Showing 48001 words to 51000 words out of 53497 words
Chapter 17 - SO BAI SAN JINI BA HAUSA NOVELS BY UMMU NASMAH.txt
mahaifinta farin gaske ne, yarinya kuwa mai haƙuri sam bata da rikici, domin kuwa bata da yawan kuka.
Washe gari da safe Daddy yasa aka ɗauko gawar RAUDA aka dawo da ita gida, duk wanda yaje yaga RAUDA kwance babu Numfashi sai yayi kuka Abban ta ma ya shiga ya ganta tare da mata Addu'a, Iya ladi mahaifiyar Mamy da Goggo Asabe sune suka yiwa gawar tata wanka, Allah sarki Rayuwa Mustafa bai samu an kai Matarsa maƙabarta dashi ba, yana can kwance shima rai a hannun Ubangiji, da Habeeb aka kai RAUDA makwancin ta, sai lokacin hawaye ya zowa Habeeb na tausayin RAUDA, rayuwarta kawai yake tunawa na da a cikin gidan su.
Allah sarki rai baƙon duniya dukkan wani mai rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa yau dai ga RAUDA rayuwa ta ƙare an rufe ta cikin ƙasa kowa ya watse ya barta daga ita sai halinta, Habeeb ya dawo suka Zauna a wajen zaman makoki, ya ɗan juma yana zaune kafin ya tashi yayiwa Daddy Magana cewa zaije Hospital yaga result ɗin MUSTAFA.
Bisa mamakin Habeeb yana shiga Hospital ɗin yaga Indo zaune gefen Momy sai famar sharɓar kuka take tana kuma riƙe da jaririyar a hanunta, sosai yayi mamakin zuwan nata, to wama ta tambaya ta fito, yayiwa kansa tambayar itama Momy hawaye ne kawai yake gudu bisa fuskar ta, sunkuyawa yayi gaban Momy ya gaisheta, bata samu damar amsawa ba sai kai data ɗaga masa, dubanta yayi yace.
" Dan Allah Momy ki daina kukan nan, ki cire damuwa cikin ranki ki yiwa RAUDA addu'a shine kawai gatan da zamu mata, ta riga ta tafi bazata taɓa dawowa ba, dan Allah kiyi hkr, shi kuma Mustafa zai tashi da yardar Allah."
Share hawayen ta Momy tayi sannan tace.
" Kuka ya kamani dole, dole nayi kuka mussaman idan na kalli wannan jaririyar da aka bari cikin maraici, ga shima Mustafa yana kwance sai yanda UBANGIJI yayi dashi, Habeeb ina tsoron na rasa Mustafa."
" Karki damu Momy insha Allah bazaki rashi ba, zai tashi Momy, bari na ƙarasa wajen result ɗin sai musan Abunda yake damunsa, insha Allah ma nan da 24 hours zai farfaɗo."
" To Allah yasa jeka karɓo result ɗin, Allah yasa muji Alkairi."
Da ameeen Habeeb ya amsa kafin Indo cikin dashewar Murya alamun taci kuka ta ƙoshi ta gaishe sa, amsawa yayi tare da karɓar jaririyar daga hanunta ya fita da ita, Momy kuwa kallon Indo kawai tayi kafin ta jingina kanta.
Koda Habeeb ya karɓi result ɗin MUSTAFA sosai hankalin sa ya tashi, number wayar Daddy ya kira tare da cewa yazo asibiti yanzu, Daddy baiyi wata-wata ba, take ya tashi ya garzayo asibitin, tare ya samesu da Momy tsaye kafin ya karaso yana tambayar jikin Mustafa, duban s Habeeb yayi cikin raunin Murya yace.
" Kaga Abunda nake faɗa maka ko Daddy, gashi yaje ya dawo, Daddy damuwa ce ta yiwa Mustafa yawa harta haifar masa da ciwon zuciya, mummunan ciwon zuciya kuwa, shine yake saka sa yawan tare da aman jini, sannan ya kamu da hawan jini, Daddy koda Mustafa ya tashi dole sai ya samu farin ciki kafin lafiyar sa ta ɗaure, idan kuma bai samu Abunda yake so ba, to Tabbas zuciyarsa zata buga ma'ana heart Sttack, domin kuwa yanzu ma Allah ne ya rufa asiri bai samu Sttack ɗin ba, a yanda zuciyarsa ta kamu da ciwo, Daddy dole Mustafa yana buƙatar farin ciki, yanzu akwai drip ɗin da zamu ɗaura masa, insha zaiji sassauci nan da 24 hours zai farfaɗo."
