Showing 99001 words to 102000 words out of 292821 words

Chapter 34 - NIHAAD COMPLETE DOCUMENT Complete by Khalisat Haidar .txt

25 Nov 2024

39473

gadon karan tana juye juye, daga karshe ta mike ta sauko kasa jikinta na rawa ta bude farau faron dake kulle ta dauka, runtse ido tayi cike da karfin hali ta kai bakinta kan kwanon ta rike breathing dinta sannan ta hau kwankwada, ajiye kwanon tayi da sauri bayan ta kwankwadi kusan rabi, saboda wani amai da taji ya taho mata, ta mike da gudu ta fita daga dakin, gwaggo da matan tsakar gidan dake surfe suka taso da sauri suna tambayarta lafiya, nan ta dinga kwararar masu aman abinda ta sha kamar xata shide, Gwaggo da duk ta rude tace "Subhanallahi, me ya sameki, gashi baya nan" Wata mata ta kawo ruwa da sauri suka ba Nihad dake maida numfashi, amsan ruwan tayi da kyar ta wanke bakinta duk jikinta na rawa, Gwaggo da hankalinta yayi mugun tashi ta kawo mata kujerar tsugunno tace "Hannu, zauna nan, zauna" Nihad ta xauna a hankali kan kujeran tana maida numfashi, Gwaggwo tace "Me ya sameki kike hararwa haka?" Da kyar tace "Bani da lafiya ne dama" Matan gidan suka dinga yi mata sannu, ganin yanda jikinta ke rawa Gwaggo ta maida ta cikin Bukkar tana mata sannu ba adadi, wata yarinya da ta aika ta dubo mata Khalil a waje ta dawo ta shigo Bukkar tace "Gwaggo bamu gansa ba" Gwaggo tace "Toh bari a mata jike jike tasha ko xaxxabin xai sauka" Daga haka Gwaggo ta fita, kuka Nihad take a hankali tana juye juye tana jin kamar kanta xai fashe don ciwo, bayan wani lokaci sai ga gwaggwo da kwano ta ajiye kasa ta dago Nihad tace "Ga nan jike jiken sassaken itatuwa na maki, tashi ki sha, ba daci ba bauri, ba hamami" Nihad ta mike tana rawan sanyi Gwaggwo ta dauko kwanon ta kai mata baki tace "Ungo sha" Cike da karfin hali Nihad dake ta kallon cikin kwanon ta kurbi ruwan ciki, Gwaggo tace "Kara sha" Nihad ta runtse ido ta kara kurba ta hadiye tsikar jikinta na tashi, dacin ruwan kuwa ba a cewa komai, Gwaggo tace "Yauwa, to koma ki kwanta yanxun nan xaki fara xufa, su ararrabi ne da sabara da tazargade, ga su nan dai" Nihad ta koma ta kwanta Gwaggwo na kokarin lullubeta Khalil ya shigo Bukkar ya nufo Nihad yana kallonta, Gwaggwo tace "Wallahi mugun zazzaɓi ne ya rufeta yanxun nan sai hararwa take" Khalil ya duka yana kallonta ya kai hannu jikinta wanda yayi zafi kamar wuta, cike da damuwa Gwaggwo tace "Akwai wani karamin asibiti a gidan Darho, kauyen da xaka wuto kafin ka zo wannan, ko xaka kai ta a dubata a bata magani ɗan nan?" Khalil yace "Toh xa mu je can" juyawa tayi ta fita daga Bukkar, Hannu ya kai goshinta duk da idonta a kulle yake yace "Ina ke maki ciwo" Ta fashe da kuka ta tura hannunsa daga goshinta tace "Ni ka maida ni gidanmu, idan ba haka ba sai Allah ya kama ka" kallonta ya tsaya yi, can ya gyada kai ya koma gefe yace "Ohkk" tayi karfin halin mikewa cikin kuka ta kamo hannunsa tace "Don Allah kayi hakuri ba don halina ba ka maida ni gida" Yace "Toh ina ke maki ciwo?" Tana shessheka tace "Kai na, kuma ina jin yunwa" Ya mike yace "Sakko" Da sauri ta mike xaune amma ta kasa tashi daga saman gadon duk yana kallonta, ya mika mata hannunsa ta rike sannan ta mike tsaye a hankali, dukawa tayi yana rike da hannunta ta dau Hijab jikinta na rawa ta saka, sannan ta dau handbag dinta, ko bin ta kan atamfarta na karshe da kayan shafe shafenta bata yi ba, a haka suka fita daga Bukkar, Gwaggwo da matan gidan suka taso, ana mata sannu in chorus, Gwaggwo tace "Can asibitin ku ka nufa ko?" Yace "Ehh" Nan dai aka dinga mata Allah ya sauwake, Fure