Showing 6001 words to 9000 words out of 53497 words

Chapter 3 - SO BAI SAN JINI BA HAUSA NOVELS BY UMMU NASMAH.txt

29 Oct 2025

451

zai sauƙe ni a gida."

Kallon tausayi Aunty Hindu take yiwa Indo har Zuciyarta taso a bata Indo sai dai babu yanda ta iya fadan daya fi ƙarfin ta dole ta maida shi wasa, ko zuwa ƙauyen DASINA ma ta fasa daman saboda Indo zata tunda kuma bazata ba ta fasa duban Indo tayi tace.

" Kiyi hkr Indo Babu yanda na iya ne naso na riƙeki har na aurar dake da hanuna, sai dai Allah bai ƙaddara hakan ba, Indo kullum nasiha ta ɗaya ce gareki shine ki kasance mutum mai haƙuri a duk inda kika tsinci kanki, domin shi haƙuri yana kai mutum zuwa ga matakin babban nasara, tabbas kuma haƙuri haske ne, karki damu da duk abunda mahaifiyar su Mustafa zata miki, zai zama tarihi wata rana ki mata biyayya karki gaza dan tana hantarar ki kice bazaki bita ba, kiyi hkr ki mata duk wata biyayya da ƴa zata yiwa mahaifiyar ta, nima kuma kafin na tafi zanzo" kuɗi Aunty Hindu ta ɗauko ta danƙawa Indo a hanunta tace.

" Gashi 10k ne ki riƙesa ko data zaki dinga saya dashi ki gaishe da su Daddyn naku."

" Karɓa Indo tayi cikin sanyin jiki ta yiwa Aunty Hindu godiya har bakin mota Aunty Hindu ta rako Indo ta shiga mota shima Habeeb sallama yayiwa Aunty Hindu sannan yaja motar suka bar gidan Aunty Hindu tana ɗaga mata hanu, sunyi nisa da tafiya babu wanda ya cewa wani komai Habeeb lura da yayi da ran Indo a ɓace yake yasashi samun gefen titi yayi parking ya dubi Indo yace.

" *HABIBTY NA* cire tagumin haka ko na juya na maida ke wajen Aunty Hindu."

Zaro Ido Indo tayi tana kallon Habeeb tace.

" Ya Habeeb *HABIBTY* kuma meyasa ka kiran da wannan sunan yau kuma?"

Murmushi Habeeb yayi yana duban ta yace.

" Bakya sone na kiraki da hakan ko kuma ban dace na kiraki da sunan ba ne?"

" A'a bawai baka dace bane gani nayi saurayi ne yake kiran *BUDURWAR SA* da wannan sunan Kuma baka taɓa kirana da sunan ba shiyasa na tambaya."

Murmushi sosai Habeeb yayi tare da cewa.

" Okey to ki ɗauke ni a matsayin *saurayin* idan har kina ganin na dace da hakan, ni kuwa ina maraba da hakan *HABIBTY NA*"

Dam! Gaban Indo ya buga maganganun Zarah ne suka fara yawo cikin ƙwaƙwalwar ta *ƙawata yaya Habeeb yana sonki da gaskiya mutumin kirki ne ya soki tun kina cikin ƙazantar ki bai taɓa nuna miki ƙyama ba*." Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un take furtawa cikin ranta ashe daman maganar Zarah gaskiya ne ya Habeeb sona yake kai anya kuwa ina ga dai yanzun ma zolayata yake, tabata da Habeeb yayi yana dariya tare da cewa.

" Tunanin me kike haka *HABIBTY NA* Kodai na saki cikin searching ne?"

Murmushin dole Indo tayi tare da haɗiye yawu dakyar tace.

" A'a babu wani tunanin da nake yaya Habeeb ai nasan hakinka da zolaya" kawar da maganar tayi ta hanyar cewa.

" Ya Habeeb yaushe zamuje Dasina, ina son zuwa naga Mama."

Murmushi Habeeb yayi tare da tayar da motar ya harba titin yana ce mata.

