Showing 9001 words to 12000 words out of 53497 words

Chapter 4 - SO BAI SAN JINI BA HAUSA NOVELS BY UMMU NASMAH.txt

29 Oct 2025

465

son Indo komai yake neman sauyawa cikin gidan ta mussaman farin cikin mijinta, tasan wannan fushin nasa yana da alaƙa da Indo tunda daga gidan su yake Kuma tasan Indo tana cikin gidan.

" Ya Allah ka dawo min da farin cikin gida na, dole na sanar da Indo Soyayyar da mijina yake mata, ko zai samu SASSAUCIN CIWON DAKE CIKIN ZUCIYAR SA wannan itace kaɗai mafitar da nake dashi.

Mustafa kuwa bedroom ɗinsa ya shige ya hau fashe fashe komai na glass dake cikin ɗakin Mustafa sai da ya fasa tamkar mahaukaci ya dawo yana maganganu.

" Akan me zaki ƙaryata Soyayyata akan me zaki ce bakya sona why! *SHATUU* so kike ki tarwatsa Zuciyata meyasa zaki hukuntani da hukunci mafi muni pls *SHATUU* karki zalunci Rayuwata nasan kina sona to meyasa yanzu zaki ce soyayya ta ƙarya ce"

Tamkar mahaukacin zaki haka Mustafa ya dawo RAUDA jin ƙarar fashe-fashe da tayi shi yasa ta nufo bedroom ɗin nasa da gudu hanunsa duk ya yanke sai zubar da jini yake da sauri ta riƙe hanun nasa tana cewa.

" Subhanallah ya Mustafa lafiya meya sameka kaida waye kaga hanunka yanda yake jini?"

Mustafa fuskar Indo yake kallon RAUDA gani yake kamar itace a gaban sa hatta muryar RAUDA ta Indo ta koma masa, Rungume ta yayi da sauri yana sauƙe ajiyar Zuciya, a hankali ya soma Magana.

" Please karki ƙara cewa bakya sona, karki barni dan Allah mutuwa zanyi idan kika ƙyale ni, ina sonki kece Rayuwata." Ya ƙarasa maganar suna zubewa saman bed, wani mungun daɗi ne ya tsargawa RAUDA yau Mustafa ne ya furta mata cewa itace rayuwar sa, ƙara ƙanƙamesa tayi tana jin wani farin ciki.

" Bakin sa Mustafa ya haɗa dana RAUDA, shi duk a haukar sa Indo ce gabansa, wani hot kiss yake mata tare da nasarar capko harcen ta, sosai yake wasa da sassan jikinta daman ya lafiyar kura bare kuma ta samu nama ita kuwa RAUDA sai wani irin miƙar daɗi take yi cikin hikima da Nasara ya samu damar rabata da suturar jikinta shima yayi fillo da nasa ƙasa RAUDA bata fara dawowa hankalin ta ba saida ta fara jin zafi ta ƙasanta, sannan ne ta fara neman zamewa amma ina Mustafa yayi nisa baya jin ƙira duk kukan RAUDA da yakushin ta Mustafa bai ƙyaleta ba sai ma cewa da yake.

" Ina sonki SHATUU dan Allah karki rabu dani wallahi mutuwa zanyi idan babu ke cikin rayuwata ina SONKI SHATUU na, tun sanda kike Dasina har zuwa yanzu da nake tare dake."

Wani irin baƙin ciki ne ya doki zuciyar RAUDA mijinta ne yake saduwa da ita yake kiran sunan wata yunƙura tayi da ƙarfi tana kuka zata ƙwaci jikinta daga nasa amma ina Mustafa yafi ƙarfin ta, duk ihun RAUDA saida Mustafa yasha romonta bai ƙyaleta ba sai da ya gaji dan kansa sannan ya mirgina gefe yana lumshe idanunsa, RAUDA kuwa kuka kawai take na baƙin ciki ga wani irin mungun zogi da ƙasanta yake mata.....



