Showing 42001 words to 45000 words out of 53497 words
Chapter 15 - SO BAI SAN JINI BA HAUSA NOVELS BY UMMU NASMAH.txt
ka nemo min MIJINA."
Kallon tausayi Habeeb yake yiwa RAUDA kafin yace.
" Tabbas banji labarin Mustafa ba, amma ina nan ina bincike kuma Office ɗin su ma zasu taya mu bincike, sannan zanje police station na sanar karki damu insha Allah zai dawo gida cikin halin lafiya, ke dai ki cigaba da addu'a karki daga Hankalin ki komai zaizo ƙarshe."
Share hawayen ta tayi tace
" Shike nan ya Habeeb insha Allah zan cigaba da addu'a, Allah ya fito min da mijina."
" Ameeen" Habeeb yace sannan yace ta koma ɗakinta ta Zauna haka kuwa ta koma part ɗin ta amma har yanzu hawaye bai tsaya daga idanunta ba.
*****************************************
" Ke Indo wato ba zaki tashi ki je ki gaishe da Goggo ba ko, tunda kika zoki kinƙi fita ko nan da waje, yau kwanan ki Uku, ai ko ziyara kya fita, tunda dai sati Uku kacal zakiyi ki koma kuma da Auren ki maza ki tashi ki fita kije kiyi ziyara."
Tura bakinta INDO tayi tace.
" Mama wlh bana son fita ne naga gidan INNA hankali na yana tashi mussaman idan na tuno Rayuwata da ita a baya Mama ina son INNA sosai naso ace INNA taga Aure na ta kaini gidan mijina da kanta sai gashi mutuwa ta hanata ganin Aure na bare har ta kaini ɗaki na."
Ita kanta Mama sai da taji wani iri, yanda Indo ta shaƙu da INNA ko ita da ta haife ta basuyi wannan shaƙuwar ba, sai dai ya zasuyi dole suyi hkr domin kuwa shine kawai Abunda zasu iya, su mata Addu'a duban Indo tayi tace.
" Haƙuri zakiyi Indo bake kaɗai ba har muma muna jin zafin rashin INNA sai dai babu yanda muka iya dole muyi mu bita da addu'a shine kawai gatan da take buƙata yanzu a wajen dukkan masoyanta."
'' shike nan Mama zan shirya yanzu na tafi bari ma naje nayi wanka sai na fita."
Cikin murmurshi Mama tace.
" Yauwa maza shirya kije, tsaraba kam na raba na bawa kowa, sai dai na innar hansai ne zan baki ki tafi mata dashi, koda Ibrahim zan haɗaku ya ɗauki buhun shinkafar ku tafi tare."
Wanka Indo ta shiga bayan ta fito ne ta shirya ta ɗauki bag ɗin ta ta yiwa Mama sallama tare da cewa mama ta bawa Ibrahim tsarabar innar hansai ya kai musu daga baya.
Tunda ta fito Indo take ziyara duk gidan da ta sani da suna zuwa sai da ta shiga kowa yaga Indo sai yayi mamakin sauyawar da tayi, wasu kamma basa ganeta sai an musu bayani, tana hanyar ta ta zuwa gidan su Zainabu ne, ta hango kamar Garba abokin faɗanta, ƙarasawa wajen tayi ta tsaya, kusa dashi ba tare da tayi masa Sallama ne, zungure masa kai tayi tace.
" Kai Garba ɗan rainin wayo wai daman kana duniyar nan baka mutu ba.?"
Sai yanzu Garba ya gane Indo da tayi Magana yana dariya ya miƙe tsaye tare da cewa.
" Hegiya Indon INNA wai daman kece kika dawo balarabiya haka, aradu ban gane ki ba, kin dawo ƴar binni, nayi zaton ai bazaki ƙara dawowa ƙauyan nan ba, aradu tunda kika bar ƙauyen nan muka daina faɗa ahe daman kece mai jawo rigimar."
Dariya sosai Indo tayi mussaman tuno tsiyar data tsula a cikin ƙauyen, tace.
" Allah sarki yarinta kace su mai gari an huta da kai ƙara Garba an tsula tsiya fah."
Shima Garba dariyar yayi tare da cewa.
