Showing 36001 words to 39000 words out of 53497 words
Chapter 13 - SO BAI SAN JINI BA HAUSA NOVELS BY UMMU NASMAH.txt
Momy, dubanta sosai Momy tayi kafin ta fara magana.
" INDO wai meyasa ke mayyace kam dole sai kin Auri ɗana ne, nace bana sonki na tsaneki amma ki dage dole sai kin haɗa jini dani, dan Allah na roƙeki ki fita daga harkar ƴaƴana kije ki sanar da Alhaji cewa kin fasa wannan auren, ni kuma na miki alƙawarin duk abunda kike so zan baki ko meye ne idan ma kuɗi kike buƙata ki faɗi ko nawa ne zan baki."
Shuru Indo tayi tana al'ajabin ƙiyayyar da Momy take mata ta rasa me ta tare mata a duniya take gwada mata wannan baƙar ƙiyayyar kanta sunkuye tace.
" Ki gafarce ni Momy gaskiya bazan iya tunkarar Daddy da wannan maganar, amma Momy idan babu me zai hana shi ya Habeeb ki sanar dashi ya faɗawa Daddy ni na amince zan haƙura da Auren ƴaƴan ki Idan har hakan zaisa ki sassauta ƙiyayyata cikin zuciyarki, bana buƙatar komai daga gareki domin kuwa babu wani abun duniya da nake buƙata a wajen ku, idan banyi addu'a Allah ya hore min na baku ba Ni ai bazan yi burin karɓar naku ba, kiyi hkr Momy idan maganganu na sun ɓata miki rai iya gaskiya ta na sanar dake."
Wani mungun kallo Momy take bin Indo dashi na tsana kafin cikin ɓacin rai tace.
" Lallai kin iya magana kam, kamar mutumiyar kirki, sai dai ki sani wannan daɗin bakin naki bazai yi tasiri a kaina ba, ni shawara na baki akan ki fita harkar ƴaƴana, amma tunda kinƙi ji to ki sani bazaki ƙi gani ba, domin kuwa bazan taɓa barin ki kiji daɗin Aure ba, muddun kika Auri ɗana."
Tana gama faɗin haka ta tashi ta fice tana ƙwafa, hawaye ne ya ziraro daga idanun Indo, kafin ta goge ta kwanta ruf da ciki, ranar haka Indo taƙi fitowa falo domin kuwa itama yanzu ta fara jin Zafin Momy, ko ganinta bata son yi saboda tsantsar jin takaicin tsanar da Momy take gwada mata.
A haka rayuwar ta dinga tafiya yayin da Mustafa ya daina koda kallon inda Habeeb yake shi kuwa Habeeb duk sanda suka haɗu sai ya yiwa Mustafa Magana amma ko kallon sa Mustafa baya yi, Mamy kuwa kullum cikin ruɗar Momy take da wajen bokan ƙarya, haka ta dinga ɓatar da ita amma Momy ta kasa ganewa.
*********************************
Yau watan cikin RAUDA tara yayin da take cikin watan ta na haihuwa, sassafe ta shirya domin zuwa gida gaida Abbanta baida lafiya, Mustafa yana bedroom ɗinsa, kwance shima ba lafiyar bace dashi, dan harma ya ɗan rame, ciwon ƙirji ne yake yawan damunsa ga nauyi da ƙirjin yake masa yana kuma yawan yin tari bedroom ɗin nasa RAUDA ta shigo ta gaishe sa kafin tace.
" Ya Mustafa baka da lafiya ne.?"
Ɗago kansa Mustafa Yayi ya dubi RAUDA cikin sanyin Murya yace.
" Lafiya ta ƙalau babu abunda yake damu na me kika gani kinga alamun rashin lafiya a tattare dani ne.?"
Zama RAUDA tayi a gefan sa tace.
" Eh mana naga alamunka duk sun nuna kamar baka da lafiya, PLS ya Mustafa ka sanar dani me yake damunka, hankali na yana tashi idan na ganka cikin wani yanayi na gwammace ni na kasance cikin wannan halin kai ka Zauna cikin farin ciki, dan Allah ka sanar dani me yake damunka."
