Showing 54001 words to 57000 words out of 81601 words
Chapter 19 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE Hausa Novels BY HAERMEEBRAH.txt
yi hakuri ku jira ku ji ya abun zai kasance har zuwa qarshe,sannan kar mu na manta cewar kowa fa da qaddarar shi a rayuwa, ba lallai ne a halicce ka ka ji daɗi all ur life ba, we ar not in this dunya to have fun, we ar here to worship Allah, kuma a cikin bautar shi ne ya ke jarabtar mu da abubuwa kala2, in ma ya jarabce mu da arziqi, ko talauci, ko ya haɗa mana dika, gaka mai arziqi amma ma talauci, ko gaka talaka amma mai arziqi, (mai wadatar zuci talaka,da mai kudi mara godiya) dan haka nake cewa ku qara hakuri, akan kome zaku karanta har mu Kai qarshen labari thank you.*
Page 24:
Ahmad a kwanakin nan ji yake duk duniya ba wanda ya fishi morewa da matar aure, ta bangaren Atiyyaerh kuwa ta sani bata yi irin auren da take so ba, Kuma har yanzu bata son Ahmad a ranta, amma ta na Jin dad'in yanda yake kula da ita, yake nuna mata soyayya, ta bangaren surukan ta ma bata da matsala da su, Inna Abu da Baba Garba basu da wata matsala, su suke ci da su ita da Ahmad d'in, dan haka ta kan fita ta ya Innar aiki bayan ta gama da na bangaren ta,Ahmad yana da Yayah da matar shi, wadda take da qananan yara biyu,Sadiq da Umar,yaran ba qaramayen marasa kunyan yara bane, yanda uwar su take ba kunya komai a tsattsaye haka suma yaran suke, Yayan Ahmad Muhammad sunan shi kowa na ce masa Yayah, bai da matsala, amma wani lokacin akan yaran shi sai a buga da shi a tsakar gida, nan ma yana samun pampo ne wajen matar shi,me suna Hajar, Hajar ko sunan surukar ta katsal take fadan shi ba sakayawa wato Abu, shiyasa yaran suma suka dauka, Abuu, Baba Garba ne kawai suke ce wa Baba, su abincin su daban suke yin shi a gidan, in ta ga dama ta zuba ta bawa surukan in bata yi niyya ba suci da yaran ta da mijin ta.
Atiyyaerh ta kasa ce ma surukar ta Abu, sai take ce mata Inna kamar yanda taji Ahmad da muhammad na kiran ta, ta kula da yanda surukan ta ke son ta, har Yayah, sannan kuma ta kula da yanda Hajar ta tsane ta, sai tana yada mata magana akan kyaun ta ai na d'an maciji ne a Jira lokaci kad'an mummunan halin Atiyyaerhn zai bayyana ne nan gaba, amma ba ta taba tanka ta, to yaushe ma tazo gidan? Kuma ma in ta dad'e me zai kaita biye mata? Ita fa a rayuwa bata son hayaniyar fad'a, rayuwar bala'i da masifa a ciki ta taso, to me zai dame ta kuma? Dan haka ganin halayen Hajar take nafila akan inda ta baro ba Wani damuwa bane a wajen ta.
Ta gama wanka kenan ta yi kwalliya daidai ita abin ta, dan rashin sabon da ta yi ne ma da Kwalliyar yasa wataran sai ta yi wanka sai ta manta bata yi Kwalliya ba se ta tina yanzu fa a gidan miji take sai ta dan yi kwalliyar kadan, to ranar Kuma an yi sa'a Ahmad a gida yace zai wuni, ita kuma kullum tana nuna masa fita neman na kai ya na dojewa dan be Saba ba, sai ya ce mata shi fa ba sana'ar da bai gwada ba basa kar bar shi ne, haka take hakura, ta biye mai ya yi ta jagwalgwala ta, bata so amma bata tab'a nuna masa ba,kuma bata taba kyamartar shi ba, dan daidai misali bai da qazanta yanzu, tana sashi gyara a inda taga bai mata ba, da dabara da Jan hankali zata nuna masa me take so ya gyara, misali wata rana suna zaune yana ta bata labarin yan ganyen abokan shi, ,
" kinga kafin na aure ki ,nida Baba Qarami sai mu sha ganye nadi shida a rana, ba abinda ya mana zafi, amma kinga nine yanzu har na d'au sati biyu ban sha koda sigari ba, sai sau d'aya,randa kk shiga yiwa Inna tuwo na sha da kk dawo na buga qasa nace ban sha ba🤣 , kika yi kika yi na kafe na ce miki ban sha ba, kin san me?"
