Showing 159001 words to 162000 words out of 292821 words

Chapter 54 - NIHAAD COMPLETE DOCUMENT Complete by Khalisat Haidar .txt

25 Nov 2024

39495

Nadeeyah tace "But who is she? Ranan na ganta gidan Aunty Maryam" Noor tace "How will i even know who she is, ni ban ma damu insan wacece ba tunda ba gabana take ba, i hate nonsense, na dai ji Aunty Maryam na ce ma Mami ai gidan iyayenta Yaya Khalil ya zauna when he was in kano, they were kind to him, they did that, they did this, bla bla bla, ita kuma tana so ta fara karatu ba a son ta zauna hostel, shine wai zata zauna nan gidanmu, cause at first Mami bata amince da zamanta a nan ba, but Aunty Maryam insisted, ta dinga kawo silly backups har sai da tayi forcing Mami yarinyar ta zauna gidan nan" Kallonta kawai Nadeeyah take babu ko kiftawa, can tayi karfin halin cewa "But who brought her here?" Noor ta karyar da kai tace "We saw her a day after yayanmu came back, which means tare kenan suka zo gidan, yes tare ma suka zo" Nadeeyah ta hadiye abu da kyar tace "Tare??" Noor tace "Yeah, and you know what?" Nadeeyah ta girgiza kai, Noor tace "You remember the video of a lady with undies that went viral last month?" Nadeeyah tayi shiru, Noor tace "Wani video that's all over social media na wata yarinya babu kaya jikinta?" Nadeeyah tace "Yeah, i heard about the video amma i didn't bother watching, so ban ta6a gani ba" Noor tace "Toh yarinyar ce" Nadeeyah ta zaro ido with surprise tace "Wace yarinya?" Noor tace "Yar rainin wayon da ta fita yanzu, ita ce a video din sure" Buda baki Nadeeyah tayi tace "Wai da gaske?" Noor tace "I mean it, bani da video din da na nuna maki, su Sajidah da Hanan ne ke da shi a waya" Nadeeyah was over shock, tayi karfin halin cewa "Kuma gidansu Kjay ya zauna a kano?" Noor tace "Yes, she was once a student of Maryam Abatcha" Nadeeyah ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Allah ya kiyaye" Noor tace "Waow its been long i hala this way, har kaina ya fara ciwo wallahi, shi sa bana son magana da yawa amma wannan yar kauyen ta sa ni magana, As i was saying...." Nan ta ci gaba da ba Nadeeyah labarin da take bata cikin nutsuwa irin na big babes, but gaba daya Nadeeyah was absentminded, Nihad ta tsaya mata a rai sosai, abinda ta mata ranan da suka hadu gidan Aunty Maryam ya fado mata, ita kuma a ranan bata dauka as komai ba, sai yanzu brain dinta ya tunatar da ita cewa warce suka hadu a mall a can kano ce fa da Kjay, mamaki da fargaba ya cikata, but why did he have to bring her all the way from kano to his parent house, sannan even for once bai ta6a ce mata tare suka dawo ba gashi yau satinsu uku, Noor dake ta magana ta lura gaba daya hankalin Nadeeyah baya wajen ta kai hannunta fuskarta tana waving, da sauri Nadeeyah tayi blinking idonta, Noor tace "What are you thinking of?" Nadeeyah bata ce komai ba amma kana ganinta kasan there is something bothering her, she looks so disturbed, Noor ta kamo hannunta tace "Tell me plss, me ya faru" Lkci daya Nadeeyah taji hawaye ya kawo idonta ɗon saurin kuka ke gareta, tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba tace "He neva told me he came all the way