Showing 126001 words to 129000 words out of 292821 words
Chapter 43 - NIHAAD COMPLETE DOCUMENT Complete by Khalisat Haidar .txt
ta shigo, Bilkisu na murmushi tace "Ina kwana" Nihad ta sauke idonta tace "Mun tashi lafiya" Bilkisu tace "Ai da kin bar shi ma xan shigo in gyara, aikina ne" Nihad dai bata ce mata komai ba ta shigo ta fara abinda zata yi, Nihad ta fita parlor, tana bude kofar first parlor taga Mami da khalil a zaune parlon, Ta gaida Mami da ladabi Mami ta amsa mata da fara'a, ta kalli Khalil suka hada ido, ta kasa barin wajen bata gaishesa ba saboda Mami dake zaune, bata yarda ta kallesa ba tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya, ga breakfast din ki" Mami tace "Bari a kai mata can parlon so that she will be comfortable" Yace "Aa za ta yi a nan" Nihad dai bata ce komai ba, can ta karasa cikin parlon tana tafiya a hankali, ya nuna mata breakfast din dake saman tray, ta dauka ya nuna mata inda xata zauna, Mami dai sai bin ta da kallo take because she is so cute and meek, Mami ta kallesa tace "Amma 'yar mai gidan da kake ce min kana zama wani lokacin a gidansa ce ko?" Khalil zai yi magana aka bude kofar parlon, Mimi da Noor ne suka shigo, suka yi wani ihu a tare ganinsa, daga inda yake zaune duk suka tafi da gudu suka rungumesa so happy seeing him, sai ga wasu set din Yan matan biyu Hanan da Farhana, su ma duk suka rungumesa so so happy seeing him, he couldn't help it but smile don shi ma yayi kewansu sosai, Mami dai sai murmushi take, Mimi ta kalli Mami ta fashe da kuka tace "Mami mene ya sa zaki boye mana yayanmu ya dawo, Abba yace he's been around since yesternight" Sai kuma ta fashe da kuka, Khalil ya jawota gefensa yana kallonta yana murmushi yace "Is there any diff between now and the yesternight" Tace "Yes of course, wallahi da nasan kana nan nima a nan zan kwana jiya, i soo miss you yayanmu" Tana fadin haka ta kara rungumesa tana hawaye, Nihad dai sai bin su take da kallo kana ganinsu kasan su ne ainahin rich kids din, duk Mimi ta fi kama da shi, Noor ma fara ce Farhana da Hanan ne kadai haskensu bai kai nasu Mimi ba, Farhana sai kallon Nihad take keenly, can ta kalli Mami tace "Mami who is she?" Mami tace "Our visitor" Tambayarta ne ya ja hankalin sauran yan matan suka kallo inda Nihad ke zaune, Noor ta Ιan juya ido tace "Ohh She looks familiar" Hanan dai kallonta take babu ko kiftawa kamar me son gano wani abu, can ta ja Noor suka fita daga parlon tana zare ido tace "Kin tuna wata yarinya da video dinta ya tafi viral weeks ago?" Noor ta zaro ido bayan tayi recalling video din tace "Ohh yess!! exactly, wallahi suna kama sosai, i think baxan rasa video din a thrash bin dina ba" Tun da Khalil yaga sisters din nasa duk sun yi concentrating kan Nihad, yace "Ohk, ohk now, i need rest za mu hadu anjima a main parlor..." Mimi tace "Yayammu who is she, nima kamar na santa" Mami tayi dariya tace "A ina kika santa, banda karya Mimi" Mimi ta juya ta sake kallon Nihad da ta sunkuyar da kai gabanta na mugun faduwa don banda nude video dinta babu abinda ya fado ranta, mikewa Khalil yayi yace "Mimi za mu hadu anjima a main parlor, i said i need rest, ku fita" Sai ga Noor da Farhana sun shigo da gudu parlon, Hanan ta biyosu da sauri, Noor ta nufi Mami har tana tuntube tana mika mata wayarta tace "Mami u remember this???" Mami ta amshi wayar ganin video din da take nuna mata tace "Wai ba nace ki goge video din nan ba Noor? What is it still doing a wayarki?" Noor na zaro idanuwanta kamar za su fito tana nuna Nihad tace "Ba ita bace warcan" Mami ta kalli Nihad da sauri, sai kuma ta amshi wayar tana kallo, Kasa cewa komai Khalil yayi, Nihad da jikinta yayi sanyi kamar warce aka kwara ma ruwan sanyi ta kasa kwakkwaran motsi inda take zaune ta dinga bin su da kallo kamar warce tayi ma sarki karya, sai kuma ta sunkuyar da kanta with tears in her eyes, Mami ta kalli Khalil da sauri, sai kuma ta kara kallon Nihad, tuni Farhana ta tafi ta kirawo wasu set din yan mata biyu duk suka tsaya bakin kofa ko warce da wayarta a hannu, da ta kalli videon sai ta leko ta kalli Nihad baki bude, Mami da ita kanta jikinta yayi sanyi qlau ta kara kallon Khalil that is saying nothing, can ta