Shuru Daddy yayi yana jinjina girmar lamarin kafin ya dubi Habeeb yace.
" Allah ya basa Lafiya daga baya zamu san yanda zamu bullowar lamarin."
Duban su Momy tayi tace
" Har sai ya tashi kafin mu sama masa Abunda yake buƙata, RAUDA ce kuma babu ita cikin wannan duniyar Tabbas ɗana zai mutu, na shiga Uku, taya zan samawa Mustafa farin ciki ina son sama masa farin ciki domin ganin na rayu da ɗana bana son rasashi."
Kusa da ita Habeeb ya ƙaraso yana duban mahaifiyar tasu duban tausayi kafin ya kama hanunta yace.
" MOMY ba RAUDA bace kawai farin cikin Mustafa, Tabbas tana daga cikin farin cikin sa sai dai kuma ba ita bace jigon farin cikin sa, Tabbas Momy damuwar Mustafa yana da nasaba da INDO wacce baƙya so cikin rayuwarki wacce kika tsani ki buɗi ido ki ganta cikin gidan ki, itace farin cikin da ɗanki yake nema itace farin cikin daya kamata ki samo masa, zaki tabbatar da haka idan har ya farka da sunan ta a bakinsa, domin kuwa duk abunda yake buƙata dashi zai tashi a bakin sa."
Wani irin duba Momy take masa kafin tace.
" Wacce irin magana kake faɗa min, ta ina zan samo masa Indo a matsayin farin cikin sa, bayan a halin yanzu ta kasance haramun a garesa, matar ɗan uwansa, cemin kawai zakayi Mustafa zai mutu domin kuwa baida sauran farin ciki."
" MOMY ɗan uwana bazai mutu ba, zai tashi ya rayu cikin iyalin sa, zai rayu da matar sa da yarsa domin kuwa ba dani aka ɗaurawa Indo Aure ba, da Mustafa aka ɗaura mata Aure, Momy tun sanda naga ɗan uwana ya daina kulani ya daina zama a inda nake duk da ƙauna da shaƙuwa dake tsakanin mu, mutumin da baya son yaga damuwa ta, yakan jure ko wani irin hali zai shiga muddun ni zan samu farin ciki, amma ya kasa jure rashin Indo hakanne ya tabbatar min ba son wasa yake mata ba, tana da matuƙar mahimmanci a cikin rayuwarta, hakanne yasa na ƙudurce a raina cewa shine zai Auri Indo ba niba domin kuwa ya fini dacewa da ita na gane cewa ba son Indo nake ba tausayin ta nake haka itama Momy bani take so ba, Mustafa shine wanda take so ko yanzu Momy kika ƙarewa Indo kallo yanda ta shiga cikin damuwa na kwanciyar Mustafa rashin lafiya zai nuna miki tsantsar Soyayyar da take masa kawai halacci zata min shiyasa ta amince da Aure na, bawai dan tana sona ba, sam bani bace a cikin Zuciyarta, Mustafa shine maƙale cikin zuciyarta, hakanne yasa na roƙi Daddy alfarma bisa waɗannan hujjojin aka ɗaura Aure tsakanin Mustafa da Indo, dan Allah kiyi hkr ki amshi Indo a matsayin surkar ki, ki sassauta ƙiyayyarta cikin zuciyarki."
INDO jin maganar Habeeb take kamar almara wani irin sanyi ne yake sauƙa cikin Zuciyarta, sosai take jin wani nutsuwa na zuwar mata.
*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*
Ummu Nasmah ce
[5/13, 3:28 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘
*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*
*Cigaban*
*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘
*Na*
*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*
*(մʍʍմ ηαςʍα)*
👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*
AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*
*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty fauza ƴar Amana*
Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.