*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*



*(Ummu Nasmah ce)*
[4/4, 10:09 PM] Ummu Nasmah: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CaoZrO2pfJ99s0CxBTC5RW


💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*Ga mai buƙatar wannan group ɗin sai yayi joining amma group ɗina yana da dokoki zan faɗo muku dokokin a ƙarshen page ɗin nan.*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*•••••9️⃣ ↗️ 1️⃣0️⃣

Lumshe idonsa yayi tare da jawota jikinsa ya ƙanƙameta yana rufe su da blanket, har yanzu RAUDA bata daina shashsheƙar kuka ba, ta kuma kwanta lamo a ƙirjinsa a haka bacci mai nauyi yayi gaba da Mustafa RAUDA kuwa idanunta da suka kaɗa sukayi jajur ta ɗago tana ƙarewa Mustafa kallo tabbas tana son mijinta sai dai sam shi bata cikin rayuwarsa, hanunta ta kai ta shafo fuskarsa tana furta cewa.

" Bani da wani aibin da zaka ƙini, kullum tunani nake menene aibina da zaka tsaneni haka, laifi na shine kawai danna soka na aureka meyasa kake ambaton sunan Indo bayan dani kake tarayya a wannan lokacin wannan shine daren farko na dakai sai dai gashi yazo min da ƙalubale a cikin sa kaicona ni RAUDA da na biyewa son zuciyata Gashi yanzu ina cikin tsaka mai wuya."

Ta ƙarasa maganar tana ƙara sakin kuka mai ban tausayi duk abunda take Mustafa bai san tana yiba baccin sa yake hankali kwance a haka itama bacci ɓarawo ya saceta, ƙiran sallar asubar farko a kunnen Mustafa a hankali ya buɗe idanunsa ya akan RAUDA ya sauƙe su ƙara ware idanunsa yayi yana mamakin meya kawo RAUDA bedroom ɗinsa har kuma saman ƙirjinsa, dafa kansa yayi zuciyarsa na tariyo masa Abunda ya faru tsakanin su tiryan-tiryan.

" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!" Ya furta tuno Abunda ya shiga tsakanin su, shikenan Abunda baya so ya kasance tsakanin sa da RAUDA ya faru yaso adana maitar sa har zuwa Ranar da Allah zai mallaka masa Indo a matsayin matar sa ta Sunnah yaso ace da ita ya fara sanin wata mace a duniya sai gashi lokaci ɗaya RAUDA ta wargaza masa tanadin daya daɗe yana yiwa *SHATUUN SA* duban sa ya ƙara kaiwa gareta Baccin ta take ganan bushashshan hawaye kuma kwance a fuskar ta, haka kawai kuma sai yaji ta basa tausayi domin shi kansa yasan tasha wahala daren jiya, a hankali ya zameta daga ƙirjinsa ya mayar mata da kanta bisa filo, tashi yayi ya shige tollet hanunsa daya yanke ya ɗauki hankicin ɗinsa ya ɗaure hanun, wankan tsarki ya fara kafin yayi wanka, ruwa mai zafi ya haɗawa RAUDA kafin ya fito ɗaure da towel ya fice daga bedroom ɗin kitchen ya nufa ya ɗebo gishiri kaɗan ya dawo bedroom ɗin tollet ɗin ya ƙara shiga ya zuba gishirin a ruwan zafin kafin ya dawo ya zauna bakin bed ɗin a hankali yake tashinta ta hanyar dukan kafarta buɗe idonta RAUDA tayi takai dubanta ga Mustafa kafin tayi saurin sauƙe kanta ƙasa tana mai jin kunyarsa, taɓe bakin sa Mustafa Yayi kafin yace.

" Ki tashi ki shiga tollet ki samu ki gasa jikinki na haɗa miki ruwan zafi" yana faɗa ne tare da kawar da kansa gefe.