dake tsaye kusa da wani ɗan mariki da aka daure tace "Gwaggwo in rakasu asibitin" Da sauri Nihad ta kalleta, murya can kasa Nihad ke girgiza ma Khalil kai tana cewa "Aa baxa mu je da ita ba" Ya ɗan kalleta ta gefen ido, Gwaggwo tace "Toh ko kama maka ita ai sai fure ta dinga yi a asibitin ko" Da sauri Nihad na Murmushi tace "Aa mama xan iya ai" Gwaggwo tace "Toh shkkn, Allah ya baki lafiya sai kun dawo" Nihad dai bata ce komai ba a ranta kuwa tunani take ina din xa su dawo da take ce masu sai sun dawo? Dalilin ma da yasa bata son Fure ta bi su kenan don in sun tafi da ita ai dole su dawo da ita kauyen, ita kuwa bata fatan abinda xai sake dawowa da ita kauyen nan, suna isa inda Khalil ya ajiye mota ya saketa ya zaga daya side din, a hankali ta bude front seat din ta shiga, bayan yayi warming motar ya ja motar, matan gidan da suka taru bakin kofar shiga gidan har da masu daurin kirji, ga yaransu duk ba wando a tsattsaye su ma, sai daga masu hannu suke kana ganinsu dai kaga yan kauyen kayau, haka ma sauran makota da suka fiffito jin karar mota, Nihad ta sauke wani ajiyar xuciya, at long last!!! har taji xaxxabin ya tafi sai kuma bakar yunwan da take ji, tafiyar minti talatin suka yi ta ga alamar sun fara shigowa gari, farin ciki gunta ba a cewa komai, bata ta6a tunanin xata fito daga kauyen can da ranta ba, ta zata sai buzunta, so truly akwai mutane irin haka a rayuwar nan, akwai mutane dake rayuwarsu cikin kauye haka? lkci daya jikinta yayi sanyi, and they are leaving happily abunsu babu wani damuwa, ko pole din wuta ita bata gani a garin ba balle a je ga an ja masu wuta, parking ta ga khalil yayi dai dai wani pharmacy, duk da bata san inda suke ba amma tasan sun shigo cikin gari gaba daya, ya kashe motar ya sauka yana kallonta yace "Sauko malama" A hankali ta bude motar ta sauko ta bi bayansa tana jan kafa saboda jiri da take gani, suka shiga pharmacy din, bayan sun gaisa da me Pharmacy din ya koma gefe ya tsaya yana kallon Nihad da ta jingina da kofar pharmacy din bata shigo ba, har ta rame tayi wani uban duhu kamar ba Nihad ba, Ya kalli me Pharmacy din yace "Ita ce bata da lafiya" Me Pharmacy din yace "Sannu Hajiya karaso" Tana jan kafa ta tafi gaban table dinsa ta xauna, Tunda aka haifeta ba a taba kawo su pharmacy idan basu da lafiya ba, sai dai asibiti, amma wai yau ita ce a pharmacy xa a mata treatment bata da lafiya instead of hospital, muryar Pharmacist din ne ya dawo da ita duniyar tunanin da ta tafi, ta sauke idonta kasa a hankali tace "Zazzaɓi nake ji da ciwon kai" Yace "Kina amai ne?" Ta gyada masa kai tace "Ehh nayi daxu" Yace "Ohk" Kallon khalil yayi yace "Xa a maganunguna da allurai...." Khalil ya rungume hannunsa yace "Sai dai magungunan kadai, don kauyen da muke akwai nisa, baxai yiwu mu dinga xuwa muna komawa ba kullum" Da mugun shock Nihad ta kallesa, bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka tace "Don girman Allah ka rufa min asiri kar ka maida ni garin nan" Khalil ya danne dariyarsa ya hade rai, Me Pharmacy ya tuntsire da dariya yana kallon Nihad da duk ta gama rikicewa, Khalil yace "Shi garin namu kike ce ma garin nan" Ta hade hannunta cikin kuka tace "Ka rufa min asiri mu wuce gida don Allah" Khalil ya kalli me pharmacy yace "Malam ba mu maganin kawai, hanyar kauyen ba shi da dadin tafiya da daddare, kaga magariba ya kusa" Kuka kawai Nihad take hankali tashe tana kallon khalil, me pharmacy dai ya basu magunguna ya sa a leda ya mika ma khalil yace "Duk prescriptions din na jiki" Khalil ya amsa yace "Nawa ne?" Me pharmacy