Showing 24001 words to 27000 words out of 53497 words

Chapter 9 - SO BAI SAN JINI BA HAUSA NOVELS BY UMMU NASMAH.txt

29 Oct 2025

462

3:45 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*

Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya.

_____________________________________

*_KU FITO MASOYA NA DOMIN NUNA MIN KALAR SOYAYYAR DA KUKE MIN TA HANYAR SAYAN NOVEL ƊIN MU, KUNDAI SAN KALAR RUBUTU NA KUN KUMA YANAYIN LABARI NA DAN HAKA KU GARZAYO DOMIN SIYAN WANNAN NOVELS ƊIN_*



*_INA KUKE MASOYAN KAINUWA WRITER MAZA KU GARZAYO KU KWASHI GARABASA DOMIN KUWA TAFE TAKE DA SABBIN LITTATTAFAN TA WANDA ZAKU AMFANA DASU KUMA KU NISHAƊANTU DOMIN KUWA MUNYI LALUBE MUN ZAƘULO MUKU FASAHAN MARUBUTAN ZAMANI WANƊA SUKA ƘWARE WAJEN KAWO MUKU TSAFTACACCEN LABARI MAI SANYA ZUCIYA SANYI_*

*_ZAKAƘURAN MARUBUTAN DAZA SU FADAKAR DAKU ACIKIN WAƊAN LITTAFAN NASU SUN HAƊA DA_*


*AISHA ABULLAHI FULANI*

Wacce ta nishaɗantar daku a cikin littafinta mai taken *MA'AURATA*.

Yanzu ma a shirye take tsaf domin ganin ta faranta muku rai tafe take da sabon salon labarin ta mai taken.

*RAYUWAR MU*



*RASHEEDAT USMAN*
*(UMMU NASMAH)*

Wacce ta nishaɗantar daku a cikin wannan shahararren Novel ɗin nata wanda yazo muku a cikin fittatu 15 daga ƙungiyar kainuwa Wato.
*INDO A BIRNI*

Yanzu ma dai tafe take da Sabon salon labari mai Ruɗa Zuciyar mai karatu kun dai santa bata wasa wajen zaƙulo muku daddaɗan labari mai cike da darasin Rayuwa tare da nishaɗi to yanzu ma dai gata tafe da sabon book ɗinta mai taken.

*RUƊANIN ZUCIYA BIYU*


*Haleematu Hassan Leemat*

Wacce ta ni shadantar daku acikin littafinta na ADALI'LIN DA NAMIJI

yanzu ma ta sake kawo muku wani sabon littafinta mesuna *LAIFIN WA?*
*(MAZAN KO MATAN)*


*FAUZIYA AUWALU ALIN BABA JINGAU*

*(YAR MUTAN JINGAU)*

Itace dai wannan shahararriyar marubuciyar da take nishaɗantar daku wacce ta jajurce wajen zaƙulo muku labari kan lamuran dake addabar mu cikin al'umma wacce ta kawo muku labarin.

*ABINDA KE FARUWA*

Yanzu mai dai tafe take da labarin da zai taɓa zuciyar mai karatu zai nishaɗantar daku ya kuma faɗakar daku mai taken.

*DAMUWA MUNGUN CIWO*


*NA'EEMA SULAIMAN*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wani ga nawa, ina kuke tarin masoya ku matso kusa ga dama ta samu a yau ma dai tafe nake da sabon salon labari wanda zai saku nishaɗi ku kasance cikin annashuwa nice dai wacce na nishaɗantar daku cikin book ɗina mai taken.

*ASHE ƳAR BABATA CE*

Nayi nitso nayi ninƙaya na zauna na baje kolin bajinta ta, na zaƙulo muku labarin da zakuji daɗin sa wanda zai faɗakar daku mai taken.

*SAI NA AURE TA*


*MARYAM UMAR*
*(MAMAN YUSUP)*

Ina kuke tarin masoya to ku matso kusa ku nuna mana tarin ƙaunar da kuke mana nice dai taku maman yusup wacce na nishaɗantar daku cikin book ɗina mai taken.