Wani irin tausayin RAUDA ya kama Mustafa, ta na yawan damuwa idan ta gansa a cikin wani hali tana lura da duk wani lamuran sa, amma sai dai shi ya kasa bata farin ciki, bazai iya sanar da kowa Abunda yake ji cikin zuciyarsa ba, ya gammaci ya mutu ko zaiji sauƙin Abunda yake damunsa baya ƙaunar Allah ya nuna masa ranar da zaiga auren Habeeb da SHATUUN sa, gara kawai yaga mutuwar sa da yaga wannan auren, duban RAUDA yayi yace.
" Karfa ki damu babu abunda yake damuna, kiyi tafiyar ki kawai, ki gaishe da Abban nima zanzo na gaishe daga baya."
Kaɗa kanta kawai RAUDA tayi badan ta yadda da Maganar Mustafa ba ta wuce abunta, bata juma da fita ba shima Mustafa ya fito yayi part ɗin Momy tana zaune ya sameta ta haɗa fuska, zama yayi yana cewa.
" Momy lafiya naga kamar ranki a ɓace."
Tsuka taja tana cewa.
" Lafiya lau waɗannan yaran nake jira su sauƙo ƴan iska mayu tun ɗazu suka haura amma sunƙi fitowa ni so nake ma ta fito ta wuce ƙauyen nasu ko zan huta."
" Wasu yara kuma Momy.?"
" Waye kuwa bayan Habeeb da wannan baƙar mayyar Indo, kasan yau zata bar garin nan zai kaita ƙauyen su, gobe idan ta koma jibi kuma za'a kai kayan Auren nasu bazata dawo ba sai an ɗaura Auren naji Daddyn ku yana cewa Habeeb ɗin ne zai kaita."
Dam ƙirjin Mustafa ya buga wani mungun kishin Indo ne ya daki zuciyarsa, hankalin sa ya kasa kwanciya mussaman da Momy tace suna ɗaki su biyu da Habeeb, tari ne ya sarƙe Mustafa sosai yake tarin sanda idanunsa sukayi jajur, hanunsa yasa yana tare bakin sa, ɗago hanun nasa da zaiyi sai jini ya gani, saurin danƙe hanun nasa yayi kar Momy ta gani Hankalin ta ya tashi goge bakin nasa yayi da ɗaya hanun yana ƙara ɓoye hanun nasa, Momy saurin duban sa tayi tana cewa.
" Lafiya meya sameka yanzu? Tana buga masa bayan sa, ganin bai daina tarin ba ya sata tashi da sauri ta tafi ɗauko masa ruwa , ai kuwa Mustafa kamar wanda yake jira Momy ta tashi, shima ya tashi cikin sauri ya bar part ɗin, part ɗin su ya nufa ya faɗa cikin motar sa ya figeta da ƙarfi ya bar unguwar gabaki ɗaya, koda Momy ta dawo tasha mamakin rashin ganin sa inda ta barsa ƙwafa kawai tayi ta ajiye ruwan tana cewa.
" Oh ni a'ishatu yanzu na barka zaune anan kana tari yanzu kuma na dawo ban sameka ba, sai kace wani aljani, ko ina kuma yayi sai Allah."
Ta ƙarasa maganar tana taɓe bakin ta
Tare suka sauƙo suna dariya, harda Zarah ma ashe suke cikin bedroom ɗin, Habeeb shine yake jan akwatin Indo, har suka sauƙo ƙasa, kusan tare suka fito da Daddy domin kuwa suna sauƙowa shima yana fitowa daga bedroom ɗin sa, murmurshi yayi yana tsokanar Indo.
" Yau dai ƴata ana murna za'a gida, naga bakin yaƙi rufuwa yau za'a ga Mama da Baba."
Dariya sosai Indo tayi sai kuma idanunta suka ciko da hawaye tana cewa Daddy.
" Daddy ai dole nayi dariya, yanda na daɗe rabona da gida, sai dai kuma Daddy zuciyata sam babu daɗi sanda zan taho birni da *INNA* na taho sai dai kuma gashi yau zan koma ƙauye babu *INNA* ba kuma zanje can na ganta ba, hankalina yana tashi idan na tuno da wannan abun Daddy da wani ido zan iya kallon gidan Inna babu ita a ciki, Daddy........"
Ringine ɗin wayar ta ne ya katseta tana duban wayar taga *SHARIFA* ce murmurshi Indo tayi tana goge hawayen fuskar ta tare da ɗaga wayar tana cewa.
" AUNTY Sharifa kin wuni lafiya."
Daga can Sharifa tayi murmurshi tare da cewa.
