Showing 45001 words to 48000 words out of 53497 words

Chapter 16 - SO BAI SAN JINI BA HAUSA NOVELS BY UMMU NASMAH.txt

29 Oct 2025

456

da gaske kasan inda ɗan uwana yake, pls Daddy ka sanar dani yanzu naje na ɗauko sa dan Allah."


Murmushi Daddy Yayi yace.



" Yanzu babu wannan lokacin muje muyi Abunda yake gaban mu idan yaso idan mun dawo sai mu ƙarasa Maganar, yauwa matar gwamma Hajiya Hari zata zo ita da ƴan uwanta za suyiwa Indo jere acan ɗaya part ɗina na baya."


Ajiyar Zuciya Momy ta sauƙe kafin tace Allah ya dawo daku lafiya.


Daddy basu wani juma ba suka isa cikin ƙauyen DASINA a gidan INNA suka sauƙa harda amininsa Alhaji Ahmed mahaifin RAUDA, su Uku suka je tarba kuma ta mutunci aka musu Daddy da kansa ya miƙawa Baba da amininsa Baba Abubakar sadakin Indo Naira dubu hamsin.

misalin ƙarfe 2 na rana bayan an sauƙo daga Sallar juma'a aka shigo da goron ɗaurin Auren Indo cikin gidan nasu, Goggo Hali ce ta saka guɗa, tabbacin an ɗaura Aure, ai kuwa Indo tana jin wannan guɗar ta saka kuka sosai take kuka ganin da gaske ta rasa Mustafa a matsayin mijin Aure.



Kuyi hkr fan's ban samu nayi editing ba zaku haɗu da typing error.




*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻*


Ummu Nasmah ce
[5/11, 12:52 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*

Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya.

_________________________________________


*P*••••••2️⃣9️⃣ ↗️ 3️⃣0️⃣

Sosai ta bawa Zahra tausayi Tabbas rashin masoyi akwai zafi sai dai ya zatayi ƙaddara ta riga fata, babu yanda zasuyi tunda Allah ya rubuta cewa Habeeb shine mijinta ba Mustafa ba, cikin tashin murya Zahra tace.


" A'isha idan har kinyi imani da Allah da kuma ƙaddarar sa, to ya kamata ace kin Rungumi ƙaddara kin daina saka damuwa a zuciyarki, nasan akwai damuwa amma haƙuri zakiyi duk sanda ya taso miki ki dinga ambaton UBANGIJI, karki manta ko babu rabuwar rayuwa tsakanin ki da Mustafa to ki sani fa akwai ƙaddarar mutuwa, ko kuma idan ya mutu zaki bishi ne, yau ina INNA ta mutu duk son da kike yiwa Mustafa dole zaku rabu koba juma ko ba daɗe tunda akwai mutuwa, to meyasa ba zakiyi hkr ba yanzu ki godewa UBANGIJIN ki ki kuma Rungumi mijin da ya baki ki godewa UBANGIJIN ki A'isha domin kuwa ya miki ni'ima maɗaukakiya, tunda harya cireki daga cikin duhun jahilci ya haska ki a cikin hasken ilimi ta sanadiyyar fitar dake daga cikin wannan ƙauyen zuwa birni, ki godewa UBANGIJIN ki."


Jikin Indo yayi sanyi ƙalau sosai nasihar Zahra ya shiga jikin ta shuru tayi tare da goge hawayen ta, Abokanan wasa kuwa sai shigowa suke suna tsokanar ta, can wajen ƙarfe Uku Mama da Goggo Asabe suka saka Indo a cikin ɗaki sosai suke mata faɗa akan zaman Aure, Mama ce ta dubeta tace.


" Kiji tsoron Allah Indo ki yiwa mijinki biyyayah domin kuwa aljannar ki tana ƙarƙashin ƙafarsa, shi zaman Aure sai da haƙuri dole domin kuwa wahalar sa yafi daɗin sa yawa, duk abunda mijinki ya umarce ki dashi to kibi muddun bai sabawa UBANGIJI ba, ki sani cewa Rayuwar ki ta da babu Aure ba ɗaya bane da rayuwarki ta yanzu da igiyar Aure ya shiga ya zargeki, sannan kiso ƴan Uwansa tamkar yadda zaki so naki ƴan uwan, kiyiwa uwar mijinki biyyayah kamar yadda zaki min domin kuwa itace mahaifiya gareki yanzu."

