Showing 39001 words to 42000 words out of 53497 words
Chapter 14 - SO BAI SAN JINI BA HAUSA NOVELS BY UMMU NASMAH.txt
suna hira kafin Habeeb ya musu sallama tare da cewa zaije gidan INNA ya kwana a ɗakin su, da farko Mama bata yadda yaje can ba a cewar ta kawai su kwana tare da Tanimu a ɗakin sa, amma sam Habeeb yaƙi, babu yanda Mama ta iya haka ta haƙura ta ƙyalesa ya tafi can ɗin, ya barsu zaune suna hira a wajen, Baba ma da ya shigo wani sabon babin hiran suka ɗaura.
Habeeb tunda ya shiga cikin gidan yake bin ɗakin Inna da kallo, yana tuno rayuwar da sukayi da ita, idanunsa ne suka ciko da hawaye yasa hanu ya goge tare da ƙara kai dubansa da ɗakinta dake kulle ɗakin su da suke sauƙa ya buɗe duk yayi ƙura, sanda ya gyara sosai ya share ko ina, wanda yasan da INNA tana nan bazai taɓa samun ɗakin da ƙura ba, fes zai samesa, fitowa yayi ya nufi randar ƙasar tata, da niyar ɗiban Ruwa yayi wanka, a bushe randar take babu ɗigon Ruwa a cikin ta, dole ta sashi ajiye bokitin ya koma ɗaki yana tunanin INNA, ya daɗe cikin takurar rashin wanka wanda ya zamo masa jiki baya iya kwanciya sai yayi sa, wayar sa ya jawo tare da kiran Daddy ya shaida masa sun isa lafiya insha Allah shima gobe zai juyo, kafin ya katse kiran ya kira Mustafa kusan six miss call mustafa baiyi picking call ɗin ba, shuru Habeeb yayi yana tunanin yanda ɗan uwan nasa yake son lalata musu ZUMUNCIN su da ƙarfin tsiya, ya rasa ya zaiyi Mustafa ya fahimce sa, ya tsani gabar da yake yi dashi yana cikin tunanin ne kiran HASINA ya shigo wayar sa ɗagawa yayi yana murmurshi sun kusa raba dare suna hira kafin ya kashe wayar ya kwanta.
**********************************
Mustafa kuwa titi ya harba ba tare daya san inda zashi ba zuciyarsa ce kawai take masa tafarfasa a yanzu kam ya yanke hukuncin cewa bazai sake komawa cikin gidan su ba, bazai iya kallon baƙin ciki ba, yana gani ɗan uwansa daya fi so a rayuwarsa ya ci amanar sa, wacce yake so Itama ta kasa fahimtar sa, ta juya masa baya, Daddy shima ya nuna masa banbanci tsakanin sa da Habeeb ya fifita Habeeb fiye dashi, ita kuma kwatakwata bata son farin cikin sa, taya zai cigaba da zama cikin mutanen da basa ƙaunar farin cikin sa, ya gwammace yaje yayi rayuwarsa shi kaɗai ba tare da kowa ba, kafin Allah yayi ikonsa a kansa dan yasan ba lallai bane ya ƙara Rayuwa mai tsayi a cikin wannan duniyar mai cike da ƙalubale a garesa, da wannan tunanin Mustafa ya isa Abnur hotel, ɗaki ya kama sannan ya dawo parking space ya bawa mai gadin hotel ɗin umarnin cewa a rufe masa motar sa da tenpol, haka kuma akayi, ɗakin Mustafa ya shiga tare da zama ya riƙe kansa dake barazanar barin jikin sa, ya rasa ya zaiyi da ransa kwanciyar hankali ya ƙaurace masa, bashi da wata nutsuwa kullum cikin tunaninta yake, ta kasa fita a zuciyarsa, baƙin ciki ya masa yawa da ƙarfi ya riƙe kansa yana runtse IDANUNSA, a daren ranar duk yacce yaso bacci ya ɗauke sa ya gagara, shawarin Kamal ne ya faɗo masa cikin rai waya ya ɗauka tare da dannawa Kamal kira bayan ya ɗauka ne yake tambayar sa, wani irin ƙwaya ranar yasa aka basa, murmurshi Kamal Yayi tare da sanar dashi sunan ƙwayar, kashe wayar gabaki ɗaya Mustafa Yayi