din ya gaya masa ya zaro kudin a aljihu ya mika masa, Yana kallon Nihad ya daure fuska yace "Tashi mu je" Ta mike tana kuka tace "Kayi min rai kar ka sake maida ni garin nan wallahi baxan iya xama ba kilan ma in mutu" Khalil yace "Fita mu je" Fita tayi daga pharmacy din ya bi bayanta, tayi mugun ba me pharmacy din dariya don sai kallonta yake, ta tafi gun mota tana kuka kamar an aikota ba tare da ta damu da mutanen dake kallonta a wajen ba, bude mata back seat yayi yace "Shiga inda kika fi jin dadin zama ki xage mutane kiyi masu rashin kunya...." Ta shiga bayan motar tana kuka kamar ranta xai fita, ya ajiye mata ledan maganinta ya koma driver seat ya ja motar suka bar wajen..... Wani eatry Khalil yayi parking ya kashe motar bayan ya ɗan sauke glass ya sauka sannan yayi locking motar, ita dai kuka kawai take don har ta saka a ranta cewar in har taga sun nufi hanyar kauyen nan to suma kawai xata yi a cikin motar kuma duk abinda xa ayi mata baxata farfado ba, ba a dau lkci sosai ba ya dawo rike da ledan take away, ya ajiye a back seat sannan ya shiga mazaunin driver yana kallonta ta madubi yace "Bari a kai ki inda xa ki yi wanka kafin mu koma, don naga babu wajen wanka a garin" daga haka yayi reverse suka bar haraban eatry din, Rokonsa Nihad ta dinga yi hankali tashe tana cewa ya rufa mata asiri su koma gida amma bai tanka ta ba, a wani hotel taga ya shiga yayi parking, tsaf ta gane hotel din don sun ta6a xuwa da su Husnah, yanxu da gaske wankan xata yi su koma wannan kauyen?? yana parking ya sauka ya kulle motar ya bude side dinta fuska daure yace "Sauko malama" A hankali ta sauko daga motar, ya dau ledan maganinta da abinci, yana gaba tana biye da shi suka shiga reception din hotel din, ya gaisa da masu aiki a nan, makulli kawai ya amsa alamar dai ya kama dakin tuntuni, ganin yayi hanyar stairs ta bi bayansa tana ji kamar iska xai kadata ta fadi, ya bude dakin ya shiga ita ma ta shiga sannan ya kulle kofar, bin dakin take yi da kallo, taga tray me dauke da kayan shayi da cup din shayi alamar an sha shayi, ya kunna wutan dakin ya sauke curtains sannan ya shiga bandaki, tana jin alamar wanka yake yi ta zamo kasa a hankali ta zauna ta jawo ledan abincin da ya ajiye ta bude, fried rice da yaji liver hade da spicy jollof rice a gefe ta gani, sai peppered chicken, tayi unwrapping cokalin daga tissue dake jiki, har wani rawa jikinta yake ta fara cin abincin, Nihad da bata wani cin abinci sai gata ta cinye abincin nan tasss naman kawai ta ci kadan ta bari don ita cin nama aiki ne a wajenta, kai ta yage yage kana bata baki da maiko, ta bude chilled chivita dake leda shi ma kadan ta sha sannan ta ajiye, Sai a sannan ta fara gani dai dai ta daina jin jirin da take ji, fitowa khalil yayi daga bandaki ya dinga kallonta da mamaki, can yace "Amma wa yace maki naki ne da kika dauka kika ci?" Ko kallonsa bata yi ba balle ya sa ran amsa, sai kuma ta mike ta wuce ta gabansa ta tafi jikin window tana kallon waje da motocin dake ta tafiya saman titi, waii lallai ta jinjina ma yan kauye, Allah Ubangiji ya kawo masu mafita. Tana jin ya fita daga dakin ta juyo a hankali ta dawo gefen gado ta zauna tana tunanin irin rayuwar da tayi na kwana biyu kacal, ita kanta tasan ta rame kuma ta yi baki, tashi tayi daga karshe ta shiga bandaki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana sallan Magrib, banda Aliyu babu wanda ke ranta, ta mike a hankali ta tafi kofar dakin ta murda taji a kulle, dawowa tayi ta fada saman gado ta lumshe ido, nan da nan bacci ya dauketa......