Sosai mama ta mata nasihar haka Goggo Asabe ma, kafin daga bisani suka turata wajen Baba shima sosai ya mata nasa faɗan Zainabu da Hansai sai Lami suma dasu akayi wunin juma'ar, shima ya Tanimu ya mata nasa faɗan, koda sukazo tafiya birni mutum huɗu ne zasu raka Indo, Goggo Asabe da Goggo Hali sai Lami da Innawuro Mama bata bar ƴartata ta tafi haka ba sai da ta kaɗata da ƴan kayayyakin su na ƙauye, haka ma ta haɗa mata da kayan gara mai yawan gaske, Indo tana kuka suka rabu da Mama.

INDO har suka shiga motar aka tayar suka tafi bata saka Habeeb a cikin idanunta ba, hakan kuma ya mata zafi cikin ranta sai dai bata nuna hakan a zuciyarta ba har suka shiga cikin birni, part ɗin Momy aka sauƙe su, Indo ganin sun sauƙa part ɗin Momy sai da zuciyarta ta tsinke amma haka ta daure suka ƙarasa har cikin falon, su taradda Momy da Mamy sai ƙanwar Momy Aunty Zulai da kuma mahaifiyar Zahra, a wannan karon sosai Momy ta bawa kowa mamaki yadda ta saki ranta take fara'a tamkar tana son Auren da kanta Momy ta haura dasu bedroom ɗin Indo, abinci kuwa kala-kala aka shiga musu dashi tare da musu ban gajiya, Hasina kuwa ta bawa marar ɗa kunya domin kuwa zaka rantse da Allah ba itace akayiwa kishiya ba, mussaman ta zo part ɗin Momy ta tare su RAUDA kuwa tun safe tana ɗaki sai muƙurƙuso take yi sosai cikin ta yake mata ciwo, ko tashi bata iya yi, Hasina ce data lura da babu RAUDA ya sata zuwa part ɗin nata taga ko lafiya, ai kuwa cikin jini ta sameta cikin mawuyacin hali, da gudu tazo ta sanar da Momy halin da RAUDA take ciki, Momy batayi wata-wata ba ta ƙira Habeeb, cikin sauri aka saka RAUDA a cikin mota sai Hospital.

Koda isarsu Hospital ɗin RAUDA ta galabaita sosai, babu sunan wanda take kira sai Mustafa, Emagency aka shige da ita DARECT, harda Habeeb cikin masu duba RAUDA, binciken da sukayi shiya tabbatar musu da haihuwa ce sai dai bata da ƙarfin da zata iya haihuwa da kanta dole sai dai a mata c's Habeeb ne ya fito ya haɗa Uban gumi ya dubi Daddy tare da cewa.


" Daddy haihuwa ce sai dai bazata iya haihuwa da kanta ba dole sai an mata C's shine muke so ka saka mana hanu tunda shi Mustafa baya kusa."


Cikin sauri Daddy yace


" Habeeb meyasa sai ka sanar dani kaima zaka iya yanke ko wani hukunci akan RAUDA matar ɗan uwanka ne fah kaje kasa hanun a madadin ɗan uwanka, mudai burin mu ta sauƙa lafiya."


Ai kuwa da sauri Habeeb ya koma cikin, a cikin mintuna kaɗan aka gama komai na shirin Cs amma RAUDA taƙi fir a shiga da ita ɗakin tiyata,tace dole sai taga Mustafa kafin ta shiga, Habeeb ne ya fito ya sanar da Daddy yace Daddy ya shiga ya mata Magana ko zataji nasa, koda Daddy ya shiga da ƙyar RAUDA ta ɗago idanunta ta kalli Daddy tare da cewa.


" Ka taimake ni Daddy ka kira min ya Mustafa na gansa akwai Maganar da nake so muyi dashi kafin na shiga ɗakin nan, ka taimaka min Daddy naga mijina kafin na tafi."


