Showing 57001 words to 60000 words out of 81601 words

Chapter 20 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE Hausa Novels BY HAERMEEBRAH.txt

26 Oct 2025

325

sallama masa kanta,ta sani ladan ta na wajen Allah, ba ta koma bacci ba sai da ta tsarkake jikin ta, sannan ta dora da nafila da karanta qur'ani, sannan ta koma.

Wataranar asabar da safe, rana ce da Atiyyaerh ba zata tab'a mantawa ba a rayuwar ta ta gidan auren  Ahmad,
Ya gama sauke buqatar shi ta auratayya kenan, se Atiyyaerh ta ji ya fara fad'a ya na kumfar baki,

"Ni fa na gaji da gafara sa ban ga qaho ba,shekara biyu da watanni ba ki tab'a ko da b'atan wata ba ne haba, ai a qalla ko b'ari kinyi, kullum sai munyi abunnan, wataran har sau uku a rana, dubi Hajar kwanan nan ta haihu, amma ke shiru, gaskiya na gaji,kullum Inna da Baba in suka ji kina zazzab'i fatan su ace ciki gare ki, ni dai gaskiya na gama maki kawaicin haihuwa nake so,"

Kallon shi ta yi cike da takaici, ta bud'e bakin ta da ke rawa saboda kukan da take son yi ta ce,

"Amma dai Bappan Umar ka san ba ni ke bada haihuwa ba ko, a wannan lokacin da ilimin addini ke shigar ka ya kamata ace kasan waye Allah, kasan Allah shi ba a masa dole, ni kaina zan so na haihu amma Allah bai nufa ba, ya kk so nayi,"

"Bawani nan dama Hajar tace tsarin iyali kk, saboda kina son komawa karatu, to bari ki ji ba a gidana ba, bazan lamunta ba, ki haihu ko d'aya ne in yaso sai ki tafi karatun naki"

Mamaki ne ma ya hana ta magana ta zauna a kujera dabas, se da ta nisa sannan ta ce,

" Hajar? Yaushe ka fara zuwa kuke hira har da zata fad'a maka hakan, ko ni yaushe nake magana da ita da zan fad'a mata Ina so na koma karatu? Kayi tinani fa, matar nan tin da nazo ta sa min ido, dan kawai kana so na, Inna da Baba na sona, shike nan fa, kuma tayi qoqarin Yayah ya daina so na, su Umar su daina kula ni suna min rashin kunya, amma ta kasa samun hakan, shine yanzu ta b'ullo ta nan, Allah na nan, yafi mu sanin abinda muke aikatawa,"

Ta miqe ta shige d'aki, zugum ya yi yana tinani, tabbas kusan duk abinda ta fad'a gaskiya ne, to amma baya mantawa randa Atiyyaerh ta tafi gidan Mama gaida Abba ya yi rashin lafiya, sunyi magana akan ci gaba da karatun ta,har ta nuna masa tana da sha'awar hakan, kuma ta bashi shawara ya koma makaranta, ta boko tinda yanzu yana zuwa islamiyya, ya mata zancen haihuwa tace ita duk abinda Allah ya yi shine daidai, to shiyasa da Hajar ta fad'a masa hakan ya yarda, ji ya yi bai ji dad'i ba da bai yi dogon tinani ba ya yanke hukunci, amma shifa gaskiya yana son haihuwa, tashi ya yi ya shige ya kwanta, bai kula ta ba, tana ta jiran ya bata hakuri ta ji shiru, juyawa ta yi ta ga yana qoqarin yin bacci, ta tada shi, yana miqewa ta saka kuka, rikicewa ya yi ya hau dudduba ta ya na son leqa fuskar ta, ita Kuma ta na kauda kai,

"Subhanallahi, Atee na me ye, meya same ki?"

Kuka take kawai tana abun shagwabbabu, tana karya kai, da kyabe baki, tashi ya yi tsam ya d'ora ta a kan cinyar shi,

"Ni ne ko, ni ne na qi kula ki? Ni ne na zarge ki akan kin qi haihuwa ko?"

