Showing 3001 words to 6000 words out of 53497 words

Chapter 2 - SO BAI SAN JINI BA HAUSA NOVELS BY UMMU NASMAH.txt

29 Oct 2025

453

Habeeb yana kwance cikin ɗaki ko sallar la'asar ma yau a ɗaki yayita shi kaɗai, wani irin ciwo kansa yake masa, magani ya ɗauko yasha sannan ya koma ya kwanta hawaye na zuba cikin idanunsa sallamar ta da yaji shine ya sashi saurin goge hawayen sa tare da amsa mata da raunanniyar Murya, tahowa Hasina tayi tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta ta zauna gefen sa tare da cewa.

" Lafiya kuwa sweetie na na jika shuru tun ɗazu baka fito kaje masallaci ba?"

Cikin ɓoye damuwar sa shine saboda kar Hasina ta fahimci Halin da yake ciki yace mata.

" Kaine yake ciwo shiyasa kawai nayi sallah a ɗaki nasha magani, kinyi kyau fa sosai SweetHeart ɗina kin ganki kuwa kamar na sace ki na gudu" ya ƙarasa maganar cikin zolaya duk dan kar Hasina ta fahimci yana cikin damuwa.

Murmushi Hasina tayi cikin jinjinawa ƙarfin hali irin na mijinta da wasa baya basa wahala a ko wani hali yake ciki tace.

" Ayya sweetie sorry gashi har idon ka yayi ja Allah ya baka lafiya, ai ba sai ka sace niba domin kuwa ni taka ce ta har abada kaga kuwa ai babu sata tsakanin mu"

Murmushin jin daɗi Habeeb yayi tare da tashi ya ɗaura kansa a cinyar ta ya kamo tafin hanunta ya haɗa da nasa ya fara magana kamar haka.

" Kimin alƙawari HASINA zaki zauna dani a ko wani irin hali na tsinci kaina a ciki bazaki taɓa rabuwa dani ba komai tsanani komai wahala, tabbas ke ɗin matar rufin asiri ce, ina ƙaunar ki Hasina dan Allah karki rabu dani komai tsanani komai wahala kimin wannan alƙawarin."

Ya ƙarasa maganar yana danƙe hanunta cikin nasa, Hasina idanunta cikowa sukayi da hawaye domin itama tana son mijinta sosai fiye da yadda yake sonta kuma a shirye take data zauna dashi a ko wani irin hali, sunkuyowa Hasina tayi da kanta ta ɗaura a nasa kayin tace.

" *Babu ƙaddarar da ta isa ta shiga tsakani na dakai miji na komai muninta kuwa, ZAN RAYU DAKAI HAR ƘARSHEN NUMFASHI NA, DA KUMA SOYAYYAR KA ZAN KOMA GA MAHALICCINA karka damu mijina na maka alƙawarin cewa zan zauna dakai a ko wani irin hali, daɗi ko wahala ina tare dakai*."

Murmushin jin daɗi Habeeb yayi cikin ransa yake furta (tabbas nayi dacen mata ta gari mai haƙuri da juriya) dubanta yayi yana murmurshi yace.

" Ina sonki HASINA Allah ya barmin ke har ƙarshen rayuwata bazan taɓa gajiya da furta miki wannan kalmar ba *I LOVE YOU*."

MURMUSHI Hasina tayi sun juma suna tattaunawa Hasina koda wasa bata nunawa Habeeb alamar taji Abunda yayi ba, haka kuma bata sauya masa ba, tuno da girkin data ɗaura ne ya sata ɗaga kan Habeeb daga cinyar ta ta ɗaura a filo ta fita da sauri, murmurshi Habeeb yayi tare da kanƙame fulo yana tuno Indo cikin Zuciyarsa.

Mustafa kuwa ko a jikin sa harkokin sa yake domin kuwa ji yake cikin zuciyarsa ya samu Indo ya gama tunda daman can da Soyayyar sa ta taso, yasan dole zata soshi, dan haka shi baida wata damuwa, RAUDA sanda tayi sallar la'asar sannan ta shigo cikin gidan yana zaune a falo yana danna laptop ɗinsa yaji sallamar ta, amsa sallamar yayi kansa yana ga laptop ɗin ba tare daya ɗago ya kalleta ba, jikinta a matukar sanyaye ta ƙaraso gefen sa ta zauna, cikin sanyin murya tare da ƙunar Zuciya ta furta masa cewa.

