nihad ta bi ta da harara, sai ga ta ta fito sanye da hijab tana rike da handbag dinta ganin xata nufi kofa Nihad ta rikota tace "Ina xa ki tafi da daddaren nan" Nihal ta fizge Hijab dinta hawaye cike idonta ta nufi kofa, Nihad ta bi bayanta da sauri tace "Ke ni fa wasa nake maki ina zaki da daddaren nan" Tuni Nihal ta fice daga parlon, Nihad ta marairaice tana kallon Khalil tace "Don Allah kayi mata magana, ni wallahi ba haka nake nufi ba" Ko kallonta Khalil bai yi ba, hakan yasa ta fita da sauri, can ta tarar da Nihal zaune bakin gate dake kulle tana rera kuka, kukan ta ita ma ta fara ta durkusa gabanta tace "Don Allah kiyi hakuri wallahi i didn't mean it, ni ba da ke nake ba, da shi nake"








*Nihad* dari biyar ne, ki fita hakkina ki karanta hankalinki kwance yar uwa


3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah ur evidence via๐Ÿ‘‡๐Ÿป






07087865788










*Assalamu alaikum er uwa, kina neman organic Supplement irin masu gyaran jiki ciki da waje? Ko kuma mai fitar Maki da duk wani infection komai nacinsa? Sannan mai maido Maki martabar fatarki? Ko kina fama da dry HQ? Ko hips ne matsalarki da boobs? To kwantar da hankalinki *GHT Organic supplement care gat ur back*




Domin karin bayani ki tuntubi wannan number ๐Ÿ‘‡๐Ÿป


+2347057607751โœ๐Ÿป




https://chat.whatsapp.com/G91KmKaihzAL76lSmkXqG9
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: ๐Ÿ’–๐Ÿ’– NIHAAD ๐Ÿ’–๐Ÿ’–


