Showing 18001 words to 21000 words out of 81601 words

Chapter 7 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE Hausa Novels BY HAERMEEBRAH.txt

26 Oct 2025

317

ya Isa gaban ta ya miqa mata hannu, makulli ta zaro ta bashi, ya bude gidan, ya wuce bai tanka ta ba, sai ta yi dariya tace,

"ka isa yanda na b'ata rannan ka tanka ni dama humm da ka ga ruwan rashin mutunci mtseww" karaf a kunnen Auwal kuwa.

Tana aje Sulaiman a gado Yousuf  ya haye kujera ya hau baccin wahala dan ba kad'an ta wahalar da yaran nan ba, ga rana ana kod'awa, juyowar nan da za ta yi ya kifa mata mari guda uku kyawawa, tsabar gigicewa matse qafa ta yi saboda matse fitsarin da ya taho mata ba shiri,daka mata tsawa ya yi ya ce,

"Fita waje ! In ki ka min fitsari anan se kin gwammace kid'a da karatu, mahaukaciya da bata San ciwon Kan ta ba"

Da gudu ta yi waje kafin ta Isa band'aki fitsari ya kufce mata, anan tsakar gidan ta gama shi ya na gama zuba kuwa ta rushe da matsanancin kuka, tana zage2 akan me zai dake ta? Me ta masa in ba cin zali ba Allah ya isan ta ,kamar Jira kuwa ya ke ya fita a sukwane ya hau jibgar ta, Yousuf da ya farka tin a tsawar da aka daka mata ne ya tafi da gudu ya na kuka ya tsaya a tsakanin su ya kalli wannan ya kalli wancan , Sulaiman ma da ya farka ganin ana ta koke2 se ya saki nashi,nan fa gida ya rikice da koke koke kamar gidan makoki, shigewa daki Auwal ya yi yana tinanin hali irin nata, ta na nan ta na sharar bacci bata basu abun karyawa ba, ya na tinanin in Yara suka tashi me za su ci Kan a yi girki? Shi ne dalilin da ya sa ya tafi siyo masu indomie da d'an kwai tinda jiya Adnan ya basu kud'i,ya na dawowa ya gan ta da qatuwar leda ta nufi shagon da ke unguwar su ta na magana ana d'aga kayan, daga nan ya fahimci me take yi, a gaban idon shi ta hau machine da yaran shi dika ta bar unguwar, ya na nan zaman jiran ta, Kuma dan ta raina masa hankali ta dawo tana Wani cin magani tana fad'in maganganun rainin hankali akan shi ita gawurtacciya ko? Shiru Auwal ya yi ya dor'a hannun shi a Kan shi da yake Jin yana sara masa ga yunwa da ke mugun cin shi,tsaki ya ja Mai qarfi ya kalli sauran kayan da ta barbaza wasu a akwatin wasu a qasa,yanzu tsabar hauka ace ta sai da kaya masu daraja da tsada ta shigo da tarkace a madadin su,haushi kam ya shashi har ya rasa wajen aje saura, addu'ar shiriya ya mata ya miqe ya fita dan nemawa kan shi abinda zai ci da d'an shi, kwance ya ganta kan kujera tana ta kuka, tausayin ta ne ya kama shi domin ba duka qanqani ya mata ba, banza ya yi da ita ya fita, har ga Allah yana son matar shi, amma bata da hali mai kyau, qyashi da hassada, da baqin ciki sun wa rayuwar ta yawa shi Kuma ba matar da ya zaci ya aura ba kenan......

Wanda ya sai rariya ya San zata zubda ruwa ai ko?
[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼



WRITTEN   BY HAERMEEBRAERH







*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani,  ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra   3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da  kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*

Page 9:



Da asuba bayan sun idar da sallah sun gabatar da duk wasu ibadun da suke yi bayan kowacce sallahr farillah, baccin su suka koma mai cike da nishadi, Adnan ji yake kamar ya dawwama a jikin  Sakeenaah ya zamana dik inda za shi ko me zai yi ta na tare da shi, Sakeenah wata ni'ima ce da Allah ya bashi a rayuwar shi, ita alkhairi ce a gare shi ta kowacce fuska,yarinya ce ita da ta San qima da darajar Kan ta da ta mutane, ga uwa uba nutsuwa da sanin ya kamata, mace ce mai ibada da tsoron Allah, lallai shi kam ya yi dace, Allah ya dubi maraicin shi ya had'a shi da macen da ta tattara komai da yake buqata,akan ce mace ta auri mijin marainiya in ta yi dacen miji, to shi Kam ya auri matar maraya za a ce, qara qanqame ta ya y, ya kai bakin shi bayan ta ya na sumbata, cikin baccin ta take jin hakan, juyowa ta yi gaba daya itama ta rungume shi suka ci gaba da baccin su.