" Ya Mustafa ashe daman Indo kake so, ka dinga wulaƙanta rayuwata, ya Mustafa meye laifi na danna soka? Meye laifin mutumin daya soka tsakani da Allah ya yarda ya zauna da kai cikin tsananin wahala domin ban taɓa jin daɗi koda na sakan ɗaya bane a cikin gidan nan, *SABODA ITA DAMAN KAKE WULAƘANTA NI* ni bazan hanaka Auren Indo ba, haka kuma bazan ɗaga hankali na ba, tunda nasan baka sona kaga babu wani amfani nayi kishi a kanka kuma bana tunanin zaka soni ko nan gaba bazanyi yaji dan zaka ƙara Aure ba, bare har na tona asirin aurena a gidan muba, sai dai ina son ka sani cewa zalintata da kake akwai Allah yana ji kuma yana gani shine kuma mai sakayya, ina maka fatan Alkairi game da neman aurenka Allah ya baka Sa'a."

Cikin kuka ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin tashi tabar wajen domin a yanzu taji ta fara tsanar Mustafa cikin rayuwarta muryar sa taji cikin tsawa yana cewa.

" To munafuka me kike nufi Allah ya isa kika jamin ko meye, munafuka da kike cewa akwai Allah yana ji yana gani Kuma shine mai sakayya, to daman ai shine mai sakayya, kuma nine zai sakawa da kika cuceni aka aura min ke dole ba tare da ina sonki ba, nine ya kamata na ja miki Allah ya isa domin aurenki cuta ce a gare ni, kuma bari kiji daman ni da Sa'a ta nake yawo da ita nazo duniya so bana buƙatar Addu'ar ki tunda ba uwata bace ke, idan kinga dama ki tayar da hankalin naki wannan damuwar kice ba nawa ba, ni wlh da zaki tafi gidan naku ma da kin taimake ni, dan zanfi sakewa nayi walwala idan babu ke cikin gidan nan *NA MAIMAITA MIKI INDO ITACE NAKE SO KUMA ITACE ZUCIYATA ITACE RAYUWATA GABA ƊAYA* Tashi ki ɓace min da gani mtsss." Ya karasa maganar tare da tsaki.

Shuru RAUDA tayi hawaye na gudu a kuncinta ta shige cikin ɗaki, zama tayi gefen gado tayi tagumi sai yanzu taji ta fara danasanin Auren Mustafa domin ƙiyayyar da yake mata ya fara yawa, wayarta ta ɗaga ta dannawa Zaliha kira ƴar baffan ta wanda suke ciki ɗaya, tana ɗagawa RAUDA tace " kizo gida na ki sameni ina cikin matsala Zaliha" tana gama faɗin haka ta katse kiran ta kwanta, can taji shigar text message cikin wayarta dubawa tayi taga Zaliha ce ta turo mata cewa.


" Bazan samu zuwa yau ba, amma gobe zanzo da yamma."

Allah ya kaimu RAUDA ta furta tare da kwanciya cikin tashin hankalin ƙalubalen da yake gabanta hawaye na cigaba da zuba cikin idanunta.


💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢

Ta juma sosai a gidan su zarah kafin drivern gidan ya dawo da ita gidan Aunty Hindu da Sallama ta shigo cikin falon muryar sa taji ya amsa mata da cewa.

" Ameeen Wa'alaikimussalam farin ciki na barka da dawowa."

Turus ta tsaya tana duban sa jin ya ambace ta da wani sabon suna wai *Farin ciki na* taɓe bakin ta tayi tuno da zancen Aunty Hindu na ɗazu da take cewa Barrister yana sonta, duban sa tayi ba tare da ta sanja masa fuska ba tace.

" Barrister Umar kaine tafe da la'asar haka, sannu da zuwa" ta furta masa tare da zama tana fuskantar sa.