Ƙoƙarin tashi RAUDA tayi tana rufe jikinta da blanket ɗin, taji wani mungun zafi a ƙasanta Wash ta furta da ƙarfi ta koma ta zauna cikin sauri tana cije leɓenta sai kuma hawaye shar, duk abunda take Mustafa yana kallon ta ta ƙasan ido tashi yayi yazo har gabanta bata ankara ba taji mutum ya ɗagata caɗak tare da wurgi da blanket ɗin gefe, rufe idonta RAUDA tayi cikin jin kunyar babu komai a jikinta, tollet yayi da ita, a cikin ruwan ya ajiye ta, ai kuwa RAUDA wani azabar zafi taji ƙara tasa tare da ƙoƙarin miƙewa daga cikin ruwan, hanunsa Mustafa yasa ya danneta a cikin ruwan cije leɓenta tayi tare da runtse idonta tana jin azaba sunfi 20 minute a haka kafin Mustafa ya saketa ƙanƙame jikinta RAUDA tayi cikin takura domin tana mungun jin kunyar ganinta da Mustafa yake a haka babu komai jikinta, taɓe bakin sa yayi yace

" Wani dare ne jemage bai gani ba kuma ai saidai daren mutuwar sa, idan kin so kiyi wankan tsarki idan kinso kuma karkiyi wannan ruwanki ne ganan towel a sama" yana gama faɗin haka ya fice daga tollet ɗin.

Binshi kawai da kallo RAUDA tayi tana ƙara sakin jikinta cikin ruwan domin yanzu ruwan ya daina mata zafi sai daɗin sa da take ji, ta juma cikin ruwan kafin tayi wankan tsarki tare da wanka ta fito ɗaure da towel ta ɗaura ɗaya kuma a kanta tana bin bango da ƙyar ta iso tsakiyar ɗakin, bata ganshi ba cikin ɗakin sai towel ɗin da ya cire ya rataye jikin drower agogon bangon ɗakin ta ɗaga kai ta kalla 5:15 hakanne ya tabbatar mata da sallah ya fita kayanta ta ɗauka ta fice tana bin bango harta samu tayi nata bedroom ɗin gadon ta ta faɗa ta kwanta tare da runtse idonta tana jin wani mungun bacci, a haka kuma baccin ya sace ta.

Mustafa kuwa bayan sun idar da sallah ne ya hango Habeeb Zaune can gefen masallaci yayi shuru yana tunani, kusa dashi Mustafa yazo ya zauna har ya zauna Habeeb baisan yazo ba dafa kafaɗar sa Mustafa Yayi, firgit Habeeb ya ɗago kansa ya kalli Mustafa yana sauƙe ajiyar Zuciya duban sa Mustafa Yayi yace.

" Bros meyake damunka haka tunanin me kake har nazo na zauna kusa da kai baka sani ba, ga kuma idonka yayi Red sosai meke damunka?"

Mustafa ya masa tambayar cikin tashin hankali domin kuwa ya tsani ganin ɗan uwansa cikin mungun yanayi ya gwammace ace shine yake ciki ba ɗan uwansa ba, Habeeb ɗago kansa yayi yana duban ɗan uwansa ji yake cikin zuciyarsa kamar ya sanar da ɗan uwansa Soyayyar Indo ce take neman zauta shi sai kuma ya tuno maganganun ɗan uwan nasa game da Indo inda yake cewa *( Nine Wanda ya dace da Indo ba Umar ba, nine Wanda na juma da ajiyar Soyayyar ta cikin zuciyata tun kafin takai ga wannan matakin Aunty Hindu SHATUU BUGUN NUMFASHI NANE INA SONTA FIYE YANDA NAKE SON KAINA HAKA KUMA INA DA TABBACIN CEWA ITAMA TANA SONA TUN TANA ƘARAMAR TA)* Runtse idonsa yayi yana jin wani mungun nauyi cikin ƙirjinsa bazai iya furtawa ɗan uwansa cewa ciwo ɗaya ke damunsu ba baisan wani hali ɗan uwansa zai shiga ba idan yaji damuwar sa, Mustafa dafa kafaɗar Habeeb yayi yace.