" Wannan ba maganar yanzu bane ki bari sai mun sami zama, keda zaki fara zuwa makaranta ina ke ina zuwa ƙauye, amma zamuyi maganar daga baya."

Indo bata sake magana ba haka shima Habeeb har suka isa cikin gidan parking Yayi kusan tare suka fito suka nufi cikin falon Momy suna zaune gabaki ɗaya suna hira Momy Mustafa Sharifa Ishaq Sharif, da Sallama suka shiga Sharifa ce ta amsa, Mustafa kuwa wani Shu'umin kallo yake bin Indo dashi yana lumshe idanunsa Momy kuwa wani ƙazamin kallo take bin Indo dashi tare da tsantsar tsana cikin idanunta, Ishaq da Sharif kuwa da gudu suka tashi suka nufi Indo suna mata Oyoyo, akwatin nata Sharif ya karɓa yana ƙoƙarin kai mata cikin ɗakin su suka ji muryar Momy ta daka masa tsawa tana cewa.

" Dan ubanka bata akwatin ta, jakinta ne kai shegen shishshigin tsiya nifa bana son kuna shigewa jikin wannan abar ƙyamar zan ci muku mutunci wlh idan baku fita harkarta ba daga ku har yayun naku."

Ajiye akwatin Sharif yayi ya koma gefe yana fushi Habeeb kasa magana yayi ya tsaya yana duban Momy domin kuwa yasan koya mata magana bazata fahimce sa ba, sai dai ma ta zagesa, Mustafa kuwa Sarkin rashin haƙuri tuni ya fara yiwa Momy Magana.

" Haba haba! Momy wai meye Indo ta ci miki haka kika tsaneta, ya kamata ki sassauta wannan ƙiyayyar da kike mata karki manta da cewa itama mutum ce kamar kowa kuma tana da Iyaye suna sonta kuma kamar yadda kema kike son naki ƴaƴan Abunda bazaki ji daɗi ba idan an miki bai kamata kiyiwa ɗan wani ba, itama fa Momy tana gata da Asali kamar yadda ƴaƴan naki suke dashi, ko mummunan laifi ta miki ya kamata ace kin yafe mata ki kuma mata fatan shiriya barema babu abunda ta miki pls Momy ki sassauta ƙiyayyarki gareta karki manta da cewa zata zama surukar ki nan gaba kaɗan."

Shuru Momy tayi tana sauraron Mustafa bata katsesa ba harya gama sannan ta fara magana.

" To ubana ka gama min faɗanne, to banji ba dan ubanka, na RANTSE DA ALLAH Mustafa zan iya rabuwa da kai na yafewa duniya kai muddun baka janye Maganar Soyayya da wannan abar ba, bare harta kaiku ga Aure idan kana neman zaman lafiya dani kana kuma neman albarkata to ka rabu da wannan YARINYAR domin na tsaneta bana ƙaunar ta cikin Rayuwata."

Gabaki ɗayan su cikin tashin hankali suke kallon Momy mussaman Mustafa da yake jin bazai iya rayuwa babu Indo ba Habeeb kuwa suman tsaye yayi yana jin maganar mahaifiyar tasu kamar sauƙar aradu, juya kawai Habeeb yayi ya fice daga falon ganin hawaye na neman zubo masa, Indo kuwa tuni hawaye ya wanke mata tata fuskar kuka take harda sheshsheƙa Abunda take gudu kenan shiyasa taƙi dawowa Aunty Hindu ta tilasta mata dole sai ta dawo yanzu ga irinta nan, jan akwatin ta kawai tayi ta shige bedroom ɗinsu, Mustafa kuwa ranshi idan yayi dubu to ya ɓaci idanunsa sun kaɗa sunyi jajur ya dubi Momy ya fara faɗin mata maganganu.