sannan ya ɗauki wayar hotel ɗin dake cikin bedroom ɗin, ma'aikatan ya kira tare da bada umarnin cewa a nemo masa ƙwayar a kawo masa cikin mintuna kaɗan kuwa aka kawo masa tare da Pepsi karɓa Yayi ya jefa kwayar a cikin Pepsi girgizawa Yayi sannan ya ɓalle murfin ya kafa a bakin sa bai ɗaga daga bakin nasa ba sai da ya shanye tas sannan yayi wurgi da gorar gefe yana dafe kansa baifi 30 minute ba kuwa yaji ɗakin yana juya masa cikin wannan halin mayen bacci ya ɗebe sa, sosai yayi baccin shine bai farka ba sai 11am da salati a bakin sa ya furta yana duban agogon ɗakin, da sauri ya miƙe yana mamakin baccin da yayi, wani irin bacci yayi haka harya makara bai tashi yayi sallar asuba ba, tollet ya faɗa yana riƙe da kansa dake masa nauyi, alwala kawai ya ɗauro ya fito ba tare da ya tsaya wanka ba da Astagfurullah har ya ɗauki sallaya ya tada Sallah bayan ya idar ne yayi addu'oin sa, yana roƙar UBANGIJI daya mutu ya huta da baƙin cikin dake damunsa bayan ya gama addu'oin ne kuma ta faɗo masa cikin zuciyarsa, wayarsa ya jawo ya kunna tare da kulle layikansa ya sakasu a jirgi yanda kiran kowa bazai shigo masa ba, pic ɗin ta ya ƙurawa ido dake saman screen ɗin wayar tasa, hoton ta ne tun tana ƙauye, wanda Habeeb ya taɓa turo masa wani sonta ne yake ƙara fisgarsa, hawaye ne suka gangaro masa saman fuskarsa, goge hawayen yayi tare da jingina kansa jikin bango, wankan ma ji yake bazai iya ba, yana cikin wannan halin ne yaji ana masa Nocking ɗin ƙofa ko bai sani ba yasan ma'aikatan hotel ɗin ne, daga inda yake cikin nauyin Murya yace.
" Waye ne?"
Daga bakin ƙofar mahaukacin yace.
" Ma'aikacin hotel ɗinne."
" Me kuke buƙata?" Ya jefa masa tambaya.
" Breakfast ne daman muke so muji me kake bukata, sannan kuma muna son zamu gyara bedroom ɗin.?"
Cikin gajiya da maganar Mustafa yace masa.
" Kaje kawai bana buƙatar ko ɗaya yanzu idan ina buƙata zan kira ku, amma yanzu kam bani da bukata."
" Okey" ya furta tare da barin wajen."
Cigaba da tunanin sa Mustafa yayi shi yanzu Abunda yafi damunsa ma shine jinin da yake gani idan yayi tari ga wani zafi da ƙirjin sa yake masa ƙwayoyin da aka kawo masa ya ɗauka tare da ɗaukar ɗaya ya je frich ya ɗauko ruwa ya wurga ƙwayar a bakin sa domin gani yake kamar ƙwayar tana rage masa damuwar haka Mustafa ya wuni cikin maye.
RAUDA hankalin ta a matukar tashe yake tun daren jiya ta kira numbobin wayar sa yafi a ƙirga switch Off ake ce mata, koda gari ya waye a cikin wannan damuwar suka shirya breakfast ita da Mustafa a tunaninta idan gari yayi haske zai dawo amma ina shuru kake ji wai Mlm yaci shirwa babu Mustafa babu labarin sa, ƙara kiran layinsa tayi har yanzu dai switch Off, iya tashin hankali RAUDA ta shigesa, sai tayi yunƙurin tashi taje ta sanarwar su momy sai ts fasa ta koma ta zauna tana tsoro karta sanar musu kuma idan ya dawo yaci mutuncin ta yace ta haɗa sa da iyayen sa, dole yasa RAUDA ta hakura ta zauna cikin damuwa da tashin hankali, ita Abunda yafi ɗaga mata hankali ma numbobin wayar sa da suke rufe, hankalin RAUDA bai ƙara tashi ba sai da taga 11pm babu Mustafa babu labarin sa, wannan daren haka RAUDA ta kwana cikin tashin hankali, bacci kuwa gagarar ta yayi."