Sosai ta bawa Daddy tausayi bai ce mata komai ba ya juya ya fito cikin sauri tare da cewa Habeeb su jirasa yana zuwa yanzu, Daddy motar sa ya hau da kansa ya tuka bai tsaya ko ina ba sai Abnur hotel, yana zuwa ya samu ma'aikatan hotel ɗin yace su duba masa waye ya kama ɗaki mai number 10 suna dubawa suka tabbatar masa da cewa Mustafa Harun shine wanda ya kama ɗakin, har ƙofar ɗakin Daddy yasa aka kaisa da kansa Daddy yayi Nocking, Allah ya taimaka lokacin Mustafa ba'a shaye yake ba, daga cikin ɗakin yace.


" Waye ne.?"


Cikin ƙula Daddy yace.


" Ubanka ne, nace Uban ka ne?"


Jin muryar Daddy yasa zuciyar Mustafa tsinkewa, da sauri yasa hanu ya buɗe bedroom ɗin, tunda ya buɗe bedroom ɗin Daddy yake binsa da kallo yanda yaga ɗan nasa gabaki ɗaya ya sauya ya fice hankalin sa, ga wani uban ƙasumba daya tara kafin Daddy ya maida dubansa ga bedroom ɗin kwalaben Shaye-Shaye ne birjik zube a cikin bedroom ɗin girgiza kansa Daddy Yayi tare da saka hanu ya ɗauke Mustafa da mari har Uku kafin yasa hanu ya figesa da ƙarfi, har cikin mota, jan motar Daddy yayi da mungun gudu har cikin Hospital ɗin, kafin ya ƙara jawo hanun Mustafa shidai Mustafa bin Daddy kawai yake cikin Ransa kuma yana ayyana waye a cikin asibiti, Momy Mamy Hasina Indo Goggo Asabe gabaki ɗayan su tashi sukayi suna kallon Daddy da Mustafa, Indo gani tayi gabaki ɗaya Mustafa ya sanja mata shima kuwa Indo yake bi da kallo har Daddy yayi cikin ɗakin da aka ajiye RAUDA kafin ya sakesa, gabaki ɗayan su su Momy suma shigowa sukayi ɗakin ƙwarai sun tausayawa halin da RAUDA take ciki Mustafa kuwa da sauri ya ƙarasa gabanta ya tsugunna cikin tashin hankali yake cewa.


" Me yake damunki RAUDA, meya sameki, kike kwance gadon asibiti.?"

Ya mata Tambayar cikin tashin hankali, murmushin farin ciki RAUDA tayi na ganin mijin nata, tana cije leɓenta yayin da take jin munguwar azaba daƙyar ta buɗe bakinta tace.


" Ya Mustafa kaine nake gani a gabana, ina kaje haka ka barni cikin tashin hankali, na shiga damuwa sosai na rashin ganin ka, kana lafiya ko ina kan babu abunda ya sameka.?"


Wani irin sanyi jiki Mustafa yayi, har kunya yaji gashi dai shi ya tafi ya barta bai taɓa tunanin ta a cikin zuciyarsa ba ko sau ɗaya, Allah Sarki ashe ita dashi take kwana take tashi, kama hanunta Mustafa yayi tare da saka ɗayan hanun nasa ya goge mata gumin da take haɗawa kafin yace.


" Kiyi RAUDA bada son raina na tafi na barki ba, ya zama min dole ne nayi nesa da ahalina domin samawa zuciyata sauƙin Abunda ke damunta ina mai baki haƙuri a karo na biyu daki yafe min.?"


Murmurshi tayi tare da kamo hanun nasa ta ɗaura a cikin ta, kafin tace.


" Kullum cikin yafiya nake gareka ban taɓa kwana ba tare dana yafe maka duk wani laifin da kamin ba, a yanzu nine nake buƙatar neman yafiyar ka domin kuwa ina ji a jikina cewa bazan fito daga ɗakin tiyatan nan ba da raina mutuwa zanyi ya Mustafa bazan tashi ba."