28


Yau ma kamar jiya hasken rana ne ya sa Nihad ta farka, da kyar ta mike xaune tana jin duk jikinta na mata ciwo barin kanta da yayi mata nauyi, sosai hankalinta ya tashi ganin khalil baya dakin, ta hade kai da gadon karan da take kai tana kuka a hankali, can dae tayi karfin halin mikewa ganin lokaci na tafiya bata yi sallah ba, ta nufi yar jakar da ta sa brush dinta da Toothpaste ta dauka ta fita daga bukkar. Bayan ta idar da sallah tana xaune saman abun da tayi sallan lkci lkci tana share hawayen dake gangaro mata, rashin ganinsa na kara saka mata damuwa a kan wanda take ciki, shadow da ta gani bakin kofa ya sa ta daga kai da sauri hoping shi ne ya dawo, amma sai ta ga ba shi bane, wata budurwa ce warce xa su yi sa'anni da Nihad din ta shigo dakin, fara ce kal kal don duk hasken Nihad yarinyar ta fi ta, ga ta kyakkyawa ajin karshe, dogon gashinta da aka kitsa gida biyu manya manya har ฦ™afadunta suke tabowa, ga uban wushiryarta a baki, Nihad ta ganeta don jiya kaya kala biyu ta bata da turare, budurwar na murmushi ta duka gaban Nihad ta ajiye mata kwanon sha dake hannunta tace "Hannu, yau kamar kin makara ko" Nihad ta kirkiri murmushin ita ma tace "An tashi lafiya" Yarinyar tace "Lafiya lau, ga farau farau nan na kawo maki, yanxu xa a dunduma tuwon sae a kawo maki" Sosai gaban Nihad ya fadi jin kalmar tuwo, ita fa bata ta6a sanin akwai wani kalan tuwo bayan fari ba, gwara gwara amala ta san baki ne, to da wannan abun da suke kira tuwo ba gwara a bata amalan ba, ta dai sakar mata wani murmushin karfin halin tace "Toh, nagode" Yarinyar na wasa da gashinta tace "Ni sunana Furera amma ana kirana Fure ke kuma fa?" Nihad ta sauke idonta tace "Sunana Nihad" Yarinyar ta zaro ido tace "Sunan yan birni, ae baxan ma iya kiran sunan ba" Nihad tace "Toh ki kirani Ummi" Fure tace "Yauwa gwara wannan, amma ae xa ku yi sati a nan ko?" Nihad ta kalleta da sauri ta girgiza kai tace "Aa yau xa mu tafi" Yarinyar tace "Gwaggo fa tace min xa ku yi sati" Nihad xata yi magana sai ga Khalil ya shigo bukkar da sallama, lkci daya kamshinsa ya cika Bukkar, Fure ta koma gefe tana d'an Murmushi, tace "Hamma wai ashe yau xa ku tafi?" Yanda take maganar kasan a kunyace take da Khalil, Khalil ya kalleta yace "In ji wa?" Fure ta nuna masa Nihad, yace "Aa xa mu yi sati" Gaban Nihad yayi mugun faduwa ta gwalo ido tana kallon khalil a ranta ta dinga nanata satin da yace, meye kuma sati, ba dai sati daya yake nufi ba, cike da murna fure tace "Yauwa dama haka Gwaggo ta sanar min, ai ko naji dadi sosai, duk xan bi in xaga da Ummi kauyen mu da wanda ke gaba da namu, a kawo maka farau farau din ne ko fura da nono xaka sha, nonon ma sabuwa ce jiya aka tatso" Yace "Toh kawo min fura da nonon" Tace "Toh" daga haka ta fita, Nihad ta marairaice tana kallonsa tace "Amma dai xaka maida ni gida sae kai ka dawo kayi satin a nan?" Ya dauko tabarma ya xauna kai ba tare da ya kalleta ba yace "Ko kuma ni in tafi bayan sati daya in xo in dauke ki ba" Bata san sanda ta fashe da wani matsanancin kuka ba tace "Don girman Allah kar ka min haka ka rufa min asiri..." sai a sannan ya daga kai ya kalleta, ta hade tafin hannunta tana kuka a hankali tace "Don Allah kayi hakuri, wallahi baxan iya ba, kaji har na rantse" Gyara xama yayi yace "Bukka guda Gwaggo xa ta bar maki kiyi rayuwarki ke kadai har bayan sati dayan babu me takura ki" Nihad ta mike da sauri ta nufesa ta durkusa gabansa tana kuka tace "Wallahi xan iya mutuwa idan ka tafi ka bar ni a nan, kar ka tafi ka bar ni" Kallonta kawai khalil yake, dai dai nan Fure ta turo kai cikin Bukkar rike da kwaryan nono da fura, Nihad ta koma gefensa da sauri ta zauna, Fure ta durkusa gabansa ta ajiye fura da nonon tana kallonsa tace "Kana son sukari?" Khalil yace "Kadan" Mikewa tayi ta nufi kofa xata fita, khalil ya bi ta da kallo, Nihad ta kallesa, sannan ta kalli yarinyar har ta fita, Khalil tankwashe kafarsa yana kallon fura da nonon dake cikin kwarya a gabansa, muryar Nihad ya ji kamar daga sama tace "Kanwarka ce?" Ya ษ—an kalleta, sai kuma yace "Aa, er makotanmu ce, Baabarta ai ta shigo kun gaisa jiya" Sai ga fure ta shigo rike da sugar a hannunta, durkusawa tayi gaban Khalil tana murmushi ta juye sugar din a kwaryan nonon, ta ษ—an kallesa tace "In dama maka?" Ya gyada mata kai yace "Ehh" Nihad dake kallonta ta mike tace "Bar shi xan yi" Fure ta kalleta sai