Showing 75001 words to 78000 words out of 81601 words

Chapter 26 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE Hausa Novels BY HAERMEEBRAH.txt

26 Oct 2025

328

kowa laifin ta zai gani musamman Mama zata ga bata sauya halin ta ba dama qarya take, duk girman ta da manyan yara ace wai wata na juyata haka hummmm rayuwa kenan?

Amarya ce ta debi chips ta had'a da kwai ta kai bakin Auwal, cike da jin dad'i ya bud'e baki ya amsa,cikin ran shi ya ke ayyana...

' Oh rayuwa kenan ashe nima da rabona a soyayya'

A hankali ya tauna yana lumshe ido, ji yayi an sumbaci saman idanun shi dake rufe,ya bud'e ido se ya ga Khadeejah ce cikin yanga ta ce,

"An kuwa tab'a fad'a maka kai d'in kyakkyawa ne? Da kai haka baka ji yanda kasa zuciya ta gudu ba, tab'a ma kaji,"

Kafin Auwal ya yi magana ta ja hannun sa ta dora akan qirjin ta, shiko yana jin ya damqi cikakku kuma tsayyayun na fillos har wani danna hannun shi yake wai zai jiyo zuciyar ta ta, dukan table d'in Rasheedah ta yi da hannayen ta biyu ta miqe tsaye,nan take suka maida hankalin su kan ta,

" Ba zan iya d'aukan wannan barikancin ba Auwal akan me....,"

Maganar ta ce ta katse saboda kallon da Amaryar ta wurga mata me matuqar rikitar wa,ai kuwa ba qaramin kidimata kallon ya yi ba, anya yarinyar nan ba asiri ta musu ba dika? Ta mallake miji dan kawai ta gana mata azaba,kamar daga sama ta ji Amarya ta fashe da kuka, harda shessheqa, cikin b'ata rai Auwal ya ce wa Rasheedahn,

"Bata hakuri,"

Rasheedah kuwa Imani ya mata yawa kawai se ta sake baki,cike da wata gigittaciyar tsawa da tinda suke bata tab'a ji ya yi irin ta ba ya maimaita cewa ta bawa Amarya hakuri,a rud'e ta ba Amaryar hakuri, kamar an kashe redio kuwa ta yi dif, ta lafe a jikin Auwal, sannan ya umarci Rasheedah da ta koma ta zauna, hawaye ne kawai ke gudu a idanun ta, quncin da take ji a zuciyar ta bata Jin zata Iya ci gaba da zama a gidan nan, saboda da dikkan alamu amaryar nan ta zo ne da niyyar kassara rayuwar ta,Auwal d'in ta ne fa, Wanda ke shanye dik Wani rashin mutunci da wulaqanci ta, Auwal d'in ta da ke susucewa akan ta ya b'ata lokaci wajen gwada mata soyayya, Auwal d'in ta ne fa uban yaran ta, amma a yanzu Yana neman fin qarfin ta, cikin kwana d'aya yarinya qarama ta gigita shi ta sa ya fita hayyacin sa, anya zata Iya rayuwa a haka kuwa? A hankali ta koma ta zauna ta na share hawayen ta da suka kasa dena zuba

"Zauna ki ci abinci da kyau Ina Gani salon ki zo yunwa ta kama ki ki rame ko ciwo ya kama ki ace bana adalci a tsakanin ku ko?"

Zama ta gyara tana hawaye tana tura abincin, yau 'yar cikin ta ke mata mugun abu haka? Oh duniya kenan juyi2, Auwal ne ya d'ebi farfesu ya Kai bakin shi sannan ya deb'o ya ce wa amarya ta bud'e baki ba zafi, ta na bud'e wa ya zuba mata a bakin ta hau taunawa cikin yanga, itama ta d'auki spoon ta d'iba ta bashi,  a haka suka ciyar da juna suka qoshi, Suna ta zuba soyayyar su,zuciyar Rasheeda kamar ta daina aiki haka take ji,ango da amarya sun lula duniyar soyayya ta zame jikin ta a hankali ta yi d'aki, ta na shiga ta rufe qofar da qarfi ta saki wani wahalallen kuka, yi take tana qarawa ba mai lallashi, haka ake ji a kishi, ko ita kad'ai ce ke jin haka?