*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
*Aunty Hauwa Maman Uswan*
Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*P*••••••3️⃣1️⃣ ↗️ 3️⃣2️⃣
Naunauyar ajiyar Zuciya Momy ta sauƙe tare da furta
" ALHAMDULILLAH!! Idan har Indo itace farin cikin Mustafa, idan har samunta a matsayin matar Auren sa zaisa ya samu cikakkiyar lafiya da kwanciyar hankali, to na amince na karɓi Indo a matsayin ƴata bama suruka ba, Tabbas na gane kuskurena na ƙiyayyar da nake nunawa Indo, bansan dalilin daya sa na tsaneta ba, amma insha Allah komai ya wuce."
Hanu Momy ta miƙawa Indo alamun tazo, tashi Indo tayi tana share hawayen fuskar ta na farin ciki taje kusa da Momy, Rungume ta Momy tayi tana cewa.
" Ki yafe ni Indo nasan ni mai kuskure ne a gareki, na miki abubuwa da dama na rashin kyautawa ina mai neman afuwar ki, naso RAUDA na nuna miki ƙiyayya sai gashi UBANGIJI daya tashi nuna min ikon sa, sai ya ɗauke wacce nake so ya barni da wanda bana so domin ya nuna min muhimmancin ki a rayuwata, ya kuma ɗaurawa ɗana Soyayyar da dole sai dake zai rayu, Tabbas UBANGIJI ya nuna min girman ikon sa ."
Murmurshi mai haɗe da kuka Indo tayi tare da cewa.
" Baki taɓa min laifi ba Momy duk abunda kika min ina ɗaukar sa a matsayin tarbiyya ne, ban taɓa kwana ba tare da na yafe miki duk wani abu da kika min ba Momy."
Murmurshi Momy tayi tare da shafa kan Indo tace.
" Allah ya miki albarka ya Albarkaci Rayuwar Auren ku ita RAUDA Allah ya mata rahama ya raya Abunda ta bari bisa sunnar Manzon rahama, shi kuma Mustafa Ubangiji Allah ya tashi kafaɗunsa ya basa Lafiya."
Daga Daddy har Habeeb murmushin farin ciki suke yi kware sunji daɗin yanda UBANGIJI yasa Momy ta sassauto lokaci ɗaya, Tabbas sai an rasa wani abu ake samun wani abun Allah ya jiƙan RAUDA da rahama.
Daddy shine ya koma wajen zaman makoki yabar Habeeb tare da su Momy a asibitin, Aunty Hindu ma ta kira Daddy ta masa ta'aziya haka Momy ma ta kirata har Momy ta haɗata da Indo, anan ne Momy take sanar da Aunty Hindu Maganar Auren Mustafa da Indo sosai Aunty Hindu da sharifa sukayi farin ciki.
*****************************************
Misalin ƙarfe goma na dare Mustafa ya buɗe idonsa, cikin bacci Indo dake zaune gefen gadon yayin da Momy take kwance a bisa taburma, Habeeb kuwa yana gefe sukaji kamar wanda ake kiran sunan Indo, da sauri suka buɗe idonsu sukayo kansa.
" Indo RAUDA dan Allah kuyi hkr karku tafi ku barni dukanku lokaci ɗaya, ku taimaki Rayuwata."
Girgiza kanta Momy tayi na tausayin ɗannata, mussaman ma yafi kiran sunan Indo, INDO ce ta matso kusa dashi tana cewa.
" Ya Mustafa bazamu tafi duka mu barka, dole ne sai ɗaya ya kasance tare da kai a tsakanin mu, ka taimake mu ka tashi domin ina buƙatar ka cikin rayuwata, rasaka tamkar rasa numfashina ne, ka buɗe idon ka ka kalle ni Indon kane take magana."
Ta ƙarasa maganar tana riƙe da hanunsa, Mustafa riƙe hanun nata yayi gan, yayin da a hankali yake buɗe idonsa harya buɗe su ras a fuskar ta lumshe idanunsa yayi ya ƙara buɗewa, cikin raunin Murya yace.
" Da gaske kece kusa dani SHATUU, da gaske ne Abunda kunnuwa na suke ji min, da gaske kin amince kina sona zaki Aure ni."
Kaɗa masa kai Indo tayi tare da cewa.