Habeeb kuwa tun 9pm ya shigo cikin gari Ganin kamar dare yayi shiya hanasa shiga wajen momy gara ya bari kawai sai da safe.
Habeeb daga masallaci bai koma part ɗinsa ba yayi na Momy tana lazimi ya sameta a bedroom ɗinta zama yayi ya jirata harta gama sannan ya gaisheta babu yabo babu fallasa Momy ta amsa bata Kuma tambaye sa ya dawo lafiya ba shima bai damu ba domin kuwa yasan Halin mahaifiyar sa mussaman ma idan akan abinda ya shafi Indo ne.
Suna zaune RAUDA ta shigo tana kuka, jikin Momy ta faɗa ta ƙara sakin kuka, dubanta Momy tayi tana cewa.
" Subhanallah RAUDA me yake faruwa ne haka na ganki cikin tashin hankali sai famar rera kuka kike, kuma kisan cewa mace mai ciki bata son damuwa."?
Cikin kukan tace.
" Ya mustafa Momy ya Mustafa ne."
Zabura Momy tayi tare da cewa.
" Mustafa kuma, me Mustafan ya miki faɗa kukayi ne dashi.?"
" A'a Momy ba faɗa mukayi ba, tun shekaran jiya, baya gida Momy idan na kira layinsa baya tafiya yau kwanan sa biyu kenan baya gidan Momy Hankali na yana tashe."
A zabure Momy ta miƙe tsaye cikin tashin hankali tace
" What kwanan Mustafa biyu baya gida, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un to ina yake me yake faruwa dashi na shiga Uku ni A'isha ina dana ya shiga, Allah ka rufa min asiri na kasa yana halin lafiya."
Habeeb shima cikin tashin hankali ya miƙe tsaye tare da cewa.
*Alƙalamin Rasheedat Usman*✍🏻
Ummu Nasmah ce
[5/9, 2:41 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘
*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*
*Cigaban*
*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘
*Na*
*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*
*(մʍʍմ ηαςʍα)*
👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*
AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*
*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty fauza ƴar Amana*
Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.
*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
*Aunty Hauwa Maman Uswan*
Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*P*••••••2️⃣7️⃣ ↗️ 2️⃣8️⃣
" Yanzu ke RAUDA kwanan Mutum biyu baya gida amma shine kika zauna kikayi shuru baki sanar ba tuntuni, wannan kuskure ne."
Cikin kuka RAUDA tace.
'' Ya Habeeb tun jiya naso nazo na sanar sai dai kuma ina tsoro ne karya dawo yamin faɗa yace na haɗasa da iyayen sa, shiyasa ban faɗa ba amma ina cikin tashin hankali nima Momy."
MOMY cikin faɗan itama tace.
" Faɗan banza faɗan wofi sai me idan ya miki faɗa dukanki zaiyi, gashi yanzu bamu san wani hali yake ciki ba."
Habeeb wayar sa ya ciro ya kira layin Mustafa, amma Switch Off.
" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Momy layin sa baya shiga."
Hawaye ne ya zubo a fuskar Momy cikin sauri ta sauka kasa suma binta sukayi cikin sauri bedroom ɗin Daddy ta faɗa cikin tashin hankali Daddy dake zaune yana danna loptop dinsa ne ya dago kansa ya kallesu tare da cewa.
" Lafiya kuka shigo min a firgice.?"
Cikin tashin hankali Momy tace.
" Ina lafiya kuwa Alhaji Tun jiya babu Mustafa babu labarin sa kwanan sa biyu baya gida."
Ɗaga kai yayi ya kalli Momy yace.
"Yaro ne Mustafan da za'ace ya ɓata, ina ga kawai fushi yayi yabar muku gidan saboda bamu masa biyayya ba, mun basa Abunda yake so, dan haka karku ɗagawa kanku Hankali yanda ya tafi haka zai dawo."