*Nihad* is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah




Ur evidence via👇🏻






07087865788✍🏻










Assalamu alaikum er uwa, kina neman organic Supplement irin masu gyaran jiki ciki da waje? Ko kuma mai fitar Maki da duk wani infection komai nacinsa? Sannan mai maido Maki martabar fatarki? Ko kina fama da dry HQ? Ko hips ne matsalarki da boobs? To kwantar da hankalinki *GHT Organic supplement care gat ur back*




Domin karin bayani ki tuntubi wannan number 👇🏻


+2347057607751✍🏻
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: 💖💖 NIHAAD 💖💖


30




Ganin Nihal taki tanka ta sai kuka take, Nihad ta mike da sauri ta koma cikin gidan zata kira Khalil, a bakin kofa ta kusa buge sa ya turata tayi baya xata fadi ganin hakan yayi saurin jawota ta fado chest dinsa, ta zaro ido ta daga kai tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba ya turata gefe ya sauka xuwa wajen Nihal, bin sa tayi da kallo, yana isa wajen ya durkusa gabanta a hankali yace "Ki yi hakuri Nihal, don't take all what she said personal" tana goge hawayen da ya ki tsaya mata tace "Ka bude min gate in tafi gida" Yace "Ba amfani hakurin da nake baki kenan?" ta girgiza masa kai kawai, yace "Now, Behave like the good girl u always are, tashi mu koma ciki" Daga haka ya mike, ita ma ta tashi tana ci gaba da goge idonta, yana gaba tana bin sa har xuwa parlon, Nihad ta riga su shiga parlon kafin su karaso, bayan sun shigo tana kallon Nihal a hankali tace "Kiyi hakuri plss, i didn't mean it" Nihal dai bata ce mata komai ba ta yi wucewarta daki, Nihad ta jefa ma Khalil wani kallo tace "Ai dai kaga abinda ka jawo, kawai ka sa yarinya a gaba kana koya mata gulma da munafurci alhalin ba halinta bane" Daga kai yayi ya kalleta, speaking calmly yace "Idan kina ci gaba da min rashin tarbiya, Billah xan tattara ki in mayar da ke kauyen can" Shiru tayi tana kallonsa, sai kuma ta 6ata fuska tace "Toh ni nace wani abu ne?" Bai sake kallonta ba, ta turo baki ta juya ta koma dakinta. Har Nihad ta gama shirin bacci Nihal bata ce mata komai ba, Nihad ta gama saka kayan baccinta wanda shi kadai ta tsira da shi a gidan ta dawo gefen Nihal da damuwa tace "Shine ina ta maki magana kin ki cewa komai ko?" Nihal ta daga ido ta kalleta tace "Me kike son in ce maki?" Nihad tace "Wallahi kema kinsan i didn't mean it, you know i love u to the extent that i will never hurt you" Nihal ta ɗan yi murmushi tace "Amma duk kwanan nan jaraba kike min a waya ai" Nihad ta marairaice tace "Toh me yasa xaki dinga magana da worst enemy dina a waya? Yanxu da Amina ce ke waya da shi ko wasu can daban ai ni baxan damu ba, amma ke fa kinsan i Cherish u so much, why will u be