... in ya yi magana sai ta d'aga kai sama ta ci gaba da kuka tana yarfe hannu, tana juya jikin ta a nashi,

"Shiiiii to kiyi hakuri, ba zan sake ba, ba zan qara ba kin ji, wancan ma akasi aka samu, kin fahimci mijin ki ko, zaki yafe masa ko yar albarka?"

Sai d'aga kai take komai yace, gefe ya yi da kan shi yana dariyar rikici irin nata, in tana irin haka ba qaramin burge shi take ba, kuka ta bare baki  ta saki irin na shagwabar nan, tana turje qafa, tana jijjiga jikin ta, hannu ya sa ya tsaida ta amma jikin ta be dena motsin ba,

"Kin ga ki na ta bawa jikin ki wahala,  se jijjiga shi ki ke,ko kina tinanin Zaki Iya kuka ba tare da jikin ki ya motsa ba?"

kallon shi ta yi ,ta ce,

"Ai zan iya me zai hana"

"Da gaskeeee to yi na gani,"

Aiko nan take ta ci gaba da jijjiga jiki tana qanqame jikin, amma still jikin ya qi dena rawa ,dariya suka saka dikkan su a tare, daga nan suka hau hira Suna wasannin su.

Hajar da ta had'a fad'a dan ta je rabo se  ta ji shiru, sai ma wata soyayya da ta kula suna qara zubawa abun su,haushi kamar ya kashe ta( hassada babban ciwo ne, jama'a mu sani hassada tana cinye kyawawan ayyuka kamar yanda wuta ke cin busasshen ciyawa, mai hassada na samun dusashewar hasken fuska, ya zama cikin baqin ciki koda yaushe, zuciyar mai hassada bata tab'a haske saboda a koda yaushe cikin tinani da saqe2n mugunta yake, hassada illar ta na da yawa ba iyaka,mu kiyayi hassada mu zauna lfy, ba sai mutum ya maka wani abu ba in kana da cutar hassada kk mai hassadar, ba sai mutum ya ma san kana mai hassada zaka fara ba, balle kuma wasu na ma mutum hassada ne da ga zarar ya kyalla ido yaga dan uwan shi ya fishi wasu abubuwan, dan haka kar kai mamaki dan kaga wani ya tsane ka ba dalili, ba komai ke kawo haka ba sai hassada, Allah ya kare mu).

"Ina son yau na je gida gaida Umman mu, da Abba na san yana gida in na je da wuri, na dad'e ban je ba,"

"Ba komai ki na iya shiryawa yanzu ki je,in kin je ina gaida su, a gaida Afrah sarkin kunya, ina mamakin yanda ta kasa sakewa da ni har yau,"

Murmushi ta yi tace,

"Haka take fa, ita dama magana bata dame ta ba,balle ta ce min wai kai sai ka dinga mata maganar manya,"

Dariya suka saka, ta na qarasa gyara gadon, ya maida ta kai, ta miqe tana masa hararar wasa,

"Ni Allah bana son haka,dubi sai da na gyara zaka wani bata min,"

Burgima ya yi, ta ko bi shi ta janyoshi, dama haka yake so, nan da nan salon wasan su ya koma na manya, (lols) sai da komai ya lafa ne sannan ta kai masa dukan wasa,

"Duk kasa sai na b'ata lokaci duk sammakon da na yi wajen tashi da wuri yau,"

Dariya ya yi sosai sannan ya ce,

"To ai mun taimaki juna ko ba komai"

Shige shi ta yi ta tafi bayi tai wanka ta zo ta shirya, bayan ta gama ne ta masa sallama yana kwance kasala ta rufe shi ta tafi, bayan ta fada masa ya tashi ya yi wanka.