" Tabbas nine nine a gabanka ya Mustafa, ina sonka fiye da yanda nake son kaina, na tabbata kasan da hakan Soyayyar ka a jini na take, da ita na girma taya kake tunanin zan iya mantawa da kai taya zan iya daina sonka, ka sani cewa yanzu ina tsaye a gabanka ne a matsayin matar ka ta Aure, wacce Daddy da kansa yasa aka ɗaura mana Aure."
Murmurshi mai haɗe da dariya Mustafa yake yi yana ƙoƙarin tashi ya zauna, tare da maida hankalin sa kan Momy da Habeeb yana murmurshi yace.
" Da gaske ne Abunda take faɗa da gaske ne an ɗaura mana Aure."
Murmurshi Momy tayi tare da cewa.
" Marassa kunya masoyan zamani, da gaske ne."
Ta faɗa masa tare da bashi labarin sadaukarwa da Habeeb ya masa, murmurshi Mustafa yake yi tare da miƙawa Habeeb hanu alamun yazo, murmurshi Habeeb yayi ya ƙarasa wajen ɗan uwansa suka Rungume juma, sosai suka yafi junan su, sai yanzu Mustafa yace.
" Ina RAUDA, tana nan ko an Kaita makwancin ta.?"
Habeeb ne yace.
" RAUDA bata nan an Kaita gidan ta na gaskiya, dan Allah ɗan uwana karka daga Hankalin ka bata buƙatar wannan a gareka addu'a take nema a wajen ka yanzu a matsayin ka na mijinta,."
Cije leɓensa yayi tare da cewa.
" Allah ya jiƙanki da rahama RAUDA Allah ya baki jin daɗi a cikin kabarin ki, nasan baki samu farin ciki a gida na ba, Allah ya baki na can, ina jaririyar ku bani ita."
Momy ce ta ɗauki jaririyar ta miƙawa Mustafa, ya karɓe ta ya juma yana kallon yarinyar yayin da ƙaunar jaririyar ke daɗa shiga cikin ransa, huɗu ba ya mata tare da miƙawa Habeeb ita yace.
" Gashi ɗan uwana, wannan itace kyautar da zan baka, kwana ki ka taɓa sanar dani cewa bincike ya tabbatar maka da cewa bazaku taɓa haihuwa ba, kaida matar ka, duk da Ita haihuwa ta UBANGIJI ne kuma insha zai baku, sai dai ga ƴata na baka kyautar ta duniya da lahira, kaine ubanta ba niba, karku taɓa nuna mata cewa nine mahaifinta, ya kasance kaine zata ɗauka a matsayin uba gareta na mata huɗu ba da sunan mahaifiyar ta."
Cikowa idanun Habeeb da Momy yayi da hawaye Tabbas Mustafa ya yiwa ɗan uwansa Hallaci, hanu Habeeb yasa ya karɓa tare da cewa.
" Bazan taɓa mantawa da wannan hallacin da ka min ba a cikin rayuwata, ada na fidda rai ga samun ɗa sai gashi lokaci ɗaya Ubangiji ya bani ƴa, Tabbas wannan yarinyar bazata taɓa kuka ba a rayuwarta, zan bata gatan da ba ko wani uba bane yake bawa ƴarsa, Allah ya raya min ƴata RAUDA ya Albarkaci Rayuwar ta."
Da ameeen duka suka amsa suna murmushin farin ciki, Indo ce ta tashi tazo gaban Habeeb ta sunkuya tare da cewa.
" Tabbas kamin alkairai da yawa a cikin rayuwata samun mutum irinka a Duniyar nan yana da matukar wahala Tabbas kai mutum ne na musamman, na gode sosai ya Habeeb bazan taɓa mantawa da alkairin ka ba a rayuwata."
Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.
" Komai mutum yayi a rayuwa kansa zai yiwa karki damu komai ya wuce tunda yanzu gaki ga masoyinki Mustafa."
Dukkan su dariya sukayi, Habeeb ya dubi Momy yace.
" MOMY tashi muje gida ki huta, ki barsa da matarsa tayi jinyar sa zuwa gobe da safe sai mu dawo, nima bari naje na kai ƴata wajen mahaifiyar ta, itama taji ɗumin jikin mamanta."
