Showing 162001 words to 165000 words out of 292821 words

Chapter 55 - NIHAAD COMPLETE DOCUMENT Complete by Khalisat Haidar .txt

25 Nov 2024

39479

maki ba ai yaci yayan naki ya gaya maki, yaushe rabon mu hadu dake cikin gidan nan balle maganar ya hadu mu? Ai mun kwana biyu bamu hadu ba" Aunty Hassana tace "Gaskiya ne, kya yaɓa min magana son ranki ai, ba laifin ki bane" Bude baki Mami tayi tana kallonta tace "Meye abun ɓacin rai a zancena Hassana?" Tuni Daga Hassana ta mike fuuu ta fice, tana komawa bangarenta ta dau waya ta hau kiran kawarta Chamo, ta yaya za ace gobe xa akai kudi ita da ta zata Mami zata ce mata an daga lokacin kai kudin, Chamo na dagawa Aunty Hassana tace "Ke gobe fa naji ana cewa xa a kai kudin auren, yaya haka?" Chamo tace "Toh in kai kudin aure sai aka yi yaya? Baki ta6a ganin inda aka fasa aure ranan daurin auren bayan an tara jama'a ba?" Aunty Hassana tace "Haka ne, to amma idan kuma hakan bata kasance ba fa? Ai risk ne wannan Chamo, kamata yayi ko kudin ma kar a kai balle a saida rana" Chamo tace "Ke dadina dake gajen hakuri wallahi, sai kace yau aka saba maki aiki kiga aikin ya ci Hassana?" Aunty Hassana ta sauke ajiyar xuciya tace "Aa ba haka bane Chamo, ni dai kawai ina ga ba sai an wani je ga ranan daurin aure a fasa ba, kawai tun ba aje ko ina ba a fasa gaskiya hankali na zai fi kwanciya" Chamo tace "Toh ai abinda baki sani Malam yace min dole ne xa a kai kudin amma a banza tunda ba auren za ayi ba, daga sanda aka kai kudin matsaloli xa su dinga billowa daga both part har aure ya ruguje daga karshe" Aunty Hassana dai tayi shiru don ita fa bata gamsu ba, tasan karkari aka kai kudin nan a sa wata daya in dai yayanta ne, can tace "Toh daga ina ne xa su bukaci a fasa auren Chamo?" Chamo tace "Shi da kansa Khalil din xai ce ya fasa, ke ni bari kiji wllh malamin ma ce min yayi bai ga auren ba kwata kwata, xa dai ayi ta kashe kashen kudi, a siya wancan a siya wannan na biki amma fa ba auren" Aunty Hassana tace "Toh yanzu Sajidar ce ko farhana?" Aunty Hassana tace "Toh ai kya bari maganar auren ya ruguje tukunna ki kawo wannan ko?" Aunty Hassana tace "Toh shikenan, sannan abu na karshe kinsan ɗan iskan yaron nan ko gaisheni ya daina yi a gidan nan?? Wallahi tun da ya dawo ga maciji bai hadani da shi balle yarana, iyaka yayi da kanninsa ko Hanan" Chamo tace "Shi khalil din??" Aunty Hassana tace "Wallahi nake gaya maki" Chamo tace "Wannan ai abu ne me sauki, xan kira malamin in gaya masa xa a san yanda xa ayi...." Aunty Hassana tace "Toh Nagode, za mu yi magana zuwa anjima" Daga haka ta katse wayar tana ta tunane tunane, ita wallahi ko kudin auren ma bata son ya shiga hannunsu, don tasan ba amsa xa ayi ba idan aka fasa auren ai, ga kudi ba na wasa ba xa a kai ta sani. Throughout ranan Nihad taki fito dakinta don ko by mistake bata son haduwa da Khalil, wani sabon tsoronsa take ji har cikin zuciyarta, saboda yanda ta sa abinda yayi mata jiya da daddare a ranta sai da tayi mafarkinsa cikin dare, wajen karfe shidda na yamma Mami ta shigo dakin nata tana tsaye bakin kofa tace "Why are you inside throughout?" Nihad ta ɗan yi yake tace "Aa ina kallo a waya ne" Mami tace "Ohk, ga can