Showing 30001 words to 33000 words out of 53497 words

Chapter 11 - SO BAI SAN JINI BA HAUSA NOVELS BY UMMU NASMAH.txt

29 Oct 2025

468

ya saka wayar Kamal ce masa yayi.

" Okey jira ni yanzu akwai maganin bacci wanda zai saka bacci yanzu kuwa bari na bayar a kawo maka yanzu."

Komawa gefe yayi yana kallon safiya kafin yace Mata.

" Lokacin ki zai fara daga yanzu, tashi kije ki karbi Coca-Cola ki karɓi kwaya wajen John ki wurga masa a ciki, daga can kya taya sa kwana ni na jawo Serah mu ƙarasa daren."

Tashi Safiya tayi tana murmurshi domin kuwa ta samu damar rama Abunda ya mata ɗazu rigarta taja wata ƴar firit wacce da ita da babu duk ɗaya tasa, wajen John ta tsaya ta karɓi cock da ƙwayar maye, ƙara tambayar sa tayi ya bata na Feeling (sha'awa) ɗaukowa yayi ya bata, karɓa tayi tare da ɓalle murfin Cock ɗin ta watsa ƙwayar a ciki girgizawa tayi sannan ta mayar ta rufe, kwankwasa ɗakin da yake tayi, Mustafa dake zaune zaman jiran Kamal ya tashi cikin sauri ya buɗe ƙofar tsaye ya ganta gabansa tana sauke masa wani Shu'umin murmurshi, kauda kansa yayi gefe tare da Cewa.

" Meya kawo ki nan ɗakin na kira ki ne.?"

Murmushi kawai tayi ba tare da ta ce masa komai ba, tasa kanta ta wuce cikin ɗakin tare da ajiye masa cock ɗin a saman tebur, hanunta tasa ta ɗauke key ɗin ɗakin da yake kan tebur ɗin ta danƙesa a hanunta yanda bazai taɓa lura dashi ba, ficewa tayi daga cikin ɗakin Still tana sakin murmurshi, tsuka yaja tare da rufe ƙofar ya sa mata kuba, sannan ya wuce ya ɗauki Cock ɗin bai kawo komai cikin ransa ba ya ɓalle murfin tare da kafasa a bakin sa, bai sauƙe ba sanda yaji babu komai ya ƙare sannan yayi wurgi da gorar, yana kwanciya rigingine ya kafawa slim ɗin ɗakin Ido, mintuna kaɗan maganin suka fara aiki a jikin sa, gabaki ɗaya ɗakin juya masa yake, komai bibbiyu yake kallon sa, ga wani bala'in Feeling da yake taso masa babu abunda yake buƙata Irin yaji mace a jikin sa, wani irin tashin hankali ya shiga, ita kuwa Safiya sanda ta daidaici time ɗin da maganin yayi nisa a jikinsa sannan tasa key ɗin ta buɗe shiga tayi tare da rufe ƙofar, faɗawa tayi jikin sa, shi kuwa kamar wanda yake jira ya kanƙameta domin kuwa babu Hankali a jikinsa, Haɗa bakinsu sukayi waje ɗaya, sun juma suna rommace ɗin junansu kafin daga baya salon nasu ya sanja.

(Wa'iyazubillah Allah ka raba mu da sharrin HATSABIBIYAR mace da mungun Aboki)

Sanda suka gama aikata masha'arsu kafin ya gangara gefe yana sauƙe ajiyar Zuciya a haka bacci mai nauyin gaske ya ɗauke sa, kallo Safiya take binsa dashi tana murmurshi tare da shafo gashin ƙirjinsa tana son gayen cikin zuciyarta sai miskili ne na ajin farko, sanda ta gama saƙe saƙen ta sannan ta dirƙo daga gadon tollet ta shiga tayi wanka sannan ta fito tare da maida kayan ta ta fice tana murmurshi.

Mustafa shine bai farka ba sai ƙarfe 12:00 na rana da salati a bakinsa ya buɗe idanunsa yana ƙarewa agogon ɗakin kallo da sauri ya tashi yana cewa.