hadiye wani abu tace "No, no may be resemblance ne kawai, ai akwai resemblance" Noor da Farhana suka wani gwalo ido har suna hada baki suka ce "Mami wallahi ita ce, the video is so clear fa ba wai yayi dishi dishi bane, ki duba mana ki ga, ita ce wllh" Da sauri Hanan ta tafi tana mika ma Mami waya wai don ta kara gani da kyau, Mami ta ki amsar wayar bata kuma sake cewa komai ba, Sajida tace "Ikon Allah, then who brought her to this house? Ance yar Maryam Abatcha American University ce fa" Mimi dake tsaye gefen Khalil ta kallesa a hankali tace "Yayanmu who is she?" Bai ce mata komai ba yana bin sisters din nasa da kallo ya nuna masu kofa yace "Ku fita" Farhana ta kyabe baki haka ma Hanan duk suka juya, Noor ma tayi ficewarta, Mimi ta dinga kallon Nihad dake ta hawaye, Ita ma ta fita daga parlon, Mami dai mutuwar zaune tayi a inda take. Daga karshe ta mike ta shiga dakinta ta zauna side din gado duk jikinta a sanyaye, a ina Khalil ya samo yarinyar nan har zai shigo da ita gidan nan? Bilkisu ta fito daga bandaki tana kallon Mami ganin yanayinta tace "Mami are you okay?" Mami tayi karfin halin cewa "Sure, ki tafi idan ina bukatarki zan kira ki Bilkisu" Tace "Toh Mami" Daga haka ta fita daga dakin, Har sannan Khalil na tsaye ya rasa abun yi, Nihad dai ta hade kai da gwiwa tana shesshekar kuka, Bayan Bilkisu ta fita ya juya ya tafi dakin Maminsa, yana shigowa dakin ya kulle Mami ta mike tana kallonsa cike da tuhuma tace "Khalil wacece warcan yarinyar ka kawo mana gidan nan? Who is she? Menene alaqarku?" Yayi gathering courage yace "Mami calm down pls, yarinyar mai gidan da nace maki nakan zauna wajensa a kano ce, kuma ai na gaya maki dalilin da ya sa muka taho tare, Banda wannan babu wani dalilin Mami" Mami tace "Toh zan tura maka kudin jirgi ka siya mata ticket ta koma, ai ta gama abinda take ko?" Ya rasa abinda xai ce, Mami ta hade rai tace "Ko baka ji abinda nace bane?" Yayi kasa da murya yace "Mami bata gama ba, bata samu amsan admission letter din ba ma" Mami tace "Toh me kake nufi? Ka gaya min me kake nufi Khalil?" Ya marairaice yace "Mami karki manta gidan babanta fa nake all this while, bai san ni ba ya yarda da ni, yayi accomodating dina na zauna cikinsu for almost 10 months now" Mami tace "Yanxu ya kake son ayi khalil? Me kake son in fada a wannan issue din? Sai kace baka san mutanen gidan nan ba ko mance halinsu ne? wait first... Wai ma ita ce a video din nan ko ba ita bace?" Ya sauke idonsa kasa bai iya yace komai ba, Mami tayi masa tsawa tace "Baka ji na ne?" Cike da karfin hali yace "Ita ce" Mami tace "Nawa ne kudin jirgin, zan tura maka yanzu" Yana girgiza kai hankali tashe yace "Mami mun yi magana da mahaifinta kan cewa ta zauna nan gunki har ta karbi admission letter din tunda bai fito ba, Mami we can't repay him this way, he is one of the nicest person i have met in life, kawai ka haifi yaro ne baka haifi halinsa ba, but her mother and father are down to earth, sun min abinda baxan mance su a rayuwa ba, sannan Mami duk yaran gidan mahaddatan qur'ani ne, kawai dai ita...." Sai kuma ya kasa ci gaba don ya rasa me xai ce, Mami ta fashe da kuka tace "Magana kake son ja min yanzu fisabilillah Khalil? A ina kake son in ajiyeta har ta zauna a gidan nan bayan kana gani duk yan matan sun shaida ita ce a videon nan kuma sun je su idar, sannan har shi Abbanku sae da ya tofa nasa a lokacin da ya ga video din nan kwanaki, he was so disappointed yayi ta addu'an Allah ya shirya mana zuri'a, sai kawai yau a ganta a gidan nan ba kuma kowa ya kawota ba kai?? Kai da kake da ta6o ta ko ina a gidan nan shine zaka kara shafa ma kanka kashin kaji? Check this out khalil, yaushe har Abban naka ya bukaci ka dawo da har zaka dawo tare da wannan issue din? Kayi min gata kayi ma kanka gata ka fitar da ita daga gidan nan kafin wani ya kara noticing dinta bayan kanninka, Plss take her out of this house Khalil"
Masu jira ina turawa su yi fowarding a dinga yi ana tunawa da hakki, ku kuma masu karantawa a bati amma fa a duniya yake bati, duk na gaisheku kyauta ya damuna?? Masu posting on Facebook, Hassan Basiru majia, Aminu Arthur and the rest, Hmm an dai ce prevention is better than cure, i warned first.