Wani irin kallon mamaki Momy take bin Daddy dashi kafin tace.
" Kasan Abunda kake faɗa kuwa Alhaji Mustafa shi waye da baza'a saceshi ba, karka manta da cewa munafukai sunyi yawa a cikin wannan ƙasar tamu ta Nigeria, ga ƴan kidnapping da sukayi yawa a duniya, ka daina wannan tunanin Alhaji kawai ka tashi mu san yanda zamuyi ɗana ya dawo gida."
Murmushin manya Daddy yayi cikin kwanciyar hankali yace wa Momy.
" Babu inda zanje ba kuma zan ɗaga Hankali na ba, Saboda nasan Mustafa bai ɓata ba, babu abunda ya samesa dan haka kuma ku kwantar da hankalin ku, ku basa wasu lokutan zai dawo da kansa."
Allah sarki tsakanin ɗa da uwa sai Allah barema yanda Momy take ƙaunar Mustafa fiye da dukkan ƴaƴan da ta haifa, kwatakwata Momy taƙi yadda da maganar Daddy haka shima Habeeb hankalinsa ya tashi domin kuwa baisan wani hali ɗan uwansa yake ciki ba mussaman idan yayi la'akari da yanda ƙasar ta lalace a hallakar da mutum ba wani abu bane sun ɗauki ran ɗan Adam tamkar kiyashi Momy ce ta dubi Daddy cikin ɓacin rai tace.
" Meye hujjar ka na cewa bai ɓata ba yana halin lafiya, idan kuma har da gaske kasan bai ɓata ba, to ina ɗana yake ina farin ciki na yake.?"
Murmushi Daddy Yayi tare da cewa.
" Ko ɗaya ni bansan Inda ɗanki yake ba, kawai dai zuciyata tana bani yana halin lafiya ne, kinga A'isha, leave me a long ina lissafi ne karki ɓata min lokacin."
Cikin tsawa Momy ta buɗe bakinta zatayi Magana Habeeb yayi saurin tare ta da cewa.
" Dan Allah karki ce komai Momy ni zanje na nemo ɗan uwana, na miki alƙawari zan dawo dashi gida muddun yana raye kai koma ya mutu zan dawo da gawarsa gida, muje dan Allah."
Ficewa tayi tana ƙwafa tare da cewa.
" Barema ɗana bai mutu ba yana raye insha Allah."
Bayan sun dawo falo ne Habeeb ya dubi Momy yace.
" Zan fita Momy naje na fara binciko shi ki mana addu'a Allah yasa mu dace kuma yana halin lafiya."
Da addu'ar kuwa Momy ta bishi, hankalin ta yana mungun tashe, ta rasa inda zata saka ranta, alƙawarin da suka yi da Mamy ma na komawa gun boka ta manta dashi tsabar ɓacin rai RAUDA kuwa kusa da ita ta zauna tana cigaba da kuka.
Habeeb duk inda yasan zai samu Mustafa yaje amma babu wani labari kowa cewa yake rabonsa dashi yau kwana Uku, hankalin Habeeb bai tashi ba sai yanzu duk yanda ya ɗauki abun ashe Zafin sa ya wuce nan tambayar da yake yiwa kansa shine ina Mustafa yaje, shin yana halin lafiya, shin maganar Daddy gaskiya ne fushi yayi akan INDO yabar gidan Tabbas idan haka ta faru bazai taɓa yafewa kansa ba, domin kuwa zai kasance shine silar shigar ɗan uwansa cikin wani hali da wannan tunanin ya dawo gida, ya kuma shirya ƙaryar da zaiyiwa Momy dan ganin hankalinta ya kwanta, a falo ya tarar dasu Zaune sunyi shuru suna jiran dawowar sa, kusa da Momy ya zauna tare da ƙaƙalo dariyar dole yace.
" Momy Mustafa fa yana cikin halin lafiya, kinsan yanayin aikinsu, yanzu da naje office dinsu ogansu yake sanar dani cewa, sun tafi wani ƙauye bincike, tafiyar ta taso musu ne cikin gaggawa, yace kuma ƙauyen da suke babu network shiyasa ba'a samun wayan su, akan ma yanzu zaizo ya sanar daku sai kuma na rigasa zuwa."