Tinda ita bata son a had'a ta da kishiya a komai nata, sai ta ji baqin cikin duniya ya mamaye mata rayuwar ta, ashe kishin miji ya fi zafi akan kowanne kishi, da kyar ta daddafa ta hau gado,ta jima kafin bacci mai dad'i ya d'ebe ta.

Bayan sun gama ne sukai wanka,suka shirya cikin shiga mai kyau, zasu tafi gaidan  su Abban, Leqawa Amarya tai dakin Rasheedah tace mata, ya kamata ta fara hada abincin rana zasu dan zagaya gidan su dawo,cike da umarni take fadan hakan, kuma fried rice za tai da coleslow, sai salad din dankalin daban, dan ita bata son ganye, Auwal yaci wancan, ita taci wannan, sai ta hada masu kunun aya, sannan ta gasa masu nama ya yi dan ruwa-ruwa,

" kinsan ni har yanzu ba wai na warke daga ciwukan da honey  ya jiman bane, lallai kina fama dama haka yake? Ayi ta abu d'aya ba ya gajiya? Lallai ki na fama"

Cike da zolaya ta sa kai ta bar d'akin ta bar Rasheedah na sharar kwalla, a mota ta same shi, zaune ya na jiran ta, bud'e mata ya yi ta hanyar miqa hannun shi ta shiga ta zauna ya ja su sai babban gidan su Adnan, inda su Mama da Abban su Rasheedah ke zaune a yanzu.

 Suna Isa Mai gadi ya bud'e masu gate, suka gaisa da Auwal da Khadeejah sannan suka qarasa ciki, hannun Khadeejah na cikin na Auwal suka Isa bakin qofar shiga sashen su Mama, da sauri ta karb'e hannun ta Cike da Jin nauyi ta yi gaba, abubuwan ta na ba shi mamaki, a gida ta zage ta na ta zuba masa soyayya, amma yanzu wai kunya take ji, Murmushi ya yi ya kad'a Kai ya bi bayan ta.

Zaune ya hango su Yousuf da Atiyyaerh wadda ta shagwabe ma Yousuf d'in kamar zata shige cikin shi shi kuma yana ta wani lallashin ta, suna ganin su Abba Auwal suka nutsu, suka durqusa su na kai gaisuwa, a hankali kowa ya hallara a parlourn da yake Babba sosai, Sulaiman da Walida, Daddy da Fauziyya ustaza wadda ta sha doguwar riga ta nade kan ta da mayafin ta,fuskar ta ba wata kwalliya sosai amma tayi kyau daidai ita,Mama da d'an tsohon mijin ta ne suka zauna a kujera Mai d'aukan mutum biyu, nan aka hau barkwanci da gaishe2 ana tsaka da gaishe gaishen kowa ya kula ba Rasheedah suka zo, Atiyyaerh ce tace,

"Abbah ina ummana?"

Khadeejah ce ta amshe da cewa,

"Tana bacci ne da za mu fito se naga bai kamata mu tada ita ba, shiyasa muka taho,"

kallon ta Atiyyaerh ta yi tai murmushin yaqe,dan gani take kamar ba gaskiya ta fad'a ba, ana ta hira ta yafici Yousuf suka zame jikin su suka bar gidan, a motar Yousuf d'in da Adnan ya sai masa suka fita, ko da suka shiga gidan sun same ta ne a zaune, Umman nata ta rafka uban tagumi tana kuka dan tin da amarya ta gama mata bayanin me zata dafa take zaune take kuka,ba abinda ya bata ranta sai kalmar ta ta qarshe, akan halittar mijin da take taqama nata ne ita daya, yau ga wata 'yar cikin ta na yabawa  halittar shi a gaban ta, tina hakan ne ya sa ta fashe da kuka,

Da gudu Atiyyaerh ta Isa gaban ta ta durqusa tare da kama hannayen ta ta ce,

"Subhanallahi, Ummana me ya faru? Me matar can ta yi miki, dan da ganin matar nan za ta yi mugun hali, "

Cikin tsananin kuka Rasheedah ta sake riqe hannun Atiyyaerh da kyau ta na qoqarin durqusawa a gaban ta ta ce,