Kaɗawa idanun Mustafa yayi yayi jajur hankalin sa yayi mungun tashi, gabaki ɗaya mutanen dake tsaye a wajen babu wanda bai tausayawa RAUDA ba, Indo kam ma uwar ƴan saurin kuka, sai sharɓar kukan take, ta maƙale jikin Zahra, hankalin ta yayi mungun tashi, domin kuwa shigen Abunda INNA tayi kafin ta rasu shi rauda takeyi yanzu, Mustafa cikin tashin hankali yace.


" Bazaki mutu ba RAUDA bazaki mutu ba, ba tare da na nuna miki Soyayya ba da kulawa tare da tattali, A yanzu ina sonki ina sonki karki tafi ki barni ki tsaya mu raini ƴarmu tare karki tafi ki barta cikin maraicin rashin uwa."


Murmurshi sosai RAUDA take mai haɗe da hawaye tana shafa cikin nata kafin tace.


" Ƴata baza tayi maraicin rashin uwa ba, muddun HASINA da INDO suna raye na Tabbata bazasu bari tayi kukan rashi na ba, alƙawari ɗaya zaka min shine ka karka bari ƴata tayi kuka ina son ka nuna mata kulawar dani na rasa a wajen ka ko yanzu nayi farin ciki da furta min kalmar so, sannan na yafe maka kaima ka yafe min ina sonka MIJINA."


Ta ƙarasa maganar tana danƙe marar ta dake mata ciwo, duban Mamy tayi dake gefe tana rausar kuka tace.


" Ki daina kuka Mamy ki min addu'a sannan kice Daddy ya yafe min nima na yafe maku, ina sonki Mamy ki cewa kalit kar yayi kewata shima yamin addu'a, Momy kema ki yafe min kinji."

Gabaki ɗayan su kuka suka saka Mamy gagara Magana tayi tsabar kuka yaci ƙarfin ta, RAUDA hanunta ta ɗaga tayiwa Indo alamar tazo, da sauri Indo ta ƙarasa gabanta tana hawaye, cikin ƙarfin hali RAUDA tace.


" Ki yafe min nasan na miki kuskure a baya ina roƙon ki yafiya, sannan ga Amanar ƴata nasan ba lallai na samu damar ganinta ba bayan na haife ta ki riƙemin ita nasan zaki kula da rayuwar ta hanu ta miƙawa Indo alamun ta mata alƙawari."


INDO kuka ta fashe dashi kafin tasa hanunta cikin na RAUDA tace na miki alƙawari kuma na yafe miki, insha Allah ma zaki tashi zaki RAYU da ƴarki bazaki mutu ba."


Habeeb ganin da yayi Maganar RAUDA ba mai ƙarewa bane ya sashi tura gadon yayi tiyata room da ita, Mustafa da sauri yabi bayan su yana ajiyar Zuciya, tana kallon sa har aka shige da ita ɗakin Cs ɗin, jin gina Mustafa yayi a gefe sai famar ajiyar Zuciya yake sauƙewa, kowa dake wajen tsaye yake cikin tashin hankali, wajen awan su Huɗu da shiga Cs ɗin sannan Habeeb ya fito riƙe da jaririya a hanunsa jikin sa a matuƙar sanyaye, Indo ce ta tashi da sauri ta amshe jaririyar daga hanun Habeeb tana ƙare mata kallo, Mustafa cikin sauri ya k'arasa wajen Habeeb ba tare daya kalli jaririyar ba yana cewa.


" Ina RAUDA ina fatan tana cikin halin lafiya ko?"


Girgiza kansa Habeeb yayi tare da cewa.


" Sai dai muyi haƙuri domin kuwa RAUDA ta amsa kiran mahaliccin ta, Allah ya mata rasuwa."


Ja da baya Mustafa yake yana nuna Habeeb da hanu yana cewa.


" Ƙarya kake RAUDA bazata mutu ta barmu ba, nasan zata tsaya ta rayu damu bazata barni nayi biyu babu ba, nasan UBANGIJI na bazai rabani da masoyana duka biyu a lokaci ɗaya ba ya barni cikin kaɗaici ba, ka daina faɗa min wannan maganar."


Gabaki ɗayan su kuka suka saka, hankulan su yayi mungun tashi Daddy ne kawai yayi ƙarfin hali a cikin su ya ke kiran sunan UBANGIJI, turo RAUDA da akayi rufe da yadin tiyata, yasa Mustafa ƙarasawa da sauri ya yaye zanin, tana kwance fuskar ta rufe, sunkuyawa kanta yayi yana cewa.


