Showing 27001 words to 30000 words out of 53497 words

Chapter 10 - SO BAI SAN JINI BA HAUSA NOVELS BY UMMU NASMAH.txt

29 Oct 2025

461

kuwa idanunsa sun bata tsoro, cije leɓensa yayi sannan ya ɗaga IDANUNSA da suka koma Red colour ya fara magana cikin dakiyar zuciya.

" Yaudarar ɗan uwa cutarwar zalincin ɗan uwa yau duk na gansu akan ɗan uwan da ban taɓa tunanin zan samesu a garesa ba, kamar yadda kace nayi haƙuri bazan iya haƙora da ita ba, kuma bazanyi jayayya da hukuncin ka ba, ni mai biyayya ne a gareka Daddy ina musu fatan Alkairi, ina Kuma matuƙar godiya cutarwar ɗan uwana, ita kuma bani kaɗai ta zalinta ba harda Zuciyarta domin na tabbata har gobe nine a cikin Zuciyarta hmmm *SHATUU* ki sani zan kasance da Soyayyar ki har ƙarshen rayuwata, sannan kuma ki sani cewa duk abinda ya faru dani kece sanadiyyar shiga ta, idan kuma na mutu a halin da kika sani ki sani cewa kece Ajalina, duk yawan tarin zunuban laifina gareki bancancanci wannan hukuncin gareki ba, Tabbas kin yanke hukunci cikin gaggawa, danasani yana gabanki, Allah ki zaman lafiya da zaɓin ƙwaƙwalwar ki domin bata zuciyarki bace."

Ya ƙarasa maganar cikin rawar Murya kuka yana neman kwace masa, miƙewa yayi tsaye ya nufi hanyar barin falon, da sauri Habeeb ya miƙe tare da dakatar da Mustafa da fitar da zaiyi ta hanyar cewa.

" Me kake nufi da maganganun ka, kana nufin Na cutar da kai koko kana nufin bana ƙaunar ka."

Murmushin baƙin ciki Mustafa Yayi jin tambayoyin Habeeb kafin ya maida masa amsa ba tare daya juyo ya dubesa ba.

" Duk yadda Zuciyarka ta fassara maganganu na haka ne *Mister Lover SO BAI SAN JINI BA SO BASHI DA HANKALI* bazan manta da waɗannan maganganun naka ba, kullum suna min amsa kuwa cikin kunnuwa na, idan har shi so bai san jini ba, to lallai kuwa dole ya kasance alaƙa ta jini ta yanke a tsakanin waɗannan ƴan uwan, a yanzu na yake alaƙa tsakanina dakai bani da wani ɗan uwa mai suna *HABEEB* na ɗauka ni kaɗai aka haife ni ba mu biyu ba."

Yana gama faɗin hakan ya fice cikin sauri domin kuwa baya son sake jin muryar kowa cikin falon Daddy dake ƙoƙarin masa magana ma bai samu damar masa ba sakamakon ficewa da yayi, duban Habeeb Daddy Yayi yace.

" Karka damu Habeeb ranshi ne ya ɓaci shiyasa yake waɗannan maganganun amma na Tabbata zai sauƙo ku barshi ya huce kafin ku ƙara tunkarar sa."

Shuru Habeeb yayi zuciyarsa cike da jin zafin maganganun ɗan uwan nasa, taya Mustafa zaice baya sonsa bayan duk duniya babu wanda yake so sama dashi, what ɗan uwana zaka min kallon mayaudari, duban Daddy Yayi yace.

" Shi kenan Daddy Allah yasa ya sauƙa da wuri bana son ganin yana fushi dani bani da ɗan uwan daya fisa amma ya sanja alaƙar dake tsakanin mu da wata manufa wanda sam babu shi a cikin Zuciyata Allah yasa Mustafa ya fahimce ni daddy bani da niyyar cutar da rayuwarsa ɗan uwana ne fa Daddy taya zanso rashin kwanciyar hankalin sa mutumin da muka kwanta ciki ɗaya dashi taya zan Cutar dashi, Daddy meyasa zai guje ni akan Mace Daddy hakan yana nufin cewa daman can babu Soyayyar da shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin mu, ka bani amsa Daddy na fara shiga cikin duhu.?"