" Yanzu kam ai mun koma ga Allah, amma dai zaki wajen mai garin ki gaishe sa, naji ma ana cewa wai auren ki ya kusa, zaki Auri jikan INNA wannan ɗan gayen mai zuwa da mota, Allah sarki INNA, kamar ba azo duniya ba, Indo kema kinyi rashi aradu."
Ciccikowa idon INDO yayi da hawaye jin Garba ya ambaci INNA, kafin tace.
" Eh saura sati Uku ma Auren, ai Wlh bazanje na gaishe da mai gari ba mutumin da baya sona ya tsaneni tun da can Allah bazanje ba."
. dariya Garba yayi yana ƙara tuno rashin mutuncin Indo sun juma suna taɗin yaushe gamo kafin Indo ta wuce gidan su Zainabu, da Sallama ta shiga Goggo Hali dake tsugunne tana shara ne ta dago kanta tana amsa sallamar tare da bata wajen zama duk bata gane Indo ba sanda Indo tace.
" Sannu da aiki Goggo ya jikin Zainabu.?"
" Da sauƙin Goggo Hali ta amsa tana cewa, sai dai ban ganeki ba baiwar Allah."
Murmushi sosai Indo tayi tace.
" Haba Goggo Hali yanzu har kin mantani, Indon INNA ce fa ta wajen Baba Musa."
Salati Goggo Hali ta ɗauka tana tafa hanu tare da cewa.
" INDO wacce na sani fitinanniyar nan ƴar wajen Mairo kece haka kika koma jawur dake kamar ƴar Larabawa lallai kuwa kin samu duniya masha Allah."
Dariya Indo tayi tana cewa.
" Ehh nice Goggo yanzu Goggo Hali har nayi sauyawar da baza'a gane niba."
Ko kafin Goggo Hali ta maida mata da amsa tuni Zainabu ta fito daga ɗaki tana dariya ta zauna kusa da Indo tare da cewa.
" Mutanen birnin sai yau kika tuno damu kenan, tun shekaran jiya Lami tace min kinzo harma taje gidan naku."
" Eh tazo mun juma ma, yanzu ma haka daga gidan nata nake, na samu ma bata nan wai gaisuwar mutuwa."
" Ai Lami ba'a cika samunta a gida ba, yawon tsiya gareta, Indo munga tsaraba mun gode sosai Allah ya saka da alheri, ya haƙurin rashin INNA ban samu na miki ta'aziya ba gashi naji Lami na cewa kin dawo ne ayi bikin ki nan da sati Uku ko ki koma binni da Auren ki, Allah dai yasa da Mustafa za'ayi Auren."
Wani irin bugawa ƙirjin Indo yayi jin an soso mata inda yake mata ƙyaiƙyayi kafin tace.
" Alhamdulillah mun godewa Allah, INNA kwana ya ƙare, eh Wlh biki na ya kusa amma ba da Ya Mustafa bane, da ɗan uwansa ne ya Habeeb."
" Subhanallah kaddai ace har yanzu ya Mustafa baya sonki kece kaɗai kike haukar sonsa, amma gaskiya banji daɗin wannan labarin ba naso ace Mustafa kika aura, koda yake shi *AURE ƘADDARA CE* sai ku gama Soyayya da saurayi amma a ƙarshe sai ya kasance ba shi bane Allah ya ƙaddara mijin ka, Allah yasa haka shi yafi Alkairi."
Murmushin takaici Indo tayi kafin ta amsa da ameeen tashi tayi tace
Kinga bari na samu na gudu kar dare yayi ina son na shiga na gaishe da innar hansai kafin na wuce gida da Goggo Hali sukayi Sallama har zauren gidan Zainabu ta raka Indo, Kafin Indo ta wuce gida sanda ta shiga gidan su hansai, INNA Lami kishiyar mahaifiyar hansai ta samu zaune tana ɓarar gyaɗa kusa da ita Indo ta zauna tana ɗaukar gyaɗar ta kai bakinta kafin tace.
" SANNU da aiki INNA lami."
" Yau sannu" tare da dago kai tana kallon Indo lokaci ɗaya ta gane Indo bata yi mamakin ganinta ba domin taji labarin zuwanta yanzu ma kuwa Ibrahim ya fita ya kawo masu tsaraba, " Su Indo gidan fitina yanzu kuwa kina fitinar ko kin tuba."
Tuntsirewa da dariya Indo tayi kafin tace.