******************************

Da sallama ta shiga gidan a bakin ta,ba laifi duk Wanda ya gan ta ba zai ce tana cikin wahala ba, saboda Mama na aika mata da sutura ba tare da Rasheedah ta sani ba,da 'yan kud'ad'e Abbahn su Rasheedah ma na mata aike akai akai,dan haka ba ta da wata matsalar sutura da kayan ado,  sai dai hasken fatar ta da ya ragu, ta shiga parlour bakin ta na maimaita sallama, Afrah ce ta tafi da gudu ta rungume ta tana mata sannu da zuwa, itama cike da farin cikin ganin 'yar uwar ta ta rungume ta,cikin murya mara hargowa Rasheedah ta ce,

"Meye haka kufa baku girma,"

Qasan ran ta kuwa ta na baqin cikin ganin Atiyyaerh na da aure ga Afrah nan ko mashinshini ta rasa ga Kuma Atiyyaerh da ganin ta bata da wata matsala a gidan auren ta, tinda dik tsahon wannan lokacin ba su tab'a Jin ta kawo qara ba, shi Kan shi mijin duk Wanda ya gan shi zai ga alamar nutsuwa da kwanciyar hankali a tattare da shi, ( Oh Allah, ina zamu saka kanmu mu Fans din Atiyyaerh, an mana auren mugunta Dan a ga mun tagayyara ,an ji shiru,yanzu gashi Kuma an zo ana Jin haushin me yasa mu ka yi aure Afrah na gida ba aure, to wai shin laifin na waye?) Sunkuyar da kai qasa ta yi ta duqa gaban Rasheedah ta ce,

"Barka da safiya Umma ya gida? Da fatan na same ku lafiya?"

A ciki ta amsa gaisuwar kamar bata so,Abba ne ya fito sanye da kyakkyawar shiga da alama fita aiki ze yi, cikin sauri Atiyyaerh ta miqe ta Isa gaban shi ta na murmushin farin cikin ganin shi, shi din ma bakin shi ya qi rufuwa cikin murnar ganin ta ya ce,

" A Ablaerh ce a gidan namu da wuri haka,ko dai ba a son ai missing ganin Abba ne yasa aka yi sammako?"

Cikin fara'a ta ce,

" Eh Abbana,na san inshaa Allah na fito da wuri zamu had'u,gashi kuwa Allah yasa, ina kwana Abbana?"

Amsawa ya yi tare da zama,

"Lafiya qlou 'yar albarka, da fatan Kuna lafiya ba dai wata matsala ko Atiyyaerh ? "

Cikin Jin kunya ta saukar da kan ta qasa ta ce,

"Abbana muna lafiya ba wata matsala gaskiya alhamdulillah, ya ce ma na gaishe ku sosai in na zo"

"To alhamdulillah Allah ya qara maku zaman lafiya Ameen, dama na jima Ina son ki shawarci mijin ki zancen komawar ki makaranta in ya amince,akwai kud'in ki da mahaifin ki ya bari da za'a saka ki a makaranta,dan haka ku yi shawara abinda ya ce se ki Sanar da ni ko ta waya ne, ni ina sauri yanzu zan fita yanzu mun Yi magana Daga baya, ki gaida shi,"

" To Abba zan Sanar da shi gaisuwa ka, zancen karatu kuma na fasa ci gaba Abba, dan ban ga amfanin kud'in da ya bari ba Abba, ba na buqatar su, in zanci gaba da karatu zan ci gaba da kud'i na na kaina, Ina tinanin fara sana'a ne Abbah inshaa  Allahu, amma na gama amfani da dukiyar shi, ya maida ni marainiya gaba da baya, ba Mummyna, ba Daddyna,rayuwa ta gaba d'aya bata tafiya min yanda nake son ta,ba haka nake son rayuwa ta ba Abbah, amma Alhamdu lilLAAHi ala kulli halin, Abba da Daddyna zai dawo, da zai zo na dinga ganin shi, daya mayen gurbin Mummyna, da na rage jin radad'in da zuciya ta take min game da shi,"