Tsuka Momy taja tare da tashi ta haura tana taɓe baki harara ta sauƙewa Habeeb sannan ta wuce, kallo kawai Daddy ya bita dashi kafin ya dawo da kallonsa kansu Habeeb ya umurci Indo da ta koma bedroom ɗin ta tayi alwala domin kuwa amfara kiran sallah, " kaima Habeeb jekayi alwala ka tafi kubar maganar zai sauƙo da kansa ransa ne ya ɓaci waɗannan tambayoyin duk ka ajiye sa a gefe.''

Ajiyar Zuciya Habeeb ya sauƙe Sannan ya miƙe ya fita itama Indo ta haura sama shima Daddy tashi yayi yaje ɗauro alwalar ya fice masallaci.

MOMY tana shiga bedroom ɗinta layin Mamy ta kira, cikin tashin hankali take cewa.

" Wani irin magani bokan nan ya bamu ne kam, nafa bata maganin nan da Idona Kuma na ganta taci, sannan yanzu ta ƙara furta cewa Habeeb take so bayan kuma shi malam yace da bakinta zata furta cewa bata son ƴaƴana, nifa Turai Hankali na a tashe yake domin kuwa bazan taɓa lamunta ɗana ya auri wannan fitsararriyar YARINYAR ba.''

Daga can Mamy tayi murmurshin mugunta tana yiwa Momy kallon wawiya marar lissafi kafin tace mata.

" Haba Hajiya A'isha ya kike gaggawa ne kam shikenan daga baki magani sai akace miki zai yi amfani lokaci ɗaya, ina kika taɓa ganin anyi haka, kinga malama ki kwantar da hankalin ki komai sannu ake binsa, a hankali zamu kamo bakin zaren har mu cinka sa dan haka kwantar da hankalin ki yanzu ma zan kira Mlm na masa bayani naji maiya kamata ayi."

Ajiyar Zuciya Momy ta sauƙe tare da cewa.

" Yauwa kira sa dai gaskiya hankalina zaifi kwanciya dan Wlh bana ƙaunar YARINYAR nan, ni ko nawa ne zan basa muddun zan samu biyan buƙata."

Murmushi sosai Mamy tayi tace.

" Gaskiya kam ya kamata ki ƙara masa kuɗi fiye da wanda kika basa a baya, dan mu samu shima ya ƙara dagewa mu samu biyan buƙatar mu da wuri kinsan dai yanzu irin wannan harkar ta koma sai ana sakewa malaman nan kuɗi sannan suka zasu samu suyi aiki da kyau komai ya koma sai da kuɗi."

" Karki damu ƙawata indai kuɗi ne kema ai kinsan bani da matsalar su, ko nawa ne zan iya kashewa muddun za'a raba ni da wannan raƙai ɗin shegiyar ƙaya mai suka, ni fa ta dameni da suka, bukata ta kawai na yageta na huta Banda damuwa da kuɗi ko nawa zan iya kashe wa domin kuwa akwai su."

Wannan karon dariya sosai Mamy tayi kafin tace.

" Ai kuwa ki kwantar da hankalin ki, zaki yageta koda kuwa da naman jikin kine dole sai tabar gangarki koda kuwa bata bar gidan ki ba."

Murmushi Momy tayi domin kuwa bata fahimci Mamy Hausa tayi mata ba, ita nufin Mamy na koda Naman jikinta ne, shine koda ɗanta zai aureta ya fitar mata da ita daga cikin gidan zuwa gidan sa, ce mata tayi.

" Da kuwa kin taimaka min wlh, yanzu kuyi Magana dashi duk abunda ake buƙata kimin magana zan turo miki ta account karki damu da yawan kuɗi ko nawa ne zan iya biya."

" Shi kenan baki da matsala, sai kin jini zuwa gobe."

"Allah ya kaimu" Momy tace kafin ta kashe wayar ta ajiye kan bed ɗin ta kafin ta shiga tollet alwala.