"Da farko kin min Auren dole kinsani na amshi matar da ban taɓa sonta ba a matsayin matar aurena na kuma miki biyayya na amshe ta a matsayin ki na mahaifiyata, duk da raina baya son ta, sai gashi yanzu nayi tozali da matar da nake so na Aura a matsayin zaɓina a karo na biyu kince baki yarda da hakan ba, anya kuwa Momy wannan karon zan iya miki biyayya anya Momy ina sonta fiye da yanda nake son komai na rayuwata ciki harda Numfashina, na daɗe da Soyayyar ta cikin Raina, meyasa Momy zaki tarwatsa Soyayyar Shekara da shekaru karkiyi wannan ɗaukar alhakin Momy domin..............."

Sauƙar marin da yaji ne yashi kasa ƙarasa maganar da yayi niyya yana duban Momy da jajen idanunsa wacce ta sauƙe masa mari magana Momy ta fara cikin tsawa wanda yasa Sharifa fashewa da kuka tana duban Momy.


" Na isa da kai! Shiyasa nayi maka katanga tsakaninka da ita, kuma dole kamin biyayya idan kuma kace bazaka min biyayya ba to kajeka babu ni babu kai karka sake takowa inda nake har abada ɓace min da gani."

Bai cewa Momy komai ba ya taka ya haura sama bedroom ɗin su Indo ya shiga ya sameta tana zaune ƙasan tayels sai riskar kuka take harda majina sunkuyawa yayi ya kamo kafaɗarta ya ɗaga ta tsaye, sannan ya kama hanunta yana ƙoƙarin janta su fita, ƙwace hanunta Indo take ƙoƙarin yi amma ina Mustafa ba riƙon wasa ya mata ba, janta kawai yake tana cijewa har suka isa gaban Momy hanunsa riƙe dana Indo ya tsaya a gaban Momy yana kallon sa, Indo kuwa tsabar tsoron Momy rufe idanunta tayi tana jiran taji sauƙar duka.........





*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah ce)*
[4/2, 11:01 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••7️⃣ ↗️ 8️⃣

Magana ya fara cikin tsantsar ɓacin rai.

" Gani ga Indo a gaban ki Momy zan ƙara maimaita miki a karo na biyu *INA SONTA INA SONTA INA SONTA!* Ina kuma fatan mu kasance ƙarƙashin inuwar Aure ɗaya, karki rusa mana farin cikin mu Momy na roƙeki da Allah kiyi hkr ki barmu muna tsantsar son junan mu Soyayyar mu daɗaɗɗiya ce dan Allah Momy ki ƙyale mu da farin cikin mu."

Cikin sauri Indo ta buɗe idonta jin maganar Mustafa kamar sauƙar aradu cikin kunnuwan ta, da ƙarfi ta fisge hanunta daga nashi tana mishi kallon marar Hankali, cikin fusata da ɓacin rai Indo ta fara maidawa Mustafa martani.

" Me kake cewa? Muna son junan mu, kai da waye? badai da Indo ba, domin kuwa ni bana sonka na tsaneka bazan kuma taɓa sonka ba har abada, daga yau karka ƙara kirana da sunan masoyiyarka domin sunan san bai dace da mungu irinka ba duk duniyar nan babu mutumin dana tsana sama dakai a rayuwata" tsagaitawa Indo tayi da maganar tana duban Momy Ido cikin ido kafin ta cigaba da cewa, " ba sai kin yiwa ɗanki baki ba Momy babu alaƙar Aure da zata shiga tsakani na dashi, Momy koda ace kina son na Aure ɗanki bazan yarda na Aure shiba domin kuwa na tsanesa ba tsanar wasa ba, kiyi hkr ki gafarce ni idan har maganata ta ɓata miki rai, na sanar dake haka ne domin ki daina zagin ɗanki, nasan kuma shima kanshi ya Mustafa ƙarya yake ba sona yake ba "

Mustafa tsayawa yayi yana kallon Indo tamkar wani gunki domin kuwa jin maganar ta yake tamkar tatsuniya cikin kunnen sa, Momy kuwa Hamdala tayi a fili daya kasance Indo bata son ɗanta, a fili ta furta cewa.

" Kin taimaki kanki da kika yankewa kanki hukunci domin kuwa ɗana yafi ƙarfin jakar ƙauye Irin ki wacce ta gagari iyayenta har saida suka dangana ta da iyayen wasu."