Kada masa kai ta yi tana dariyar tina kafiyar da ya mata yana zaro ido kamar mage ta sha wanka,
"A ranar sai na ji wani haushin kaina dan me zan sha abinda ba ki so, bayan ke tinda na aure ki ba ki da burin da ya wuce na ki faranta min? Shiyasa na yi ta qoqari na daina, dana ji ina son shan Wani abun maye gwanda na zauna a gida na yi ta Koda kallon ki ne Ina Jin nishad'in da bana Jin irin shi a cikin kayan Mayen, shine zakiga na dame ki na maqale maki, ke kuma nasan kin gaji amma a haka ki ke hakuri dani,na gode Atiyyaerh 'yar aljannah ki ta taya ni da addu'a kin ji? Watarana inshaa Allahu zan dena ne"
Tausayi ya bata ta daga masa kai kawai alamar "To" tare da tsagaita dariyar ta, a hankali ya ja ta jikin shi, bakin shi ta ji yana wani bugawa, zuciyar ta ta hautsine kamar zata yi amai, tabbas ta bari ya kai bakin shi nata zata yi amai ne kawai,dan haka cikin dabara ta janye ta na murmushi, ta ce Masa,
"Mijina ina zuwa na je na yi brush, nazo na maka wani abu, dan yau sai na baka ladan qoqarin ka na daina shaye2, duk kuma randa ka min alqawarin daina neman mata ni kadai na san me zan maka a gidannan,"
Ta shi ta yi tana taku mai Jan hankalin da ita Kan ta se da ta yi mamakin yaushe ta Iya hakan? ya kwanta yana hango ta yanda take tafiya jikin ta na juyawa cikin salo, hankalin Ahmad in ya yi dubu to Atiyyaerh ta d'age shi, brush din ta ta d'auka ta saka toothpast, sai ta juya tana kallon shi, tace,
"Mijin Ablaerh na saka maka ne kaima ko na bari?"
Cikin zumudi yace,
"Saka min nima , ai dole nima na tsaftace nawa bakin kar naiwa kaina mugunta, bansan dad'in da za a ban a ciki ba,"
Dariyar samun nasara ta yi, suka je suka wanke baki, a zuciyar ta tana mamakin ina ta iya irin wadannan abubuwan?( niko nace Ablaerh ko wacce mace jaruma ce, mai ilimi ce, kuma mai fasaha ce, dan haka mace mai wayo da dabara ita zata iya sarrafa wadannan abubuwan, kowa Allah ya halicce ta da kissar ta a tare da ita, ya dangan ta da wacece ke kafin ki mori abinda Allah ya baki na baiwa, in ke cikakkiyar mace ce zaki amfana da sirrikan dake tattare dake, in mata kk rako to komai kina zaune ki na jiran sai an fada maki, sai kin ce baki iya ba a koya maki, bayan a take zaki iya maganin matsalar ki da kalaman ki, da jikin ki, sannan da kallon ki,) can na hango malama Atiyyaerh na kwance saman jikin Ahmad, Ahmad ya rude sai sambatu yake, ta gama susuta shi, qara maimaitawa yake,
"Daga yau na maki alqawarin bani ba shan ganye,bare sigari, har abada, Ablaerh ki dinga min irin wannan kullum,"
Hajar ce ta zo wucewa ta ji duk abinda ke faruwa, kad'a kai ta yi ta tafi, bayan sun gama.abinda suke ne, suka yi wanka a makewayin su, ta saka wasu kayan tace masa bari ta shiga ciki ta taya Inna aiki, dama tin dazun take son zuwa , suka zauna hira, cewa ya yi da shi za a, ta yi iya yin ta kar ya bita amma inaa ya qi, hakura ta yi suka shiga ciki tare, tankad'e ta tarar Inna nayi, ta yi sauri ta karb'a ta ja kujera ta miqa masa dan ya zauna, ita Kuma ta tsugunna ta ci gaba da tankad'en, Innace ta bata ta ta kujerar amma taqi karba, tankad'e take suna hira, sannan tana duba ruwan tuwon, dan yawanci abincin su baya wuce tuwo miyar kuka, se juma'a a dafa shinkafa ko taliya 'yar murji, Atiyyaerh ce ma data zo ta sa ake d'an canja miyar kala2,in yau an yi kuka gobe a Yi kubewa ko ayoyo, Hajar ce ta shiga sashen Inna Abun itama ta samu bakin qofar d'akin Innar ta zauna ta ce,
" Au nan ku ka shigo ashe, ai zuwana wajen ku wajen sau uku kenan ina komawa, gaba d'aya kun rikita mana gida da sambatu kamar Kan ku aka fara aure"
Wata uwar kunya ce ta kama Atiyyaerh kamar ta tsaga qasa ta shige, hannun ta kasa riqe rariyar ya yi, sai ta ji ta mata nauyi, kula da hakan ne ya bata ran gogan nata,cikin son baqantawa Hajar Shima ya ce,
" Eh muna can muna abinda muka yi aure domin shi, kin ganta nan na san ba sona take ba, amma bata rowa,kuma 'yar albarkar ba sai an siyo mata tsiren Talle mai nama ba kan a kusance ta, a bata so na take hakuri da babu na, duk da ita gidan ubale akwai, kuma a......"