Tausayin ta ne ya kama Auwal da Afrah, Auwal ne ya ce,

"Kiyi hakuri Atiyyaerh, Daddyn ki na matuqar son ki, wannan dalilin ne yasa baya son ya dawo qasar nan ba tare da kin gama karatun jami'a ba, na masa alqawarin daga sanda kk gama jami'a daga ranar zan fad'a masa, shi kuma a satin zai dawo, shiyasa tinda akai auren ku kika ga ina ta bin kan ki, akan ki ci gaba da karatu kk qi, na sani kina da hujja mai qarfi, ba lallai sai kinyi karatu ne zai dawo ba, a ganin ki karatun ki bai da alaqa da dawowar shi,haka ne, amma ni banda masaniya akan dalilin shi na fadar hakan, ki daure ki shawarci mijin ki akai ya na da matuqar mahimmanci ki ci gaba da karatun a wajen Daddyn ki"

Gyada masa kai kawai ta yi tana ci gaba da kuka ita ta riga ta San Daddyn ta be son ta Abbah na kwantar mata da hankali ne kawai, Rasheedah ce ta kyab'e baki a ranta ko tana ayyana ta ga yanda zata bar Atiyyaerh ta ci gaba da karatun, fatan ta Allah ya sa kar mijin ya yarda ma, ita yanzu damuwar ta rashin auren Afrah, ga Atiyyaeeh na da aure, wata mummunar dabara ce ta fado a ranta tai murmushi, bayan Abba ya fita ne itama ta fita ta barsu da ita da Afrah, taje chemist din unguwar su ta dawo, hira suke suna taya Umman nasu girkin rana, ta wuce su ta je jakar Atiyyaerh ta saka wani abu ta zuge ta koma ta zauna, kamar ba ita ba.

Bayan Atiyyaerh ta wuni a gidan ne ta yi wa su Afrah da Umman ta sallama tace ma Afrah,

"Ga saqo Afrah ki ce wa Yah Sulaiman wannan karon in ya dawo ya taimaka ya zo, tinda ya je min sau d'aya bai qara zuwa ba,"

Amsawa ta yi da

"Inshaa Allah tare ma zamu zo,"

"Allahu ya yarda, Yayah wannan watan zai gama bautar qasa ko,"

" Eh in Allah ya yarda, "

"kaiii amma na ji dad'i,Allah ya bada sa'a,a randa ya dawo nake so ki zo ki gayan na zo na mai congrats kin ji,"

"To in Allah ya yarda kuwa"

kamar kar su rabu haka suke ji, haka ta fita Cike da kewar su,ta yi 'yar tafiya kadan ta fada gidan auren ta, Ahmad ta gani zaune a bakin qofa yana kad'a qafa, mamaki da tsoro ne kwance a fuskar ta,bata taba ganin shi haka  ba cikin b'acin rai,

"Bappan Umar me ya same ka haka?"

Wani mugun kallon da ya hautsina mata ciki ya wurga mata, ja da baya ta yi dan tsoro, tsawa ya daka mata ya ce,

"Ban jakar ki,"

Da sauri ta wurga masa jakar  ta ja baya, bud'ewa ya yi ya duba sai ga magani a ciki, hannu ya sa ya dakko,se ta ga ya zira hannu a aljihun shi ya dakko magani ya had'a da na jakar ta ta se ya ga tabbas wannan shine wanda Umman ta ta nuna masa, hawaye ne ya fara bin fuskar shi,

" Haba Atiyyaerh, me na yi miki da zafi haka? ko dan ina son ki shi yasa ki ka tsane ni haka Ko zuri'a baki son had'awa da ni? Atiyyaerh kin sani tun ina qarami na nake son ki, ban tab'a dainawa ba har girma na, umman ki da kanta ta nuna min irin b'arnar da ki ka dad'e kina min, ashe magani kk sha kar ki haihu? Ta fadan ta gani a jakar ki ta ɗauka ta je shago ta tambaya aka ce mata na hana haihuwa ne, shine ta zo ta tambayen da sanina nake barin ki kike tsarin iyali? To ina ma kk taba ciki bare mu haihu balle mu tsara iyalin? Ba zan iya zama da ke a haka ba, na hakura da ke Atiyyaerh tinda na kula ba Zaki tab'a so na ba har abada, qarshen qiyayyar da zaki min kenan ki nuna kyamar had'a zuri'a da ni, zan zauna har qarshen rayuwa ta ina nadamar son ki da nake yi, saidai zan miki godiya wataqila dama Allah ya kawon ke ne cikin rayuwa ta dan na samu shiriya, na gode maki da wannan qoqarin da ki Kai Dan ganin na zama mutumin kirki, Atiyyaerh ki je na sake ki saki d'aya, biyu, uku Atiyyaerh, bana son na sake ganin ki ki je ba zan iya zama da macen da take tsananin qi na ba a fuska ta nuna min ba komai,"