Shima cikin happy yake kallon ta kamar zai haɗiyeta yace.

" Wlh kuwa nine tafe na jiraki harna fara ƙosawa ina kikaje haka tun ɗazu nake zaman jiran ki?"

Murmushi Indo Tayi ba tare da ta nuna masa wani sauyawa cikin fuskar ta ba tace.

" Naje gidan su Bestie nane kace kasha jirana, to sorry."

Murmushi Barrister Umar yayi cikin zolaya yace.


" Sorry for what Hajiya?"

Murmushi itama tayi kafin tace.

" Sorry for waiting me, naga kamar ka gaji da yawa na jirana dama gashi rago ne kai ɗin Allah dai yasa Ummi ta baka ruwan sanyi kasha nasanka da son ruwan sanyi."

Cikin dariya ta ƙarasa maganar tana duban sa.

Murmushi Barrister Umar yayi yace.

" Ke kuwa ina kika taɓa ganin inda uwa ta hana ɗanta ruwan sanyi ai ina zama ummi na tana kawo min ruwa, kinga aiki zan tafi nasan yanzu haka Oga Mustafa yana can yana jira na, daman na biyo na ganki ne kawai na wuce."

Jin sunan Mustafa da Indo tayi Habeeb ya ambata sai da gabanta ya faɗi, murmurshi kawai tayi tace.

" Na gode Barrister Allah ya bada Sa'a a dawo lafiya."

" Ameen bye."

Murmushi INDO tayi itama ta tashi tayi ɗaki wajen Aunty Hindu.

" Ina kika shiga A'isha? nayi zaton gida kika dawo nazo na tarar bakya nan."

" Ummi gidan su Zarah naje."

Girgiza kanta Aunty Hindu tayi ba tare da tayiwa Indo maganar Mustafa ba da Barrister Umar tace

" Daddyn ku yace bazai yiwu ki bimu Egypt saboda baya son kiyi nesa dasu yace ma gobe ki koma gida, dan haka ki haɗa kayan ki duka gobe da yamma zaki koma can."

Shuru Indo Tayi idonta ya ciko da hawaye tace.

" Yanzu Ummi tafiya zakuyi ku barni, Ummi bana son zaman gidan Momy PLS Ummi ki tafi dani dan Allah nafi son na zauna tare dake."

" Kiyi hkr Indo bai kamata muyi musu da Daddyn kuba, ki koma gabansa ki zauna ki ɗauko hakuri da juriya ki sa a cikin rayuwarki na tabbata wata rana zaki ci ribar haƙuri ki musu biyayya tamkar yanda za kiyiwa iyayenki hakan shi zaisa ki shiga ran kowa."

Sosai Indo taci kukan rabata da Aunty Hindu da Daddy Yayi amma babu yanda ta iya haka taci kukanta tayi shiru ta ɗauƙi dan gana.


Da sallama ya shiga office ɗin nasa, yana jin sallamar tasa yayi banza dashi kamar bai jiba, sanda yayi sau wajen uku kafin ya amsa da ƙyar, ƙarasowa Barrister Umar yayi ya zauna yana miƙawa Mustafa hanu, amsa yayi sukayi musabaha sannan Barrister Umar yace.

" Sorry Oga nayi let na biya wani waje ne amin afuwa, na haɗa duka infomations ɗin da kake buƙata sai dai ......."

Dakatar dashi Mustafa Yayi ta hanyar ɗaga masa hanu yace.

" Ba wannan bane a gaba na, so nake ka fara sanar dani *MENENE YAKE TSAKANIN KA DA SHATUU IDAN BAKA GANE BA INA NUFIN INDO*.?"

Shuru Barrister Umar yayi yana kallon sa Kafin ya buɗe bakin sa yace...............





*Muje zuwa yanzu aka fara wasan*🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀


*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*




*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*



*(Ummu Nasmah ce)*
[3/31, 10:00 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••5️⃣ ↗️ 6️⃣

" Meyasa kamin wannan tambayar Barrister?

Barrister Umar ya jefowa Mustafa Wannan tambayar cikin mamaki.

Murmushin gefen baki Mustafa Yayi cikin isgili ya cewa Barrister Umar.