" Kai INNA Lami wato har yanzu baki manta da haura katangar banɗaki ba kenan, da ɗinma fa INNA Lami yarinta ce, kuma kinga ai yanzu na girma bazanyi ba, amma fa INNA Lami Ranar na tsula miki tsiya, Allah sarki yarinta mai daɗi."
Ta ƙarasa maganar tana dariya,
" Ta yaya zan manta da wannan Ranar da kika kusa sani fita waje tsirara, ja'ira yarinta ko tsiya, gashi kuwa ai yanzu birni ya gyara ki,."
Suna cikin hirar ne innar hansai ta fito gaisawa sukayi da ita sun juma suna hira kafin Indo ta musu sallama ta tafi, Indo har zata shige gidan su ta hango gidan INNA fasa shiga cikin gidan nasu tayi ta shige na INNA tun daga zauren gidan idanunta suka fara zubar da hawayen kallo take bin gidan dashi ta ko ina idanunta ne ya sauƙa a bedroom ɗin INNA ƙarasawa tayi tasa hanu ta tura ɗakin ta shiga ganan komai nata a ajiye komai yana nan babu abunda aka taɓa, gadon nata ta hau ta kwanta sai kuma ta fashe da kuka tana cewa.
" Allah sarki INNA kin tafi kin barni da kewarki, ganan komai naki a ajiye amma sai dai ke bakya nan, Allah ya jiƙanki INNA ashe barinki ƙauyen nan kin barsa kenan har abada bazaki dawo ba,"
Share hawayen ta tayi tana tuno Ranar data saka fararen kaya ta tsoratar da ita da mutuwa Allah sarki ashe kuma mutuwar taki tana kusa, Indo ta juma tana tuno rayuwarta da INNA, kamar wacce aka tsikara ta tashi da sauri ta ɗauki tsintsiya tahau shara, sanda ta gyara komai na gidan tana cewa.
" INNA gidan ki bazai wulaƙanta ba dan babu ranki zan cigaba da gyarawa har na bar ƙauyen nan."
INDO dai bata bar gidan INNA ba har magaruba sannan ta shiga cikin gidan su, daddare ma Sharifa ta kirata sun juma suna taɗi harta haɗata da Aunty Hindu ma suka gaisa sosai Aunty Hindu ta bawa INDO haƙuri na rashin samun halartar aurenta da bazasu yiba sakamakon bullowar wannan cutar ta coronavirus da ta tsayar da komai na duniya sun juma suna tattaunawa kafin daga baya suka kashe wayar.
**************************************
Allah sarki Rayuwa yau kimanin satin Mustafa biyu a kulle cikin hotel yayi wani irin rama har duhu yayi ga wani ƙasumba daya cike masa fuska baida aikin daya wuce ya wuni yana Shaye-Shaye wasu ƙwayoyin ma Kamal da kansa yake zuwa ya kawo masa ya koma, amma fa sanda Mustafa ya hani Kamal daya sanar da kowa inda yake, kwata kwata yanzu rayuwar Mustafa ta sauya ga shi yanzu wani sa'in haka zaita aman jini ga tari dake damunsa amma tsabar taurin kai irin na Mustafa yaƙi fita yaga likita ko ya kira likitan yazo ya dubasa, kullum kuma cikin sambatu kiran *SHATUUN SA* Yake Rayuwar sa ta koma abin tausayi.
Haka Habeeb yana cikin munguwar damuwa na rashin ɗan uwansa duk bincike da zaiyi yayi amma babu Mustafa babu labarin sa hankalin sa a matuƙar tashe yake, ko Maganar Auren nasa yanzu baya yi ɗan uwansa ne kawai a cikin ransa, haka ko kiran Indo a waya bayayi haka itama Indo bata kiran Habeeb ɗin domin kuwa kwanakin nan da Mustafa take kwana take tashi a zuciyarta ga wani irin tsinkewa da zuciyarta take yi, haka zata shiga cikin ɗaki ta yi kukanta ta goge hawayenta ta fito, RAUDA kuwa tafi kowa shiga cikin damuwa domin kuwa yanzu kuka shine ya zame mata abincin ta ta daina cin abinci, ta rame sosai tayi baƙi, ga yawan ciwo da cikin ta da ƙirjinta yake mata, duk wanda yasan RAUDA ya ganta yanzu sai ys tausaya mata, haka Momy itama tana cikin damuwa kullum cikin hawaye take tana roƙon ubangiji daya bayyana mata ɗanta, domin kuwa Habeeb ya sanar da ita gaskiyar Abunda yake faruwa ganin har yanzu babu labarin Mustafa, shine ya yanke shawarar sanar da Momy domin ta tayasa da addu'a saboda bakin uwa bashi da hijabi da UBANGIJI, wato yanzu tsabar tashin hankali Momy har mantawa take da Habeeb zai Auri Indo domin kuwa yanzu hankalin ta yana kan ɗanta, ko sanda Mamy ta kirata take sanar da ita Maganar zuwa wajen boka Momy cewa tayi ta rabu da ita kawai yanzu ba shi bane a gabanta, sosai Mamy taji haushin Abunda Momy ta gaya mata, domin kuwa bata so su tsaya iya nan ba taso ace tafi haka yagar kuɗi a wajen Momy.
