Showing 18001 words to 21000 words out of 53497 words
Chapter 7 - SO BAI SAN JINI BA HAUSA NOVELS BY UMMU NASMAH.txt
sa duk da basu gama maganar da suka fara ba, tashi Habeeb Yayi yana tangal-tangal ya fito bayan sa Mustafa ya biyo yana dariya tare da dafa kafaɗar sa yace.
" Alhamdulillah! Bros mafarkina zai cika zan mallaki shafukan Indo a matsayin matar da na daɗe ina mafarkin samu gaskiya yau DADDY ya faranta min raina ina cikin farin ciki yau."
Murmushin mai ciwo Habeeb yayi cikin danne damuwarsa ya miƙawa Mustafa hanu yace.
" Congratulation Bros kayi dacen mata Allah ya sanya Alkairi."
Murmushi mustafa yayi tsabar daɗin da yake ji yasa ya kasa gane halin damuwar da ɗan uwansa yake ciki amsa masa yayi da.
" Ameeen bros yau zan wuni cikin farin ciki."
Murmushin ƙarfin hali kawai Habeeb yake har suka rabu da Mustafa kowa yayi part ɗinsa, Habeeb zama kawai yayi a falo ya dafe ƙirjin sa yau tsabar baƙin ciki yasashi kukan ma ya kasa, a jiyar ZUCIYA kawai yake shi kaɗai yasan Abunda yake damunsa.
Can kuwa Daddy duban Momy yayi yace.
" A'ishatu ki fita a idona na rufe, ina sanar dake cewa idan kika kuskura kika kawo min matsala cikin wannan lamarin to Tabbas kisa a ranki cewa zamu samu mummunan saɓani, ranki zaiyi mungun ɓaci kina ji ko."
" Ina ji Alhaji sai dai ka sani bazan taɓa lamunta da wannan haɗin ba, bazan taɓa yadda ɗana ya auri wannan fitsararriyar YARINYAR ba wlh komai zai faru sai dai ya faru."
Tana gama faɗin haka ta juya ta haura sama kaɗa kansa Daddy Yayi yana yiwa Momy kallon rashin Hankali sannan shima ya wuce nasa bedroom ɗin.
INDO kuwa tun shigar ta bedroom ɗin nasu ta kasa sukuni tausayin Habeeb kawai take ji cikin zuciyarta, Tabbas ya mata Alkairi, to meyasa ita bazata saka masa da Alkairi ba, idan har ta bar Habeeb a cikin wannan halin Tabbas ta cika cikakkiyar butulu, idan da akwai wanda ya dace ta Aura to Habeeb ne, Mustafa sam bai dace da rayuwar ta mutumin daya dinga wulaƙanta rayuwarta mutumin daya ƙyamace ta, mutumin da kullum yake ciki hantarar mutumin da baisan darajata ba to akan meyasa zata auresa duk abunda ya mata yaci banza kenan, shi kuma ya Habeeb ya yiwa rayuwar ta Hallaci kuma har gobe a cikin mata Hallaci yake dole ma ta Saka masa, Indo takai kusan 11pm tana tunani ta kasa bacci kamar yadda haka yake shima Habeeb a garesa ya kasa sukuni muƙurƙusu kawai yake yau da wuri ya rufe bedroom ɗinsa SABODA baya so Hasina ta shigo ta samesa a Halin da yake ciki, yasan hankalin ta zai tashi sosai ita Hasina daman ta fuskanci halin da yake ciki shiyasa ma bata tunkaro bedroom ɗinsa ba, Habeeb yana cikin wannan halin ne yaji wayar sa tana ringine dubansa yakai ga screen ɗin wayar sunan Indo ya Baiyana tashi yayi tare da ɗaga wayar ba tare da Sallama ba yace.
" Meya hanaki bacci a wannan lokacin.?"
Share hawayen ta Indo tayi tace.
" Abunda ya hanaka bacci nima shiya hanani bacci, ka fito ka sameni ina tsakar gidan ku."
Cikin mamaki Habeeb yace.
" What! Tsakar gidan mu kuma taya kika fito har kika shigo nan."