" Wai kai a haka lauyer kake ɗaukar kanka ko? Hmmm su malam lauyer manya, a matsayinka na lauyer akwai dokar da ta ce ka maida tambaya cikin tambaya kafin amsar tambayar farko, na tambayeka baka bani amsa ba shine kake kuma jefo min wata tambaya robbish lauyer kenan kake ƙoƙarin maida kanka, da a gaban Shari'a kake tabbas da ka faɗi, ya kamata kake aiki da doka a matsayinka na Barrister, answer Question meye tsakaninka da *INDO*?"

SHURU Barrister Umar yayi na wasu lokuta dan ya ɗan ji zafin maganganun Mustafa kafin ya dubesa cikin ɓacin rai yace.

" Oga banda amsar tambayar ka ta biyu, a yanzu, sai dai ga amsar ka ta farko, ina zaton cewa zuciyata ta kamo da matsanancin ƙaunar ta, wacce take tafiya tare da ko wanni bugun numfashina Rayuwata ce ita ɗin.?"

Runtse idonsa Mustafa Yayi yana jin maganganun Barrister Umar cikin ƙwaƙwalwar sa da kunnen sa tamkar ana masa feshin wuta, buɗe idanunsa yayi waɗanda suka kaɗa suka koma jajaye lokaci ɗaya, ya fara maidawa Barrister Umar Magana son ransa.

" Ya kamata zuciyarka tayi gaggawar cire INDO cikin ta, domin kuwa Indo bazata taɓa sonka ba, kayiwa Zuciyar ka faɗa tun kafin lokaci ya ƙure maka ta kasa amfanan ka, ka tausashi numfashinka tun kafin ya fara neman ɗauke maka kana jawosa yana ƙoƙarin barin jikin ka, domin kuwa Indo ba matar Auren ka bane ina sanar dakai wannan shawarar ce a matsayina na abokinka domin ina tausayawa zuciyarka kamuwa da mungun ciwon Soyayyar wacce bazata sameta ba domin ta maka zarra."

Wani irin kallo Barrister Umar yake bin Mustafa dashi mai cike da alamomin tambaya, cikin tashin hankali Barrister Umar yake tambayar Mustafa.

" Me kake nufi da wannan maganar taka, shin Indo tana da wanda take so tuntuni ko me kake nufi.?"

Murmushi Mustafa Yayi yana duban Barrister Umar Kafin yace.

" Yes ka amsawa kanka tambayar ka, tana da wanda take tsantsar so wanda bazata taɓa iya rayuwa babu shiba, ba zata iya ciresa cikin Zuciyarta ba, wannan mutumin shine rayuwar ta, shine duniyar ta, shine farin cikin ta, dan haka ka cire kanka cikin niyyar shiga tsakanin masoya dan zakayi danasani ne a gaba marar Amfani amma shawara ce idan ka ɗauka."

Murmushi sosai Barrister Umar yayi kafin yace.

" Na fahimce ka, na kuma fahimci shi wanda kake kira tana so, sai dai kuma banga Soyayyar wani cikin Zuciyarta ba, tunda gashi na fara hango soyayyata cikin idanunta, karka damu da wahalar da zan shan indai akan Indo ne na shiryawa hakan zan iya shiga ko wani irin hali ne saboda farin cikin zuciyata, zan kuma iya karawa dashi wanda kake kira duniyar ta, *ITA MACE AI ALLURAR CIKIN RUWA CE MAI RABO SHIKE ƊAUKA* dan haka ina yiwa mai rabo fatan Alkairi, mu zuba muga wanda zai ɗauka nasan ina tafe da nasara ta a ko yaushe."

Barrister Umar yana gama faɗin haka ya sarawa Mustafa tare da juyawa ya fice daga cikin office ɗin ba tare daya ƙara sauraron Mustafa ba.

Murmushi mustafa Yayi yana yiwa Barrister Umar kallon tausayi dan yana da tabbacin cewa muddun yana raye Indo bazata taɓa son wani Namiji ba, tashi yayi ya kwashi Key's ɗinsa ganin an kusa fara kiran sallar magaruba, bai shiga cikin gidan sa ba, sai da yayi sallar magaruba sannan ya fara shiga part ɗin Momy domin kai mata hira.