Basu farka ba sai wajen tara na safe, miqewa ta yi ta fara ayyukan da ta dora wa Kan ta tinda ta na da masu aiki amma ta gwammace ta yi hidimar mijin ta da kan ta, abincin karyawa ta musu sannan ta dora girkin da zata Kai wa iyayen ta, ta matsu lokacin tafiya gidan ya yi ta yi kewar su sosai,( ba lallai bane Dan Zaki gidan ku ki yi masu girki ya na dai Daga cikin kyautatawa, Dan ba kowanne miji bane Zaki dauki abincin shi ki Kai gidan ku be sa Ido akai ba, amma in gidan iyayen shi Zaki Kai se ki ga be damu ba,kaiwa naku gidan se ya zame maki abin magana Dan haka in Zaki Kai abinci gidan ku ki tabbata ba zai zama da zubewar mutuncin iyayen ki ba) qarfe  1:15pm ta gama komai, Adnan kuwa  ya na gama karyawa ya zauna a dan qaramin parlourn su da laptop d'in shi yana ayyukan shi tare da duba emails din shi, shiga goma fita goma sai ta bi ta gefen shi, ta dan masa wassanni, in ko ta wuce bata kula shi ba ze shagwabe mata fuska kamar qaramin yaron da maman shi ke aiki ta manta da shi, a haka ta gama ta hada masu ruwan wanka ta fiddo masu kaya, inda ta dakko masu wata shadda ruwan toka da ta sha aiki me kyau, daka ganta ka san an kashe kudi wajen siyan ta da dinkata, anko ya masu shi da ita, zuwa ta yi ta zauna ta ja laptop din gaban ta ta yi saving masa ayyukan shi sannan ta yi hibernating laptop din, ta juya gare shi ta na kallo shi cikin wani salo na musamman shi ɗin ma qura mata ido ya yikamar ranar ya fara ganin ta, d'an hade fuska ta yi sannan ta ce,

"To a tashi haka nan muje wanka ko"

Adnan na ganin haka ya sake shigewa cikin kujera,ya na matuqar son yanda take tarairayar shi kamar Wani qaramin yaro, a gaban ta ne kawai ya ke Iya sakin jikin shi ya yi Duk abinda yake so,hamma ya yi tare da miqa shi a dole ya gaji kamar Wanda ya yi aikin qarfi, Sakeenah na ganin haka ta girgiza Kan ta ta na Murmushi, yau Adnan shagwab'a yake ji,ita kuwa zata Yi pampering din shi kamar jinjiri, tashi ta yi ta tsaya a gaban shi, ta bashi hannun ta guda d'aya dan ya kama, Cike da kasala ya miqa mata hannun shi d'aya, yunqurawa ya yi kamar zai tashi ya ja ta ta fad'a jikin shi, dariya ya Sanya mata,

"Kin gani? Wata 'yar yarinya da ke a wajen ki ke son d'aga ni,"

Tura baki ta yi Cike da shagwab'a, sannan ta ce,

"Ni dai Dan Allah Mine mu je mu yi wanka, wannan dai ba wuni zani gida ba, tinda yanzu har kusan 2:30pm fa"

Tashi ya yi tsaye tare da ita jingine a gefen shi suka wuce wanka, sun fito ya ga ta na ta daure fuska ta qi fara'a ya kalle ta Cike da kulawa ya ce,

"Babyn Adnan me ya faru ki ke b'ata fuska?"

"Ba Kai bane ka sa muka b'ata lokaci kalli time fa, yanzu wajen 3:11pm ko sallah ba mu yi ba, ni dai gaskiya se in bar tafiyar ma se gobe na je da wuri wannan ai zuwan yamma za mu yi"

Janta ya yi jikin shi ya na qarasa balle mata bra d'in da take sanyawa, ya dauki under skirt din ta ya zura mata ya Sanya mata doguwar rigar shaddar ta sannan ya miqa mata dankwalin kayan Dan ya San yanda take saurin nan ko Kwalliya ba zata tsaya yi ba,

"I am sorry My love, yanzu zamu tafi, ki ka sani ko jinkirin da muka Yi ya zama alkhairi Adnan ya zama Daddy?ko bakya so?"

Wata iriyar kunya ce ta kama ta ta saki murmushin jin dad'i ta kwantar da jikin ta a nashi,

"Allah ya nuna min wannan ranar da na fi kowa farin ciki a rayuwa ta"

"Ameen"

Qarasa shiryawa suka yi ta shafa lipstick da powder se ta sa kwalli ta kafa dauri me kyau, Kan ta gama ya qarasa shiryawa Shima se suka tada sallah, su na idarwa suka yi addu'ar su suka rufe sashen su sai gidan su Sakeenatuwa.