Atiyyaerh kusan suma ta yi a wajen,shi kuwa ya shige dakin ya dakko biro da takarda a irin littafan da take koyar da shi ya yaga ya rubuta mata ya wurga mata ya koma dakin ya saka sakata ya na kuka sosai.

Ba tare da ta Iya furta komai ba, jiki ba kwari ta d'auki jakar ta da magungunan da ya zubar a qasa ta kama hanya zata tafi gida,Innar shi ta zo ta na mata magana bata Iya bud'e baki ta amsa ba tsabar baqin cikin da take ciki,Hajar Kan ta da ke son a tsani Atiyyaerh abun ya zo mata a bazata,cikin kuka ta koma gida.

Rasheedah ta tarar zaune ta na Shan juice din orange, Suna kallo ita da Afrah, cikin zubar hawaye ta kalle ta ta zaro magungunan ta nuna mata sannan ta share hawayen ta da ke zuba ta ja majinar kuka ta ce,

" Umma me na miki a rayuwa tane? Me  na tsare maki? Me kk so ki fad'a min na bar miki shi har abada? Ba zan iya daukar wannan baqin cikin ba, Ahmad ya sake ni saboda abinda ban san na aikata ba, ashe na koya mai karatu da rubutu ne dan ya saken da su, bana son shi amma na saba da shi, na saba da nunamin yanda yake so na, na saba da kalaman shi masu taushi, na saba da nuna min yafi sona sama dake, me zai sa ki lalata rayuwata? Wannan karon ba zan zauna da ke ba, ba zan bi wasiyyar Mummyna ba ke Kuma ki nakasa min rayuwa ta ba"

Afrah kanta ya kulle, d'aukar takardar ta yi ta bud'e, zubewa ta yi a qasa kwaraf, hawaye na zuba mata, kallon Umman ta ta yi ta kalli Ablaerh

"Meke faruwa ne, me ya sa ya sake ki daga komawar ki ko kin masa Wani abu ne kafin ki fito dama?"

" Ki tambaye ta, ban san me na mata ba, ta je ta nunawa Ahmad maganin tsarin iyali wai ni nake sha, Ahmad na da son haihuwa sosai fiye da komai a rayuwar shi, gashi ta sa ya yanke hukunci cikin fushi ya yi min saki har uku a lokaci d'aya, na rasa wace iriyar qiyayya take min, yau ko 'yar tsuntuwa ce ni ba Zaki na mata wannan abubuwan ba Umma, ballantana a ce ni d'in jinin ki ce ko kina so ko baki so, idan Kuma kin gaji da gani na ne a duniya ki kashe ni kawai ki huta"

Tana gama fad'a ta haye sama da gudu ta na kuka, Afrah qarasa zauna wa ta yi a wajen, ta saka kuka, tana kallon Umman su da take rarraba, ido, tabbas ita ta had'a komai, amma yanzu jikin ta ya yi sanyi,dan tina me zai je yazo da ta yi, in Auwal kuwa ya sani ta ta ta qare, sannan ga Yousuf da Sulaiman, tana tinanin nan ta ji sakkowar Ablaerh daga sama da ta hau cikin sauri da b'acin ran da bata tab'a nunawa a fuskar ta ba,ta dauki mayafin ta dake  qasa, ta koma gidan ta ta kwashi kayan ta a kwati, ta kama hanya......
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼






 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH











Page 25:








Duka ya sake kai mata ta goce, Atiyyaerh ce ta ya yi sauri ta shiga tsakiyar su, ta kwab'e baki kamar na me Shirin yin kuka, dan kuwa ji take kamar ta Saka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login