" LAFIYA lau Indo, kwana biyu shuru matar ya Habeeb, shine Wato ko ki bani labarin cewa tsuntsun Soyayyar ya tashi daga kan ya Mustafa ya koma kan ya Habeeb, anya kuwa kin yiwa kanki adalci Indo Wanda kike so daban wanda kika zaɓa a matsayin miji daban, meyasa kika yanke wannan hukuncin.?"
Runtse idonta tayi tana murmushin dole tare da duban ya Habeeb da Daddy sannan tacewa Sharifa.
" AUNTY Sharifa Yanxu ina hanya ne zanje DASINA idan na ƙarasa insha Allah zan kira ki sai muyi Maganar."
Daga can Sharifa tace
" Shikenan Allah ya kaiku lafiya, ki gaishe da Mama idan kin isa."
" Shike nan zataji insha Allah ki gaishe min da Ummi idan na ƙarasa zaki haɗamu."
" Zataji " Sharifa tace tare da kashe wayar tana ganin tsantsar wautar Indo.
Daddy ne yakai dubansa ga Indo yace.
" Karki saka damuwar rashin Inna a zuciyarki, duk sanda kika tuno ta ki mata Addu'a, dukkan mai rai mamaci ne fatan mu Allah ya mata Rahma, gacan siyayyar da na miki nasa an haɗa miki a mota tare da na Habeeb wanda ya saya miki, idan kin ƙarasa zan kira ki, ki gaishe da mahaifan naki."
" Zasuji insha Allah Daddy na gode Allah ya saka da Alkairi."
Wajen Momy ta ƙarasa tare da sunkuyawa a gabanta tace.
" MOMY zan tafi gida kimin addu'a idan kuma akwai Abunda na miki ba dai-dai ba ki yafe min Saboda bani da tabbacin cewa zan dawo ko bazan dawo ba, saboda halin tafiya."
Taɓe bakin ta Momy tayi tana mata kallon tsana da ƙiyayya kafin tace.
" Ni uwarki ce da zan miki addu'a, to bazanyi ba, idan kinga dama karki dawo idan kin tafi, ai dole ki roƙe ni gafara tunda kinsan kin cuceni kin liƙe min kin liƙewa ƴaƴana to wlh babu yafiya tsakanina dake, kawai ki rabu da ɗana sai mu Zauna lafiya idan kuma ba haka ba, Allah ya isa yanzu na fara ja miki ita."
Sosai maganganun Momy suka yiwa indo zafi, hawaye ne suka ɗigo daga idanunta tasa hanu ta goge su sannan ta miƙe tsaye tare daya cewa Daddy "na tafi Daddy Allah ya sada mu da Alkairin sa"
Gabaki ɗayan su ransu baiyi daɗi ba game da maganganun da Momy ta sanarwa Indo SOSAI maganganun suka yi masa zafi, murmushin takaici Daddy Yayi yana duban Momy cikin ɓacin rai bai kuma cemata komai ba, ya nunawa su Indo hanya alamun su tafi, tafiyar kuwa sukayi a harabar gidan suka ci karo da Hasina itama sukayi Sallama, Indo harta shiga cikin motar sai kuma Mustafa ya faɗo mata cikin zuciryata, ji tayi bazata iya tafiya ba tare da ta gansa ba, duban Habeeb tayi tace.
" Ya Habeeb na manta ban samu nayi Sallama da Aunty RAUDA ba, please dan Allah kumin afuwa naje na mata Sallama yanzu zan fito mu tafi."
Habeeb bai kawo komai a cikin ransa ba, ya amsa mata da to, ita kuwa Zahra sarai ta harbo jirgin Indo mustafa kawai take buƙatar gani ta fake da RAUDA kaɗa kanta kawai Zahra tayi tare da kwantar da kanta a sit ɗin motar, ficewa Indo tayi daga cikin motar ta doshi part ɗin Mustafa, sai dai kash a kulle ta samu part ɗin, sosai taji haushin hakan, zamewa tayi a ƙasa ta saki wani kuka mai cin rai sanda tayi ya isheta kafin ta tashi ta goge fuskar ta, ta dawo motar, zama tayi tare da cewa.
" Zamu iya tafiya."
Habeeb ne yace.
" Lafiya kuwa HABIBTY na naga kamar mood ɗinki ya sauya lafiya kuwa.?"
Murmushin ƙarfin hali tayi tace.
" Babu komai fa, muje kawai."
