Showing 51001 words to 53497 words out of 53497 words
Chapter 18 - SO BAI SAN JINI BA HAUSA NOVELS BY UMMU NASMAH.txt
ki nuna min cewa ban iya raino ba, to na dai fiki iya raino, kuma nasan ma tafi sona fiye dake."
Dariya Hasina tayi tace.
" Kaji wata tatsuniya, to bari muga" kallon ƴarinyar tayi tana mata wasa tare da cewa.
" Baby na waye kika fi so tsakanin ummi da Abba faɗa min."
Ita dai RAUDA ƙarama babu abunda take sai dariya, domin kuwa ita bata sanma me suke yi ba, kallon Habeeb Hasina tayi tace.
" Kaga tamin ni tafi so kenan."
Dariya Habeeb yayi yana kara cillata sama tare da cewa.
" Wannan kuma zance kike tafi son Abban ta ko Baby na."
Dariya kawai Hasina tayi tare da tashi ta shige kitchen tana girgiza kanta.
A bedroom ɗin ta ya shigo ya sameta kwance sai famar tura baki take, murmurshi Mustafa yayi tare da zama ya ɗaura kansa bisa kagaɗar Indo tare da cewa.
" Hasken rayuwata ya dai me kuma ya faru kike famar tura baki, faɗa min wani marar adalci ne ya taɓa min Rayuwata."
" Masoyi ba kai bane tun jiya nake binka cewa ka barni naje a amshi kayan Auren Zahra dani amma kaƙi kasan dai idan banje ba gaskiya ban yiwa Zahra adalci ba."
Murmurshi Mustafa yayi tare da cewa.
" Daman wannan ne fushin naki to kwantar da hankalin ki, itama Zahra tace ta yafe miki zuwa tunda tasan baki da lafiya, kina fama da wannan laulayin ne zaki wani karɓar kayan Aure."
" Shikenan tunda haka kace Allah ya sanya Alkairi daga baya naje naga kayan."
Rungume ta yayi tare da kai mata kiss a kumatun ta, yana cewa.
"Ya Mustafa kamin kuss irin wanda ake yi a tibin Hajiya INNA"
Murmurshi Indo tayi ganin Mustafa ya tuno mata yarintar ta, dubanta yayi yace.
" Miƙo min bakin na miki kuss, ƴar ƙauyen DASINA, yanzu ba sai kin nemo agajin jama'a ba na suzo su taya ki rokata na kuss yanzu ba ke kaɗai kike sona ba, nima ina sonki matata."
Dariya Indo tayi tare da haɗe bakinta dana Mustafa tana tsotsa kamar wacce ta samu sweet, sun juma a haka kafin salon nasu ya sauya.
Daddare Indo ta kira Zahra a waya sun juma suna taɗi da Zahra kafin Indo ta kashe kiran.
************************************
Rayuwa tana gudu yayin da kwanaki sai tafiya suke, cikin Indo ya cika wata Tare da kwana goma ranar wata juma'a Indo ta tashi da naƙuda sosai hankalin Mustafa ya tashi babu abunda yake tunowa sai RAUDA, ranar da take naƙuda a asibitin su Habeeb a kai Indo haihuwa, sosai hankalin Mustafa yake tashe da Momy aka kai Indo haihuwa ita dai Momy addu'a kawai take yiwa indo Allah ya sauƙeta lafiya, cikin ikon Allah kuwa Indo ta haihu bayan taci baƙar wahala yayin da ta haifi yaranta biyu wato ƴan biyu mace da namiji wayyo Allah kuzo kuga farin ciki wajen wannan family, sosai sukayi farin ciki da samun wannan ƙaruwa da sukayi, yaran aka fara fitowa dasu naɗe a cikin towel, farare dasu kyawawa, Momy ce ta amshi namijin tana dariya tare da cewa.
" Gaskiya bazan ɗauki kishiya ba, gara na ɗauƙi mijin yafi min.''
Dariya Habeeb yayi da ya fito daga Office ɗin sa kasancewar ba shi bane ya karɓi haihuwar doctor Zainab ce ta amsa karɓar yarinyar yayi daga hanun doctor Zainab yace.
" Kai Momy irin wannan tsoron kishiya haka, lallai ƴata da kwarin ta tazo tunda har ta fara sakawa wasu tsoro cikin zuciyarsu."
Dariya Momy tayi tace.
" Haba ta isa ta samin tsoro, Baby RAUDA ma ya ta ƙare dani bare kuma ita ƙaramar ƙwaro data iso duniyar yanzu."
Dariya sosai Habeeb yayi Mustafa yace.