" Nasan bacci kike, ki tashi ki faɗa musu su daina miki kuka ke baki mutu ba da ranki ki tashi ki gaya musu, bazaki tashi ki gaya musu ba, nasan bazaki tafi ki barni ni kaɗai ba.?"

Ganin da Daddy yayi Mustafa yana ƙoƙarin zaucewa ya sashi ƙarasowa gabansa tare da dafa sa yace.


" Wanda ya mutu bazai taɓa dawowa ba, ka dawo cikin hankalin ka, ka yiwa matar ka addu'a domin kuwa ta rigaka gidan gaskiya, ita da ta rigaka tafiya ba sauri tayi ba, haka kaima da kake nan bakayi jinkiri ba, duka a hanya ɗaya muke kowa jiranta yake, dan haka kayi tawakkali ga UBANGIJIN ka."


Tari Mustafa ya fara sosai yake tarin, yayin da jini kuwa sai bulbulowa yake daga bakinsa danƙe ƙirjin sa Mustafa yayi yana cigaba da tarin da sauri Momy ta karaso wajen ko kafin Momy ta iso ma tuni Mustafa ya yanki jiki ya faɗi ƙasa.

Kansa sukayo cikin kiɗima Indo kuwa ƙara fashewa tayi da kuka tana ƙanƙame da jaririyar a hanunta, ta ƙarasa wajen Mustafa tana cewa.


" INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJU'UN, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!! Dan Allah ya Mustafa ka tashi karka tafi ka barni ka tashi, Daddy kace masa ya tashi, Momy kina ganinsa ko ki tashesa Momy" ganin da tayi basa tanka ta ba yasata tashi ta riƙe hanun Habeeb tana cewa, " ka tashe shi ya Habeeb ka tashe shi tunda kai likita ne, idan ya mutu nima mutuwa zanyi dan Allah kuce masa ya tashi."


Wani irin mungun kallo Habeeb yake bin Indo dashi hanunsa yasa ya karɓi jaririyar ya miƙawa Momy ita, doctors ya kira suka kama Mustafa suka shiga dashi Emergency, duk ƙoƙarin likitotin na ganin Mustafa ya farfaɗo amma abun yaci tura, bincike suka duƙufa akansa na ganin sun gano meke damunsa, amma har aka kira sallar magaruba basu gano komai ba, sai dai sun saka masa oxgying tare wasu drug, yana kwance ne dai shi ba macacce ba shi ba rayayye ba.

Daddy ne yasa su dukan su su koma, gida, amma Indo fir taƙi yarda ta koma a cewar ta bazata iya tafiya tabar Mustafa a cikin wannan halin ba sanda Daddy ya mata jan ido sannan ta koma aka bar Momy da Habeeb tare da Mustafa, RAUDA kuwa mutuware aka shiga da ita Daddy yace sai gobe misalin ƙarfe goma za'a mata sallah a kaita makwancin ta (Allahu Akbar rai baƙon duniya yau dai ga RAUDA ta tafi gidan ta na gaskiya)


Mamy bata koma gidan ta ba gidan Momy ta wuce tana kuka mai cin rai sai yanzu take nadamar watsar da RAUDA da tayi tunda tayi Aure Abban ta ma an sanar dashi sosai shima yaji bakin cikin rashin ƴarta sa, sai dai shi yayi tawakkali, Indo kuwa kuka take tsakanin ta da Allah anyi rarrashin duniya taƙi shuru, idanunta har sun kunbura, cikin ƙanƙanin lokaci mutuwar RAUDA ta zagaye dangi kota ina zuwa ake.

Babu wanda baiji mutuwar RAUDA ba, Ranar Indo kwana tayi tana kuka kusan ma dai zance duka gidan babu wanda ya RUNTSA Habeeb madarar yara ya siyowa jaririyar shi aka kwana ana bata, yarinyar kuwa kyakkyawa sak uwar ta babu inda tabar RAUDA sai fari da tafi RAUDA kasancewar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login