Kaɗa kansa yayi sannan yaja motar suka bar gidan, Zahra taɓe bakinta tayi ba tare da tace musu komai ba, har suka isa govt hause ɗin suka sauƙe Zahra, Sallama sukayi tare da alƙawarin cewa zata zo daf da bikin idan anyi biki ma dawo tare."
Cikin awa biyu suka Isa cikin garin DASINA sosai Indo take ƙarewa garin nasu kallo tana ganin sauye-sauye sosai ba kamar yadda ta tafi tabar ƙauyen ba, har suka yi parking a ƙofar gidan nasu, fitowa Indo tayi karaf idanunta suka sauƙa a ƙofar gidan INNA, wani iri taji cikin zuciyarta, yau gata cikin ƙauyen DASINA babu INNA cikin ta, ƙofar gidan nasu ta ƙarasa su Baba dukansu suna Zaune a rumfar ƙofar gidan, ƙarasawa sukayi wajen nasu tare da sunkuyawa suka gaishe su Mlm Abubakar ne yace.
" *INDO* kece haka na kasa gane ki sai da kikayi Magana, um um kinga yanda kikayi jawur dake kuwa sai kace baturiya."
Murmushi Indo tayi shima Habeeb murmushin yayi, Baba ne yace.
" Mlm Abubakar ai dole tayi jawur, gidan Mlm Haruna fa take, kasan kuma ƴar taka da son jin daɗi."
Dukan su dariya sukayi kafin INDO tace.
" Kuji Baba da wani zance, waye baya son jin daɗi, ai Baba ko kaine ka samu jin daɗi, ina ga yaro ƙarami zaka dawo wannan furfurar duk sai an nemeta an rasata."
Ta ƙarasa maganar tana dariya cikin salon zolaya, dariya Baba Yayi shida Mlm Abubakar, yana cewa.
" Kaji ja'irar yarinya ko, Muhammadu Habibu, maza ka ƙarasa ka samu kasha ruwa ka huta ka rabu da wannan ja'irar yarinyar."
Dariya sukayi Indo ta tashi ta musu jagora har cikin gidan nasu da Sallama suka shiga Mama tana sunkuye tana shara taji sallamar Indo ɗago kanta Mama tayi cikin fara'a da gudu Indo ta ƙarasa ta rungume Mama tana cewa.
" Mamana sannu da aiki nayi missing ɗinki.''
Cikin farin cikin ganin ƴarta ta Mama tace.
" INDO yau kece tafe cikin ƙauyen nan, sannu da hanya, kunsha tafiya."
Sake Mama Indo tayi tana dariya tace.
" Nine Mama, tun jiya na kasa bacci Allah Allah nake gari ya waye mu taho na ganku mama ina ya Tanimu yake?."
" Tanimu yaje cin kasuwar Ɓaure sai dare zai dawo, ina ga zai kai bayan Sallar isha'i."
" Allah ya dawo dashi lafiya Mama."
Sai yanzu Mama ta lura da Habeeb dake tsaye a gefe yana kallon su cikin burgewa sosai suka basa sha'awa yanda yaga soyayya mai ƙarfi tsakanin su, murmurshi Mama tayi tace.
" Wai daman da Habibu kuke tafe ne baki sanar dani ba muka barsa a tsaye, bismillah Habibu ga taburma ka Zauna."
Zama Habeeb yayi yana murmurshi tare da cewa.
" Ba komai Mama kinsan ƴartaki Sarkin zumuɗi, dole ta manta dani tunda yau anga Baba da Mama amma dai zan rama nima."
Cikin dariya INDO tace.
"Ai kuwa sai dai ka rame badai ka rama ba, domin nasan ba iyawa zakayi ba, Kuma kasan dai ni bana biyan bashi kona ɗauka, sai dai mutum yayi haƙuri."
" Au haka kikace, kinji ko Mama wai bazan iya ramawa ba, to bari mu zuba mu gani ko Mama.?"
Murmushi Mama tayi tana ƙoƙarin tashi tare da cewa.
" Kunga ni dai babu ruwana cikin lamarin ku domin kuwa kunfi kusa, kona shiga tsakanin ku Anjuma kaɗan zaku bani kunya, bari naje na kawo muku ruwa tukunna kusha, idan yaso sai ku ɗaura daga inda kuka tsaya."