" Babu wani nan ke dai kawai kin tsorata kinga manyan mata sunzo."
Cikin farin ciki da ráha suke wasa da dariya, har aka fito da Indo zuwa ɗakin hutu, bayan sun mata allurar bacci Saboda ta samu hutu.
Ƙarfe biyar na yamma Indo ta farka Momy ta gani zaune yaranta kuma suna kwance gefen ta, bin yaran take da kallo yayin da take jin wani sonsu na shiga zuciyarta, ai kuwa kamar wacce suke jira ta tashi, macen ta fara callara kuka, Momy ne ta tashi tace.
" Maza tashi ki Zauna ki bata nono tasha."
Sunkuyar da kanta Indo tayi alamun kunya, murmurshi Momy tayi tare da cewa.
" Wai kunya ta kike jine, kinga tashi ki bata tasha aima sunyi ƙoƙari tun safe fa basu nemi nonon ba, tashi Indo tayi ta zauna, Momy da kanta ta ɗauki yarinyar tasa mata a cinyar ta, aikuwa Indo na samata nonon a bakin ta, tana fara zuƙa Indo taji wani azabar zafi da sauri ta cire nonon daga bakin ƴarinyar tana cije leɓenta, murmurshi Momy dake kallon su tayi tace.
" Daurewa fa zakiyi ki basu nonon nan da zarar ruwan nonon ya fara kaiwa bakinta zaki daina jin zafin duk wata macen data haihu sai da taji wannan zafin shayarwar, bata maza ina kallon ki."
INDO bata ce komai ba ta mayar mata da nonon bakinta, tana runtse idonta, haka ta daure ta bawa yarinyar nonon.
Da magaruba Mustafa ya shigo asibitin lokacin kuma Momy ta fito shan iska waje, a gefen gadon ya zauna, tare da duban Indo, ya sunkuyawa ya manna mata kiss a goshin ta yace.
" Sannu Uwar biyu, ya dai ina dai normal kike jin jikin ki babu Wata matsala, sun bamu sallama ne yanzu."
Murmurshi Indo tayi tana kallon mijin nata tace.
" Babu Abunda nake ji komai normal."
" ALHAMDULILLAH!!" Ya furta tare da saka hanu ya ɗago macen da take hanun Indo dabino ya ciro daga aljihun sa yasa a bakinsa ya tauna sannan ya dinga sawa ƴarinyar a bakinta, Bayan ya gama ne ya ɗauko zamzam shima ya bata, kafin ya kama kunnenta ya mata kiran sallah, har sau Uku, sannan ya ajiye ta ya ɗauko namijin shima yanda ya yiwa macen haka ya masa kafin ya dubi Indo yace.
" Alhamdulillah!! Na godewa UBANGIJIN na daya nuna min wannan ranar da kika kasance matsayin uwar ƴaƴa na, na daɗe ina mafarkin wannan ranar sai gashi Allah ya cika min buri na, tabbas Ubangiji ya min ni'ima, fatana Allah ya yiwa Rayuwar waɗannan yara uku da Ubangiji ya bani Albarka, ya jiƙan mahaifiyar Baby."
Da ameeen Indo ta amsa tana murmurshi, shigowar Momy shine ya katse musu zancen nasu, cewa Momy tayi.
" Bari na haɗa kayan mu shige ko."
Tashi Mustafa yayi tare da cewa.
" Bari naje na musu bill ɗin kuɗin su kafin ki haɗa kayan sai mu wuce."
Fita Mustafa yayi ita kuma Momy ta hau haɗa kayan.
Ƙarfe tara suka shigo cikin gidan, Inda suka samu Hasina tana Zaune ta gama gyara musu gidan, Mustafa a falo ya samu RAUDA ƙarama wacce suke kira da Baby, ɗaga ta sama Mustafa yayi yana mata wasa, ita ko sai dariya take Rungume ta yayi a jikin sa yana jin ƙaunar ta, bedroom ɗin sa ya shige da ita a kafaɗar sa, murmurshi Hasina tayi, domin kuwa tana ganin darajar Mustafa a cikin idonta domin kuwa ya mata Hallaci a rayuwarta ada kullum tana cikin kukan rashin haihuwa, sai gashi lokaci ɗaya Mustafa ya share musu hawayen su ta hanyar basa kyautar ƴa, tun sanda ya musu wannan kyautar basu ƙara tunanin haihuwa ba.