Dariya sosai Mustafa yake tamkar wani sabon mahaukaci Abunda bai cika yiba cikin tarihin rayuwar sa wato yawan dariya yana duban Indo yace.

" Ƙarya take Momy tana sona cikin ranta duk duniyar nan babu wanda take so sama dani cikin rayuwarta, ki duba cikin ƙwayar idonta zaki ga zallar soyayyata cikin su, karki cuci kanki Indo ta hanyar haramtawa kanki Abunda kike so, idan kuma kikayi wannan kuskuren to tabbas zaki dasawa zuciyarki babbar cuta na tabbata nine *DUNIYAR KI NINE FARIN CIKIN KI NINE KUMA MAFARKIN KI*."

Girgiza kanta Indo takeyi tamkar ƙadangare tana dubansa kafin tace.

" Ƙarya kake babu wata Soyayyar ka a tattare dani sai tsantsar ƙiyayyarka Na kuma ƙara furta maka *I HATE TO YOU*" tana gama faɗin haka ta haura step ɗin da gudu tana sakin wani kuka mai cin Zuciya.

Daddy daya daɗe tsaye bakin falon yana sauraron su basu san da zuwan sa ba, ya juya ya koma waje domin baya buƙatar susan yaji wannan abunda ya faru tsakanin su yana lura da take-taken kowa Kuma insha Allah ya kusa maganin matsalar.

Shima Mustafa juyawa yayi cikin mungun ɓacin rai yana haɗa hanya cikin layi tamkar mashayi ya fice daga falon cikin ikon Allah kuma bai lura da Daddy dake zaune compaunt ɗin gidan ba harya fice Daddy yana masa kallon tausayi, Momy kuwa ko a jikinta ta samu waje ta zauna tana Hamdala Indo bata son ɗanta yanzu hankalin ta ya kwanta saura kuma tasan yanda zatayi ta koreta daga cikin gidan kota ƙarfin tsiya ne, Sharifa tashi tayi ta haura step ɗin tana hawaye tayi bedroom ɗin su ruf da ciki ta samu Indo sai Rusar kuka take tare da sauƙe a jiyar ZUCIYA magana Sharifa ta soma mata.

" Meyasa zaki ƙaryata Soyayyar ki? Bayan ganan Soyayyar sa a cikin idanunki ana ganinsu, duk wanda ya sanki a cikin garin Dasina yasan kina son ya Mustafa, soyayya kuma ta gaskiya kuma har yanzu kina sonsa karki cuci kanki Indo ki amshi Soyayyar sa, na tabbata zaki samu kulawa domin shi mutum ne mai daraja Abunda yake yaso bai iya son abuba idan yana son abu yana iya komai dan ganin ya adana Sa, na tabbata ya Mustafa yana miki mahaukacin SO na hango Soyayyar gaskiya cikin idanunsa pls ki basa dama dan Allah ko sau ɗaya ne."

Tashi Indo tayi tana goge hawayen idonta tana duban Sharifa cikin muryar kuka tace.

" ki daina wannan zargin cikin Ranki ni babu Soyayyar Mustafa cikin zuciyata na daɗe da mantashi cikin babin rayuwata da kike maganar cewa yana min Soyayyar gaskiya, wannan zancen naki ba gaskiya bane, Mustafa baya sona da gaskiya domin kuwa da Soyayyar gaskiya yake min daya soni tun ina ƴar ƙauye ta daya kawo min gyara cikin rayuwata amma duk baiyi hakan ba sai ƙyama da tsangwama daya dinga nuna min mugunta kala-kala ya nuna min haka zagi iri-iri yamin hakan shi kike ƙira Soyayyar gaskiya eh tabbas naso Mustafa a baya amma a yanzu na tsanesa, na tabbata yanzu ma akwai Abunda yake buƙata a jiki na ne shiyasa ya shiryo min wannan yaudarar da zarar kuma ya samu Abunda yake buƙata zaiyi watsi da rayuwata, dan Allah ina riƙon ki Aunty Sharifa ki daina shiga cikin lamarina da Mustafa domin ni nasan abinda ke baki sani ba game dashi, *ƊAN UWAN KI MACIJIN SARI KA NOƘE NE LUMBU LUMBU NE SHI WUTAR ƘAIƘAYI* dan haka ki ƙyale maganar haka ta wuce."