" Subhanallah 12:00 wani irin bacci nayi haka oh my maganin da wannan ɗan Iskan ya bani, mema ya sani karɓa ne, oh shart duk *SHATUU* kece kika jawo min zuwa Wannan wajen harta kaini ga kwana" dafe goshin sa yayi yana tariyo Abunda ya faru dashi daren jiya tiryan-tiryan yake dawo Masa mussaman Abunda suka aikata da Safiyya wasu xafafan hawaye ne suka gangaro daga cikin idanunsa tunda yake a rayuwarsa bai taɓa kusantar Zina ba, sai gashi rana tsaka ya afka cikin ta, lallai wannan YARINYAR sheɗaniya ce, sai dai ba kowa bane ya jawo min wannan masifar sai *SHATUU da HABEEB* duk sune suka jefa ni cikin wannan halakar, "innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, Astagfurullah Allah na tuba ka yafen badan hali na ba, Allah ka yafe min ban aikata maka wannan zunubin da niyya ba, Allah kaga zuciyata nafi kowa kyamatar Zina sai gashi yau ƙaddara tasa na afka cikin ta, ya Ubangiji nasan ni mai laifi ne a wajen ka Allah ka yafe min." Cikin hawaye yake Maganar tashi yayi ya wuce tollet yayi wankan tsarki tare da wanka ya maida kayan jikinsa ya fito a zuciye Allah kawai yake roƙo ya haɗasa da Kamal da Safiyya shi kaɗai yasan kalar walaƙancin da zai musu, sai kash kafin Mustafa ya fito tuni Kamal ya kama gabansa, dube-dube Mustafa yake ta ina zai hango su, ita kawai ya hango jikin wani mutumin daban ba Kamal ba, girgiza kansa Mustafa Yayi a fili ya furta. *ƳAR AKUYA KENAN MAI BIN DUK WANI BUNSURU* nufar wajen nata yayi a zuciye, yana zuwa ya sauƙe mata kyakkyawan mari mai lafiya, gabaki ɗaya jama'ar wajen dawo da hankalin su sukayi wajen su, cike da mamaki, riƙe kumatun ta tayi tana kallon sa, wanda take jikinsa ne shima ya tashi cikin zuciya yana nuna Mustafa da yatsa yace.

" Waye kai da zaka zo har nan ka mari Sofy kasan waye ni kuwa da zaka mareta a gabana, Lallai kayi kuskure."

Murmushi mustafa yayi yana ƙare masa kallo tare da kamo yatsar da yake nuna masan ya murɗeta da ƙarfi har sai da ya danna ƙara sannan Mustafa yace.


" Bansan waye kai ba kuma bana buƙatar sanin hakan Bunsuru ɗan AKUYA kawai, kuskure kuwa kaine wanda ka tafka sa da kayi kuskuren nuna min yatsa domin kuwa ba'a min haka, ka bari tukunna banzo kanka ba da wannan Akuyar idan nazo idan yaso sai ka isar min da saƙon naka, yanzu dai kaje ka fara jinyar yatsar ka tukunna dan ina da tabbacin ta karye" ya sake masa yatsar yana ƙara ɗauke Safiyya da mari tare da jideta ta faɗi kasa belt ɗin jikinsa ya zare ya hau zabga mata, ihu Safiyya take sosai sai dai abun takaici an rasa mai kwatarta a hanunsa domin kuwa ga baki ɗaya wajen shakkar Mustafa suke sanda ya tabbatar tayi lilis yanda dakyar take motsi sannan ya ƙyaleta nuna ta yayi da yatsa yana cewa.

" Gobe ki ƙara kwatantawa wani makamancin Abunda kika min, banza daƙiƙiya ballagaza jaka cikon lissafi kekam wlh iyayenki sunyi asarar haihuwar ki, dubi yanda kika maida bariki sana'a kika watsar da rayuwarki, bisa titi, kika sayar da mutuncin ki, kika kasa jikinki a kasuwa, da wanda yakai da wanda bai kaiba ma yazo ya saya, kiji tsoron Allah ki yiwa Rayuwar ki karatun ta nutsu ki tuba zuwa ga UBANGIJIN ki kafin lokaci ya ƙure miki, kizo kina munguwar nadamar da bata da Amfani." Yana gama faɗin haka ya juya ya fice daga cikin club ɗin motar sa ya hau yana tunanin wani hali RAUDA ta shiga ganin bai kwana a gida ba, harya ɗauki hanyar gidan sai kuma yayi ribas ya karya hancin motar ya harba zuwa makarantar su *INDO* domin kuwa yasan yanzu tana can ta daɗe da tsufa a can.


" Allah Zarah yau pro Sani ya bani dariya, shi fa tsakanin sa da Allah yake son sai munje Delta practical ɗin nan."

