Showing 12001 words to 15000 words out of 53497 words

Chapter 5 - SO BAI SAN JINI BA HAUSA NOVELS BY UMMU NASMAH.txt

29 Oct 2025

452

💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*Duk wanda yace wannan BOOK ƊIN na kuɗi ne ƙarya yake Damfarar ku zaiyi book ɗina FREE ne bana kuɗi bane, book ɗina na kuɗi shine RUƊANIN ZUCIYA BIYU kuma ban fara sakin sa bama tukunna, dan haka SO BAI SAN JINI BA free ne bana kuɗi ba*.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••1️⃣1️⃣ ↗️ 1️⃣2️⃣

" AUNTY Sharifa da gaske dake Ummi zata tafi Egypt, yanzu ni kaɗai zan zauna a bedroom ɗin nan bazanji daɗi ba Aunty Sharifa idan kika tafi zanyi kewarki sosai."

" Kiyi hkr Indo ni kaina ba son tafiyar nake ba dole ne tasa zan tafi tunda umarnin Daddy ne, itama Aunty Hindun tana zuwa Anjuma naso ace kece kika tafi Egypt domin na tabbata zakiji daɗin zama da Aunty Hindu fiye da zama da Momy da kike cikin takura kina hkr da Momy Indo ni shaidace akan haka ki kuma ƙara hkr insha Allah komai zai wuce tamkar bai taɓa faruwa ba."

Murmushi Indo tayi tana duban Sharifa tace.

" Aunty Sharifa waya ce miki bana jin daɗin zama da Momy, nikam ina jin daɗin zama da ita sosai ki daina cewa bana jin daɗin zama da Momy karki ƙara dan Allah, tafiyan ki Egypt kuma Allah yasa hakan shi yafi Alkairi."

Ameeen Sharifa ta amsa tana cigaba da danna wayarta Ishaq ne ya shigo cikin bedroom ɗin yace.

" AUNTY Indo wai kije inji Daddy yana falon ƙasa kema Aunty Sharifa harda ke."

Da to Indo ta amsa sannan ta tashi tare da ɗaukar ɗan kwalinta ta yafa tabi bayan Ishaq, Indo bata juma da fita ba itama Sharifa ta bi bayan ta, kusa da Daddy Indo ta Zauna tana cewa.

" Barka da HUTAWA Daddy."

Murmushi Daddy Yayi amsa mata da cewa.

" Barka ƴata, Ishaq yace ina kiran ki ko.?

" Eh Daddy shiyasa ma na zoni."

MOMY haɗa ranta tayi tana hararar Indo tare da jin haushin ta, gyaran murya Daddy Yayi yace.

" Masha Allah ya dai zaman gidan kina jin daɗin sa kuwa.?

Kanta sunkuye Indo tace.

" Ina jin daɗi sosai daddy.''

Dubanta Daddy Yayi kafin yace.

" Ki faɗa min gaskiya kina jin daɗin zaman gidan nan babu wata matsalar da kike fuskanta idan akwai karki ɓoye min ki sanar dani a matsayina na mahaifin ki kema nan gidan kune baki da banbanci da ƴaƴan dana haifi ."

Murmushi Indo Tayi tace.

" Babu wata matsala fa Daddy ina jin daɗin zaman gidan SOSAI."

Kara jefa mata tambaya Daddy Yayi cikin rashin yarda da maganar ta yace.

" Kin tabbata babu wata matsalar dai ko.?

" Da gaske Daddy babu komai, normal komai yake tafiya Banda wata matsala."

" Okey daman kiran da na miki akan maganar cigaban karatun kine so na samu abokina prof Usman Abba Gaɗan munyi magana sosai so ya bani admission ya kuma cemin na bada kuɗin registration ɗinki kawai ana farawa zai miki nace Cose ɗinki kuma ya cike miki ɓangaren Maths Education Allah ya baki Sa'a, yace zai kira ya sanar damu ranar da zaki fara lectures yau sati Uku kenan da maganar da mukayi dashi to sai ɗazu ya kira ni yake shaida min cewa ya miki registration a University of Dutse ranar monday zaki fara lectures, Allah yasa Cose ɗin da na zaɓa miki ya miki."