" Yanzu ba lokacin Tambaya bane ka fito kawai ina jiran ka."
Katse wayar yayi ya sauƙo daga bed d'in sannan ya nufo waje
A tsaye ya ganta tana jingine jikin part ɗin nasa tsayuwa yayi yace.
" Meya fito dake cikin wannan daren?"
Kallon sa tayi Ido cikin ido sannan ta fara magana cikin raunin murya.
" Ya mutuwa zanyi zan mutu ya Habeeb."
Cikin tashin hankali ya dubeta yace.
" Wacce Irin magana kike wannan waya ce miki zaki mutu.?"
" Ya Habeeb kasani cewa muddun ka bari jibi aka kawo kayan aurena da ya Mustafa to ka sani mutuwata ce aka kawo domin a ranar zan haɗiyi zuciya na mutu."
Murmushin baƙin ciki Habeeb yayi yace.
" Babu Abunda zai kasheki karki manta da mustafan ki kika samu to me zai kasheki bayan kin samu burin ki na shekara da shekaru."
" Bana son ya mustafa kai nake ya Habeeb kaine zaɓina kuma na tabbata kaima kana sona ya Habeeb kaje ka ware Aure tsakanina da ya Mustafa ni kaine zaɓina."
Murmushin rainin hankali Habeeb yake yiwa Indo kafin yace.
" Baki taɓa ji daga bakina nace ina sonki ba, dan haka kije ki riƙe zabin iyayen ki."
Yana gama faɗin haka ya juya zai bar wajen sai yaji muryar ta tana cewa.
" Ranar Litinin itace ranar da za'a sallaci gawata domin itace ranar mutuwata Ranar da za'a kawo min bakaƙen akwati a matsayin na aure na, ka tanadi likkafani da igiya domin kaine nake son ka kaine makwancina."
A firgice ya juyo idanunsa sun sauya kala cikin firgici yake cewa.
" Bazaki taɓa mutuwa ki barni ba, ba gawa za'a sallata ba gawawwaki za'a sallata domin bazaki ke kaɗai ba sai dai mu mutu tare, ki sani duk abunda nima ya sameni idan Gurguwa kika zama to ki sani nima zan sa adda na sare ƙafafuna duka mu zauna idan kuwa tsautsayi ne afka idanunki kika makance to ki sani ba ɗan jagora zan zame miki ba, zan nemi kara ne na tsokane nawa idanun muyi dai-dai ki daina ambaton mutuwa domin kuwa kina ɗaga min hankali idan kina ambaton sa."
Murmushi Indo tayi hawaye na gudu a idanunta tace.
" Idan har baka son ganin mutuwa ta to ina so a wayewar safiya kaje ka sanar da Daddy muna son juna idan ya kirani zan tabbatar masa da hakan."
______________________________________
Tirƙashi yau ake yinta ko ya waɗannan ƴan uwa zasu kasance wai me yake shirin faruwa ne tsakanin wannan family?
Ku biyoni domin warware muku.😄
*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*
*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*
*(Ummu Nasmah ce)*
[4/12, 11:57 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘
*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*
*Cigaban*
*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘
*Na*
*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*
*(մʍʍմ ηαςʍα)*
👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*
AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*
Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.
*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*
Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya.
________________________________________
*P*•••••1️⃣7️⃣ ↗️ 1️⃣8️⃣
" Da wani Ido kike so na kalli ɗan uwana, bana son ganinsa cikin damuwa, gara kawai ni ki barni cikin damuwata bana son abunda zaisa ya ji haushi na."
" TABBAS ya Habeeb baka ƙaunar Rayuwata na tabbata da kana ƙaunar Rayuwata da zaka ceci rayuwata, na gode amma ka sani muddun baka sanar da Daddy Soyayyar mu ba ka sani babu makawa sai na mutu idan kuma na mutu sai kai ka rayu da ɗan uwanna ka kuma kaine sanadi na."
Tana gama faɗin haka ta juya a guje tabar wajen a hankali ta bugawa mai gadi get buɗewa Yayi yana cewa.