Nihaad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence viaππ»
07087865788......
*Wato duk me son sanin wani turare Nihaad ke sakawa da ke sa Khalil jiyo kamshinta da ta gifta waje upon the hatred ya biyoni pc don abun sirri ne, nima shi nake sa wa Barrister ke jiyo kamshina tun daga gate, joke apart..., kuma saboda wannan kamshin ya min alkawarin daga ni ba kari* π€π₯°
_SCENTMANIA_π―
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: ππ NIHAAD ππ
36
Khalil na isa hotel din ya nufi dakin direct ya bude kofar, sosai ya ji gabansa ya fadi ganin babu kowa cikin dakin, da sauri ya karasa ciki yana kallon abincin da ya ajiye mata yaga ko ta6awa bata yi ba, lkci daya yaji zufa na keto masa, kallon kofar bandaki yayi nufi can da sauri ya bude kofar nan ma babu ita a ciki, nan yaji hankalinsa ya kara tashi ya fice daga dakin ya sauka kasa yana kallon receptionist din wajen yace "Don Allah yarinyar da muka shigo dazu..." Kafin ya karasa receptionist din tace "Ta fita ai" kasa daina kallonta yayi, yayi karfin halin cewa "Ta fita? When pls?" Matar tace "Some minutes ago" juyawa yayi da sauri ya nufi kofar fita daga cikin hotel din, receptionist din ta bi sa da kallo, Khalil na fita bakin titi yana waiga gefensa ya ganta can zaune daga jikin hotel din kamar marainiya, lokaci daya ya hade rai ya nufeta, ita bata ma lura da shi ba tayi nisa cikin tunanin da take, yana isa dai dai inda take yace "Baki da hankali ne zaki fito nan bayan kinsan jakata na dakin?" Ta daga kai ta kallesa, sae kuma a hankali tace "To ba kai nake nema ba" yace "Me yasa zaki nemeni? Saboda me?" Ita dai bata ce komai ba, sai a sannan ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, ya juya ya bar ta wajen, ordering wani bolt din ya mayar da wayarsa a aljihu ya juyo yana kallonta yace "Ki jira ni a nan" Daga haka ya koma dakin don dauko jakarsa, yana fitowa sai ga motar, bayan sun gaisa da drivern ya sa jakarsa a booth, ya juya ya kalli Nihad dake kallonsa, ai bata ma jira yace ta taso ba ta taso ta nufosa, ya zaga ta daya side din ya shiga motar, tana dai ta tsaye, jin bai ce mata komai ba ta bude bangaren da take tsaye ta shiga ta jawo kofar motar a hankali. Kamar me Bolt din dazu wannan ma sae da ya tambayi khalil ko zai iya shiga ciki ganin unguwan da suka zo, Khalil ya sauke glass din side dinsa ya daga ma securities din wajen hannu sannan suka wuce, Nihad dai tun da suka shigo anguwan nan take kalle kalle uwa idanuwanta za su fito, she is wondering where he is taking her to, duk inda suka wuce sai taga securities, very tight security, bata ta6a jin tsoron kasancewa da Khalil ba sai wannan moment din, she looked at him looking very afraid, to ko dai inda ake yankan kai ma zai kaita, sosai gabanta ya dinga faduwa hankalinta yayi mugun tashi, ta dinga kallon Mad houses din da suke ta wucewa na masu kudi da suka amsa sunan su kudi a kasar, hakurin Nihad ya soma karewa ta juya a hankali ta sake kallon Khalil for the 5th time, gabansa kawai yake kallo fuskarsa babu yabo babu fallasa, Ai bata san sanda ta marairaice masa ba cikin rawan tace "Don girman Allah ina zaka kai ni? Don Allah kayi hakuri ka rufa min asiri, ina ne nan ka kawo ni?" Sai ta sakar masa kuka a hankali jin ya ki ce mata komai, shi dai ko kallonta baya yi, ko ma wanene yanda Khalil yayi keeping serious and straight face sai ya tsorata balle Nihad da dama can matsoraciya ce, Shi kam drivern bolt din slowly yake tafiya sbda Securities that are everywhere don zuwa lkcn gari yayi duhu, amma sai kayi tunanin rana ce don ko ta ina haske ne tarr, har dai suka isa dai dai gidansu Khalil, sai dai ba ta inda ya