from kano with her, even for once bai gaya min ba" Noor ta zaro ido tace "Ohh that? Meye abun damuwa a nan bayan dai kinsan aurenki zai yi? In 3 days time fa xa a kai kudin aurenku da shi, and baxa a sa ya wuce sati biyar ba, so why bother ur self about one filthy lady that's all over social media half naked? ke sai kace baki san halin KJay ba? Ba abinda ya hada sa da yarinyar banda gidansu da ya zauna don ni tunda ta dawo gidan nan ma ko magana bana ganin yana hadasa da ita, you know he have class" Nadeeyah ta sauke ajiyar zuciya bata dai ce komai ba tana share idonta, Noor tace "C'mon chill plss, wannan bata kai ta sa ki shiga damuwa ba har ki zubda hawayenki a banza, me xai yi da ita? Da akwai wani abu tsakaninsu ma ai baxai fara kawota gidan nan ba, kuma saboda mugun abinda tayi shi yasa ma ba a son ta zauna hostel may be parent dinta suka yi requesting ta zauna a nan, shi sa ma kika ganta a nan" Nadeeyah ta gyada mata kai kawai, Noor ta ci gaba yi mata hiran da take mata a nutse..... Har karfe biyar khalil na zaune inda yake a cikin compound din yana danna waya, so yake ya maida Nadeeyah gida kafin ya je inda yake son zuwa, wayarsa dake hannunsa ya fara ring, ya dinga kallon number wanda ke kiransa, ya dai yi picking daga karshe yakai kunne, bayan sun gaisa Farooq yace "Dama wani aiki ne ya shigo da ni Abuja yau, so gobe da safe in sha Allah xan koma kd, shine nake son inji wani wajen ku ke a Abujan?" Khalil ya sauke idonsa yace "Ohk, maa sha Allah, goben za ka zo kenan?" Farooq yace "No, na gama abinda nake yi yanzu, goben da sassafe nake son tafiya" at first khalil ya rasa abinda xai ce masa, Farooq yace "Hello" Khalil yace "Eh ina jin ka, xan tura maka address din yanzu" Farooq yace "Toh ina jira" Daga haka ya katse wayar, Daga nisa ya dinga kallon Nadeeyah har ta iso inda yake, ta dauke kai tace "Xan tafi gida" Ganin mood din ta yace "What happened Nady? Are you okay?" Ta ki ce masa komai, ya mike yana kallonta, lokaci daya hawaye ya cika idonta, da damuwa yace "Talk to me plss, me ya faru?" Cikin rawan murya tace "But you neva told me ba kai kadai ka dawo Abuja ba" Yace "Shit... Toh menene tsakanina da warce na dawo da? There is nothing Nady kawai karatu ta zo yi a garin nan, and she have no where to stay shine take zaune gidan nan, bayan nan babu wani abu kuma trust me" Ta goge Idonta tace "Naji, I want to go home" yace "Noo, not in this manner pls, but ta maki wani abu ne?" Nadeeyah tace "Kawai shigowa tayi ta hararemu ta fita babu sallama balle gaisuwa" Khalil yayi wani sigh yace "But you guys shouldn't have taken it personal, she is a sociopath...." Nadeeyah ta tabe baki dai bata ce komai ba, khalil ya kalli wayarsa dake ring da sauri, ganin Farooq ne ya daga yace "Ina tura maka ne" Farooq yace "Ohk" Daga haka ya katse wayar, Khalil yace "Look Ki koma ciki yanzu, i will be having a visitor immediately, idan ya tafi sai muje ki sha ice cream sannan in maida ki gida" Murmushi kawai tayi ta juya ta fara tafiya, yea dama murmushin kawai yake son yaga ta yi which means komai ya wuce kenan, ya sauke ajiyar zuciya ya zauna ya shiga sending ma Farooq address.....