Habeeb kuwa suna zaune da HASINA yaji ringine ɗin wayar sa, dubawa yayi yaga kiran Aunty Hindu ne, kallon HASINA yayi yace.

" Aunty ce take kira bari muji Allah dai yasa lafiya"

Da "ameeen" Hasina ta amsa shi kuma Habeeb ya ɗaga wayar basu wani juma ba ya katse kiran yana duban Hasina yace.

" Kira na Aunty take, tace nazo yanzu bari naje na dawo.''

Duban Habeeb tayi tace.

" Allah yasa dai lfy Ummi take neman ka yanzu kaje Allah ya dawo da kai lafiya."

" Ameen" Habeeb yace tare da ɗaukar key ɗinsa ya fice, tunda Habeeb ya fita ƙirjin Hasina yake bugawa domin kuwa tasan dole zai haɗu da Indo a can, dafe ƙirjin ta tayi tana lumshe idanunta tare da jin wani kishin Indo yana taso mata.

Cikin mintuna kaɗan Habeeb ya shiga cikin gidan Aunty Hindu, a falo ya tarar da ita tasa Indo a gaba ga akwati a gaban su Indo sai famar sharɓar kuka take, cikin sauri Habeeb ya ƙaraso wajen nasu yana cewa.

" Subhanallah! AUNTY meya faru take faman kuka haka?"

Duban sa Aunty Hindu tayi tace.

" Ko kaima ka tambaya, kiran dana maka kenan, gata nan dan kawai nace ta haɗa kayan ta, Anjuma driver ya maidata gidan ku shine take rusar wannan kukan ita dole bazata koma ba, kuma kasan Daddyn ku cewa yayi gobe tayi sammako ta dawo, shine ta koma kawai yanzu yafi tayi sammakon, tace ita dole saita jira Abban Hasina ya dawo daga Abuja kuma shi dawowarsa babu lokaci, dan wata ƙilma nice zanje canna samesa mu wuce Egypt."

Murmushi Habeeb yayi tare da zama yana duban Indo yace.

" Barni da ita Aunty jekiyi Aikin ki kawai."

Tashi Aunty Hindu tayi ta wuce bedroom ɗin ta tana yiwa Indo sababi.

Haɗa ransa Habeeb yayi yana duban Indo da itama ta maida dubanta garesa yace.


" Da a ina kike kafin Aunty Hindu tazo kasarnan okey na gane wato bakya son gidan mu saboda ba'a biya miki bukatunki ko? Ba'a miki Abunda kike so babu mai kula da lamarin ki ko okey ba damuwa wata ƙila mu bamu da Abunda zamu baki shiyasa zaki gujemu yanzu."

Zaro ido Indo tayi tana kallon Habeeb cikin yanayin tashin hankali tace.

" Me kake faɗa haka ya Habeeb babu ko daɗin ji, ya Habeeb ni kuwa ina inke da gatan daya fi wanda kamin kaida Daddy, koni butulu ce bazan ce wani gida yafi na Daddy ba, kawai na shaƙu da Ummi ne shiyasa nake ji kamar bazan iya rabuwa da ita ba, amma dan Allah ka daina faɗin wannan maganar."

" Bakya san rabuwa da Aunty Hindu amma kina son ɓacin ran daddy ko?"

Muryar Indo kamar zata sake fashewa da kuka tace.

" Ya Habeeb ya za'ayi naso ɓacin ran Daddy haba ya Habeeb ka daina faɗa min wannan maganar haka, na yadda ka tashi kawai mu tafi ka daina faɗamin."

Murmushi Habeeb yayi cikin ransa ganin harya samo kanta cikin sauƙi kafin yace.

" Jeki kuyi sallama da Aunty Hindu sai kizo mu tafi."

Tafiya Indo tayi bedroom ɗin Aunty Hindu ta sameta Zaune bakin bed ɗinta tana ninke kayan ta zama tayi gefen ta tace.

" Ummi zamu tafi da ya Habeeb

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login