Sosai Indo tayi farin ciki da jin zata fara zuwa jami'a tayi farin ciki sosai duk da dai Cose ɗin da take so bashi Daddy ya zaɓa mata ba ita Science taso tayi shi kuma Daddy ya cike mata Maths Education duk da haka taji daɗi sosai duban Daddy tayi tace.

" Daddy yayi sosai bani da wani zabi zaɓinka shine dai-dai a wajena, na gode sosai da kulawar ka gareni Daddy na gode Allah ya ƙara buɗi."

" To alhamdulillah tunda ya miki babu damuwa Allah ya miki jagora yasa ki fara a Sa'a A'isha karki sa wasa cikin ranki kiyi Abunda ya kaiki kiyi karatu sosai banda shiga shirgin ƙawaye Allah ya miki albarka ya Albarkaci karatun da zaki fara ki gama cikin nasara."

Da "Ameen" Indo ta amsa tana murmurshi, kafin Daddy ya kai dubansa ga Sharifa yana mata nasiha game da tafiya da zasuyi Egypt da Aunty Hindu sosai ya mata faɗa, har Aunty Hindu tazo.

Wuni kas Aunty Hindu tayi duk Inda tayi Indo tana kusa da ita har wajen Hasina sukaje tare sanda suka je Habeeb baya nan ya fita aiki, Hasina kaɗai suka samu Kuma ko a fuska Hasina bata nunawa Indo wani sauyi ba yanda suka saba mu'amala yauma haka sukayi cikin wasa da dariya, har suka tafi haka suka shiga wajen RAUDA ma sun sami Mustafa yana Zaune falon ita kuma RAUDA tana zaune a gefe cikin sakin fuska RAUDA ta tarbesu hatta Indo RAUDA bata sanja mata fuska ba sai dai harga Allah tana jin zafin Indo cikin ranta amma bata yadda hakan ya fito a fuskar taba, Mustafa kuwa tun shigowar su hankalinsa yana kan Indo, gaishe da Aunty Hindu yayi yana cewa.

" AUNTY kardai ace sallamar kenan Egypt tayi kira."

Dariya Aunty Hindu tayi tace.

" Eh mana Egypt tayi kira aima naga wannan karon mun juma cikin Nigeria."

" Gaskiya kunsha Nigeria sosai ma kuwa, wannan kam Aunty kin sadakar mana ita muna nan tare babu ita babu komawa Egypt" ya ƙarasa maganar yana nuna HASINA.

Dukkan su dariya sukayi Hasina tana dariya tace.

" Bashi kaci zan rama, naga alamar so kake nayi azarɓaɓi a gaban Ummi to bazan yiba amma dai zamu haɗu zan rama."

Murmushi yayi yace.

" Ai kuwa sai dai ki rame malama badai ki rama ba" nuna Indo Yayi yana cewa " Aunty wai ita wannan kurma ta zama ne, naga ta kasa Magana oh sorry ashe dai tana kunyar yiwa masoyinta magana a gaban surkarta, Aunty Hindu kin min kofsi kin hana naji muryar masoyiyata." Ya ƙarasa maganar yana kannewa Indo Ido.

Harara Indo ta doka masa tana kawar da kanta gefe HASINA kallon tausayi take yiwa Mustafa kai harma da Habeeb da baya wajen ita tsoron ta ma kar Soyayyar Indo tayi sanadiyar rabuwa tsakanin waɗannan ƴan uwa biyu da suke tsantsar son junan su, cikin zuciyarta take addu'ar Allah ya hana hakan faruwa, Aunty Hindu kuwa murmurshi tayi tace.

