Showing 183001 words to 186000 words out of 292821 words
Chapter 62 - NIHAAD COMPLETE DOCUMENT Complete by Khalisat Haidar .txt
iya kokarinta na ganin Abba bai dauke Nihad daga wajenta ya damka ma Umma ba har hakan sai da yayi sanadin igiyar aurenta daya a gidan, babu irin bakaken maganganun da Inna bata gaggaya mata ba a wancan lokacin wai bata da kara bata da kunya akan yar ta ta fari, ina ruwanta da er ta na fari da har zata zakalkake a kanta tana nuna tafi kowa iko da ita sae kace ba bafillatana ba, banda zamani ya lalace, su zamaninsu babu macen da ta isa tayi haka, har inna ke kara tunatar mata cewa Umma bata rike ɗan ta na fari da na biyu ba bata ma san ta yanda suka girma ba ta kauda kai a kansu kamar ba ita ta haifesu ba, Ya Farooq da ya Usman basu taso wajenta ba, tun daga yaye inna ta daukesu suka koma wajenta a Bauchi kuma Umma bata taɓa cewa don me ba, yawancin rayuwarsu duk a wajen Inna suka yi a lokacin ma kakansu na da rai, sae ya kasance Kamila ce kawai gaban Umma and she never complained for once, har dai ta zo ta haifi Nihal, washegari kuma Mumy ta haifi Nihad, wanda sai da Mumy tayi shekara goma a gidan kafin ta haihu, duk tana gidan aka haifi Usman da Kamila amma ita Allah bai bata haihuwa ba, dalilin da yasa da ta haifi Nihad Abba ya dau son duniya ya daura mata gashi fara ce kal kamar zaka latsa ta jini ya fito, ga masifar kyau kamar er larabawa, dama shi farin yaro da shegan shiga rai yake, ita kuma Nihal baƙa ce amma suna kama sosai da Nihad, sai ya dau Nihad sau goma bai dau Nihal sau daya ba don Nihal tana da kiwiya sosai shi sa ma bai bin ta kanta, ba ta yarda da kowa sai Umma, hakan yasa yafi shakuwa da Nihad da ko muryarsa taji ta dingi kuka kenan sai ta gansa ya dauketa, shakuwa me tsanani ya shiga tsakaninsu ya dau soyayya mara iyaka ya daura mata, har cikin ransa yake jin Nihad, wanda Mumy na lura da Umma kamar hakan baya mata dadi don bata iya boye hakan a fuska, ga kuma er ta Nihal shegen kiwiya da kuka, Mumy kan ce ma Abba ya daina bambanta su kar a samu matsala, nuna banbancin bashi da amfani don duk daya suke a wajensa, amma sai yace mata ai Nihal kiwiya gareta bata yarda da kowa, haka rayuwa ya ci gaba har aka yayesu, tun Nihad na shekara uku Umma ta fara nuna tafi damuwa da ita akan Nihal kamar yanda taga Abba ke yi, ta sha attempting mayar da Nihad dakinta gaba daya amma Mumy taki bada fuskar hakan, don babu Alkunya take shiga ta dauke er ta ko da kuwa bacci take a dakin Umma komin dare kuwa, ko hularta bata yarda ta bari a dakin Umma, Umma bata hakura ba har sai da ta san yanda ta hada makircin da ta hada tare da goyon bayan Inna Nihad ta dawo wajenta, Wanda har sai da Abba ya saki Mumy akan issue din wai tana son raba masa kan gida, ga inna ta saka ta gaba da gore gore wai ai ba da ita ta zo gidan ba sannan ina ruwanta da er ta ta fari idan ba rashin kunya ba, karfi da yaji dai aka raba Mumy da Nihad, babu yanda Mumy ta iya tana ji tana gani ta cire hannunta akan wasu lamarin Nihad ta bar ma Umma gaba daya, and that was the genesis of the whole problem.... Mumy ta kasa ci gaba da zama dakin ta