*MUTUM CE KUWA*

Yanzu ma dai gani tafe cikin sabon salon labari na sabon zubi sabon ɗauka mai taken.

*KYAUTAR ZUCIYA*


________________________________

Ina matuƙar baku haƙuri masoyana na tsaida posting ɗin *SO BAI SAN JINI BA* da nayi sakamokon abubuwa da suka min yawa.

Sai dai ina muku Albishir da cewa zan sake muku complete ɗin book ɗin gabaki ɗaya Ranar bikin ƙaramar Sallah ta uku a matsayin *HAPPY SALLAH* kumin UZIRI pls.🙏🏻


Sannan kuma ina muku Albishir da cewa zan fara sakin sabon Novel ɗina mai taken *RUƊANIN ZUCIYA BIYU* Wanda ina da tabbacin cewa salon labarin sa na daban ne ina kuma da tabbacin cewa sai yafi *INDO A BIRNI* haɗuwa ku sani cewa ba wani dalili yasa na saki *RUƊANIN ZUCIYA BIYU* a matsayin na kuɗi ba sai Saboda kunsan sha'anin ƙarfe wata rana dole wayar ka zata buƙaci gyara ga kuma matsalar Siyan data da kuma na Battery nasan dai nafi ƙarfin wannan kuɗin a wajen ku, ku fito ku nuna min ƙauna ta hanyar ciyen littattafan mu.

Sai ku tuntuɓe mu ta numbobin wayar mu da suke da suke ƙasa domin sanin yanda zaku biya kuɗin


_Zaku sami waɗannan littatafan namu a cikin farashi mai rahusa, domin kuwa ƙungiyar bata tsawalla ba farashi ne mai sauƙin biya, ku fito masoyan mu ku nuna mana ƙauna ta hanyar sayen littatafan mu kan farashi 👇🏻

Duka guda bakwai ɗin zaku samesa ne akan farashi Naira 500 kacal👌🏻

Mai son shida kuma zai biya Naira 450.

Mai son guda biyar zai biya Naira 400.

Mai son guda huɗu zai biya Naira 450.

Mai son guda uku zai biya Naira 350.

Mai son guda biyu zai biya Naira 300.

Mai son guda ɗaya zai biya Naira 200.

Farashi ne mai sauƙi muka baku domin ƴan uwana ku sami damar biya kuma cikin nishaɗi.

Ku tuntuɓe mu ta waɗannan numbers domin sayan book ɗin mu.

*08147537180*
*09035027743*
*08106795647*
*08176841985*

Gareku ƴan Niger kuma fa baza'a barku a baya ba ku kwantar da hankalin ku domin ku sami damar siyan littatafan mu zaku iya tuntubar wannan NUMBER👇🏻

*+2278456476*


Muna muku barka da zuwa daga Shahararriyar ƙungiyar ku Wato KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION✍🏻
[4/22, 8:17 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*

Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya.

______________________________________

*P*••••••2️⃣1️⃣ ↗️ 2️⃣2️⃣

Daƙyar ta ɗago kanta ta kalli HASINA tace.

" Bana jin daɗi wlh kwana na huɗu ina kwance ya Habeeb bai sanar dake ba ne wataƙil ina ga Ya Mustafa zai sanar dashi."

" Subhanallah sannu wlh ban sani ba kuma Habeeb bai sanar dani ba, amma ina ga gaskiya bai sani ba dan daya sani zai sanar dani gaskiya daya sani kam zaima ce nazo na duba ki.''

" Nima nayi wannan tunanin gaskiya dan daya sani shi kanshi zai shigo ya dubani kinsan Halin ya Mustafa bana gabansa shiyasa duk wani lamurana baya damuwa bare ya sanar da wani, HASINA ina rayuwar Aure ne cikin baƙin ciki na tabbata Rabon cikin da yake jikina ne ya kawo ni cikin wannan wahalar domin ni ban taɓa jin daɗin Aure ba, Hasina ji nake kamar bazanyi wani dogon Rayuwa ba Zuciyata tana min nauyi ji nake kamar mutuwa ta tana kusantoni kullum cikin baƙin ciki nake Rayuwar Aure na sam babu daɗi."