*Nihad* is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence of payment via 07087865788
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: 💖💖 NIHAAD 💖💖


47




Mikewa Khalil yayi ya tafi har bakin kofa ya tsaya ya rungume hannu yana kallon yanda take kuka, calmly yace "In da gaske kina son bin sa me yasa tun zuwansa baki ce masa xaki bi sa ba kika zo nan kina min kukan munafurci, tunda kinsan tafiya zai yi ba nan zai kwana ba" Nihad ta hadiye kukan da take ta daga kai tana kallonsa fuska daure, can ta mike tsaye tace "Ina ruwanka da ni? Kaga dai ba ruwana da kai a gidan nan, don yayana yace in daina kulaka duk abinda xaka min, kuma ni dai naji maganarsa, don haka kai ma ka fita harkata because bana son inyi disobeying yayana, idan baxa ka iya cewa inyi hakuri ba dole sai ka min maganan" ta karasa maganar kamar xata fashe da sabon kuka, kallon bakinta kawai yake, can yace "Ohk yace ki daina kulani kenan?" Tace "Ehh, kuma ko kana daga min shoulder dinka baxan san kana yi ba tunda ba ruwana da kai, I will pretend I don't know" Tana kai wa nan ta nufosa fuska daure tace "Ka matsa min ni in fita" ita haushinta maimakon yace tayi hakuri shine yake neman tsokanarta kuma, Yace "Aa bari dai a baki kudin mota ki bi sa kawai, ai yana nan Abuja bai yi nisa ba" Wani kallo ta dinga masa, ya sa hannu cikin aljihun 3 quarter din jikinsa ya ciro 100 dollar ya mika mata yana kallonta, ta dinga kallon kudin sai kuma ta kwace ta cukuikuye ta jefar kasa, tana kallonsa da kyau tace "Kudin da ba naka ba" Kallonta ya tsaya yi baki bude, can yace "Kinsan hukunci warce ke ma namiji rashin kunya, namijin ma wanda aka aura mata daga gidansu?" Ta wani kallesa tace "Ohh dama kai mijina ne? Ai ban san ina da miji ba, kuma ai shi namiji baya neman tsokanar mace" Jin yayi shiru bai ce mata komai ba ta dauke kai ta turo baki, a hankali ya kai hannu ya kashe switch din dakin ta juya da sauri ganin duhu ya gauraye ko ina sai ɗan hasken screen din Iphone dinsa da ya ajiye saman gado, taji kuma yana sa makulli a kofa, komawa baya tayi a tsorace tana zaro ido tace "Meye haka kake yi?" Ba abinda ta ji yace mata, Ganin he is advancing toward her ta fara komawa baya da sauri cikin rikicewa tana cewa "Wayyo don girman Allah kayi hakuri, duk abinda na fada ba da kai nake ba don Allah kayi hakuri, dama yayana yace in daina maka rashin kunya kuma na daina tun...." Wani kara tayi a tsorace jin saura kadan ta fada saman gado don bata san har ta iso wajen gadon ba, zata tashi da sauri ya mayar da ita ta fada kan gadon, zaro ido tayi a mugun tsorace ganin he just lied directly on her, cikin rawan murya ko ina na jikinta na ɓari tace "Don girman Allah kayi hakuri, wallahi baxan sake maka rashin kunya ba har abada, kaji na rantse..." Gaba daya ta gigice tana kokarin turasa amma ta kasa, cause his weight is out of the world, nan kuma ba duk weight din nasa ya sakar mata ba, ta fashe masa da kuka tana sauke numfashi da kyar ga kamshinsa da ya cika ko wani breathing dinta, yayi kasa da murya still adjusting on her yace "Baki san kina da miji ba ko?" Cikin kuka tace "Wallahi na sani, kawai wasa nake maka, don Allah ka yafe min kayi hakuri baxan kara ba.... Wallahi numfashina zai iya daukewa" a hankali yace "Ya dauke mana" Bata san sanda tayi wrapping hannunta a bayansa tana kuka sosai tace "My chest is paining me plss" ai ko ya lumshe ido ya kara sakar mata weight hakan da tayi masa, as if he is going to sleep, sae kuma yayi placing forehead dinsa kan nata, joining his nose directly with hers, cike da karfin hali tace "I am sorry plsss" murda kofar dakin aka yi, yayi brushing lips dinsu ya mike da sauri ya sauka saman gadon, Nihad ta ja wani numfashin wahala ta mike da sauri, jikinta na rawa ta silalo kasa hawaye na sauka idonta, ya tafi gun switch din dakin ya kunna, ya fara dube duben Jallabiyarsa a dakin ya dauka ya daura kan kayan jikinsa sannan ya tafi ya bude kofar dakin, Mimi dai sai bin su take da ido ya amshi cup din hannunta da sauri yace "Thank you dear... Zata bi yayanta inda ya tafi shine na kulle kofar har ki zo, may be u can tell her not to" Nihad dai ta kasa dago kanta daga inda take durkushe a kasa har sannan bata ji kirjinta ya dawo dai dai ba, ga wani bugawa da zuciyarta yake alamar ba karamin tsorata tayi ba, Mimi ta karasa ciki ta durkusa gabanta soothingly tace "Kiyi hakuri, tunda yasan gidan definitely zai dinga zuwa wajenki ai, so ba sai kince zaki bi sa ba" Nihad taki yarda ta kalleta kamar munafuka, Khalil dake tsaye bakin kofa yace "Kawai ki tafi ki kyaleta idan ta gama kukan sai ta fita...." Zumbur Nihad ta mike har sai da ta ba Mimi tsoro, Mimi ta mike tana kallonta ganin she looks so afraid tace "Are you