fita kawai ta koma parlor tana jin xuciyarta na mata zafi, Umma ta cuceta ta cuceta, ita kuwa bata ma er ta irin rikon da tayi ma Nihad ba, Nihal da kanta ta koma bangaren Mumy a lokacin ma tayi shekara goma, tana ji tana gani sae Umma ta hana Nihad shigowa wajenta, babu kusanci kwata kwata tsakaninta da Nihad, to amma ya zata yi, tunda ga abinda mijinta da uwar mijinta suka ce, kawai sae ta rungume Nihal tana ganinta kamar yar cikinta. Nihad ta ci kukanta ta koshi ta mike ta koma saman gadon Mumy ta kwanta ta rufe idonta a hankali tana jin kanta na ciwo, a haka har bacci ya dauke ta. Wajen karfe goma da wani abu Nihad ta bude ido a hankali ta dalilin tashinta da aka yi, ta mike zaune tana kallon Nihal dake zaune gefenta, Nihal tace "Ana kiranki a parlor" Nihad na murza idonta tace "Waye?" Nihal ta mike tace "Ki fito" Daga haka ta mike ta fita daga dakin, Nihad ta mike da kyar ta nufi kofa ta fita Parlon Mumy, zaune ta gansa duk ya wani birkice yana kallon kofar dakin eagerly, suna hada ido ta sunkuyar da kai a hankali, Nihal ta juya ta fita ta rufe kofar parlon, sai a sannan ya mike da sauri, Nihad tayi saurin juyawa zata koma dakin yayi hanzarin bin ta har ciki ya fizgota, zaro ido tayi tace "Don Allah ka bari kar wani ya shigo" kin yarda su hada ido tayi taki dago kanta, da taga he is trying to raise her head up kawai ta kwanta saman kirjinsa tayi lamo, she could feel how fast his heart is beating, ta lumshe idonta a hankali, ya rungumeta sosai, Underneath his breathe taji yayi maganan da ita kanta bata ji ba, jin hawayenta a jikinsa ya dago kanta da sauri yana kallonta, kasa barin su hada ido tayi, cikin rawan murya tace "I am... Am sorry, i..." sai kuma ta kasa ci gaba ta fashe da kuka, Lokaci daya ya saketa jin an bude kofar parlor, ta goge idonta da sauri ta fito parlon sai ta ga Nihal ce ta shigo rike da ruwa da lemo, Khalil ya fito parlon shi ma ya zauna, Nihal dai bata yarda ta hada ido da su ba. Tashin hankalin da Mami ta shiga ba a cewa komai da ta shiga dakin Khalil da sassafe taga baya ciki, kuma bata ga alamar ma a dakin ya kwana ba, tun sannan take kiran duk layinsa taji su a kashe, ta ma rasa takamaiman abinda zata yi, tun cikin dare take Allah Allah gari ya waye ta samesa tace masa ko za su je can kano ne gidan iyayenta ko Allah ya sa can ta tafi, sai gashi ta shigo babu shi a dakin, ta dawo bangarenta cike da damuwa, tana zaune tare da Mimi a parlon tace "Kuma ko number yayanta baki da shi ko?" Mimi ta girgiza kai a hankali tace "Bani da shi" Bude kofar parlon aka yi, duk suka daga kai, Mami ta dinga kallonsa da mamaki don in ba dai tana kwance ba lafiya ba baya shigowa bangarenta kai tsaye haka, sannan ko minti ashirun bai yi da dawowa gidan ba, kuma ba ita ce ma da girki ba, Mimi ta mike ita ma tana kallonsa tace "Good morning sir" Bai amsa mata ba ta nufi kofa ta fita, Mami na ganin yanayinsa ta san ba lafiya, to me kuma ya faru, ta dai mike cikin dakewa tace "Lafiya kuwa Yallabai? Is everything alright" Yana huci yace "Stop asking me that, Ina Ibrahim? Provide him now" Mami sai da gabanta ya fadi, tayi karfin halin