takalmi Noor ta siya har da ke" Nihad ta dinga kallon Mami jin wai Noor, ko dai Mimi take son cewa, da sauri tace "Toh Mami, xan fito yanzu" Mami ta juya ta fita, a hankali Nihad ta mike ta dau mayafinta sannan ta fito daga dakin. Tana shiga parlon Mami taga Mimi zaune tana operating laptop dinta, Mimi tace "Kinyi scarce yau fa, hope you know you are having lectures tomorrow" Nihad ta ɗan yi murmushi kawai ta zauna ta gyada mata kai, Mimi ta dau takalmi ta mika ma Nihad tace "Noor got this for us all, same color same design" Nihad ta amsa tana kallon takalmin tace "I appreciate it" bude kofar parlon aka yi Khalil ya shigo, Mimi tace "Awnn Yayanmu you look good daga wajen Sis Nadeeyah kake ko?" Yace "Yeah, ina Mami?" Tace "She went in not too long" Ya ɗan kalli Nihad suka hada ido, ta ɗan daburce tace "erm... Good evening" Yace "Evening" Daga haka ya nufi dakin Mami yana murmushi, Mimi ta wara ido tace "That's sweet of u Nihad, kuma naji dadi da kika ji maganata" Nihad dai bata ce komai ba, can kuma dai ta dau takalminta tace "Zan je inyi sallah, it's almost magrib" Mimi tace "Ohk" Daga haka Nihad ta mike ta fice daga parlon don bata ma son ya fito ya sameta. Tare Khalil da Mami suka tafi bangaren Abba ta dalilin kiranta da Abban ya aika khalil yayi, Mami ta gaishesa bayan sun samesa a parlor tare da Aunty Hassana, Mami tace "How was the trip?" Yace "Alhamdulillah" Mami tace "I was thinking ba sai ka dawo ba, representative dinka kawai zaka aika goben" Abban ya ajiye takardun hannunsa yace "Ni ba saboda shi na dawo ba ai, kuma i think gobe xan yi tafiya portharcourt..." Mami tace "Allah ya kai mu" Shi dai khalil na zaune nesa da su yana danna wayarsa, Abba na kallon Mami yace "Dama i want to confirm if ke ce ke aikosa ya zo nan yayi min rashin da'a" Aunty Hassana ta sauke wani ajiyar xuciya, Mami ta kalli khalil da sauri, Khalil ya ajiye wayarsa yace "But i see nothing wrong don na tambayi hakkina Abba, i am asking you for my property, i seriously need them" Abba ya mike yace "Toh daga yau ka sake shigo min nan da wannan maganar i am promising u i won't take it likely with you..... Nace baxan bayar ba kuma i mean it" da mamaki Khalil yace "But why? I have all right to ask Abba" cike da damuwa Mami tace "Me yasa idan na maka magana baka ji Khalil? Me yasa kake daukan maganata for granted pls" Khalil ya mike yana jin ransa na ɓaci yace "Mami to saboda me za a rike min abubuwana akan laifin da ban aikata ba? Akan something i knew nothing about, why???" Aunty Hassana ta bude baki tace "Akan laifin da baka aikata ba? Ehh lallai ka cika mara kunya kuma fitsararre, Sannan da ka mike a zabure haka dukan uban naka za kayi ko yaya?" A fusace yace "Kee ni ban sa bakinki ba Hajiya, babu ruwanki da issue dina da mahaifina, stay in ur lane and stay out of family issues da bai shafe ki ba" Aunty Hassana ta fashe da kuka ta rufe fuskarta da gefen gyalenta tana girgiza kai, sake baki Abba yayi yana kallon Khalil, ya juya ya nufi kofa ya fice daga parlon fuuu, Mami dai ta ma rasa abun cewa, wato khalil baxai ta6a canzawa ba kenan, Abba ya hau kai komo a parlon fuskarsa a murtuke, cike da karfin hali Mami na kallon Aunty Hassana