*******************************

RAUDA sosai cikin jikinta ya fito ga wani ƙiba da tayi, yanzu laulayin ma da sauƙi ya sassauta mata, Zaune take tasa ayaba a gaba tana ci, ya shigo cikin fushi ko Sallama baiyi ba, ya shige bedroom ɗinsa, kallo kawai RAUDA ta bishi dashi cikin mamaki domin kuwa rabon da ya shigo cikin wannan yanayin harta manta lokacin, bata gama dawowa daga tunanin ba, sai kuma ta gansa ya fito riƙe da key a hannun sa ya fice still ba tare daya kalleta ba, tashi tayi ta ɗaga labulen window tana leƙensa motar sa ya shiga ya ja da ƙarfi ya fice daga cikin gidan, sake labulen RAUDA tayi tana tunanin kome aka masa, zama tayi ta cigaba da cin ayabar ta domin kuwa tasan halin sa sarai zai iya wannan fushin ma ba tare da amsa wani laifi ba.

Shiko Mustafa gudu kawai yake a titi ba tare da yasan inda zashi ba, maganar zuci kawai yake shi ɗaya.

(Wai yau ni Habeeb zai wulaƙanta ni Habeeb yake shirin kwacewa numfashina daga jikina wani irin laifi na masa haka da zai min Hukunci mai muni irin wannan ko a mafarki ban taɓa tunanin haka daga garesa ba)

Jin ƙarar haɗuwar motar sune ya sashi saurin dawowa daga tunanin sa, yana ƙoƙarin riƙe sitiyarin motar, da ƙyar ya samu ya taka burki ya tsaya yana dafe kansa tare da ambaton ubangi, shi kuwa Barrister Kamal cikin masifa ya fito daga motar yana ƙoƙarin zagin Mustafa sai dai mai yana sako kansa su kayi Ido huɗu da Mustafa daya dafe kansa yana sauƙe ajiyar Zuciya, nunasa da hanu Kamal Yayi yace.

" Barrister mustafa kaine kake wannan gudu haka bisa titi ko kasan wannan wasa da Rayuwar ka kake yi."

Ajiyar Zuciya Mustafa ya sauƙe tare da ɗago idanunsa da suka koma Red color da ƙyar cikin nauyin Murya yace.

" Sorry Barrister Kamal na maka asara a motar ka ko, Ni kaina bansan wani irin tuƙi nake ba, gabaki ɗaya bana cikin tunani na bamma san inda zani ba kawai tafiyar nake, sorry"


Cikin mamaki Barrister Kamal yace masa.


" Baka san inda zaka ba kuma lafiya kuwa kake Barrister mustafa? naga alamar kamar baka cikin nutsuwar ka, kaga bari naja mota ta mu wuce, *Amada club* ma ƙarasa maganar a can."


Cike da mamaki Mustafa ya tambayi kamal.


" Club kuma Barrister Kamal me zai kaika Club kuma?"


Murmushi kamal yayi tare da cewa.


" Kaga Barrister mustafa babu Time ɗin tambaya yanzu muje kawai tunda kaga kaima ba wai wajen zuwa kake dashi ba."


Kaɗa kansa kawai Mustafa Yayi sannan suka ja motar, suka nufi Club ɗin, koda sukayi parking shiga sukayi cikin club ɗin, babu abunda yake tashi sai sautin ƙiɗa, mata ne ƴan bariki birjik cikin Club ɗin ga baki ɗayan su babu wani mai suturar arziki a jikinsa, waje suka samu suka zauna bisa kujerun dake zagaye cikin Club ɗin yayin da maza da matan dake wajen suke sheƙe ayar su ta tsiya, shidai Mustafa zama yayi tare da jin gina kansa yana sauraron kiɗan dake tashi a wajen, zuciyarsa Kuma har yanzu bata daina suya ba, wasu ƴan mata biyu dake tsaye gefe daga su sai wando 3 cutter da wata ƴar ƙaramar Best, ɗayar ce ta zubawa Mustafa ido tana jin wani irin feeling a kansa, itafa gayen ya mata domin kuwa yayi bala'in haɗuwa, Magana suke ƙasa ƙasa ita da ɗayar, wanda baza kaji Abunda suke cewa ba, Still wata ce ta taho cikin sauri ta faɗa jikin Kamal, tare da kai masa kiss a kumatun ta, Wani irin kallon takaici Mustafa ya bita dashi tare da runtse idonsa yana tir da halin ta, kamal kuwa ƙara ƙanƙameta yayi a jikin sa kafin ya dubi Mustafa yace.