" Ke ya bawa dariya ko ni kuma wai iya mata mu goma zamu, idan akwai gaskiya mai zai hana a saka da maza cikin tafiyar, nikam ma gashi daman ya daɗe yana kaimin hari mayen Mata"

INDO ta ƙarasa maganar tana dariya har tana dafa Zarah, ya daɗe tsaye cikin motar yana kallon yanda take walwala abunta har da dariya ita ko a jikinta, shi ta bari cikin wahala da damuwa fitowa yayi daga cikin motar ya nufe ta, ko Sallama bai mata ba ya tsaya a kanta yace.

" Tashi mu tafi."

Murmushi Indo tayi cikin jin daɗin ganinsa dama tun jiya take ƙaunar ganin halin da yake ciki, sam Hankalin ta baya kwance, ƙin dago kai tayi ta kallesa bare yasa ran zata tashi, cikin ƙula da halin ko inkula data nuna masa cikin tsawa yace.

" ba dake nake Magana bane kinyi banza dani!!"

Har yanzu Indo bata ce masa komai ba kuma bata da niyar tashi, iya ƙula Mustafa ya ƙula ransa idan yayi dubu to ya ɓaci, Zahra ce ta dubeta tace.

" Haba kawata ya mutum yana miki Magana kina ji kinyi shuru, ki tashi kije kiji mai zai faɗin miki."

Duban Zahra tayi tace.

" Me zance masa sannan me zai sanar dani, duk abunda zai faɗa ya faɗesa a nan badai kunne na bane yake jin Magana sai ya faɗa ai idan ina da amsar Maganar sa na basa idan kuma babu sai yayi hkr, babu wata alaƙa yanzu tsakanina dakai daya wuce na ƴan uwantaka, meyasa bazai gane haka bane, ki sanar dashi Zahra dan Allah yayi hkr ya kyale ni, na riga da na fidda mijin da zan Aura."

Sam Zarah bata ji daɗin Abunda Indo ta yiwa Mustafa ba, buɗe baki tayi tace.

" Amma dai ya kamata kije ki sauraresa koma menene yake tsakanin ku bai kamata ki wulaƙanta sa ba karki manta da ɗan uwanki ne koda babu alaƙar Soyayya tsakanin ku."

Idonsa sun rufe tsabar ɓacin a yanzu ya fara tunanin da gaske zai iya rasa, ya kuma san rasata tamkar rasa Rayuwar sa ne, duba yake Binta dashi kafin ya durƙusa a gabanta yana dubanta da idanunsa da sukayi ja yace.

" Gani durƙushe gabanki ina mai neman afuwar ki, na tuba nasan tabbas na miki laifi a baya, na kuma amshi kuskurena, ki taimake ni karki gujeni, Wlh kece Rayuwata rasaki tamkar rasa numfashina ne, ki taimakeni karki Auri wani ba niba Wlh ina sonki fiye da yanda nake son Rayuwata, ki taimake ni karki Auri wani ba niba nasan mutuwa zanyi muddun na rasaki."


Ga baki daya jikin su yayi sanyi mussaman Indo wani irin tausayin sa take ji, sam Zuciyarta bata mata daɗi ba ganinsa a cikin wani mawuyacin hali, amma duk da haka sai ta daure zuciyarta ta ɗago cikin ƙarfin gwiwwa tace masa.

" Ƙarya kake ya Mustafa baka sona da kana sona da baka wulaƙanta ni ba, da kana sona da baka kyamace niba da kana sona da baka dokeni ba. Shi Wannan ɗin duka a cikin Soyayya ce, baka taɓa nuna min hanya mai kyau ba duk kaucewar da nayi baka taɓa ajiyeni ka nuna min cewa ga inda zanbi rayuwata tayi kyau ba, baka taɓa ɗaukata a matsayin mutum sai ma dangana ni kake da suffar aljanu da dabbobi, idan ban manta ba akwai sanda ka ce min ( Allah ya sauwaƙa naso ƙazama Irin ki kazamar ƙauye, waima tukunna waye zai miki kiss da waɗannan yellow haƙwaran naki ɓace min da gani kafin na targaɗaki, mahaukaciya kawai marar lissafi, amma dai Wlh Allah ya isa tsakanina dake, ki rasa waye zaki ce kina so sai ni, to Wlh Allah ya isa kin cuceni) ka kuma cemin.