Sannan ta shige ta ɗebo musu ruwa a randar ƙasa, bayan sunsha ruwan sun huta ne Mama ta kawo musu abinci tuwan dawa ne miyar ɗanyar kuɓewa tasha manshanu tare da nama, SOSAI Habeeb yaci abincin kasancewar sa mutum mai son Abincin gargajiya da la'asar lis Habeeb yasa yara suka shigo da kayan tsarabar da sukazo dashi, lami kuwa jin labarin zuwan Indo yasata zuwa gidan da la'asar ɗin tare da goyon ta a bayanta sosai Indo taji daɗin ganin aminiyar tata ƙawar tsokana, duban Lami Indo tayi tana cewa.
" Oh Lami kece haka, an daɗe ba'a gamu ba, wai ya na ganki da goyo ne, YARINYAR waye kika goyo.?"
Sauƙe goyon Lami tayi ta dawo da ita saman cinyar ta, tana duban Indo kafin tace.
" Ke Indo kinga kuwa yanda kikayi jawur dake, kinyi kyau, har wani ɗauke Ido kike, dubi fa yanda kika dawo wata ƴar gaye dake, sai kace ba wannan INDOn dana sani ba mai jiki duk dauɗa gaskiya ƙawata birni ya karɓe ki."
Tsuka Indo taja tana cewa.
" Bana son walaƙanci Lami ya kike tuno da Abunda ya riga ya wuce, kema fa kince birni kinga kuwa ai dole na sanja nidai tambayar ki nayi wannan ɗin ƴar waye ne.?"
" Ƴata ce wai baki san nayi Aure bane, to kinga bana shekara ta biyu da Aure, nayi zaton ai kinji labari."
" A'a banji labari ba wlh, yanzu wannan ƴarki ce Lami, ikon Allah nima fa yanzu da ammin Aure ko, ina su Hansai da Zainabu.?"
" Hansai ma tayi Aure shekaran jiya ma ta HAIHU tana can tsallaken ɗan masari, ita ma Zainabu tayi Aure amma ta dawo gida bata da lafiya wai Mayu sun kamata, ɗazun nan ma naje na gaishe ta, tana jin jiki gaskiya."
Ajiyar Zuciya Indo ta sauƙe tare da cewa.
" Ikon Allah dukkan ku da ƴaƴan ku, to Allah ya raya ita kuma Zainabu Allah ya bata Lafiya, yanzu dare yayi da munje mun gaishe ta, amma insha Allah gobe idan na fita zan biya na dubata."
Allah ya kaimu Lami ta furta sun juma suna hira kafin Lami ta koma gidan ta da sakaliyar la'asar Habeeb kuwa da daddare ya shigo cikin gidan ya zauna hira da Indo da Mama kasancewar shi Baba yana waje bai shigo ba, suna tsaka da hirar Tanimu yayi sallama ɗaure da buhu a kafaɗar sa, a gefe ya ajiye buhun yana sake wata sallamar jin kamar basu jisa ba, Habeeb da Mama ne suka amsa, Indo kuwa tashi tayi ta nufi Ya Tanimu da gudu ta faɗa jikin sa tana cewa.
" Oyoyo ya Tanimu sannu da dawowa tun ɗazu nake tsumayar dawowarka.?"
Murmushi Tanimu yayi yana girgiza kai tare da cewa.
" Oh ni Tanimu wato dai shi mai hali baya fasa halinsa, har yanzu dai kina nan da shiriritar ki, baki daina ba.?"
Tura bakinta Indo tayi tana cewa, kai ya Tanimu ka jika da wata magana, duk wannan hankalin da nayi shine zaka wani cemin shiriritacciya, wlh nayi Hankali, ko ya Habeeb.?"
Ta ƙarasa maganar tana kallon ya Habeeb murmushi sosai Habeeb yayi kafin yace.
" Ai kuwa yanzu Indo tayi cikakkiyar Hankali dan kuwa ba waccar Indo da ka sani a baya bane ta ƙauye wannan *INDON BIRNI CE* wacce Hankali da tunani ya wadace ta, kuma Mama ma ta shaida da hakan."
Dukan su dariya sukayi ya Tanimu ya shige ya ɗibi ruwa a bokiti ya shiga wanka, bayan ya fito ne ya zauna kusa dashi Mama ta kawo masa abincin sa, kafin suka shiga hiran yaushe gamo, Tanimu sosai yaji daɗin yanda yaga ƙanwar tasa fes da ita babu alamar wahala a tattare da ita sannan Abunda yafi masa daɗi ganin yanda Indo tayi sanyi hankali yazo jikin ta, sun juma