" Hajiya ai ɗazun na gaji da jiran kine shiyasa na taho Saboda kar wani abu ya faru kiyi sauri ki shige a hankali kar wani ya ganki."
Godiya Indo ta yiwa mai gadi sanna ta wuce a hankali harta shiga ɗakin sannan ta rufe a hankali tasa key still a hankali ta haura sama ta shige bedroom ɗinta, faɗawa tayi saman bed ta saki kuka mai cin rai tana cewa.
" Ina SONKA ya Mustafa Tabbas Soyayyar ka a jini na yake sai dai ka wulaƙanta rayuwata ka ƙyamaci ni ka tsangwame ni baka taɓa nuna min ƙauna ko kulawa ba a sanda nake gigin sonka duk da a lokacin ban gama sanin meye Rayuwa ba, sai dai nasan zafin Soyayyar ka duk da ƙanƙantar shekaru na, sai yanzu dana zama mutum zaka ce kai lallai kana sona, ya Mustafa ina sonka amma dole zan danne Soyayyar ka zanyi ƙoƙarin ganin na cireka a rayuwata, domin kuwa ya Habeeb shine wanda ya dace da rayuwata ina da tabbacin zan samu ingantacciyar rayuwa a wajen sa Tabbas zai kula dani zai riƙeni bisa Amana, Ya Habeeb kaine wanda zan aura insha Allah zan soka koda a gidan kane Tabbas kaine ka dace da na bawa soyayyata."
Ta ƙarasa maganar tana sakin kuka harda majina sam bata saka Abunda Momy tayi ba a cikin ranta domin kuwa idan da sabo ta saba da tsanar da Momy take mata dan haka ba tayi mamakin Abunda Momy tayi ba yau.
Habeeb kuwa komawa yayi ya zauna tare da zuba tagumi yana nazarin maganganun Indo hankalin sa yayi mungun tashi da maganganun ta domin kuwa yana jin tsoron furucin ta hanunsa ya ɗaga sama sannan yace.
" Ya Allah gani gareka ya Allah ka zaɓa min abunda yafi Alkairi a rayuwata, idan har akwai Alkairi tsakanina da Indo Allah ka bani ƙwarin gwiwwar tunkarar Daddy, idan kuma babu Alkairi tsakanin mu Allah ka cire min Soyayyar ta cikin Raina."
Kwantawa yayi tare da yin shiru a haka bacci ɓarawo ya sacesa cike da tarin mafarkai ya kwana.
Mustafa kuwa yau cikin HAPPY yake ko masifar da yake yiwa RAUDA yau bai mata ba duk da itama fama take da kanta wani sa'in sai ta wuni a ɗaki bata fito ba gobe kam tayi niyar zuwa asibiti shiyasa tana jin shigowar sa ta fito falon sannu da dawowa ta masa bisa mamakinta sai taji ya amsa cikin sakin fuska, sanar dashi tayi cewa tana son zuwa asibiti gobe DAKATAR da ita yayi yace bari ya kira likita yazo dubata babu wani ɓata lokaci kuma ya kira doctor Sadiq cikin ƙanƙanin lokaci kuwa ya iso ya dubata sosai inda ya bata har gwajin fitsari, bayan ya gama dube-duben sane ya tabbatar musu da cewa tana da shigar ciki har na tsawon wata ɗaya da sati biyu, daga Mustafa har RAUDA babu wanda baiyi farin ciki ba, mussaman Mustafa har kyauta ya yiwa doctor.
MOMY kwana tayi ba tayi bacci ba tsabar tashin Hankalin maganganun Daddy wai Jinin ta ne zai Auri Wannan fitinanniyar YARINYAR INDO ina bazai taɓa yiwuwa ba, dole na wargaza Auren nan ko ta Halin yaya ne, da wannan mungun ƙudirin Momy ta kwana.
Washe gari da safe Indo ce ta haɗa breakfast cikin sauri domin kuwa tana da lectures 11:00am bayan ta jera komai a daining ne ta haura sama tayi wanka 10:30 dai-dai ta gama shirinta sannan ta sauƙo ƙasa Momy da Daddy sai su Ishaq ta samu a daining har sun fara breakfast zama tayi tare da cewa.