" Kai da yaron nan baka da kunya a gaban nawa kake furta waɗannan kalmomi, aidai ka saya ko dan albarkacin idon ƴata RAUDA ko, kunga ku tashi mu wuce kafin ya ƙara ɗauko wata maganar."

Ita dai RAUDA bata ce komai ba sauraransu kawai take amma cikin zuciyarta tana jin zafi ita kanta ta matsu subar cikin gidan, shi kuwa gogan dariya yayi yace.

" Au dan kawai na faɗi iya gaskiya ta Aunty shine rashin kunyar, to ai Aunty indai ina kusa da *ABINCIN ZUCIYATA* bazan taɓa iya control ɗin kaina ba."

Tsuka mai ƙarfi Indo taja tare da tashi ta fice daga falon, ai kuwa shima Mustafa rufa mata baya yayi Aunty Hindu da RAUDA har Hasina binsu da kallon mamaki suke, ita Hasina tausayin su take ji domin kuwa tana hango zallar soyayyar Indo cikin idanun Mustafa kamar dai yadda ta saba gani a idanun mijin ta.

Da ƙarfi ya fisgo ta tare da janta yayi garden da ita, ƙoƙarin fisgewa Indo take daga hanunsa amma ta kasa har suka isa Garden ɗin sannan ya sake ta yana Binta da kallo, cikin haki da masifa Indo tace masa.

" Meye haka Malam zaka wani jawoni tamkar wata ƴarka, wai me kake nema a waje nane ka takurawa rayuwata haka.?"

Murmushi sosai Mustafa yake cikin confidence ya amsa mata da cewa.

" *SOYAYYAR KI* Soyayyar ki ita nake nema itace kawai dalilina na takurar da kike ƙira ina miki duk da dai ni nasan babu wani takurawar da nake miki."

Duban sa Indo take Ido cikin Ido kafin ta bushe da dariya sosai take dariya tana nunasa da hanu, shiko binta kawai yake da kallo yana ƙara hango tsantsar kyawun ta, mussaman dumple ɗinta da suke lotsawa ji yake kamar ya jawota jikinsa ya rungume, wani irin Soyayyar tace yake fisgar sa, muryar ta daya ji ne yasa shi dawowa daga duniyar daya faɗa cewa take.

" Ni kuma nace bana sonka, bana ƙaunarka dabadan alkairin da ya Habeeb ya min ba cikin rayuwata da sai nace ko mai kama da kai bana ƙauna amma bazance haka ba, saboda ya Habeeb Ya Mustafa na roƙeka da ka ƙyale ni ka daina damuna akan Soyayyar ka ta ƙarya domin kai maha'inci ne mayaudari bazan kuma taɓa yadda na faɗa tarkon yaudarar ka ba."

Shima dariyar yayi kafin yace.

" Ina mamakin yadda kike iya ƙaryata Abunda ya bayyana a gareki tare da alamomin su, ko kin manta a gaban wa kike furta wannan kalaman ne, Mustafan kine fa Wanda kike so tun ƙuruciyarki wanda duk ƙauyen ku anshaida wannan Soyayyar da kike min ko kin manta da *kifiyar Soyayyata da kike furta cewa suna sukan ki aduk sanda naje garin ku* ashe itama duk ƙarya ce?"

Murmushi Indo tayi tare da kaɗa kanta sannan tace.

" Alhamdulillah tunda a cikin kalamanka ka furta *ADA* kaima kace da kuma ai kaga da da yanzu ba ɗaya bane wancan haukar yarinta ce tare da tsantsar ƙuruciya, *Mlm Mustafa ya kamata fa yanzu kasan cewa Yanzu ba Indon dasina bace a gaban ka wannan A'ISHA CE wacce ta waye ta kuma goge Ras a cikin birni kaga kuwa kamata yayi kasan cewa yanzu na kai matakin da zan iya BANBANCE TSAKANIN FARI DA BAƘI dan haka yanzu na wuce tunanin ka Mlm, idan ma kana tunanin cewa Indon da kasani dace wacce zaka taka ta ta bika to yanzu ka dawo daga shirmen tunanin ka domin kuwa BANA SONKA sai kabi wani sarkin kuma badai wannan ba*."