cewa "Is everything alright" tsawa ya daka mata yace "Ina maki tambaya kina amsa min da tambaya?" Ta koma ta zauna bata sake ce masa komai ba, ya sake jefo mata tambayar ina Ibrahim, a fusace tace "Tunda dai ba goya Ibrahim nake ba ta ina xan san inda yake da sassafen nan? Ba dai ka san hanyar dakinsa ba" Yana muzurai yace "Ohh haka kika ce?" Tace "Ya kake son ince? Naga dai ba nan yake kwana ba da ka zo nemansa a nan, za ka wani zo ka isheni ina Ibrahim" Ya fi second ashirin yana kallonta yana gyada kai, kafin ya juya ya fice daga parlon almost ripping the door off, tagumi tayi tana tunanin to me kuma yaron nan yayi? Wannan wani irin fitina ne ita kam, Noor ce ta shigo parlon tana kallon Mami a sanyaye tace "Mami kin san me Yayanmu yayi?" Mami da taji gabanta na faduwa sosai tace "Me yayi Noor?" Noor ta zauna cikin sanyin murya tace "He broke into Abba's room and collected all what Abba seized from him, lalata makullin dakin ma fa yayi" Buda baki Mami tayi ta kasa cewa komai zuciyarta na bugawa, Noor tace "Ina jin cikin dare kowa na bacci yayi haƙan, he scattered everywhere in the room" Mami ta saki salati ta rafka uban tagumi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" sai ga Aunty Hassana ta shigo parlon babu ko sallama cike da rashin mutunci tace "Ke kam fatima kin haifar mana fitina a gidan nan, don Khalil fitina ne wallahi...." Mami ta dakatar da ita tace "Ban haifi fitina ba sai in ke kika haifi fitina wallahi"
*Thanks for being patient with Khaleesat*
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: 💖 NIHAAD 💖
54
Mami bata tsaya ta kara sauraran Aunty Hassana ba ta mike ta shige dakinta ta shirya ta fice ta bar masu gidan daga ita har yayan nata zuwa gidan Hajiya Safeenah. Tana zaune parlon Hajiya Safeenah abun duniya ya isheta, Hajiya Safeenah tace "Na fa ce ki kwantar da hankalinki Hajiya Fatima, yarinyar da har nude video dinta yayi yawo a gari ai kinsan dama can idonta a bude yake kome aka ce ta aikata to zata iya aikatawa, ke dai kawai Allah ya shirya mana zuri'a, kuma babu tantama kila gidan nasu ta koma, ke kuma kina nan duk kin bi kin daga hankali" Mami dake ta kallonta tace "You have a point, sai yanzu da kika yi maganan nan na tuna wacece yarinyar, duk yaron da idonsa yayi budewar da nata yayi koma meye zai iya aikatawa gaskiya kika fada, ni fa wallahi bani da yanda xanyi ne amma ni ba wai son zamanta nake a gidana ba, haka kawai taje ta kara aikata wani abun da ba shikenan ba, gashi baka gane gabanta balle bayanta, nukurcinta yayi yawa, sannan kwana biyun nan ina ta lura da yanda Khalil din ke shige mata, sam bana son haka...." Hajiya Safeenah ta rike haɓa tace "Au, ashe kema dai kin lura, jiya bayan mun dawo gida zancen da Nadeeyah ta kawo min kenan...." Mami tayi shiru da tunani iri iri a ranta, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi abun ya dameni, to yace mana wajen iyayenta ya zauna a kano ya zanyi masa, ga Maryam me goyan bayansa, tukunna ma dai wasu irin iyaye ne xasu hada yar su da gandameme kamar Khalil wai su taho Abuja tare sannan ya bar ta a gidansu wai zata yi karatu? A ina aka