****************************

A gidan Rasheedah kuwa tun safe ta yi wa yaran wanka, amma sai bata saka masu kaya ba domin ta kwana da burin zuwa gida a ranar, yousuf ta yanka wa warning din kar ya fito tsakar gida ya b'ata jikin shi, Auwal na kallon su be ce mata komai ba, Dan shi yanzu gaba d'aya lamarin ta ya fita akan shi, haka ya gama komai ya shirya ya fita bata gama abin karyawa ba,a haka ta gyara waje sama2,  ta dora masu abinci suka ci, cikin daya daga atampopin da ta siyo bayan ta Saida kayan da Sakeenah ta kawo mata tsaraba ta Kai aka dinka mata, se ta dakko  mayafin da ya dace da kayan wani shara2 me bala'in kyau ta sab'a goyon ta sannan ta yafa mayafin, ba qaramin kyau Rasheedah ta yi ba, dama can ita me kyau ce rashin halin kirki ke sa ake mantawa da kyan nata,shape din ta ya bayyana sosai a waje, ta riqo hannun Yousuf da ta wa kwalliya da kayan da Sakeenaa ta had'o masu tsaraba, shima Sulaiman kwalliyar da ta masa kenan, ga takalmi mai tsini ta saka,ta feshe jikin ta da turarukan da Sakeenaa ta kawo mata tsaraba, Arebians, qamshi ko ta ina na tashi kamar wadda tai barin turaruka a jikin ta, haka ta tako fuskar nan ta sha ado, a haka ta ja qofar gidan ta rufe da makulli ta yi gaba.

Duk inda ta gilma haka zaka ga  idon mutane na bin ta yuuuuu,a haka ta tako ta zo bakin titin unguwar su, ta dad'e tsaye tana neman abun hawa bata samu ba, masu manyan motoci sai qara rage gudu suke suna kallon ta, har wani fari take tana yanga, cikin ranta kuwa fad'i take,

"Kaiiii arziqi yayi a rayuwa, dube ni kalar babbar mota,Sam be kamata kamar ni ace yawo nake a qasa ba Mtseeww Allah ya tsinewa talauci,"

Dogon tsakin da ta ja ne ya sa Yousuf ya daga kai ya kalle ta, a haka ta samu adaidaita suka kama hanya sai gida,suna isa qofar gidan, suma su Sakeenaa na sako motar su, wani qululun baqin cikin ganin su ne ya taso mata, ji tai kamar tace a maida su gida, amma ba hali, sai su raina ta suga ko shakkar su take , ita ko Sakeenaa ta bangaren ta ba qaramin farin ciki ne ya lullube ta ba, yau zasu yi yini tare da yayar ta a gida,ta San Mama zata ji dad'i sosai, Adnan kam in ranshi yai d'ari ya baci,ji ya yi kamar su koma gida kawai, da yasan wannan uwar raqai din zata zo da basu  zo ba yau, d'aure fuska ya yi sosai ya kalli yanda matar shi ke murnar ganin yayar ta, sai ya sassauta dan kar ya b'ata ran ta,ya San halin ta yanzu tana iya jin haushin shi, fita ya yi ya buɗe mata, ta sako qafar ta waje,sai da Rasheeda ta hadiyi yawu, dan ba qaramin burge ta suka yi ba, sannan ga wani arnen takalmi a qafar Sakeenaa, mai a daidaita sahu ne yai magana,

"Malama ki ban kudina nai gaba ina da abin yi in ke ba ki da shi,"

Da ya San wacece Rasheedah da be tsokano wa Kan shi jidali ba, kamar Jira take kuwa duk wani haushin dake ranta ta fara sauke masa shi a ka, hayaniyar su ce ta ja hankalin mazan dake zaune a d'an nesa da su, daidai Sakeenaa da Adnan sun dakko warmers da suka sako abinci suna takowa wajen, sun riga matasan isowa dan haka Mai adaidaita Sahu ya maimaita me ya faru ita Kuma ta ce qarya yake zagin ta ya yi, Adnan na ji ya San me adaidaita sahu ya fita gaskiya, matasan na zuwa suka fara hayya hayya za su daki me adaidaita Adnan ya hana ya sallame su, sannan ya sallami Mai adaidaita ya bashi hakuri shi kuwa Mai adaidaita ya ja adaidaitan shi ya yi gaba ya na fad'in

" 'Yar bala'i da baqin ciki tinda ki ka hango su a mota luqeqiya ki ka hau hanqoron nishin baqin ciki ke da shiga irin motar nan kuwa se dai a qiyama in ana shiga shegiya 'yar has,"

" Uwar ka ce 'yar has d'in dan uban ka matsiyacin banza ni Wani ya Isa na Masa hassada ne kaf duniyar nan, shege mara mutunci kawai,"

Hannun ta Sakeenaa ta riqe ta ja da niyyar su shiga ciki ta fisge ta kama hannun Yousuf,

"In ki ka kama hannuna wa zai kama na d'ana? Ko dan baki san zafin su ba sai na shige na bar shi anan?"