" Atiyyaerh ki yafe min, in baki yafe min ba ba zan tab'a ganin daidai ba a rayuwa ta, matar nan so take ta sa zuciyata ta tarwatse, ban tab'a sanin haka kishi yake da ciwo ba sai yanzu, ashe da hassada ce ke d'awainiya da ni, na rasa gane tsakanin cutar hassada data kishi waccece tafi zafi, gaba d'aya ina da su Yousuf, tabbas ina daf da fad'awa jerin masu ciwon zuciya, Atiyyaerh ba kiji yanda qirji na ke bugawa ba,"

Tana kaiwa nan a maganar ta se ta tina d'azu da Amarya ta dorawa Auwal hannun shi akan qirjin ta,wani kuka ta saki me qarfi kamar wata qaramar yarinya, hakan da ta yi ya yi matuqar ba Atiyyaerh tsoro, kar Umman tasu ta kamu da wani ciwon fa, kamar wadda aka mintsine su ka ga umman sun ta miqe ta daura dankwali ta yi waje,bin ta Atiyyaerh ta yi itama, a kitchen ta same ta, tana qoqarin d'ora abinci, haduwa suka yi ta taya ta suka yi komai a tare suka gama, Atiyyaerh ce ta dinga d'iban abincin ta na sa wa a motar Yousuf , sannan suka shirya har Rasheedah suka nufi can babban gidan.

Khadeejah na ganin Suna shiga da warmers na abinci se ta yii murmushi kawai, tare da jinjinawa zuciya mai kyau irin ta Atiyyaerh, dan in itace sai Rasheeda ta gane shayi ruwa ne, bata ce komai ba ta yi mata sannu da aiki, itama bata nuna mata komai ba ta amsa, da yauwa,

Atiyyaerh ji ta yi an dafa kafad'ar ta sannan aka ce,

"Abun haka ne Aunty Atee ba gayya a aikin? Yaushe ma ki ka bar gidan?"

Ta na juyawa se ta ga walida ce ashe matar Sulaiman, Murmushi ta mata kawai, ta ce,

"Ba komai amaryar mu ki huta,wataran kema zaki yi naki ai,"

Tashi suka yi dikan su suka gyara inda za a ci abincin, kallon Rasheedah da ke rakub'e a kujera Atiyyaerh ta yi kamar kazar da kwai ya fashewa haka ta biyo su zalo2, gaisuwa ta kai wajen su Abbah da Adnan da hankalin shi ke kan matar shi,ita kuma sauran yaran suka gaida ta,ana ta hira amma banda ita ta yi shiru kamar marainiya, Auwal na ta saka ta a hirar amma shiru kk ji, dan ita yanzu tsoron su take, in sunkoma kuma su gasa ta, bangaren Mama kuma ta ji dad'in ganin sauyawar ta, a tinanin ta jan girman ta take yi.

A haka suka tashi bayan sunci sun sha, mazan suka wuce masjid matan suka tattara wajen suka gyara kowa ta yi bangaren ta, Atiyyaerh ta taya su Rasheedah debe kaya suka mayar mota su Rasheedah suka shiga mota suka bar gidan.

Atiyyaerh ta kasa bacci cikin dare, sai juya abinda ta gani take a ran ta, ta San irin rayuwar kana so ka yi abu amma a hana ka, ta yanda ko magana ba ka da izinin yi sai an Hana ka, juyi ta yi ta rungume Yousuf da ya yi shiru ya na kallon sama, a hankali ta ce

" Yayah ni kam nace ko za a samo wa Umma yar aiki ne, kasan bata wani saba da aiki ba,gashi yanzu ba ita kad'ai bace akwai kishiya, kar aiki yazo yana mata yawa,"

"Batta kawai zata iya, aikowa neman ladan aure yake itama a barta ta nemi ladan nata auren"

Ya ja ta jikin shi da kyau,ya kwantar da ita, gaba d'aya hankalin ta baya jikin ta, ya na can wajen tunanin halin da Umman ta ke ciki.