" Tunanin me kake haka Bros please tell me Hankali na ya tashi ka sanar dani dan Allah meke damunka na tabbata ba ƙaramin abu bane zaisa ka shiga wannan halin, nasan ka fiye da yadda nasan yunwar ciki na babu abunda yake ɓata maka rai yasa ka cikin damuwa
Duk duniyar nan domin kuwa kana dannesa gashi kuma har Rama kayi na tabbata akwai gagarumin Abunda yake damunka pls ka sanar dani ko zan iya maganin matsalar ka."

Hawaye ne yake ƙoƙarin fitowa daga Idon Habeeb saurin mai dashi yayi ya dubi ɗan uwansa yace.

" Babu wani Abunda yake damuna fa kawai kwana nayi da ciwon kai ban samu nayi bacci ba shiyasa kaga idona yayi Red bani da wata damuwa ɗan uwa na ka kwantar da hankalin ka."


Kaɗa kansa Mustafa Yayi yana cewa.

" Ban yarda ba Bros tabbas akwai Abunda yake damunka na tabbata ba ciwon kai bane idan ba haka ba meyasa ka rame lokaci guda me Kuma ya haɗa ciwon kai da tunani akwai Abunda yake damunka sai dai idan sanar dani ne baka son yi, kamin adalci ɗan uwana ka sanar dani matsalar ka, ko ka manta da cewa bama iya ɓoyewa junanmu damuwar mu ka manta da cewa matsalar ɗaya daga cikin mu matsalar muce duka karka barni cikin tunanin Abunda yake damunka pls ka sanar dani."

Sosai jikin Habeeb yayi sanyi amma yasan komai zai faru bazai taɓa furtawa Mustafa damuwar sa ba, yasan idan ya furta masa sai ya shiga halin da yafi wanda shi yake ciki kallon Mustafa Yayi yace.

" Brother na gaya maka damuwata fa babu wani Abunda yake damuna kasan dai rashin bacci yana kawo rama ko, sannan shi ciwo yana saka mutum cikin tunani, karka ɗan uwana babu abunda yake damuna bayan ciwon kai, idan na faɗa maka wani abu bayan wannan to ƙarya kawai zan maka Please ka dakatar da Tambayar haka."

Kaɗa kansa Mustafa Yayi ba tare daya yarda da maganar Habeeb ba, duban sa yayi yace.


" Okay ka tashi ka shiga cikin gida kaje kasha magani sai ka kwanta ko zaka samu kayi bacci Allah ya sauwaƙa."

"Ameeen" Habeeb ya furta sannan ya miƙe tare suka shiga da Mustafa ya tsaya bakin part ɗin Habeeb har sai da yaga shigewar sa cikin gidan sannan yayi nasa part ɗin yana tunanin damuwar ɗan uwansa.

Habeeb yana shiga yaji wasu hawaye masu zafi sun zubo masa RAUDA da ta gama gyaran part ɗin nata ta zauna tana ɗan hutawa kafin ta ɗaura breakfast taga shigowar Habeeb cikin tashin hankali a kujerar da take ya zauna ta ɗaura kansa a kafaɗarta sai kuma ya saki kuka kamar ƙaramin Yaro shuru HASINA tayi domin yanzu ta fara sabawa da halin da mijinta yake ciki amma duk da haka duk sanda ta gansa cikin damuwa hankalinta yana mungun tashi shafa kansa tayi tace.

" Sweetie na menene kuma ya saka kuka da sassafe haka haba karka bada maza mana kaifa namiji ne wanda aka sanshi da jarumta da juriya dan Allah ka daina ɗaga hankalin ka akan ƙaramin abu."

Saurin tashi daga kafaɗar ta yayi ya ɗago ido yana dubeta yana goge hawayen sa yace.