taɓa haka kamar dai garin gaɓa gaɓa aka taso? Idan ma haka ne ai kamata yayi uwar ko uban wani ya biyota sai a damka mana ita a hannu ace gata nan don Allah zata yi karatu a sa mata ido, to wai sai aka hadata daga ita sai khalil ya kawo mana ita, ko marasu addini baxa su yi haka ba, ni wallahi na rasa yanda zanyi ne, i have a big question mark on this issue, ga Maryam tayi ɓake ɓake kan lamarin sai goyan bayansa take wai sai an riketa tunda iyayenta suka rike shi, to shi ba namiji bane ko da da kafafuwansa yaje gidan nasu shi kadai, ita kuwa ai sai cikin iyayen wani ya rakota saboda halin rayuwa, komai fa na son tsari a rayuwar nan, amma sam wannan lamarin ba tsari, a hada baligi da baliga wa enda ba muharraman juna ba" Hajiya Safeenah tace "Gaskiya abun dubawa ne wannan, kuma kika ce kwanaki yayanta yaje gidan ko?" Mami tace "Ehh yaje kam, amma ko da iyayen ma baxa su biyota ba ai sai su ba yayan nata ya kawota ba Khalil ba, it's making no sense to me now, tun farko ya kamata inyi masa wannan tuhumar amma hankalina bai je ba, sannan ban taɓa jin an kirata daga can gidan nasu ba ko kuma ita ta kirasu" Hajiya Safeenah tace "Toh dai ki kara kiran layukan Khalil din ko xaki samu, aji in gidan ta koma kin ga hankalin kowa sai ya kwanta, sai kuma a koma next issue that's on ground" Mami ta sake dialing number Khalil, luckily ya fara ring, gyara zama tayi ta sa handsfree tana jiran ya daga, sai da ya kusa katsewa sannan ya dauka, tace "Khalil me ya kai ka dakin Abbanka?" Khalil ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Ajiyata na dauka Mami" Mami ta bude baki tana kallon Hajiya Safeenah, can tace "Ajiyarka? Wato khalil duk yanda zaka daga min hankali shi kake nema a rayuwarka ko? Ba nace ka fita batun abubuwanka da ke hannun Abbanka ba? Me yasa baka jin magana ta ne fisabilillah" Khalil yayi kasa da murya yace "Mami i did nothing wrong, bayan takarduna babu wani abu da na taɓa masa a dakinsa, i seriously need them Mami, tunda ke baxa ki iya dauko min ba shine fa na dauka da kaina Mami...." Mami ta buda baki, ta ma rasa abinda xata ce masa, can tayi karfin hali tace "Duk inda kake ka dawo ina nemanka immediately, sannan kada kayi making mistake din zuwa gida ka zo nan gidan Hajiya Safeenah ka sameni" Ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Toh" Mami zata katse wayar, Hajiya Safeenah tace "To baki tambayesa batun yarinyar ba" Mami da har ta manta tace "Ohh, Sannan ita kuma yarinyar can ina fatan gidansu ta tafi?" Khalil yayi shiru kamar baxai ce mata komai ba, sai kuma yace "Eh" Mami tace "Toh madallah, sai ka gaya ma iyayen nata taki zama Abujan, it's better kawai su nema mata transfer ta koma Kanon da karatu ya fi" Khalil dai bai ce mata komai ba, tace "Baka ji na ne?" A hankali yace "Ina ji" Tace "Then do as i say, kai kuma immediately ka taho gidan Hajiya Safeenah ina jiranka" Yace "Ni bana Abuja yanzu" Buda baki Mami tayi tace "Kana ina?" Yace "Ina kano" Tace "Ohh kanon ka bi ta? Kana nufin kanon ka kama hanya ka tafi ko gaya min baka yi ba? To ka kyauta, maza maza ka nemi next flight ka taho Abuja yanzu" Yace "Ba