Ta ƙarasa maganar cikin kuka tana duban Hasina kafin taci gaba da cewa.

" HASINA tunda nayi Aure Mamy bata zo taga ɗaki na ba, babu wanda yazo daga cikin gidan mu haka dangi babu wanda ya leƙoni, sai Abba kawai da yake kira na a waya HASINA baƙin ciki ne ya min yawa a cikin zuciyata har nake tunanin kamar shi zai kashe ni, Ga Rayuwar Auren ma babu daɗi."

Shuru HASINA tayi tana sauraron RAUDA cikin tausayin halin da take ciki domin kuwa wannan babbar damuwa ce ace bakayi dacen gidan Aure ba, ga dangi babu wanda ya kalle ka to da wanne zakaji, duban RAUDA tayi cikin muryar rarrashi tace.

" Damuwa ba ta nufin mutuwa kedai kisa hkr da juriya cikin zuciyarki ki dinga yawaita addu'a insha Allah komai zai wuce kamar bai taɓa faruwa ba, mijinki Kuma zai soki ki daina sa damuwa a cikin ranki mussaman yanzu da kike sanar dani kina ɗauke da ciki, mai ciki bata son damuwa domin kuwa yana haifar mata da matsala, kiyi hkr komai mai wuce wane babu abunda yazo zama duniya fatan dai Allah ya baki lafiya."

" Shikenan Hasina na gode sosai insha Allah zanyi ƙoƙarin ganin na kiyaye na gode sosai."

Hasina ta juma suna hira da RAUDA kafin ta tashi ta mata shara tare da girki sanda ta tabbatar ta gyara mata komai na part ɗin kafin ta koma nata part ɗin, sosai RAUDA taji daɗin Abunda Hasina ta mata.

**************************

Wasa wasa yau har anci wajen wata huɗu yayin da cikin RAUDA yake da wata 6 a yanzu tana ɗan samun kula daga wajen Mustafa duk da ba yanda take so ba amma dai abubuwan da sauƙi sosai tunda ya ɗauke mata aikin komai ya ɗauko mata mai aiki amma itace take masa girki Momy ma kullum sai ta shigo ta dubata haka Momy da Mamy sunje wajen bokan ya gama tsarawa Momy ƙarya tare da bata wasu surkullen ƙarya yace taje ta zubawa yarinyar a cikin abinci da kanta zata ce bata son yaran nata haka kuma akayi ta zuba mata kuma taci.

Haka Daddy har yau bai sake kiran su ba kan maganar Auren yayi shuru yaƙi cewa komai, ya kira can Dasina ya sanar dasu cewa ya ɗaga auren zuwa wani lokaci sosai suka fahimci juna da malam musa, daga Habeeb har Mustafa hankalin su baya kwance kullum cikin zullumi suke na wani irin hukunci Daddy zai yanke domin kuwa shurun nasa ya fara basu tsoro, Mustafa kuwa har wata ƴar rama yayi mussaman yanda Indo take masa walaƙanci sam bata sauraronsa sosai take nuna masa ƙiyayya a fili tsakanin sa da Habeeb yanzu Ido koda Habeeb ya hango Mustafa kafin ya iso wajen Mustafa zai tashi yabar wajen haka kuma ko a ɗakin Momy suka haɗu Mustafa tashi yake ya barwa Habeeb wajen idan kuwa shine yazo ya sami Habeeb a wajen to juyawa yake yabar gurin.

Wajen Indo kuma abun ba haka yake ba kawai tana daure zuciyarta ne amma har yau Soyayyar Mustafa tana cikin ranta sai dai wannan alƙawarin ta ɗauke sa koda Soyayyar sa zata kashe ta bazata taɓa Auren sa ba Habeeb shine wanda zata aura.