shigo dazu bane, wannan second gate din gidan ne dake ta baya, drivern ya tsaya yana duban ma'aikatan da suka nufo motar gadan gadan, Khalil ya bude motar ya sauka, suna ganinsa suka gaishesa suna komawa baya, Ganin Nihad taki saukowa daga motar ya zaga ta inda take ya bude motar yana kallonta babu yabo babu fallasa yace "Malama kina bata masa lokaci" Ta marairaice tana kallonsa cikin rawan murya tace "Don girman Allah ina ne nan din ka kawoni, kayi hakuri ka gaya min" Gaba daya tayi zuru zuru da ita kamar ba Nihad ba, shi dai kallonta kawai yake, can yace "Neman taimako na zo yi nan din, tunda kin ga bamu da inda za mu je" Ta gwalo ido sosai tana kallonsa da mamaki, can tayi karfin halin cewa "Taimako kuma? Unguwar masu kudi ne sosai fa, ba kowa ne ke shigowa nan ba wallahi, kuma ko kallonmu baxa su yi ba sai ma su kore mu ko su sakar mana karnuka, wllh ka shigo idan ba haka ba securities din nan za su iya sa mu tsallan kwado yanzun nan" ya dafa motar yana kallonta da kyau yace "Sa'armu za mu gwada, kuma ni nasan ina da sa'a sai in ke ce baki da, Malama ki sakko kina bata ma me mota lokaci" Da sauri Nihad ta kalli me tukin motar dake jiranta ta sauka patiently, can ta kalli khalil pleadingly tace "Ni dai don Allah ka zo ka shiga mu koma, babu abinda za su mana a nan" Yace "Idan muka koma kina da kudin da za mu ci abinci gobe? Ko kina da kudin da zaki sake biya mana daki a hotel din?" Kallonsa ta dinga yi, lkci daya jikinta yayi sanyi, hawaye ya kawo idonta, sai kuma ta sa hannu ta share idon nata a hankali tace "Sai ka bani waya in kira ya Farooq nasan zai turo mana kudi" Yana kallonta yace "Aa, wannan gidan dai nake son shiga in gwada sa'a ta" Ta kallesa zata yi magana ya hade rai yace "Kina bata masa lokaci malama" a hankali ta sauko daga motar tana kallon Khalil hawaye na bin kuncinta, ya daga ma mai bolt din hannu ya ja motarsa ya bar wajen, cikin kuka tace "Toh ni dai da kace ya maida ni in jiraka a can hotel din, in ya so kai kadai sai ka shiga gidan" Wani kallo yayi mata ya nufi gate din gidan da tuni aka bude masa, Ta gefen ido take kallon securities din gabanta na faduwa don wasu dirka dirkan bayin Allah ne, can dai tana ganin Khalil ya shiga cikin gidan ta bi bayansa da sauri, ga mamakinta basu kulle ba suka jira har ta shiga sannan suka rufe gate din, Nihad ta dinga bin makeken compound din me dauke da wani ubansun mansion da kallo, kai kana ganin gidan nan kawai kasan ba karya malam, Compound din kuwa yayi ukun nasu ga parking lot kaca kaca, ko wanne da ride lafiyayye a parke, ita bata ma san ta bayan gidan suka shigo ba, don ta can ne zata ga ainahin kyan gidan, chalet da aka yi can gefe da ta hango kuwa ya kusa nasu main building din, tafiya kawai yake tana binsa zuciyarta na bugawa, but how comes yana ta tafiya kansa tsaye and nobody is even stopping him, taga sun zaga ta baya ya shiga wani stairs wanda aka shimfida ma carpet grass, shi kansa tsakar gidan wajen duk malale yake da Carpet grass din, bude wani kofa yayi bayan sun haura sama sun mike wani babban corridor, ya bude wata kofar duk tana biye da shi a baya a tsorace, ko nisa bata son yayi mata, gaba daya she is really confused at how he is just badging in babu shakka ba komai, ita tsoronta kada a kama su ayi masu dukan tsiya, da ido ta dinga bin parlon da ya shiga tana makale bakin kofa ta kasa shiga zuciyarta na bugawa, Can taga ya shiga wata kofar da sauri ta bi bayansa ko kulle kofa bata yi ba, nan taga kofar da ya shiga wani parlon ne wanda ya fi wanda suka baro haduwa, at this point, she is super confuse, bayan ya isa kofar dakin Maminsa ya juyo yana kallonta, ya fi