" Barrister Meke faruwa ne, bani meya fito da kai daga gida cikin fushi."

Taɓe bakin sa yayi yana ƙare musu kallo daga shi har yarinyar kafin yayi Magana yana nuna yarinyar da yatsa.


" A gaban wannan abar kake cewa na faɗa maka damuwata ta, a gaban wannan renon barikin, ba dai ni ba.''


Murmushi Kamal Yayi sanin halin Mustafa sarai yasan idan yaja da yawa ma, zai iya kaiwa wannan yarinyar mari, ita kuwa Ranta idan yayi dubu ya ɓaci domin kuwa babu wanda ya taɓa shigowa cikin Club ɗin ya zageta sai shi, Kamal dubanta Yayi yace.

" Sorry Safiya jeki idan mun gama zan nemeki.?"

Cikin ɓacin rai tace masa

" But amma............"


Dakatar da ita Mustafa Yayi cikin tsawa wanda har saida hankalin mutane ya dawo kansu.

" Keeeeeeee!!!!! Get out wuce ki bamu waje ballagaza cikon lissafi, ko kunya bakya ji kina mace mai daraja, ki zubar da rayuwarki kina rayuwar bariki, kinzo wani ginɗin-ginɗin dake ki ɗafe jikinsa kamar wanda kika samu jikin mijinki, ki gyara rayuwar ki domin ki samawa kanki ƙarshe mai kyau."

Iya ɓacin rai wannan baiwar Allah ta jishi domin kuwa gani take ya mata mungun wulaƙanci, ya tozarta ta cikin mutane, ita kuma tayi alwashin cewa sai ta rama Abunda ya mata, juyawa tayi cikin ɓacin rai tabar wajen yayin da sauran matan wajen suka sheƙe mata da dariya shi kanshi Kamal baiji daɗin Abunda Mustafa ya mata ba cikin mutane.

( Wannan shi ake kira bariki gidan da babu kunya a cikin sa)

Juyowa kamal yayi tare da cewa.


" Baka kyauta ba Barrister ka tsinka ta cikin mutane."

Murmushin takaici Mustafa Yayi kafin yace.


" Kabar wannan maganar muyi Abunda ya kawo ni."


" Okey ina sauraron ka tell me?"


Ajiyar Zuciya Mustafa ya sauƙe tare da duban Kamal ya fara zayyano masa abubuwan da suke faruwa, kafin ya ƙarasa maganar da cewa.


" Ban taɓa tunanin cewa Habeeb zaimin haka zuciyata ɗaya na ɗauke sa, amma abun takaici ɗan uwana na jini wanda muka kwanta ciki ɗaya muka girma tare muka rayu tare wai shine yanzu yake ƙoƙarin rabani da farin ciki na, ƙarin abun takaicin ma wai Daddy ya biye musu, Kamal kana TUNANIN cewa sun min adalci kuwa.?"

Ajiyar Zuciya Kamal ya sauƙe yana duban Mustafa kafin yayi murmurshi yace.

" *Shege SO* mai haɗa faɗa a tsakanin Aminta, yanzu kai Barrister mustafa menene abun mamaki a nan, indai *SO* ne zaiyi fiye da haka, karka manta da shi so *BAI SAN JINI BA* yana haɗa ɗa da uba ma faɗa wannan kaɗan ne daga cikin aikin soyayya yakan raba aminta, ni a nawa tunanin karka wani zargi ɗan uwan ka, kawai ka rabu dasu, suje su karata badai Mace bace ƙwaya ɗaya tak, Barrister shiga gari zaka samu goman ta waɗanda suka fita ma kyau, mussaman kai da kake juya Naira ka kuma taka ta, na Tabbata Mata har wawanka sai sunyi saboda yanzu harka da mai Naira ake yinta, ka manta da ita ka cireta cikin rayuwar ka, idanma zuciyarka zata dameka da tunanin ta, ka nemeni ina da maganin wannan damuwar akwai barasa da kuma ƙwayoyi na Tabbata zasu rage maka matsala zama su yaye maka ita gabaki ɗaya."