Kuyi hkr da wannan Wlh yau ina busy ne naso nayi typing ɗin yafi haka yawa afuwan fan's🙏🏻

Na tsayar da posting ɗin so bai san jini ba sai zuwa bayan Sallah idan Allah ya kaimu dan gaskiya bazai yiwu na gama book ɗin ba kafin azumi gashi kuma azumi ya kawo kai, ga kuma uzirori da suka sani gaba suke hanani typing insha Allah sai Bayan Sallah idan Allah ya kaimu zan cigaba da posting.

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*



*(Ummu Nasmah ce)*
[4/10, 1:47 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*

Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya.

*Da nace na tsayar da wannan book ɗin sai bayan Sallah, sai gashi kuma Fan's sun sakoni a gaba cewa lallai nayi hkr na cigaba da musu posting kafin azumi*.

*Zan cigaba da posting amma a duk sanda na samu Lokaci it means ba kullum ba*.


*A ƘAFTA FAN'S MUJE KARATU📖*
__________________________________

*P*••••••1️⃣3️⃣ ↗️ 1️⃣4️⃣

" Hmmm *ƘARYA KIKE SHATUU!* Ba ki isa ki rusa min farin ciki na ba, bazaki wargaza min mafarki na ba domin duk duniya babu macen da nake so sama dake ki sani cewa rasaki tamkar rasa numfashina nane, eh rasa numfashina domin kuwa babu ta yadda za'ayi numfashi ya daidaita ba tare da taimakon hanci da baki ba, idan hanci ya toshe baki kan taimakawa wajen shaƙar isa haka zalika idan baki na rufe hanci shike bada numfashi, kinga idan babu su babu Rayuwa kenan domin sune masu taimakawa ruhi wajen tafiyar da daidaiton Rayuwa, misalin yadda Soyayyar ki take a gareni kenan, rasaki tamkar rasa Rayuwata ne karki kasance daga cikin masu neman rayuwar ɗan adam mussaman ni da na kasance masoyi gareki idan har na mutu sanadin Soyayyar ki to TABBAS kece ajalina zan kuma yi farin cikin cewa na mutu da Soyayyar ki cikin zuciyata, ta wani ɓangaren kuma zanyi baƙin cikin har na mutu ba tare da kin furta min kalmar *I LOVE YOU* karki kasance cikin mata masu son kansu *SHATUU karki zama ajalina SHATUU*."

Tsagaitawa Yayi da maganar yana duban ta da idanunsa da suka kaɗa suka koma jajaye ya na mungun jin zafin maganganun ta a cikin ransa, murmurshi Indo tayi kafin ta maida masa amsa da cewa.

" idan har ka cigaba da ƙaryata kalamai ma to tabbas ƙwaƙwalwar ka ta toshe, idan har kana ɗauka cewa nice farin cikin ka to daga yau ka fara ɗaukata a Matsayin Baƙin cikin ka, idan har nice mafarkin ka, to ka daina bacci domin kuwa mafarkin ka ƙarya ne bazai taɓa zama gaskiya ba bare kuma ya tabbata, idan har nice macen da kake so ina mai baka shawarar cewa ka ɗauki wannan ƙaryar Soyayyar taka ka bawa matar ka ta sunan domin kuwa itace ta dace da kai sam ni bana ɗaukar ka a matsayin masoyi sai Maƙiyi, idan kuma har na kasance nice Numfashin ka kamar yanda ka ambata to daga yau ka fara lissafin ranar mutuwar ka, domin kuwa saina toshe duk ta inda wannan Numfashin zai isa gareka, karka yaudari kanka Mlm ka yi tunanin zaka yaudareni da waɗannan kalaman naka ina mai baka shawara daka taushi zuciyarka ka bata shawarar cewa ta fice daga cikin rayuwata domin wahalar banza take sha, idan kuma har ta cigaba da sani cikin ta to tabbas *ZUCIYAR KA TANA GAF DA BUGAWA DOMIN BAZAN TAƁA SONKA BA* Ina kuma tabbatar maka da cewa idan baka gaji da furta min *I LOVE YOU* ba to ni kuwa bazan gaji da furta maka *I HATE TO YOU* ba ka taimaki kanka ka fita daga cikin rayuwata ka barni na huta kaima ka hutar da zuciyarka."