tace "Kiyi hakuri Hassana zan je in...." Wani tsawa ta daka ma Mami tace "Bana bukata, duk ba ke ke sa shi yake raina mu ba, kiri kiri yaron nan ya daina gaishe da ni da Amina a gidan nan, yaron da a haife na haifesa, yanzu kuma rashin kunyar tasa da fitsara har ya kai kan ubansa, kayi laifi amma kafi kowa bakin magana, miliyan dari takwas wasa ne yanzu? An daga maka kafa albarkacin tausasa yaya da muke tayi ka dawo gida amma kace mune makiyanka? Yanzu da nawa ɗan nan zai yarda da abinda khalil yayi min yanzu? Ba tashin hankali xa ayi ba kenan??" Abba yace "Ki bar zancen nan, i know how to handle it, ke Fatima yarinyar da kika kawo gidan nan without my knowledge wacece? Kuma daga ina take??" Mami ta kallesa da mamaki, sai kuma tace "Sauran yaran da ake kawowa gidan nan su karaci zamansu su wuce ka ta6a tambayar daga inda suke ko wa ya kawosu Yallabai? Yaran da har kudin makaranta kai ke biya masu sai wannan da ko biyar dinka babu a makarantar da aka biya mata?" Hassana ta mike a fusace tace "Kar ki kuskura kice zaki masa magana yanda kika ga dama a gabana Fatima, ke kiyi ɗan ki yayi, to baku isa ba, kuma wallahi baxan dauka ba don kiji in gaya maki" Mami ta daga kai tana kallonta, can ta kalli Abba tace "To er ɗan uwana ne, kuma karatu ya kawota gidan...." Mami na fadin haka ta mike ta fice daga parlon, Aunty Hassana tace "Toh wa yaki zamanta a gidan nan dama? Abinda Allah kadai yasan ladan ciyar da ɗan mutum, ai mu bamu ki tayi ta zama har abada ba ma, kawai damuwar mu kamar yanda na gaya maka Yaya, kwanaki can wani videon yarinya tsirara na ta yawo a kafofin sada zumunta, to ita ce yarinyar" Abba na kallonta da kyau yace "Ke kin tabbata Hassana?" Aunty Hassana tace "Zan maka karya ne yaya? Wallahi ita ce yara duk sun shaida mu ma kuma mun shaida, babu amfanin nuna video din ne yanzu da sai in nuna maka, sannan tun da yarinyar ta zo gidan nan bata gaida mu, sai dai mu wuce ta wuce saboda ta isa" Abba ya dinga zaga parlon yana nazari bai dai ce komai ba, ran Aunty Hassana yayi fari tass don duk hanyar da zata kuntata ma Mami nemansa take ido rufe.....
Mumy ce ta shigo bangaren Umma ta sameta a parlor tare da Kamila, Mumy tace "Dama kina gidan nan Kamila?" Da sauri Umma ta amshe tace "Daxu ta zo, yanzu ma mijin take jira wai" Mumy tace "Ohk, dama tambayarki zanyi kinji daga Nihal kuwa? Tun jiya bana samunta a waya wallahi" Da damuwa Umma tace "Yanzu ma abinda muke jajantawa kenan, har na gaji da kiran wayartata wallahi, na kira farooq yace min yana Abuja amma gobe zai shiga kaduna sai ya karasa Zaria yaga ko lafiya" Mumy tace "Toh duk yanda aka yi sace mata wayar aka yi" Kamila tace "Nima abinda nace kenan, amma Umma duk ta daga hankalinta, babu tantama an dauke wayar ne" Umma tace "Sai ta rasa wayar da xata kira mu da shi a kawayenta tace an dauke mata waya?" Mumy tace "In sha Allahu lafiya lau take" Umma tace "Toh Allah ya sa" Juyawa Mumy tayi ta fita daga parlon, Kamila tace "Ke abu indai ya shafi Nihal duk ki daga hankalinki ki daga na wasu, ni gashi na kawo maki damuwata ko bin ta kaina baki yi ba sai korata kike in bar gidan nan tun jiya" ko kulata Umma bata yi ba ta mike ta fita daga parlon.