( Nidai wannan YARINYAR ta zamo min masifa duk randa zanzo ƙauyen Nan, da tsinkewar Zuciya nake zuwa, tunda nasan zan haɗu da bala'i)

Kayi tunanin duk na manta da waɗannan maganganun naka ne, to yanzu kuma me zakayi da ƙaramar ƙauye mahaukaciya mai yellow haƙori marar lissafi wacce ka yiwa Allah ya isa, ka kirani da macuciya ka kirani da masifa da bala'i wanda har na zamo tsinkewar Zuciyar ka duk kawai dan nace ina sonka, meye laifina a nan ka faɗa min meye laifin Zuciyata dan ta ce kaine take so sai dai alhamdulillah ko yanzu na godewa Allah daya cire min Soyayyar ka cikin zuciyata, kaje ka riƙe matar ka ina ga hakan zaifi maka, nikam na riga da na yankewa kaina hukunci bana ƙaunar ka a yanzu."

Ta ƙarasa maganar cikin zubar hawaye da rawar Murya, kallon tausayi Zarah take binsu dashi Tabbas tasan suna son junan su har gobe, sai dai ƙaddara ta gifta tsakanin su, wanda har ta kaisu ga rasa Aure tsakanin su, Tabbas wannan shi ake kira *SO BAI SAN JINI BA* domin kuwa da yasan jini bazai taɓa shiga zuciyoyin waɗannan ƴan uwa biyun ba, gashi har yana son shiga tsakanin *ZUMUNCIN SU* Shi kuwa Mustafa cikin mungun tashin hankali yake duban ta, jin maganganun da take tuna masa shi harga Allah ya manta ma da wannan maganar da take tuno masa sanda ta faɗa masa sannan ya tuna dashi ashe ita tana sane da shi cikin zuciyarta, Tabbas ya tafka babban kuskure, dubanta yayi tare da cewa.

" Tabbas na aikata miki kuskure wai yawa na amshi laifi na, ina mai baki haƙuri da ki yafe min dan Allah komai ya wuce ki ceci Rayuwata karni bari Rayuwata ta lalace ta sanadin Soyayyar ki."

Murmushi Indo Tayi mai cin rai kafin tace.


" Lokaci ya riga daya ƙure maka domin kuwa nima bazan yarda nayi sanadin shigar wanda ya taimaki rayuwata ba ta lalace sanadin Soyayya ta, kayi hkr ka cire Soyayyata cikin ranka domin kuwa ba kai nake so ba ɗan uwanka nake so *YA HABEEB* shine zaɓin Rayuwata shine wanda ya cancanci nayi rayuwa dashi ba kai ba ka cire Soyayyata cikin ranka ko karka cire wannan damuwar kane ba tawa ba, domin kuwa son maso wani kake."

Tana gama faɗin haka ta tashi tabar wajen cikin sauri jin kuka yana neman kwace mata Soyayyar sa yana son karya mata zuciya yasa har tausayin sa yasa ta kauce layi ta hanyar yiwa Habeeb butulci, kuma Abunda bazata taɓa yadda ya faru ba kenan.

Runtse idonsa yayi cikin jin Zafin maganganun ta, wani irin ƙuna Zuciyar sa take masa, baisan ya zaiyi SHATUU ta fahimce sa ba, ta kasa gane kalar Soyayyar da yake mata, tausayin sa sosai Zahra taji, dubansa tayi tace.

" Kayi hkr Mustafa na fahimce halin da kake ciki, ka daurewa Zuciyarka, ka cireta cikin ranka tunda kaga har iyaye sun yanke hukunci, nasan irin zafin da kake ji amma ya zakayi ƙaddara ta riga fata."

Tashi yayi tsaye ba tare da cewa Zarah komai ba ya shige cikin motarsa yana layi, girgiza kanta Zahra tayi sannan itama ta tashi tabi bayan INDO, a Class ta sameta ta kifa kanta jikin kujera sai Rusar kuka take zama Zarah tayi tare da dafa kafaɗar ta tace.

" Meye amfanin kukan? karfa ki sawa zuciyarki wani ciwo."

Ɗago kanta tayi idanunta sunyi jajur tace.


" Dole nayi kuka Zarah na rasa farin ciki na, gashi yana cikin wani mawuyacin hali, bana son ganinsa cikin damuwa Zahra ina son Ya mustafa bana son ganinsa cikin damuwa."