DADDY yana zaune a kasuwa gabaki ɗaya yau tunanin sa yana kan ɗannasa zuwa yanzu abun ya fara basa tsoro, ya juma yana tunani duk binciken daya kamata yayi yayi amma babu wani good imfomotion, jin kiran Sallah yasa Daddy tashi ya ɗauro alwala ya shige massalaci bayan sun idar ne Daddy yana zaune a massalaci Kamal ya masa Sallama, Amsa sallamar Daddy yayi kamal ya mikawa Daddy hanu sukayi musabaha sannan ne kamal yace.
" Sunana Kamal ni abokin aikin ɗanka Mustafa ne, na kawo maka infomations ne akansa."
Maida hankalin sa Daddy Yayi kan Kamal tare da cewa.
" Bismillah ina sauraronka."
" Alhaji Mustafa ba ɓata yayi ba yana nan cikin garin nan, a nan Abnur hotel ya kama ɗaki mai no 10 yana can ya mayar da Shaye-Shaye abincin sa, babu kalar ƙwayar da Mustafa baya sha na masa faɗa amma Mustafa yaƙi dainawa na ce masa ya dawo gida nan ma yaƙi, ban san dalilin sa na barin gida ba, amma dai nasan yana Abnur hotel."
Ran Daddy yayi mungun ɓaci har wani duhu idanunsa yake masa Tabbas Mustafa yayi mungun raina sa ya ci masa mutunci, wato dan yaƙi aura masa Indo shine zai fita yabar gida, har ya koma Shaye-Shaye murmushin takaici Daddy yayi sannan ya cewa Kamal.
" Na gode sosai Yaro na gode da sanar dani halin da ɗana yake ciki, zan kuma ɗauki mataki."
Murmushin mungunta Kamal yayi tare da cewa Daddy.
" Amma Alhaji dan Allah karka sanar dashi cewa nine na faɗa maka inda yake."
" Karka damu yaro insha Allah bazan sanar dashi ba."
Godiya Kamal yayi wa Daddy kafin ya tafi, Daddy ransa ya ɓaci sosai ya kuma yi alƙawarin cewa bazai sanar da kowa halin da Mustafa yake ciki ba, Abunda ya fitar dashi daga gida shine zai dawo dashi.
*****************************************
Rana bata ƙarya sai dai uwar gijiya taji kunya, yau Alhamis gobe juma'a itace ranar daurin auren Habeeb da Indo, Momy yanzu ko Maganar Auren bata yi, saboda ba shi bane damuwar ta yanzu, yau da misalin ƙarfe biyu na rana Daddy ya dawo da akwati nan Auren Indo akwati shida Daddy ya haɗa mata
Momy ko kallo kayan basu isheta ba, Habeeb kuwa babu nairar sa cikin kayan duka Daddy shiya haɗa da kuɗin sa, HASINA da RAUDA ce kawai suka ga kayan, itama RAUDA ƙarfin hali ne kawai ya sata ganin kayan turmi talatin Daddy ya sa mata masu tsadar gaskiya kaya fa masha Allah komai yayi.
Daddy kuwa bai sanar da kowa labarin da yaji game da Mustafa ba, yayi shuru ya ƙyale maganar, haka kuma ya kwantar da hankalin sa.