Littafin Nihaad na kudi ne, ki biya ki karanta cikin salama, idan ba haka ba akwai dari biyar tsakaninmu.


Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: 💖💖 NIHAAD 💖💖


46




Farooq was perplexed bayan yayi parking dai dai inda Khalil yace ya tsaya ya jirasa, yana kallon sojojin dake opposite dinsa amma nesa da shi, ya dinga bin area din da kallo with mouth agape, ina ne nan din khalil yace ya zo? And why will he tell him to come and wait here? He could see 3 of the soldiers advancing toward his car with haste, and bai san me xai masu ya kawo shi nan ba idan sun karaso, can nesa ya hango khalil na tahowa ta inda sojojin suka yi creating barriers, sojoji ukun suka karaso har inda yake suna masa alamar ya sakko fuskarsu a murtuke babu rahama, Farooq ya kashe motarsa ya sauko with calmness ya gaishesu, Maimakon su amsa strictly suke tambayarsa where is he from kuma tsayuwar me yayi a nan? Farooq yayi karfin halin nuna masu khalil dake tahowa yace "I was waiting for him...." Da sauri khalil ya fito daga wajen barrier din ganin sojojin da suka tsare farooq, ya daga ma sauran soldiers din dake wajen a zaune hannu ya nufi gun farooq, sojojin dake gaban farooq na ganinsa suka juya suka koma position dinsu, Khalil na Murmushi yace "Yi hakuri na bar ka a tsaye, barka da isowa yallabai" farooq dai sai kallonsa yake still surprise, can dai yace "Ina ne nan din Khalil?" Khalil ya zaga daya side din motar not wanting to answer him yace "Mu karasa can ciki Yallabai, ba a tsayawa a nan...." Farooq ya shiga motarsa har sannan mamaki ne shimfide a fuskarsa Khalil yace "Mu je can gaba" da wani expression Farooq ya masa wani kallo yace "Mu je ina??" Cause ta wajen barriers din da sojojin ke tsaye yaga Khalil na nuna masa wai su bi, Ba tare da Khalil ya kallesa ba yace "Gaba xa mu yi, kuma hanya ce ai" Farooq yace "Ta gaban sojojin can xa mu bi kake nufi?" Khalil yace "Ba komai, nace maka hanyar kowa da kowa ne" Bayan few seconds Farooq dai ya tada motar yana driving din a hankali yaga sojojin sun daga masa karfen da ya rufe layin, ya wuce ciki still driving careful, Bayan sun shiga Farooq na kallon Khalil yace "Wai ina ne nan din Khalil?" Khalil na nuna masa gaba yace "Can gaba xa mu karasa, ba nisa sosai" Farooq dai ya ci gaba da driving din amma carefully cause the security in there isn't funny, very tight security, gasu fuskarsu babu rahama duk a murtuke, Farooq dai na driving yana kare ma anguwan kallo, bayan tafiyar few minutes, Khalil ya nuna masa gate yace "Baƙin gate din can xaka yi horn" Farooq ya juya yana kallon Khalil, Khalil bai yarda ya kallesa ba ya danna horn din da kansa, Sojojin wajen suka taso zuwa gun motar, tuni khalil ya sauke glass ganinsa suka koma, aka bude gate din, sai da Khalil yace "Mu shiga yallabai" sannan Farooq ya ja motar zuwa cikin compound din, Khalil ya nuna masa inda xai yi parking, kai kana ganin farooq kasan abun ya gama daure masa kai, he is more than confuse, Khalil ya sauka daga motar ya zaga yana kallon farooq, farooq ya sauko daga motar shi ma yana kallonsa amma ya kasa cewa komai, Khalil na dan murmushi yace "Ya kwana da yawa Yallabai? It's a pleasure meeting with