alright Neehad?" Nihad tayi karfin halin gyada mata kai, Mimi tace "Toh mu tafi" Tana makale bayan Mimi suka nufi kofa, taki yarda ta kalli inda yake tsaye, ya bi ta da ido har suka fita sannan yayi wani murmushi ya kulle kofarsa... Duk zaman da Nihad tayi part din Mami bayan sun koma da Mimi she is so silent duk da dama can ba wai tana magana bane amma na yanxu yayi worst, gaba daya ta kasa cire abinda yayi mata a zuciyarta, abincin ma kasa ci tayi wai ta koshi, Mimi duk tunaninta ai tafiyar farooq ne ya sa ta zama haka, shi yasa ma bata yi bothering dinta ba. Wajen karfe tara Khalil ya shigo parlon wearing on his pajamas, sai da gaban Nihad ya fadi ganinsa da tayi taki yarda kuma su hada ido, yana kallon Mimi yace "Mami na ciki?" Mimi tace "Aa tana downstairs tun dazu" Yace "Ohk, ni bani da abinci yau a gidan kenan?" Mimi ta ɗan zaro ido tace "Yayanmu wanda muka kai maka daki fa?" Yace "I called Noor ta fita da shi ban ci ba, ai wannan yayi yawa sosai" Mimi tace "Ohk sorry pls, should i get you another one now?" Yace "Yeahh, but ba nan zaki kawo min ba, and ki ɗan kara hada min irin wannan coffeen da kika yi min" Sosai gaban Nihad ya fadi da ta lura Mimi fita zata yi daga parlon, sai zazzare ido take uwa warce tayi ma sarki karya, Mimi ta dau after dress dinta ta daura kan sleeping dress din jikinta tace "I am coming Nihad" Nihad was shocked and confused on what to do, haba ai bata san sanda ta mike da sauri xata ce mata tana son bin ta amma tuni Mimi har ya fita, kamar munafuka ta fara tafiya zuwa kofa, Khalil dake kallonta yace "Kee" Ta tsaya a tsorace ta kallesa kamar zata yi kuka tace "Ni rakata zan yi" Bata jira me xai ce ba ta karasa kofar da gudu ta bude ta shige next parlor amma taga Mimi har ta fice daga nan ma ta kulle kofar, bin bayanta Khalil yayi tana ganin haka ta kwasa a guje ko kusa da kofar bata kai ba ta take dogon hijab din dake jikinta na Mimi, sai ga tim a kasa ta zaro ido tana yarfe hannu, dai dai nan aka bude kofar parlon, Mami ta koma baya tana kallonta tace "Subhanallah, garin yaya?" Nihad ta mike tsaye da sauri xuciyarta na bugawa tace "Zan tafi in kwanta ne, shine na fadu" tuni khalil ya koma daya parlon, Mami na kallonta tace "Toh ki dinga yi a hankali, Hope you are not injured?" Ta gyada mata kai da sauri, Mami tace "Toh sai da safe" Nihad tayi saurin fita daga parlon, Mami ta bi ta da kallo, sai kuma ta karasa next parlor din, zaune ta tadda khalil yana waya, the way he is talking on the phone xaka yi zata ya kai minti talatin yana wayar, Mami tayi wucewarta cikin bedroom dinta. Sai da Nihad ta shiga dakin da take taji knees dinta na mata zafi, ta zauna gefen gado tana dubawa taga ba ciwo amma zafi yake mata, da kyar ta samu ta shiga bandaki tayi wanka ta fito, ta saka kayan barci bayan ta shafa turare ta kwanta saman gado tayi lamo, incident din daxu ne ya dinga dawo mata, but what's the meaning of that?? Lokaci daya ta kawar da tunanin ta jawo wayarta a hankali tana dubawa, taga miss calls din Ayman har biyu, zata ajiye wayar sai ga wani kiran nasa, dagawa tayi ta rufe har kanta da duvet, ko minti goma basu yi da fara wayan ba taji an kwankwasa kofar dakin, da sauri ta mike zaune ta katse wayar tana kallon kofar, aka sake Knocking sauka tayi a hankali ta tafi gun kofar tace "Waye?" Mimi tace "It's me" Daga haka Mimi ta bude tana kallonta tace "Mami said i should ask if u are okay?" Nihad tace "Sure, thank you" Mimi tace "Ohk good night" Nihad ta dan mata murmushi ta gyada kai kawai, daga haka Mimi ta juya ta bar wajen Nihad ta kulle kofarta ta koma ta kwanta. Washegari Khalil na tare da Mami a parlonta Aunty Hassana ta shigo da sallama, Khalil na jin muryarta yayi saurin kara waya a kunne yana maganan da babu shi, Mami dai bata ce komai ba, har Aunty Hassana ta karaso, shi kuma ya mike ya fice daga parlon still making fake call, Mami tace "Mun tashi lafiya Hajiya Hassana" Aunty Hassana da ta bi sa da kallon gefen ido tayi saurin cewa "Lafiya lau, ya yaran?" Mami tace "Alhamdulillah, ya su Sajidah" Aunty Hassana tace "Toh ni naji kin min shiru, baki ce ga abinda ake ciki ba, don last week naji Abbansu yace xa a kai kudin auren yaron nan, to mu ba wani shirye shiryen da xa muyi a nan ne?" Mami tace "Ai gobe ne idan Allah ya kai mu" Aunty Hassana tayi shiru tana kallonta da mamaki, can tace "Gobe goben nan amma ba labari?" Mami tace "Ni ai na zata Amina ta gaya maki don muna tare da ita a parlon Yallabai ya saka lokacin, and that was last week" Aunty Hassana ta hade rai tace "Saboda Amina ce tafi kusanci da ni ko me?" Mami tace "Ba dai ta yanda xa ayi kice baki ji daga bakinta ba Hassana, ko ita bata gaya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login