*****************************************
A can Dasina kuma sosai Mama suke hidimar su da ƴan uwanta, haka maƙota duk sun shigo musu, Lami kuwa tun safe take cikin gidan, Indo tana ɗaki sai sharɓar kuka take mussaman idan ta tuno gobe ne ɗaurin Auren ta kuma da wani daban ba ya Mustafa ba, zuciyarta na mungun bugawa idan ta tuno da wannan, jin kamar Muryar Zahra ne a tsakar gidan nasu ya sata saurin goge hawayen ta ta sauko daga saman gadon Mama ta fito da sauri, Zahra ce kuwa da gudu Indo taje ta rungume ta tana mata Oyoyo, gaggaisawa Zahra tayi da jama'ar wajen kafin Indo ta kama hanunta suka fice zuwa ɗakin Mama, sanda aka kawowa Zahra ruwa tasha bayan ta huta ne Indo tace.
" Sannu da hanya, da ai nayi zaton bazaki zo ba da naga shuru tun jiya baki zoba."
Murmushi Zahra tayi tare da cewa.
" Ai kuwa da bazan zoba, saboda wannan cutar wai Abba babu ruwansa yana tsoron coronavirus gashi cikin jama'a zan shiga da ƙyar dai ummi ta lallashe sa Kafin ya barni na taho, Amarya amarya s gidan ya Habeeb sai ƙanshi fa kike hajiyata."
Cikowa idanunta sukayi da hawaye kafin tace.
"Zahra har yau ban ƙara jin labarin ya Mustafa ba, ina son sanin halin da yake ciki nasan yana cikin damuwa."
Ta ƙarasa maganar hawaye na sauƙa a idanunta, Zahra kuwa tsuka taja tare da cewa.
" Haba A'isha meyasa kika kasa ciresa a cikin ranki, karki manta fa wannan mutumin bashi zaki AURA ba gobe ɗaurin Auren ki, kuma yanzu nake jin cewa ya kamata ace kin ciresa a ranki ki yiwa kanki ƙiyamal laili karki je gidan wani da tunanin wani."
.
" Zahra kinsan dai............."
" Karki ƙarasa wannan maganar kawai ki cire shi a cikin ranki, ni yanzu ba wannan ba, ina son ki haɗani da Baba muyi Magana, saboda Ummi na ta miki komi na saitin ɗaki har kayan kitchen ta Kuma sanar da Daddy, yanzu haka nabar Ummi sun tafi miki jere."
Sosai Indo tayi farin ciki, bata yi ƙasa a gwiwwa ba ta ɗauki Zahra sukayi wajen Mama da Baba, suma sosai sukayi murna, daman kuma Baba bai sayi saitin ba, yana sone sai gobe idan za'a tafi da ita ya bada kuɗin aje birni a saya mata irin nasu na birnin.
Rana bata ƙarya yau ne juma'a Ranar ɗaurin Auren INDO da Habeeb yayin da Indo take jin wani irin mungun nauyi a cikin zuciyarta sam bata murnar wannan Aure da za'a ɗaura ita Abunda yake ɗaga mata Hankali ma, yanda Habeeb ya daina kiranta a waya ko jiya da ta kirasa ma ƙin ɗagawa yayi kuma har yanzu bai biyo kiran ba, to me yake nufi da nine, tana maganar zucin ne tana kuka, Zahra da take gefe girgiza kanta kawai tayi, domin kuwa ko bata tambaya ba tasan damuwar ƙawar tata.
MOMY kuwa yau baƙin ciki biyu ne ya haɗu mata na wannan auren da ya zama mata dole tayi haƙuri tana gani a ɗaura sa da kuma na ɓacewar ɗanta wanda yafi soyuwa a zuciyarta, tana cikin tunanin ne taga Daddy ya fito cikin manyan kaya, shida Habeeb kallon ta Daddy yayi tare da cewa.
" To A'i mufa mun shige ɗauro auren ɗanki sai ki mana addu'a."
A dole kuma cikin ƙarfin hali Momy tace.
" Allah ya dawo daku lafiya, amma yanzu dan Allah Alhaji muna cikin wannan jimamin na rashin ɗan mu shine kai kuma kake ta tafiya ɗaurin Aure, kamar wanda baka damu da rayuwar ɗanka ba."
Murmushi Daddy Yayi yace.
" Karki damu ɗanki naji labarin sa, yana nan cikin halin lafiya, yama kusa dawowa kawai yaji ya muku saboda kun hanasa Auren Indo."
Daga Habeeb har Momy kallon mamaki suke bin Daddy dashi kafin Habeeb yace.
" What Daddy