communicating with my worst enemy?" Nihal tace "Toh shikenan, na maki alƙawarin baxan sake waya da shi ba, dama yawanci ina ce masa ya kai maki waya ne...." Nihad tace "No, just block him kawai" Nihal tace "If that will please u" Tana fadin haka ta dauko wayarta tayi blocking number Khalil sanan tayi deleting number daga wayar tana kallon Nihad tace "Done!!" Nihad tayi Murmushi tace "Kin hakura yanxu?" Nihal tace "On one condition" Nihad na kallonta tace "Ina jin ki" Nihal tace "Ki tashi ki tafi dakinsa" da mamaki Nihad ke kallonta, can tace "Amma ina ga baki da hankali, inje dakinsa inyi masa me? So now u are keeping it in mind cewar mijina ne shi da har xa ki ce in je dakinsa? Why will u leave such thought a xuciyarki idan har ke masoyiyata ce?" Nihal bata ce mata komai ba ta ja bargo ta lumshe ido, Nihad ta ja tsaki ta mike ta koma can edge din gadon, ta fi minti sha biyar zaune kafin daga karshe ta mike fuskarta daure tana kallon Nihal tace "If that will please you shikenan" Daga haka ta dau Hijab dinta ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, bayan ta saka hijab dinta ta kunna wutan corridor din tana kallon kofar dakinsa, can ta kyabe baki a ranta tace ba gwara taje parlor ta kwanta abunta kawai, kashe wutan tayi ta karasa cikin parlon tana tafiya a hankali sbda duhu, laluban dogon kujeran da xata kwanta ta shiga yi bayan ta shigo tsakiyar parlon, a tsorace ta koma baya rana zaro ido bayan lalubenta ya kai ta har jikinsa, ya mike zaune yana haskata da karamar wayarsa, kunya taji ya kamata ta juya tana sosa kai xata bar wajen, yace "Da wani abun da kike so ne???" Ta juyo duk da bata ganin fuskarsa sbda haskata da yayi ta daure fuska tace "Wani abu kamar me?" Yace "Kin fi ni sani ai tunda kika biyo ni nan kina tattaba ni" Tsayawa tayi tana kallonsa kamar me son fahimtar abinda yake nufi, can tace "Kai kasan abinda kake nufi ni ban sani ba" yace "Aa ki dai fada abinda kike so" a takaice tace "Abinda ke ranka shi nake so" daga haka ta xabga masa harara xata bar wajen ya fixgota ta fado gefensa, a tsorace tace "Don Allah kayi hakuri wallahi kwanciya na zo in yi, ni ba wajen ka na zo ba" Cikin husky voice dinsa yace "Duk dakinki babu wajen kwanciya sai kin fito parlor?" Ta boye fuskarta a huge muscles dinsa tace "Nihal ce tace idan ina son ta hakura sai na je dakinka, to ni kuma ina son ta hakura" kallonta kawai yake yana kara tabbatar da ainahin childishness dinta, Wani sanyayyen kamshi ke tashi a jikinta har gashin kanta, lkci daya kuma ya hade rai ya saketa, ta dago kai a hankali tana kallonsa, matsawa yayi daga kusa da ita ya koma daya side


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login