" Idan ma kina sonsa ya kika iya tunda dai ƙaddara ta riga fata Daddy ya riga ya yanke hukunci, meye aibun Habeeb da kika kasa sonsa, meye banbancin Habeeb da Mustafa, basu da wani banbanci koda kuwa ta kama ce, kawai ki kalli Habeeb a matsayin shine Mustafa wala Allah zaki samu sassauci a cikin zuciyarki."

" Ba zaki taɓa ganewa ba Zarah, ke bakya ganin banbancin su amma ni ina gani suna banbanci sosai, ki daina furta min kalmar na manta dashi bazan taɓa iya mantawa da ya Mustafa ba CIKIN RAYUWATA, ni kaɗai nasan Abunda nake ji akansa."

Shuru Zahra tayi bata ƙara cewa Indo komai ba haka itama Indo har suka gama lectures suka tashi jikin Indo a mace yake murus tana tunanin wani Hali mustapha yake ciki.


Bayan yayi parking ne a harabar gidan sannan ya fito ya dumfari part ɗin Habeeb yana huci kamar mayunwacin zaki babu ko Sallama ya faɗa falon Habeeb yana kwance bisa cinyar HASINA sukaji tsayuwar mutum a kansu da sauri suka ɗago idanunsu Mustafa ne suka gani tsaye, tashi Habeeb yayi ya zauna yana kallon Mustafa domin kuwa yasan ba Alkairi bane ya kawo sa, cikin sakin fuska yace.

" Bros kaine bismillah ka Zauna mana kana tsaye.?"

Wani irin mungun kallo Mustafa yake bin Habeeb dashi kafin yace.


" Hmm!! Kana TUNANIN cewa akwai Abunda zai kawo ni ɗakin maci Amana irin ka har na samu wajen Zama Allah ya sauwaƙa ko yanzu ina jin takaici da baƙin cikin kasancewar ka ɗan uwa a gare ni, da ace ina da ikon sanja ƙaddara to Tabbas da saina cireka daga sahun alhalin mu."


Sa ke baki Hasina tayi tana kallon sa domin kuwa Abunda bata taɓa gani ba kenan tashin hankali tsakanin su ikon Allah kawai ta tsaya kallo shi kuwa Habeeb runtse idonsa yayi yana jin Zafin maganganun ɗan uwan nasa, cigaba da cigaba da cewa Mustafa Yayi.


" Nazo ne na sanarda kai cewa kayi gaggawan fita a harkar SHATUU domin kuwa SHATUU mallaki nace, idan kuma kaƙi to Wlh ka guji Abunda zai biyo baya dan bana tunanin zai maka kyau, maha'inci maci Amana dubeka ko kunya baka ji kana son BUDURWAR ɗan uwan ka, na dai sanar da kai ka fice daga harkar ta *IDAN KUNNE YAJI JIKI YA TSIRA*." Yana gama faɗin haka ya fice ba tare da ya saurari abinda Habeeb zai faɗa ba.

Harya fice Hasina na binsa da kallon mamaki, kafin ta maida dubanta ga mijinta tare da jefa masa tambaya.

" Meya haɗaka da ɗan uwanka, waye kuma SHATUU, naga ya Mustafa a fusace yana faɗin magana marassa daɗin sauraro pls meya shiga tsakanin ku.?"

Ta ƙarasa maganar tana kallon idonsa, ajiyar Zuciya Habeeb ya sauƙe tare da cewa.

" Soyayya itace ta shiga tsakanina da ɗan uwana, ba wata dabam bace SHATUU INDO ce haka yake kiranta dashi, tabbas maganganun sa babu daɗin ji, amma nasan ɓacin raine ya jawo yamin haka karki damu komai zai wuce."

" Idan har na fahimce ka dai-dai INDO kuke so dukanku, sannan kuna shirin wargaza zumuncin ku saboda Soyayya koh, yaushe ka fara son ƙanwarmu Indo, ban taɓa jin labarin ba, kuma baka taɓa nuna min ba ko a fuskar ka, wata ƙila zan kawo maka matsala ne cikin Soyayyar ku ko, meyasa ƙaddara ta haɗaku son abu ɗaya bayan tasan ƙarfin alaƙar jinin ku tabbas ƙaddara bata muku adalci ba, da ta zukatan *JINI ƊAYA* masu ƙaunar junan su meyasa so zai muku haka.?"

Ta ƙarasa maganar ba tare ta nuna masa tasan Maganar ba zuciyarta kuma tayi sanyi, shuru yayi yana matukar jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login