Ajiyar Zuciya mai nauyi Momy ta sauƙe tare da cewa.
" Alhamdulillah! Sai yanzu naji Hankali na ya kwanta, amma kuma ai shi ogan nasu bai kyauta mana ba, kamata yayi ya sanar mana tuntuni amma tunda ansan inda yake ai arziki yayi, yanzu yaushe suka ce maka zai dawo."
Shuru Habeeb yayi sai can yace.
" Gaskiya Momy sunce babu rana dan sunce binciken da aka tura su yana da matuƙar hatsari dole sai sunbi a hankali, amma may be suyi one month."
Da Allah ya kaimu Momy ta furta sannan ne hankalinta ya kwanta ita kuwa RAUDA sam bata yarda da maganar Habeeb ba, zuciyarta taƙi amincewa da Maganar tasa tashi Habeeb yayi ya nufi bedroom ɗin Daddy da Sallama ya shiga Daddy amsa gefen Daddy ya zauna yayi shuru, ganin haka da Daddy yayi ya sashi rufe system ɗinsa ya maida dubansa ga Habeeb kafin yace.
" Habeeb akwai Magana ne naga ka nutsu."
" Eh Daddy akwai Magana."
" Okey ina sauraron ka meyake faruwa.?"
" Daddy akan maganar Mustafa ne, Daddy Mustafa fa baya kusa dan duk inda ya nasan yana zuwa Daddy naje baya nan, a duba lamarin nan Daddy yanzu haka ƙarya na yiwa Momy sannan hankalinta ya kwanta na ce mata daga Office ɗin su aka tura su wani ƙauye bincike kuma ƙauyen babu network shiyasa ba'a samun wayar sa, PLS Daddy."
Murmushi Daddy Yayi kafin yace.
" Shikenan Habeeb zan saka amin bincike, insha Allah komai zaizo da sauƙi jiya munyi waya da Mlm Musa mahaifin Indo akan Maganar kai kayan da za'ayi mu tattauna dashi mun tsayar da Magana cewa babu maganar kai kayan Auren saboda wannan cutar data addabi duniya coronavirus, SO taron Auren ma nace masa bazai yiwu ayi taron biki ba, idan an ɗaura Aure kawai washegari mutum Uku ko hudu su kawo ta ya isa in suka ga ɗakinta sai su koma, kasan sati Uku kawai auren ya rage so sai kaje kayi gyare-gyaren daya zakayi idan kuma akwai taimakon da kake nema a waje na sai ka sanar dani insha Allah zan taimaka maka."
Shuru Habeeb yayi sai can yace.
'' Daddy me zai hana a dakatar da Maganar Auren yanzu mun tunkari abinda yake gaban mu, na neman ɗan uwana, Daddy bazan ji daɗin wannan auren ba, muddun ba'aji labarin ɗan uwana ba, pls Daddy a ɗaga wannan Aure har sai munga dawowar Mustafa."
Haɗa fuska Daddy yayi cikin seriours ya yiwa Habeeb Magana.
" Babu Abunda zai dakatar da wannan auren sai dai idan mutuwa akayi bari kaji na sanar dakai ɓacewar Mustafa bazai sa na ɗaga wannan auren ba, zamu cigaba da neman sa duk da ina ji a jikina Mustafa bai ɓata ba, kawai yayi fushi ne akan ban basa Auren Indo ba, kafin ya tafi kwana nawa baizo ya gaishe ni ba, ka tashi ka tafi kaima ka bani waje."
Tashi Habeeb yayi ya fita yana cewa Allah ya huci Zuciyarka Daddy, sannan ya fice a falo ya samu Momy ya mata Sallama sannan ya fita da sauri RAUDA tabi bayan sa tana cewa.
" Ya Habeeb kawai ka faɗawa Momy haka ne domin ka kwantar mata da hankali amma ina ji a jikina baka samu labarin Ya Mustafa ba pls dan Allah ya Habeeb