Juyawa tayi da niyar barin wajen kawai sai tayi kicibus da Habeeb a gabanta domin kuwa yadda fuskar sa ta sauya tabbas hakan ya nuna mata cewa yaji komai dake faruwa tsakanin su Tambayar kanta Indo take yaushe Ya Habeeb ya zo nan kallon sa tayi tace.

" Ya Habeeb yaushe......."

Dakatar da ita Habeeb yayi ya ɗaga mata hanu cikin tsantsar ɓacin rai tare da cewa.

" Ba sai kince komai ba jeki kawai ki jeki."


" Amma ya Habeeb.........."


Cikin tsawa Habeeb yace.

" Nace ya isa ko! Ki shige daga gabana malama."

Zaro ido Indo tayi tana duban Habeeb cikin mamaki to mai ta masa ko dan tace bata son ɗan uwansa shine shima zai tsaneta, da gudu ta fice tare da sakin kuka, runtse idonsa Habeeb yayi yana ƙoƙarin juyawa yaji muryar Mustafa yana cewa.

" *Me nake hangowa cikin idanunka kamar kishi Allah yasa kar zargina ya kasance gaskiya muna son abu ɗaya nida ɗan uwana wanda wannan abun dole mutum ɗaya ne zai mallakesa, menene yasa idanunka juyawa lokaci ɗaya menene dalilin daya sa zuciyarka fusata har ka kasa jure hakan sanda fuskar ka ta nuna, a tunanina TSANTSAR KISHI NE KAWAI YAKE JAWO HAKAN* Kasanar dani menene amsar tambayoyina shin hasashe na gaskiya ne.?"

Shuru Habeeb yayi zuciyarsa na bugawa da ƙarfi gashi har yanzu tsantsar kishin ɗan uwansa yake ji cikin ransa tunda ya shigo cikin gidan yaji labarin cewa Indo tana tare da Mustafa a garden hankalinsa ya kasa kwanciya shine dalilin daya sa harya zo nan wajen duk da baisan Abunda suke tattaunawa ba zuwan sa wajen kenan Indo ta juyo, amma zuciyarsa na sanar dashi cewa SOYAYYA suke mussaman daya kasance cikin Garden suke, ba tare daya amsawa Mustafa tambayar sa ba ya nufi hanyar fita, kiransa Mustafa yake amma Habeeb bai sauraresa ba, taɓe bakin sa Mustafa Yayi tare da juyawa yana jin cikin ransa yanzu ma ya fara son *SHATUUN SA* domin a tunaninsa gani yake kamar Abunda ya mata a ƙauye take ramawa yana tunanin zata sosa idan harta huce.

INDO kuwa fitowar ta bata ga kowa ba babu su Aunty Hindu, ba tare da wata tambaya ba, kawai itama ta fice daga cikin gidan, Habeeb kuwa a fusace ya wuce part ɗinsa zuciyarsa na wani irin tafasa Wato Indo amanarsa zata ci ta kasa gano cewa yana sonta har yanzu duk abunda Mustafa ya mata na wulaƙanci harta mantasu tazo ta basa haɗin kai har suna Soyayya TABBAS ɗan Adam butulu ne, fashewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login