Murmurshi Momy tayi ta tashi suka fice, har sun fita Habeeb ya sake leƙowa tare da cewa.
" Asha soyayya lafiya."
Murmurshi kawai Mustafa yayi shi kuma Habeeb ya fice, Mustafa hanu ya miƙowa Indo yace tazo garesa tashi Indo tayi tazo kusa dashi ta zauna murmurshi Mustafa yayi tare da kama hanunta yace.
" Ina farin cikin samunki a matsayin matar Aure na cikar farin ciki na SHATUU, ina sonki."
" Murmurshi itama Indo tayi tare da cewa.
" Haka nima ina matuƙar farin ciki da kasancewa a matsayin ƙarƙashin Inuwar auren ka, kamin bazaka taɓa rabuwa dani ba har ƙarshen Rayuwar mu."
Murmurshi Mustafa yayi tare da cije lips ɗinsa yana jin ƙirjinsa na masa ciwo yace.
" Bazan taɓa sakaci da rayuwarki ba, zan tattalaki kamar yadda ake tattalin ƙoyi karya fashe, zan ƙauna ce ki fiye da yanda zan ƙauna ci kaina."
Murmushin jin daɗi sosai Indo tayi, kusan kwana sukayi daren ranar suna hira washe gari da safe ya kama kwanan RAUDA Uku ranar ne kuma akayi sadakar ukun kowa ya watse daga zaman makokin, yayin da ƴan uwa da abokan arziki suke garzayo wa asibitin suna gaishe da Mustafa tare da masa ta'aziya, ƴan Dasina ma har asibitin suka zo suka yiwa Mustafa Sallama a yana kwance ma check ya rubuta na dubu ɗari yace Habeeb yaje ya cire musu kuɗin ya basu, Indo ma binsu tayi taga tafiyar su tana musu Allah ya kiyaye tare da kewarsu.
a Hospital ɗin ma sun ɗaura Mustafa akan magani tare da saka masa dokoki sun kuma sanar dashi cewa ya guji sake shiga damuwa.
Kwanan sa bakwai a asibitin suka sallame sa ya dawo gida da farko part ɗinsa yaso zama, Daddy yace a'a ya ɗauki matarsa su kuma sabon part ɗin da aka yiwa INDO jere, haka kuma akayi Indo da Mustafa suka koma nasu part.
Rayuwa gudu take yayin da yau rasuwar RAUDA wata biyu, Habeeb da Hasina sosai suke kula da RAUDA ƙarama, suna son ƴarinyar sosai, mussaman Hasina ko kukan yarinyar bata son ji, tana jin ta fara kuka zata shiga damuwa harsai taga ta daina kukan.
Mustafa sosai yake samun sauƙi dan kwata-kwata yanzu baya jin ciwon ƙirjin, shaƙuwa kuwa sosai ta shiga tsakanin sa da Indo, kullum suna liƙe kamar cingum babu dare babu rana
Wata daren ranar Alhamis ne auratayya ya shiga tsakanin Indo da Mustafa a ranar abun ya zowa Indo a bazata ta kuma sha munguwar wahala wajen Mustafa, sai dai daman ai ta mace dole sai wannan daren ya risketa, Mustafa yaji daɗin yanda ya samu matarsa cikakkiyar budurwa, wannan kenan.
Rayuwa sai gudu take Yayin da Soyayya mai ƙarfi ke sake shiga tsakanin Mustafa da Indo, kwatsam rana tsaka Indo ta tashi da wani matsanancin ciwon ciki, ga zazzaɓi da yawan tashin zuciya, sosai hankalin Mustafa ya tashi, koda sukaje asibiti aka tabbatar musu cewa Indo tana ɗauke da ciki harna tsawon wata ɗaya, kuzo kuga murna da farin ciki wajen Mustafa haka suka dawo cikin farin ciki ya cigaba da tattalin matar sa.
************************************
" A'a fa Abban RAUDA karka yar min da yarinya naga sai wani faman cilla min ita, kake sama, bani ƴata kayi na kuɗin ka."
Dariya Habeeb yayi tare da cewa.
" Ikon Allah, wato dai so kike