"Ke ! ko da wasa kar ki kuskura ki b'atawa mata ta rai, ba dan  ke ta zo ba, ni da na san yau zaki zo ma da ban bar ta zuwa yau ba, to ki kiyaye ni, duk abinda ya samu iyalina ta dalilin ki ranki sai ya yi mugun baci shashasha kawai"

Cikin fushi ya wuce cikin gidan ya barsu tsaye har Sakeenaah be kula ba Dan ya San a hakan ma haushin shi take ji ya yi wa yayar ta ihu,cikin yaqe Sakeenaah ta kama hannun Yousuf suka shiga, ita kuma 'yar jarabar tana ta fama, suna isa suka tadda Adnan gaban su Abba, suna gaisawa, Mama bakin ta har kunne ganin yaran nata ga jikokin ta, cikin ranta godewa Allah kawai take tare da fatan Allah ya azurta Sakeenah itama da haifi nata, suma zama suka yi a qasa suka gaida iyayen nasu, Yousuf Abba ya kira,yana zuwa kuwa ya kama guiwa shima ya yi gaisuwa, dariya aka sa a wajen dika, banda Rasheedah, Sakeenah cikin dariya ta ce,

"Lallai Yousuf ka gaji ni wajen gai suwa ko Maa? Haka kk ce ina yi sanda ina qarama ko?"

" kwarai kuwa haka kk yi, ko wa kk gani har wanda baki sani ba sai kin dafe guiwa kin kai gaisuwa,"

Dariya aka qara sawa, Rasheedah kuwa da haushin maganar su ya kama ta se ta kyab'e baki ta ce,

"Hmmm to ai sai ki bari in kk sillibo naki sun yi koyi dake, amma wannan mahaifin shi ya gada, dan baban shi ma haka yake,"

Ta qarasa maganar ta tana wani marmara ido, baki iyayen suka sake, Sakeenaah ko yaqe ta yi tace,

"Auu habaa, Allah sarki,"

Ba ta son iyayen su San cewa har yanzu basu jituwa, amma Abba sai da ya gane, cikin d'an had'e fuska ya ce,

"Ke wai dan Allah yaushe zaki yi hankali, yaushe zaki gane irin son da qanwar ki take maki, bazaki na koyi da kyawawan halayen ta ba kema ki zama ta gari? Kullum qara baud'ewa kike kamar saniya?"

Aiko ran Rasheedah in ya yi dubu ya baci da Jin Kalaman mahaifin nata akan ta, wato ita ce ma saniyar? Adnan kuwa na Jin haka ya yi caraf ya cafe maganar da cewa,

"Ai Abba dama ina da niyyar zuwa na fad'a maku irin wadannan abubuwan da Rasheedah ke yi wa Sakeenah, amma in na tuna Sakeenaa ta ji na kawo qarar Rasheedah wajen ku ranta zai b'aci yake sa na bar maganar,amma damuwar da Rasheedah ke kunsawa Sakeenaa ba kad'an bace da kuwa kwanaki har likita cewa ya yi ta rage damuwa dan ko gab take da kamuwa da hawan jini, kuma wannan baiwar Allah itace sanadi,"

Dik abubuwan da ke faruwa Adnan be rage ba ya sanar da iyayen nasu, wanda hakan ba qaramin kuka ya saka Sakeenaah ba, sannan ta ji haushi matuqa da Adnan ya zayyana wannan abu gaban iyayen su, a nashi bangaren ya fad'a ne dan wataqila in iyayen suka yi ma Rasheedah fad'a zata nutsu ta kyale masa matar shi ta dena hantarar ta da nuna mata tsanana fili, bai san cewa duk fad'an da za a wa Rasheedahn ba qara mata tsanar Sakeenaahr ze yi fiye da da, ji take kamar ta tashi ta shaqe ta ta mutu kowa ya huta, hakuri iyayen suka bata bayan sun gama wa Rasheedah fada, hira aka koma yi, ana raha amma zuciyoyin su ba dad'i,musamman Sakeenaah data ke jin haushin Adnan na fadan wannan abun,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login