MOMY tollet ta shige ta haɗa ruwan wanka mai ɗumi sannan tasa Indo a gaba har tollet ɗin Momy da kanta ta gasawa Indo jikin ta da towel, sannan ta fito ta barta a tollet ɗin zatayi wanka soso da sabulu, Momy bata yiwa yaran wanka ba kasancewar sunce dole sai gobe kafin a musu wanka, sosai Indo taji daɗin jikinta da tayi wankan, Hasina ce ta daga yaran tana yiwa indo SANNU, Momy kallon tausayi take yiwa Hasina domin kuwa rashin haihuwa akwai ciwo.
Ƴan Dasina ma an buga musu an sanar dasu haihuwar, Goggo Asabe da kanta ta ɗauko hanya washe gari domin itace zata zaunawa Indo har tayi arba'in.
Washe gari da safe Momy ta wanke yaran tas ta shirya su cikin pink ɗin riga da wando sosai yaran sukayi kyau Mustafa sanda ya shigo dubasu ne yayiwa yaran huɗu ba, sannan ya musu Sallama ya shige wajen aiki, Zahra ma ba'a barta a baya ba, duk da ranar ce bikin ta, amma sanda ta silalo tazo taga yaran aminiyar tata, duban Zahra Indo tayi tare da cewa.
" Ƙawata gaskiya naso ace wannan bikin naki dani za'a yisa, sai kuma gashi yaranki sun mini cikas sunzo da wuri."
Murmurshi Zahra tayi tace.
" Karki damu ƙawata, kinsan fa komai sai Allah yayi Allah ya yiwa Rayuwar su albarka, kinga yanzu bari na samu na tafi daƙyar ummi ta barni na fito, tace ma tana gaidaki kafin tazo."
" Shikenan ƙawata babu damuwa na gode sosai, ki cewa ummi ina gaisheta bari ma na baki saƙo ki kaiwa Ummi."
Tashi Indo tayi ta buɗe durowar ta ta ciro wani shegen agogon bango mai tsadar gaske tare da rafar kuɗi tazo tacewa Zahra gashi ki kaiwa Ummi kice ina gaisheta, karɓa Zahra tayi kafin Indo ta rakata har parking space, Goggo Asabe ta iso lafiya yayin da Indo tayi murnar zuwan nata.
Ana gobe suna Aunty Hindu da sharifa suka diro ƙasar, sosai Indo tayi farin cikin ganin Sharifa, Ranar kusan kwana sukayi suna hirar yaushe gamo, washe gari suna yarinya macen taci sunan *HAJIYA INNAH* wato *NANA KHADIJAH* shi kuma namijin sunan Baban Indo yaci *MUSA* Inda Sharifa tace ake kiran macen da *Ijlal* shi kuma namijin ake kiran sa da *Mus'af* taro yayi taro sosai Indo ta samu kaya sosai Aunty Hindu ma akwati biyu ta mata cike da kayan baby, Mustafa kam ba'a maganan Abunda yayi domin kuwa faɗin Abunda yayi ma bata lokaci ne, Habeeb ma ya taka rawar gani.
Haka akayi taro lafiya aka tashi lafiya cikin farin ciki.
Kwanan su Indo talatin da haihuwa sosai Kuma take samun kulawa a wajen mijinta da uwar mijinta ranar da ta cika kwana arba'in washe garin ranar Goggo Asabe ta koma da tara ta arziki, a nan ne take sanar da Indo cewa Mustafa ya saka an rushe gidan su an musu ginin zamani, tace har ruwan bohol yasa aka ja musu a cikin garin sannan ya buɗewa Tanimu babban shagon tireda wanda babu Irin sa kaf cikin garin, sosai Indo tayi farin ciki, harda hawayen ta domin kuwa taji daɗin ruwan daya ja musu domin kuwa Dasina sun juma suna fama da rashin ruwa sai na rafi na rafin ma wahala yake musu a rani.
Yau Indo da shirin ta tsaf ta shiga bedroom ɗin mijin nata bayan ta kintsa yaranta, a gadon su dake gefen na mahaifin su ta kwantar dasu, sannan ta faɗa saman bed ɗin mijin nata, murmurshi tayi tare da cewa.
" Thank miji na, bazan taɓa mantawa da alkairin da ka min ba."
Jawota Mustafa yayi jikin sa tare da cewa.
" sorry for what numfashina."
Murmurshi Indo tayi tare da cewa.
Abun alkairin da kamin na gyara gidan mu, da kuma buɗewa ya Tanimu shago, da ruwa daka kawo mana gaskiya naji daɗi sosai Allah ya saka da Alkairi ya kara arziki."
Murmurshi Mustafa yayi ba tare daya ce mata komai ba ya haɗe bakin su waje ɗaya yana mata wani hut kiss, yayin da itama ta biye masa suka lula duniyar ma'aurata.