jirgin da zai tashi yau saboda weather" rai bace Mami tace "To wannan kai ta shafa ka biyo mota kawai ka dawo na gaya maka" Daga haka ta katse wayarta, cike da fada tace "Banda ma lalacewa tunda yarinyar ta zo gidan daga uwar har uban babu wanda ya taɓa kira muka yi magana da su, don su ma ji ya yarinyar take, kawai ga ta nan dai kamar bata da iyaye, kana da ya mace har hankalinka zai kwanta idan bata gabanka, babu wanda fa ke bibiyar lamarinta nake gaya maki, duk ina lura da komai, kinga ai saboda tsabar yanda idonta ya bude ai Kano ta kama hanya tayi wucewarta daren jiya, wanda bai saba ba ai baxai yi haka ba, ko tsoron dare bata ji ba, dama can ta saɓa abunta ne, Allah ya shirya" Hajiya Safeenah ta sauke ajiyar zuciya, Mami tace "Tun farko da ya samu matsala da uban Yemen nace ya tafi ya ki, na dawo nace ko zai je Uk nan ma yaki, all that while ban san yana kano ba na dai san yana Nigeria, to gidan wasu irin mutane ne ya zauna wa enda basu da kula haka? Ka sakar ma duniya yar ka mace a wannan zamanin, sannan ga dai abinda yarinyar nan tayi ko wata uku ba ayi ba amma har ku sakankance baku bibiyar lamarinta, a'a ban taɓa ganin haka ba tun da nake" Hajiya Safeenah tace "Yanzu dai Hajiya Fatima kiyi hakuri, a bi komai a sannu ki kirasa ya bar zuwan nasa gobe tunda yace ba jirgi, biyo mota daga kano zuwa Abuja ai aiki ne babba yanzu, kawai ki masa hakuri ya bari har gobe, bari in kirasa" Daga haka Hajiya Safeenah ta kira Khalil, nan ta sanar masa kawai ya bari gobe sai ya biyo jirgin safe, bayan ta katse wayar Mami tace "Dama yana dawowa duk zan amshe takardun in mayar ma uban baxan iya fitina ba, idan jiƙawa zai yi ya shanye sai ya jika ya shanye, babu abinda zai raga Khalil da shi" Hajiya Safeenah tace "Aa kar kiyi haka, ki bar wannan issue din tsakaninsa da ubansa kawai kar kiyi involving kanki, gaskiya kar kiyi haka, kamar yanda ya fada ke baki amsar masa ba kuma ya amsa sai kice xaki mayar?" Mami tace "Wallahi mayar masa shine kadai mafi alkhairi gare mu gaba daya, sai kace baki san General ba, ni duk wani abun tashin hankali bana so wallahi, har fargaban zuwa asibiti nake yanzu yanda nake ji a jikina sai ya iya yiwuwa jini na ya hau" Hajiya Safeenah tace "Allah ma baxai sa hakan ba, kawai kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki Hajiya, komai zae zo da sauki" Mami ta taɓa baki tace "Ya batun programs na bikin, kun gama shawaran da Hajiya Hauwa?"
Bayan Azahar ganin Khalil bai shigo ba Mumy na kallon Nihad tace "Ki je kiyi masa magana ya shigo ya ci abinci" Nihad da tunda tayi sallah take zaune saman darduma a bedroom din Mumy ta mike ta dauke darduman ta linke sannan ta fita, Hijab ne har kasa jikinta don ta shiga bedroom dinta ta kwaso sauran kayanta ta kawo bangaren Mumy ta ajiye, har zuwa sannan kuma Umma bata dawo gidan ba, babu kowa main parlor din ta fito compound ta gansa zaune tare da Aminu, ɗan zaman da Khalil yayi a wajen babu abinda Aminu bai sanar masa ba da ya faru a gidan bayan tafiyarsu sai wanda ya manta, dawowar Kamila gida, matsalar da Usman ya samu wajen aikinsa, rashin walwalan Abba a ko da yaushe tun