*********************************

Da sauri ta sauƙo daga step ɗin hanunta ɗauke da bag ɗin ta sauri ta ke domin kuwa sunyi alƙawari da Zarah zasu fita shopping by 4:00pm gashi har 5:00 har zata fice taji muryar Daddy yana cewa

" *A'ISHA* Ina zaki haka kike sauri dawo ki Zauna a nan"

juyowa tayi ta dawo ta zauna kusa da Daddy tare da cewa.

" Daddy dama kana nan ban hango ka ba ai.''

Murmushi Daddy Yayi yace.

" Ina kuwa zaki ganni hankalin ki yayi gaba ina zaki haka kike wannan saurin?"

" Daddy jiya ba nace maka zanje shopping ba, shine ai yanzu zan tafi."

Murmushi Daddy Yayi yace.

" Sarkin shopping ba to yau dai ki haƙura da shopping ɗin nan sai gobe yanzu akwai abu mai mahimmanci da zamu tattauna da ƴan uwanki na kira su suna shigowa yanzu."

Bata ce komai ba sai kiran Zarah da tayi a waya tace mata tayi hkr sai zuwa gobe su fita "Yanzu ba hali Daddy ya ce ta tsaya za suyi meeting."

Da to Zarah ta amsa mata kafin suka katse wayar.

INDO suna zaune a wajen har suka zo su, Habeeb ne ya fara shigowa kafin Mustafa, sai Momy da ta sauƙo cikin isa domin kuwa tana da tabbacin cewa yau Indo da bakinta zata furta bata son ƴaƴan nata, zama tayi tana murmushin mugunta, yau cikin sakin fuska ta amsa gaisuwar ƴaƴan nata bayan kowa ya zauna ne Daddy ya buɗe taron da addu'a kafin yace.

" *A'isha* Indo na tara ku anan ne badan komai ba sai don naji ra'ayin ki da farko na yanke hukunci kai tsaye ba tare da bincike ba, sai daga baya nake jin wata magana, ina so ki sanar dani wa kike so tsakanin Mustafa da ɗan Uwansa Habeeb?"

Dukan su ukun dam!Dam! Dam gabansu yake faɗuwa sunkuyar da kanta Indo Tayi ƙasa ta kasa magana, su kuwa gabaki ɗaya ita suka mayarwa hankalinsu don jin me zai fito daga bakinta, Momy kuwa wani Shu'umin murmurshi tayi tana jiran Indo tace bata sansu.

Ganin Indo bata da niyar Magana yasa Daddy ce mata.

" Please *A'isha* karkiji tsoro tell me wa kike so karki ɓoye min komai."

INDO ta rasa ya zatayi domin kuwa har ga Allah Mustafa shine muradin Zuciyarta, Habeeb kuma shine zaɓinta daure zuciyarta tayi kanta na ƙasa ba tare da ta ɗago ba ta amsawa Daddy da cewa.

" *YA HABEEB* shine zaɓi na Daddy shine Wanda nake so, babu soyayya tsakanina da *ya Mustafa*"

Ajiyar Zuciya mai nauyi Habeeb ya sauƙe yana godewa UBANGIJIN sa daya tseratar da Zuciyarsa, wani ɓangare daga cikin zuciyarsa ce tace masa " to shi kuma ɗan uwan naka fa kana tunanin ka masa adalci kuwa shin wani hali zaka jefasa ciki?" Ɗaya Zuciyar kuwa ce masa tayi, " ina ruwanka da halin da zai shiga komai ya samesa ai shine ya jawa kansa ba shine mai walaƙanta mata ba, ga nan matar sa ta cikin gida ma ya kasa riƙe ta kullum yana cikin walagigi da rayuwarta, karkayi sake ka bar masa Indo yazo yana wulaƙanta ta, Kamar yadda yake yiwa RAUDA, kaine ya kamata ka aureta domin zakafi kowa riƙeta bisa Amana da gaskiya, idan ka lura ma ai kaine kake mata son gaskiya." Da wannan huɗubar na Zuciyarsa Habeeb ya yarda tare da sakin murmurshin farin cikin samun Indo.