" Baki san damuwata bace shiyasa kike ambatar sa da ƙaramin abu amma a waje na babban abune wanda idan nayi wasa zai kawo min babbar illah cikin lafiyata ki daina kiran Abunda baki sani ba da ƙaramin abu."

HASINA dafa kafaɗar sa tayi cikin hikima da dabara tace.

" Hakane bansan damuwar ka ba, shiyasa na faɗi haka tabbas nayi kuskure cikin maganata, sai ina ga ba laifi na bane laifin kane a matsayinka na mijina sirri na ka kasa sanar dani damuwar ka, sai dai kullum ka shigo min cikin gida rai ɓace a tunani na rashin yadda da kuma rashin bani mahimmanci cikin rayuwarka shine yasa ka kasa sanar dani matsalar ka, Abunda ya kaini ga fara tunanin fara ɓoye maka nawa sirrin tunda naga kamar babu yadda tsakanin mu."

" Subhanallah! HASINA da bakinki kike furta min wannan maganar marar daɗin sauraro, ni kuwa idan ban baki yarda ta ba waye zan bawa, ba komai yasa na ɓoye miki damuwata ba, sai dan jinta baida wani amfani gareki saima cikin ƙunci da zaki shiga wanda ni bazan iya jurar ganinki cikin wannan halin ba, ki cigaba da taya ni da addu'a Allah ya yaye min wannan halin da nake ciki, karki matsa sai kinji matsalata domin bana son ki sani, ki cire duk wani zargi cikin zuciyarki ki kasance cikin kwanciyar hankali hakan yana sani farin ciki *INA ƘAUNAR KI HASINA I LOVE YOU*."

Murmushi Hasina tayi ta faɗa jikin mijinta tana cewa.

" I love You too sweetie na, insha Allah Ubangiji zai yaye maka damuwarka."

Sun ɗan juma a haka suna tattaunawa kafin HASINA ta tashi domin ɗaura musu breakfast shi kuma Habeeb kwanciya yayi bisa kujerar yana cigaba da tunanin sa kafin ya tashi yayi bedroom ɗinsa Shirin fita aiki.


💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢

Misalin ƙarfe biyu na rana tana kwance bedroom ɗinsu gefenta kuma Sharifa ne kwance tana wasa da wayarta chart Indo take shigowar saƙon Barrister Umar ta gani bata buɗe saƙon nasa ba saida ta gama duba sauran saƙonnin kafin ta duba nasa.

" Hajiya ta na kira ki ɗazu baki ɗaga kira na lafiya kuwa, kinsan dai bana jin daɗi idan harna wuni ba tare da naji muryar ki ba ko."

Tsuka mai ƙarfi Indo taja tare da tura masa cewa.


" Bana kusa da wayar ne da na zo na ga miss Call ɗin kuma na kira network ya hanasa shiga."

Tana tura masa ta kashe datar ta, tana duban Sharifa tace.

" Ke Kuma Aunty Sharifa shirin me kike naga ɗazu da safe sai wani saka kaya cikin akwati kike, ina zuwa haka."

" Wai baki da labarin cewa gobe zamu wuce Egypt da Aunty Hindu?"

Shuru Indo tayi take taji ranta babu daɗi hankalin ta ya tashi jin Sharifa zata tafi ta barta.........


Kuyi hkr da wannan yau ina busy ne mu haɗu a next page, gashi ban samu nayi editing ba sorry for typing error.


DOKOKIN group ɗina sune👇🏻

Amsa sallama dole.

Dole ki fito ayi hira dake muddun kina online.

Yin sharhi dole domin shine ƙwarin gwiwwar WRITER'S.

Banda turo min Link ko TALLAH banda turo Abunda ya danganci batsa idan kuma kika turo zanyi remove ɗinki take.

Banda faɗa ko cece kuce banda zagin WRITER'S idan kin taka min doka ni kuma zanyi waje dake.

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*



*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*



*(Ummu Nasmah ce)*
[4/8, 7:23 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login