" Good morning Daddy"
Murmushi Daddy Yayi yace.
" Morning my daughter da fatan kin tashi lfy."
" Lfy lau Daddy" duban Momy tayi tace.
" Good morning Momy"
Inda Indo take Momy bata kalla ba bare tasa rai zata amsa mata, girgiza kansa kawai Daddy Yayi sannan yace.
" Allah ya sauwaƙa, Ci Abincin ƴata karkiyi let ɗin school."
Cikin sanyin jiki Indo ta ɗebi abinci muryar Sharif taji yace.
" Good morning Aunty Indo."
Murmushi Indo tayi domin kuwa Momy bata sonta amma ƴaƴan ta suna sonta dalilin daya sa take haɗiye duk wani Abunda Momy take mata.
" Morning Sharif, ba zaku school bane yau."
" Eh Aunty bazamu ba sai ranar monday yau Friday."
" To Allah ya kaimu."
Shima Ishaq gaishe da ita yayi, bayan sun gama breakfast ne Indo ta tashi ta haura sama ɗauko bag ɗinta, tana haurawa su kuma Mustafa da Habeeb suna shigowa, gaishe da Daddy sukayi ya amsa cikin sakin fuska, Momy suka juyo suka gaisar amma Momy bata amsa gaisuwar Mustafa ba, ta Habeeb kawai ta amsa nanma fuskar ta a haɗe zama sukayi Habeeb da zuciyarsa ke dukan Uku Uku yana son sanar da Daddy kuma ya rasa ta inda zai fara maganganun Indo ne suke faɗo masa cikin zuciyarsa tiryan-tiryan hakanne ya basa ƙarfin gwiwwar cewa.
" Daddy ina da Magana ne, bansan kuma yaya zaka kalli maganar tawa ba.''
Maida hankalinsa Daddy Yayi ga Habeeb yace.
" Umhumm ina sauraronka sanar dani menene.?"
Kauda kansa gefe Habeeb yayi sannan yace.
" *DADDY AKWAI ALAƘAR SOYAYYA TSAKANINA DA INDO MUN JUMA MUNA SON JUNAN MU, KUSKUREN FAHIMTA KAYI INDO DA MUSTAFA SAM BABU WATA SOYAYYA TSAKANIN SU DADDY NINE WANDA YA DACE NA AURI INDO BA MUSTAFA BA.*"
Wani iri Mustafa yake jin maganganun Habeeb ji yake tamkar kunnen sa ƙarya yake masa, domin kuwa yasan ɗan uwansa bazai taɓa son abunda yasan yana so ba sai Gashi yanzu yana jin kunnen sa yana masa ƙarya, Momy kuwa cikin sauri ta ɗago idanunta tana bin Habeeb da wani mungun kallo wani irin tsanar Indo ne ya ƙara ɗarsuwa a zuciyar Momy lallai YARINYAR nan ta cika mayya tunda gashi ta lashe mata Zuciyar ƴaƴan ta duban Habeeb Mustafa yake cikin ƙaraji yayi kukan kura ya tsakumi wuyan HABEEB yace.
" Me kake cewa ka faɗa min me kake cewa! Kuna soyayya da SHATUU oh kace kuna cin amanata, kai kai kai 👉🏻 kaine zaka ci amanata Habeeb, ɗan uwana ne fa kai wanda muka kwanta ciki ɗaya da kai aka haife mu rana ɗaya muka sha nono tare muka tashi tare har girman mu bamu taɓa samun saɓani ba, bama son abunda zai taɓa ɗaya daga cikin mu, shine yau zaka ci amanata na yadda da kai ban kuma taɓa tunanin cewa zaka taɓa yunƙurin rabani da farin ciki na ba sai gashi ka ɗauko hanya idan wasa kake Habeeb ka daina domin bamu saba Irin wannan wasan da kai ba kaji ɗan uwana." Ya ƙarasa maganar yana sakin wuyan Habeeb tare da ja da baya yana huci.
Sunkuyar da kansa Habeeb yayi ya kasa haɗa Ido da Mustafa kafin ya fara cewa.