Mustafa kuwa wani irin bugawa Zuciyar sa tayi, jiri ne yaji yana ɗebarsa domin kuwa ga baki ɗaya ɗakin juya masa yake IDANUNSA sun kaɗa sun koma kamar gauta wani irin tsanar Habeeb ne ya ɗarsu cikin zuciyarsa yayin da Zuciyar tasa ta masa nauyi tsabar baƙin ciki gagara Magana yayi, yayin da yake bin Indo wani irin mungun kallo ita kuwa kanta sunkuye yake taƙi ɗago sa domin kuwa ita kaɗai tasan Abunda take ji a cikin Zuciyarta gani take kamar bata yiwa kanta adalci ba sai dai babu yanda zatayi Auren Habeeb shine kawai mafita a gareta.

Wani irin zabura Momy tayi tana ƙarewa Indo kallon tsana domin kuwa tasha mamaki yarinyar da ta samata magani a cikin abinci kuma tana kallo tacii abincin sannan kuma yanzu ta furta da bakinta tana son Habeeb a madadin tace bata sonsa sai tana sonsa ne ya fito daga bakinta, to wani irin magani bokan nan ya bamu, *TABBAS WANNAN YARINYAR MAYYA CE* dole sai na tashi na tsaya domin kuwa bazan taɓa yadda na haɗa zuri'a da ke ba, shuru tayi bata ce musu komai ba domin kuwa ita tasan bazata taɓa yadda wannan auren ya ƙullu ba, ba kuma zata sake faɗa na faɗa da mijinta ba.

Daddy kuwa murmurshi yayi tare da furta cewa.

" Alhamdulillah! Hakan yayi kyau Mustafa da Habeeb ai duk ɗaya suke babu bare kuma daman burina kenan ki zaɓi mijin da kike so da kanki Allah yasa hakan shi yafi Alkairi, Habeeb kaine wanda *A'ISHA* ta zaɓa a matsayin mijin Auren ta, sai kayi ƙoƙari wajen ganin ka kyautatawa Rayuwar ta, insha Allah nan da wata biyar masu zuwa za'a tada Maganar Auren, Kafin nan kaga sun sami hutun makaranta sai taje ta duba iyayen ta."

Murmushi Habeeb yayi tare da cewa.

" Shi kenan Daddy Allah ya nuna mana lokacin na gode sosai Daddy da wannan damar da ka bamu domin ganin ka bawa kowa haƙƙinsa Allah ya saka da Alkairi."

Da ameeen Daddy ya amsa kafin ya maida dubansa ga Mustafa da kansa ke sunkuye baice musu ƙala ba sai zogin da yake ji cikin zuciyarsa sa kafin Daddy yace.

" Muhammad Mustafa, da farko na yanke hukunci bisa rashin Sani sai kuma daga baya naji cewa *A'ISHA* ba kai take so ba ɗan uwanka take so hakanne yasa na yanke shawarar Tambayar ta da bakinta naji waye ne zaɓin ta, to kadai ji da bakinta ta furta cewa Habeeb take so ba kai ba ni kuma bazan mata Auren dole ba shiyasa na bata wanda take so a tunanina dakai da Habeeb duk ɗaya ne kuma zaka iya Hkr ka bar masa Ita duk Soyayyar da kake mata domin ganin farin cikin ɗan uwanka kayi hkr karka saka damuwa cikin zuciyarka domin na fahimci akwai Soyayyar ta cikin zuciyarka."

Sai yanzu ya ɗago kansa ya dubi Habeeb sannan ya maida dubansa ga Indo Wanda Yayi dai-dai da ɗago nata idanun suka haɗa ido da sauri ta maida kanta ƙasa cikin tsoro da tsinkewar Zuciya domin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login