Cikin ikon Allah Walida da Atiyyaerh nada wata biyar a gidan suka samu ciki,cikin walida nada wata uku, Atiyyaerh na da wata hud'u, ba qaramin murna kowa ya yi ba da samuwar cikin nasu, musamman ma cikin Atiyyaerh Mama ta ji tsoron kar itama ta yi jinkiri irin na Sakeenaah se gashi cikin qanqanin lokaci ta samu,se da ta yi wata rashin lafiya ne kowa ya San ta na da cikin dan boyewa take, wai kunya take ji, Sulaiman ya sha fadawa Yayahn shi hasashen shi na anya Atiyyaerh bata da ciki kamar walidan shi?  Sai Yousuf d'in yace,

"kaii anya kuwa ! Yanzu Kai wannan marar ce za a ce akwai d'an mutum? Inaaa bana Jin ta na d'auke da ciki gaskiya"

Haka Sulaiman ke barin maganar ba dan ya yarda cewar babu d'in ba,to fa sai da ta yi wannan zazzabin mai zafi aka je asibiti aka tabbatar akwai sannan Yousuf ya yarda,ranar kuwa kowa ya ga rawar Kai a wajen shi ji ya dinga yi  kamar zai hadiye ta dan murna, ta roqe shi ya rage rawar Kai ya qi, Suna barin asibiti basu zame ko Ina ba sai gida, a babban parlour ya kwaza labarin samuwar cikin nata, ta hanyar tsokanar Mama zata samu d'an jikar ta ta wajen su ba da jimawa ba, aiko Atiyyaerh ji ta yi kamar qasa ta bud'e ta shige dan kunya.

"To da ka ke ta fad'a wa mutane ai ba ni kad'ai bace, har da Walidah da Afrah,"

Ta fad'a ta na tura baki, dariya aka Sanya Baki d'aya, Mama na ta godewa Allah a cikin zuciyar ta da bakin ta, ganin yanda ta gama rayuwa da Ahmad ba labarin ciki ya Sanya ta tsoron ko itama zata yi jinkirin haihuwa irin na Sakeenah se gashi abun farin cikin ya samu da wuri, Daddy Adnan kuwa kallon 'yar tashi yake Cike da so da qauna da tausayawa irin ta d'a da mahaifi, fatan alkhairi da Sanya albarka iyayen nasu suka musu, tsabar kunya ko amsawa bata yi ba ta gudu d'aki aka bar Yousuf da amsawa da bada labarin sunan da yake so a Sanya in macece, in namiji ne ga sunan da yake so,dariya kawai akai ta mishi saboda sai halin shi na 'yan fari ya bayyana a ranar, Sulaiman ne me Jin kunya shi kuwa Sam be ga abun kunya ba a wajen.

Sanda labarin ya riski Rasheedah kuwa ta yi murna sosai,ta Sanya albarka tare da fatan Allah ya sauke su lafiya.

Bayan shekara shida, gidan su Atiyyaerh ya zama babban gidan iyali, Atiyyaerh na da yara hud'u,haihuwar ta ta fari ta samu d'iya mace suka Sanya mata sunan marigayiya wato Sakeenah sai Kuma aka samu Mai sunan Abbah daga baya Kuma ta haifi 'yan biyu mata, Walida Kuma nada yara uku,dika maza, babban dan Afrah a nan gidan yake da zama, mai sunan Adnan, takwaran daddy kenan, khadeejah na da Yara biyu mace da namiji aka sake maimaita sunan Sakeenaah  namijin Kuma Hisham, sai Fauziyyah wadda ke dauke da cikin fari yanzu, Adnan yana fatan ta haifi mace ya Sanya mata sunan Sakeenaah,gani yake in za a cike gidan da suna Sakeenaah ba laifi bane.

Atiyyaerh da Yousuf ne Kwance a babbar kujera a parlourn su Suna ta hirar wajen aikin Yousuf d'in Yana Sanar mata qarin matsayin da ya samu ta na ta zuba masa addu'a, suka Jiyo kukan Little wato Auwal qarami, Wanda shi ne autan Atiyyaerh, Rasheedah ce ke d'auke da shi a hannun ta, ta na tafe ta na mitar ya hana su bacci,kwanan ta goma sha uku a gidan ta zo wajen Mama dan jinyar ta saboda fama da take da ciwon qafafu ,kukan da ya sake tsanyarawa ne ya sa Atiyyaerh tashi zaune da kyau dan ta ji shin shi din ne ko yaya? Da sallama ta shiga parlourn ta miqa wa Atiyyaerh shi sannan ta ce,