Wani irin kallon mahaukaci Mustafa yake bin Kamal dashi wai ya manta da *SHATUUN SA* Lallai Kamal ya cika cikakken mahaukaci, duban sa yayi kafin yace.

" Na gaji!! Na gaji!! Da jin wannan kalmar *SO BAI SAN JINI BA* bazan taɓa iya mantawa da ita ba domin kuwa numfashina ne ita, da zaka tara min matan duniya duka idona bazai taɓa kallon wacce tafi SHATUU ba sai kasa da ita babu wanda zai taɓa maye gurbin ta cikin sarautar zuciyata, ka daina kira min wannan banzar maganar, kamal ina da munguwar sha'awa da jarabar mata sai dai ko kaɗan bai ɗaura min son matan banza ba, basu kuma taɓa burgeni ba, ba kuma zasu taɓa burgeni ba, Kamal naga alamar baka da shawara mai mahimmanci da zaka bani kaga tafiyata."

Murmushi Kamal Yayi yana duban agogon hanunsa yace.


" Ina zaka yanzu ƙarfe 2:00pm ka haƙura kawai sai gobe yanzu kam dare ya kusa rabawa."

Dafa kansa Mustafa Yayi yana ƙarewa agogon hanunsa kallo, dole tasa Mustafa komawa ya zauna yasan bai isa yanzu ya koma gida cikin daren nan ba, tashi kamal yayi ya je ya kamawa Mustafa ɗaki shi kuma yayi ɗakin ABOKIYAR shashancin nasa, zama Mustafa Yayi bakin gadon ya dafe kansa wani irin Soyayyar INDO na ƙara bugar zuciyarsa ita kawai yake kallo cikin ƙwayar idanunsa, daya kwanta ma juyi kawai yake, yana jin wani irin ɓacin rai na Habeeb duk yanda yaso bacci ya ɗauke sa abun yaci tura domin kuwa duk satar bacci Ranar ya gagara satar Mustafa, gashi yana son Yayi baccin ko zai samu *SASSAUCIN CIWON DAKE CIKIN ZUCIYAR SA* ganin abun na ƙara damunsa Zuciyarsa na ƙara bugawa ya sashi fara tunanin ko dai ya kira Kamal ne ko zai samu maganin bacci a wajen sa.




____________________________________________

Tirƙashi wannan shi ake kira ƙayar baya wai garin nema ƙiba an tafi neman rama, to wai ya wannan daren zai kasance a wajen Mustafa ne cikin Club.?


Ku dai ku biyoni.

Sorry for typing error banyi editing ba.



*Alƙalamin Rasheedat Usman*✍🏻



*(Ummu Nasmah ce)*
[4/27, 10:23 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


2️⃣3️⃣ ↗️ 2️⃣4️⃣

Har Ƙarfe Uku da rabi bacci ya gagari Mustafa babu abunda zuciyarsa take masa sai saƙa ga mungun faɗuwar gaba da yake damunsa wayar sa ya ɗaga ya kira kamal lokacin daya kira sa suna tsaka da tambaɗewar su, wajen miss Call uku kafin Kamal yasa hanu ya jawo wayar daƙyar ya buɗe idanunsa da jaraba ya rufe su, ya duba screen ɗin wayar Barrister mustafa ya gani saurin tashi yayi daga kan Safiya ya ɗaga wayar tare da cewa.

" Lafiya kuwa Barrister kira tsakiyar dare haka."

Daga can Mustafa yace

" Na gagara bacci Kamal, zuciyata tana buga min ji nake kamar zata bar jiki na, GIZO take min cikin idanuwa na, ta hanani bacci, ƙirji na kuma yana min nauyi, PLS Kamal maganin bacci nake so, ko zanji relief Idan ba haka ba ƙwaƙwalwa ta zata zauce."

Murmushi Kamal Yayi yana kannewa Safiya Ido da take sauraron duk abunda Mustafa ke faɗa kasancewar a handsfree

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login