you after a while" A hankali Farooq yace "Now tell me, why did u chose to hide ur Identity? Why?" Khalil ya sauke idonsa kasa yace "I was left with no choice Farooq, but the beautiful part of all is that i meant no harm to your family, something's are better left unsaid, and mind you this is my father's house not my house, kuma shi namiji ai baya tutiya da gidan ubansa, all what u are seeing in here is for my dad, and i am not him in anyway" Khalil bai jira abinda Farooq xai ce ba yayi gripping hannunsa yace "Mu shiga ciki" Daga haka suka bar wajen, Farooq couldn't stop looking at Khalil, babban tambayar da yaji yake bukatar amsarta shine me khalil yaje yi gidansu? meye manufarsa na zuwa gidansu yace zai yi driving? Driving fa?? Shi dai From day one yasan there is something about Khalil that is hidden, he knows that, and here is what was hidden today, Suna shiga Main parlor Khalil ya sake hannunsa, Farhana dake parlon ta bi su da kallo, Daga khalil har Farooq da yake tafiya with calmness babu wanda ya kalli inda take har suka haura sama, Farooq couldn't hide how amazed he was with all what he is seeing, and he felt so happy for his Lil sis, har suka iso parlon Mami, Khalil na kallonsa yace "This is my mum's part, za ku gaisa da ita" Farooq na murmushi yace "Sure" Suka shiga first parlor sannan second, Nadiya dake zaune ita kadai tana danna waya ta daga kai jin an bude kofa, Farooq yayi sallama ya shiga bayan Khalil yayi taking lead, Nadiyah ta kalli Khalil sannan farooq, Khalil yayi mata murmushi yace "Meet my frnd Farooq" Da fara'a Nadeeyah ta gaida Farooq ya amsa with calm smile written all over his face sannan ya zauna saman kujera, Tuni Khalil ya shiga dakin Maminsa, bayan few minutes sai ga shi ya fito tare da Mami, da fara'a Mami suka gaisa da Farooq dake ta kallonta saboda resemblance dinta da khalil is very obvious, khalil ya zauna gefen Farooq yana kallon Mami yace "Yayan Nihad kenan Mami, he is Farooq by name...." Mami tace "Maa sha Allah, you are welcome son" Khalil na Murmushi yana patting shoulder din Farooq gratefully yace "They are the most nicest family i have met so far in life, they really made my stay with dem a memorable one, they made me felt at home all through my stay with them, and i owe them for that..." Farooq dai kawai yayi murmushi, Mami tace "Allah sarki Allah Ubangiji ya karfafa zumunci, Allah ya saka da alkhairi.... This is so beautiful to hear" Farooq wish he could express how happy he is for his Lil sis at this moment, a ko da yaushe addu'arsa ga Nihad shine Allah ya dauwamar da ita cikin farin ciki bayan all What she's gone through, yana mata addu'ar Allah yasa aurenta da Khalil ya zama sillar farin cikinta na har abada, he sees her as a strong young girl, don yau ace Nihal ce abubuwan nan suka faru da yasan she is definitely going to break, yasan she can never endure it for long, duk abubuwan da Khalil ke fada akan karamcin da suka masa a kano Farooq hankalinsa ba nan yake ba, ganin komai yake kamar a mafarki, tuni Mami ta kira Bilkisu ta kawo masa drinks and small chops, Mimi ta shigo parlon rike da laptop


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login