" Banci amanar kaba Ɗan uwana, ka sani babu wasa a cikin soyayya duk maganar da nake faɗa gaskiya ne kuma har zuciyata nake faɗa maka shi, nayi duk yanda zanyi dan ganin na cireta a cikin raina amma na kasa sonta har barazana yake min da rayuwata, karka ga laifi na ɗan uwana domin kuwa shi *SO BAI SAN JINI BA* idan ya tashi shiga zuciya kawai yake ba tare da tunani ko lissafi ba, da so yana da lissafi da bai shiga zuciyar ɗaya daga cikin mu ba kamata yayi kawai ya tsaya a zuciyar mutum ɗaya Ni ko Kai amma tsabar rashin adalci Irin na SO shine ya shiga zuciyoyin mu duka biyu, *SO BASHI DA HANKALI ƊAN UWANA* ka daina ganin laifi na kaida kanka ka nuna cewa baka ƙaunar Indo kasha faɗa min da bakin ka, hakanne yasa nayi sakacin barin Soyayyar ta ta shiga cikin zuciyata komai ya faru laifin kane da tun farko ka amshi Soyayyar ta kamar yadda ta nuna maka da bazan taɓa yadda sonta ya shiga zuciyata ba, bare har yamin mungun kamu, kace min kana sonta tun tana DASINA idan har da gaske ka sonta a wannan lokacin to meyasa ka ƙita kake ƙyamar ta meyasa ka kasa kula da lamuranta meyasa kake zaginta a duk sanda kuka haɗu hakan duk yana cikin SOYAYYA ne? Ka bani amsar tambayata ."
Ja da baya Mustafa yake yana nuna Habeeb da hanu yana cewa.
" Kana jinshi ko Daddy kana ji fa daddy wai SHATUU yake so numfashina yake so Daddy kasheni yake neman yi rayuwata zai karɓa Daddy, anya kuwa shi ɗan uwana ne Daddy, daddy anya ɗan uwana Habeeb ne dana sani Daddy ƙarya yake baya soyayya da SHATUU nasan ni kaɗai take so nine kawai a cikin ranta kana ji Daddy har wani banzar tambaya yake min ."
MOMY da ta gama ƙula ne ta tashi cikin fusata ta ɗauke Habeeb da tagwayen mari, sannan ta taka har gaban Mustafa shima ta ɗaukesa da mari cikin ƙaraji take cewa.
" Meye a jikinta har kuke neman raba alaƙar dake tsakanin ku, me zakuyi da ita wannan tantiriyar data gagari iyayenta sanda suka haɗota damu me zakuyi da wannan taburmar ƙayar, to bari kuji idan nine uwar ku dana sunkuya nayi naƙudar ku na rabaku da wannan YARINYAR babu ku babu ita har abada domin kuwa bazan taɓa yadda ɗaya daga......"
Tsawa Daddy ya daka mata yace.
" Ya isheki haka A'ISHA ki rufe min baki karna ƙara jin maganar ki anan wai meyasa ne kike haɗa hankalinki da tuwo kike cinyewa ne, ki kama girman ki tun kafin ƴaƴan ki su daina ganin girman ki, ki kuma sassauta wannan munguwar ƙiyayyar da kike gwadawa yarinyar nan domin kuwa baki san gaba ya zata kasance ba wata ƙila ta amfane ki fiye da ƴaƴan ki da kika haifa ki sani cewa *ƳAƳA DA DUKIYA BA'A MUSU MUGUNTA* Saboda baka san wa zai taimake ka ba gaba, ki riƙe wannan a ƙwaƙwalwar ki ƙi kuma shiga hankalin ki."
A fusace Momy tace.
" Babu wata ranar da wannan YARINYAR zata min yarinyar da bata yiwa iyayen ta rana ba wa zata yiwa Rana, nifa Alhaji ina kan bakata Wlh babu ƴaƴa na babu wannan YARINYAR."
Tana gama faɗin haka ta ɗauki jakarta da hijab ɗin ta dama unguwa zata ta fice tana jefa yarannata mungun kallo, Daddy maida hankalin sa