***********************************************
*AGURGUJE*
Da ƙaton cikin ta na hango ta tana ƙwalawa yaran kira dake famar wasa a compaunt ɗin gidan.
" Ijlal wai ba kiran ku nake bane, kuzo maza ku ɗauki bag ɗin ku, ku tafi islamiyya lokaci yayi, ashe daman tun ɗazu dana sa muku uniform ɗin nan kuka fito kuka tsaya wasa."
Da gudu Ijlal ta ƙaraso wajen ta tana cewa.
" Ummu brother Mus'af nake jira, fa yace zaije ya kira Aunty Baby a part ɗin su, kuma Ummu yanzu uncle Ishaq ma yace idan muka yarda har ya dawo daga masallaci bamu tafi school ba, sai ya zane mu."
Kama hanunta Indo tayi tana cewa.
" Ai gara ya zana kun ko zaku daina let ɗin school muje maza ki shirya kafin shima Mus'af ɗin ya shigo ya sameni."
Ai kuwa bata rufe bakinta ba Mus'af ya fito da gudu daga part ɗin Hasina yana cewa.
" Ummu Aunty Baby harta shirya mu kawai take jira."
Tisa ƙeyarsu Indo tayi a gaba har bedroom ɗin su, ta ɗauki bag ɗin nasu ta basu tana cewa.
" Kuyi addu'ar fita daga gida fa karku manta."
To suka ce mata sannan suka fice da gudu, Indo ajiyar zuciya ta sauƙe Sannan ta nufi kitchen ta cigaba da aikin abincin dare, ta bayan ta taji an Rungume ta, tasan ba kowa bane sai ogan nata, juyowa tayi tana kallon sa kafin tace.
" Hmmm, wato dai kai da yaran ka bazaku barni na huta ba, na samu na kora su school nazo kitchen zanyi aiki shine kaima ka shigo ka hanani aiki ko, wai ma tukunna mai ya dawo da kai daga wajen aiki yanzu.?"
Murmurshi Mustafa yayi tare da kwantar da kansa a kafaɗarta yana shafa cikin ta da yayi ta haihuwa ko yau ko gobe yace.
" Na dawo da wuri ne domin naga *BUGUN NUMFASHI NA* naga INDON ƘAUYE DA YANZU TA DAWO INDON BIRNI uwar biyu, wai ma tukunna ya naji kitchen ɗin ya turniƙe da ƙamshi ne, me ake dafa mana *MASOYIYA*."
MURMURSHI INDO tayi tare da turasa waje tana cewa.
" Na dai ga alama so kake ka hanani aiki, *MASOYI* maza samu waje ka jirani idan na kammala na fito na same ka" ta ƙarasa maganar tare da kanne masa Ido.
Murmurshi kawai Mustafa yayi, shima ya kanne mata ido tare da cewa.
" Ina sonki masoyiya."
Murmushin itama ta mayar masa tace.
" Ina sonka Bugun numfashina."
Tamat bil hamdulillah.
Anan na kawo ƙarshen wannan littafin.
Abunda na faɗa dai-dai ina roƙon ubangiji ya bani ladansa, kuskuren dana yi kuma ya yafe min.
Ina roƙon ubangiji daya sa makaranta su amfana da darasin dake cikin wannan littafin.
Masoyana bazan taɓa mantawa daku ba domin kuwa Tabbas kun nuna min ƙauna a cikin wannan littafin tun daga part one har zuwa part two, ina sonku masoyana a duk inda kuke.
To masoyana bari na baku wani albishir, kuce min goro.
Yanzu ma dai inan tafe da sabon labari na, wanda na daɗe ina muku nazarin sa labari ne wanda yasha banban da labaran da nake kawo muku labarin ya ƙunshi tsantsar SOYAYYA tausayi yaudara cin amana ƙiyayya, Rashin yarda Damuwa duk cikin labari na mai taken *RUƊANIN ZUCIYA BIYU* Wanda zan fara saki muku shi ranar ƙaramar sallah.
Shi dai *RUƊANIN ZUCIYA BIYU* na kuɗi ne zan sake muku shi akan farashi mai sauƙi *200* Kacal zaku biya ku karanta cikin sauƙi karku manta da cewa ta hanyar Siyan LITTAFI nane kawai zai sa ku nuna min ƙaunar da kuke min ga mai buƙatar Siyan LITTAFI na sai tuntuɓeni ta wannan number.
*08147537180*
*Alƙalamim Rasheedat Usman✍🏻*
*Ummu Nasmah ce*