Shuru Sharifa tayi sai can tace.

" Shikenan na ƙyale, sai dai ina son na baki Hkr game da abubuwan da Momy take miki......."

Dakatar da sharifa Indo tayi ta hanyar cewa.

" Ba sai kin bani Hkr ba, duk abunda Momy tamin takai tamin ne, tana da iko dani dan haka ban damu ba dan ta zage ni."

Shuru Sharifa tayi tana jingina kanta da jikin bed ɗin tana jinjinawa hkrn Indo wanda lokaci ɗaya Allah ya bata shi ta tabbata da sanda Indo take Indon ta ne sai ta rama zagin da Momy ta mata sai kuma gashi yanzu cikin ikon Allah har a zagi Indo ta ƙyale Lallai UBANGIJI shine mai gyara bawansa a duk sanda yaso, komawa Indo tayi ta kwanta tana cigaba da zubar da hawaye cikin ƙunar Zuciya.

Habeeb kuwa cikin fushi ya shiga part ɗin nasa a falo ya sami Hasina ta shirya abinci a daining tasha wanka cikin ƙananan kaya tana jiransa, da sauri ta tashi tana cewa.

" Sannu da dawowa sweetie na, gaskiya ka juma da yawa harna fara gajiya da jiranka ina shirin kiranka sai gashi ka shigo.''

A taƙaice Habeeb ya cewa Hasina.

" Eh na shiga part ɗin Momy ne shiyasa na ɗan juma." Yana maganar yana shigewa bedroom ɗinsa, tsayawa Hasina tayi tana dubansa cikin mamaki domin ba haka ya saba shigo mata cikin gida ba, da fara'a yake shigowa harma ya rungume ta yanzu kuma taga saɓanin haka ya shigo mata rai ɓace binsa tayi cikin bedroom ɗin nasa yana zaune saman kujerar ɗakin mai biyu ya jingina kansa yayi shuru yana kallon silim, zama tayi kusa dashi tace.

" Lafiya kuwa sweetie na naga ka shigo cikin ɓacin rai?"

A taƙaice yace mata.

" Lafiya lau babu komai."

" Amma ba haka ka saba shigowa ba sai nake ga kamar akwai Abunda yake damunka pls ka sanar dani dan Allah ko na maka wani laifi ne mijina bana son ganinka cikin ɓacin rai.''

Cikin fara gajiya da tambayoyin Hasina gashi shi ya tsani idan yana cikin damuwa ake masa magana ce mata yayi.

" Nace miki babu komai ko zan miki ƙarya ne ni babu abunda kika min kawai banji HAPPY ne yanzu."

" Shikenan to ga nan abinci na gama daman kai nake jira, idan kuma wanka zaka fara sai na kai maka ruwa.?"

" Na ƙoshi bazan ci Abincin ba wankan ma bazan yiba " ya faɗa mata cikin ƙaguwa da maganganun ta.

" Ka ƙoshi kuma me kaci da zaka ce ka........"

Cikin tsawa ya dakatar da ita ta hanyar cewa.

" Kin fara isata da magana malama! Nace miki bazan ciba ana dole ne, pls And pls live me a long, bana son damuwa ki fice min daga ɗaki nace bana buƙatar ki kusa dani."

Tashi Hasina tayi baki buɗe tana ja da baya cikin tsoro domin kuwa tunda take da Habeeb bai taɓa mata tsawa ba sai yau Tambayar kanta take laifin me ta masa haka yake mata tsawa, harta fice daga ɗakin nasa ta faɗa nata zama tayi ta fashe da kuka tana tuhumar kanta laifin me tayiwa mijinta sosai take kuka, domin ta fahimci tunda Habeeb ya fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login