kuma ta mike tace "Toh" Kallonta kawai khalil yake babu yabo babu fallasa ta dawo gabansa ta durkusa ta dau ludayi ta saka cikin kwaryan, Fure ta mike ta fita, Nihad na kiciniyar dama fura da nonon kwaryan ya kife duk suka malale a kasa, da mamaki Khalil da ya koma baya yake kallonta, kana ganinta kasan bata ta6a dama fura da nono ba, ta turo baki ta mike ta bar wajen ta koma can karshen gadon kara ta zauna tana kallon mess din da tayi a kasa, khalil yace "Na kara sati daya a kan satin da nace xa ki yi a nan" da sauri ta mike ta nufosa ta fashe da kuka tace "Wallahi ba da gangan nayi ba, kwa6ewa yayi a hannuna" Ya hade rai yace "Da baki iya ba me yasa baki bar warce ta iya ba tayi" Tana goge hawayen idonta tace "Toh meye xata wani zo tana ma mutane yauki kamar kubewa a nan?" Mikewa khalil yayi yace "Ni dai na gaya maki, ki shirya kwana sha biyu nan gaba a nan" Nihad na kuka ta riko rigarsa da sauri ganin xae fita cikin rawan murya tace "Don Allah kayi hakuri, idan na kara ko kwana daya a kauyen nan yunwa xae iya kashe ni" Ya janye rigarsa daga hannunsa ya fice daga bukkar, Nihad ta sulale kan inda ya tashi tana kuka a hankali. Goge idonta tayi da sauri jin ana sallama, ta kalli matan da suka fara tururuwan xuwa kofar Bukkar da take don gaisheta, da murmushi take amsa masu gaisuwar tasu cike da karfin hali don yunwa ba na wasa ba take ji, tunda take bata ta6a jin irin wannan kalan yunwan da take ji ba, wata mata ta shigo ta kwashe kasar dai dai inda fura da nono ya xuba ta fita da shi, Nihad ta bi ta da kallo, to ko kiwon dabba ake yi ai a tunaninta ba a kiwonsa a ordinary sand balle mutum, ko kaji ma ana shimfida masu kwali.... Nan ko ga kasa kiri kiri a daki kamar a kofar gida, Gwaggo ce ta shigo daga karshe rike da kwanon dumamen tuwo ta ajiye mata tace "Hannu Ummi, an tashi qlau dai ko?" Nihad na Murmushin karfin hali tace "Ina kwana Mama" Gwaggo tace "Lafiya lau, ga tuwo ki ci kafin kiyi wanka, ko dai kina son yajin daddawa a kawo maki da man shanu" Da sauri Nihad tace "Aa nagode xan ci haka" Gwaggo tace "Toh, Don naga jiya ma kamar baki wani ci tuwon ba, wannan na barbada maki me tauraro a kai, xaki ji dadinsa, kinsan ku yan birni baku amfani da manda a girki" Nihad dai sai ka rantse tallan close up take yanda take murmushin karfin hali tana kallon tsohuwar, Gwaggo tace "Ko a damo maki hurar ki hada da tuwon naga faro faron ma baki sha ba" Nihad ta girgiza kai tace "Aa wannan ya isa mama, nagode" Gwaggwo tace "Idan kin gama ci sai ki fito an kai maki ruwan wanka" Nihad tace "Toh" Bayan fitarta da kamar minti sha biyar Nihad ta mike ta fita tsakar gida, haka duk matan gidan dake shirin surfe suka bi ta da kallo, Gwaggwo ta taso tace "Har kin cinye" Nihad tace "Ina son xan yi wanka" Gwaggo ta rakata xuwa bandakin ta bude mata kofar karan tace "Ga ruwan a ciki" Nihad ta saka kai ta shiga ciki, bayan matar ta bar wajen kawai ta fashe da kuka, yau ita ke ganin rayuwa haka, yanzu a haka xata yi wankan?? A daddafe ta watsa ruwa tana rike numfashi sbda uban zarnin da wajen ke yi ta fito da sauri, har ta shiga bukka kallonta matan tsakar gidan suke, ko mai Nihad bata shafa ba ta saka kayanta ta xauna gefen gadon kara jiki a sanyaye tana bin kudajen dake ta shawagi a dakin da kallo, Sai kuma ta hade kai da gwiwa ta fara shesshekar kuka tana jin kamar Ulcer xai iya kamata at anytime. Har rana bata ga Khalil ba, aka kawo mata gwaza da mai da gishiri, da farko tayi xaton doya ce amma bayan warce ta kawo mata ta fita, ta dauka tana kare masa kallo kafin ta 6are ta kai baki a hankali, da sauri ta fito da shi tana yamutse fuska, a haka ta matsar da kwanon a inda kwanon tuwo da faro faro suke tayi tagumi, cike da tausayin kanta. Kusan karfe hudu saura Gwaggo ta leko bukkar tace "Ke baki fitowa shan iska Ummi, ai da xafi dakin..." Nihad ta girgiza kai a hankali tana mata murmushin karfin hali, alamar bata son ta fitowa, Gwaggo ta kyaleta ta tafi ta ci gaba da abinda take, duk motsin da xata ji sai ta leka ko Khalil ne amma sai taga ba shi bane, a haka har ta fita taje tayi alwala ta dawo tayi la'asar, xuwa lkcn jikinta rawa yake saboda yunwa, she is very very hungry, amma babu abinda xata iya ci cikin abubuwan da aka kawo mata, kukan ma ta gaji da yin sa yanxu ta daina, tana idar da sallah ta kwanta saman


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login