"To ga shi nan na dawo da Kai wajen Ammin taka,dan nema me rikicin tsiya, in sake zuwa ka ce zaka bini, ya hana mutane bacci,sai kace a dawa yake, ba a cikin gida ba,"

Dariya Atiyyaerh ta yi ta rungume shi sannan ta ce,

"Yi shiru Babana na kainaaa, Umma dai haushi take ji ka ce baka auren da ita, shi yasa rabu da ita ba za ka sai mata ragon sallah ba bana"

"Yo wannan Banda aukin zuba Kashi da fitsari a tsaye me ya sani?"

A hankali Atiyyaerh ta lallab'a shi ya koma bacci sannan ta je d'aki ta kwantar da shi ta dawo,

"Haka yake yi fa ko cikin dare sai ya baro d'akin su yazo wajena,Abbin su ya yi ta fad'a wai ni ke sangarta shi shi ya sa ya cika d'afa,ko yaron ma nawa yake oho"

"Aiko dai ya cika d'afa da gaske haba, Ina ne baya shiga da wannan siraran qafafun nashi kamar na sauro, amma da ya yi bacci a Wani wajen se an kawo miki shi"

Dariya suka yi dika Yousuf ya ce

"Ai gobe zai je ya ga budurwar shi can gidan Afrah Yaya zai Kai mu mu yini mata an kwana biyu ba a had'u ba" Yousuf ne ya kalle ta ya had'e gira sannan ya shafa gemun shi da ya ke tsaye a saman fuskar shi, sannan ya ce,

"Wai ke waya baki izini ne har ki ke lissafin fita? Tabbas kin tambaya amma ban fa ce na yarda ba,"

Cike da shagwab'a ta kalli Umman tasu da ke bin su da kallon burgewa ta ce,

" Ummaaa,"

Ta tura baki gaba ta na jiran taimakon Rasheedahn, cikin Murmushi Mai sauti ta ce,

"A'a Yousuf, ka barsu su sada zumunci mana ni Rasheedah na ga illar rashin son zumunci a rayuwa ta Wanda bana fatan daidai da daqiqa d'aya Allah ya sa Wani a zuri'a ta ya yi irin wannan halin, ko da wasa kar kana son raba abinda Allah ya riga ya had'a yake son kuma a dabbaqa shi,"

Cike da ladabi ya amince masu da tafiyar, Umman su na fita Atiyyaerh ta haye cinyar shi ta na murna,dan ita fa a kullum Jin ta take kamar wata qaramar yarinya bata Jin ta girma Sam sam,

"Dole ne a baka tukuicin barin mu zuwa unguwa da ka yi Mijin Ablaerh,"

Tini Atiyyaerh ta hau birkita masa lissafin kan shi, cikin in Ina ya ce,

"Daga yau ki dinga tambayar unguwa dik qarshen wata zan dinga barin ki indai wannan ne tukuici na"

Ta bangaren Rasheedah da amaryar ta kuwa komai ya wuce kamar Wani saba'ni be tab'a shiga tsakanin su ba, girmamawa sosai Khadeejah ke Yi w
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼






 WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH


*Ina masu tambayar yaushe za a gama Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA?   To ina mai yi maku albishir da samuwar Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA dan kuwa ya kammalu ya zama ready, ga masu so su mallaki nasu ku yi min magana ta 09031416423 idan an yi payment ɗin #500 ta wannan account ɗin 0006366584 Ja'iz bank, Hamida Sanusi Ahmad,zan tura wa mutum nashi da yardar Allah...kar ku bari labarin Muid'o da Jiddah ya wuce ku💃🏻❤️*

*Duk mai son ta koyi yanda zata haɗa kayan gyaran jiki domin  sana'a ta neme ni a 09031416423 Dan ta mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA A FARASHIN #1000 kacal*

Page 32:

Yau kwana hud'u kenan da dawowar Adnan daga Dubai,tin sanda ya je balcony d'in shi ya ga me kama da marigayiya be sake komawa ba, saboda ya na so ya gujewa hana ta fita nata balcony d'in dan Shan iska, idan ya ji ya na buqatar fresh air sai ya ja glass door d'in ya bud'e ya ja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login