" Dan Allah ka yi hakuri ka rabu da bata amsa irin haka, baka kula Inna ta tashi ta bar wajennan ba sabida kunyar maganganun ka? Ni kaina ka ja min kunya yanzu da wanne ido kk son na kalle ta?"
Ta qarasa cike da shagwaba, wanda dama da ita take qara susuta shi, matsawa ya yi daf da ita ya fara bata hakuri, Hajar da ta cika ta yi fam,dan bata tab'a zatan Ahmad duk yasan wadannan abubuwan game da ita ba, gaskiyar shi ne kuma a haka wai tana son Muhammad, akan shi ba abinda ba zata yi ba dan kar ya mata kishiya,amma fa haqqin shi in zai sauke sai jama'a sun ji, indai ba ita ke so ba,
"Sannu 'yan bariki,ni zaku gwadawa bariki? To bari ka ji mu zuba ni da ku a gidannan naga wa ya fi wani bariki, kina wani sunne kai kamar ta Allah, yanda aka ce gidan ku akwai tarbiyya ashe qarya ne, kin gama rabawa gayu a titi, dan dai qarya kk kice a nan kk koyi komai,"
Bata ankara ba ta ji an kafe ta da mari, jikin Ablaerh na rawa ta ja shi, amma inaaa yau dabar ta motsa, ita kan ta Hajar ta tsorata,dan ko a bige yake bai tab'a bata tsoro kamar na yau ba, dama tinda Hajar ta miqe ta na magana da qarfi gidan ya d'auka da ana fad'a tsakanin amarya da Hajar, nan da nan 'yan d'aya gefen da ke zaman haya suka leqo, dama ashe ana rade2n tunda tai boko bama budurwa bace, dan salin, alin suka yi abunsu, bata yi wani iface2n da maqota zasu ji ba,to shikenan ake zargin ta, se yau Hajar ta fallasa qus qus d'in da ake akan ta,
" Amadu kai hakuri ka tafi sashen ku,"
In ji Innah Abu da ta fito daga d'aki,
Jikin Ahmad kuwa se b'ari yake cikin rawar murya ya ce da Innar tasu,
"Qazafi fa ta yi wa mata ta Innah, waye ya kusantar min ita har da ya ji ba budurwa bace? Yau se na illata ki a gidan nan Hajar"
Zabura ya yi ya sungumi tab'arya zai rantama mata akai Atiyyaerh ta riqe ta na hawaye ta ce,
"Dan Allah Bappan Umar ka yi hakuri, mu tafi, tamun qazafi kuma Allah mai hisabi ne akan kowa da komai, Allah zai mun sakayya, muje bana son daga zuwana a na samun hayaniya haka,"
kwalla ce ta sakko mata a kunci, aiko yana ganin haka ya qara zabura zai make hajar, cikin zafin nama ta janye, ashar ya dinga durawa irin na asalin yan tashan nan,
" Matar tawa ce ta rabawa gayu jikin ta? Uban wa ya kwantan da ita daren farko ya ji ta a matsayin budaddiya da har zaki ce haka? Ni da mata ta ki mata sharri a gabana? Yau na lahira sai ya fiki jin dadi Hajara se kin fad'an gayen da ta rabawa jikin nata ko na yi maki dukan mutuwa".........
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 26:
Da abincin su ta shiga dakin ta aje a parlour, sannan ta shige uwar d'aka, kwance ta gan shi ya na bacci, kallo ta bishi da shi daga fuskar shi har zuwa yatsun qafar shi, Ahmad ba shi da makusa in ba ta ilimin shi ba, shi d'in ma zama da ita ya sa ya fara koyan wasu abubuwa masu mahimmanci a rayuwa musamman ta bangaren da ya shafi ibada da bautar Allah,ya fara Iya koyon rubutun Hausa da karatu, bashi da girman Kai wajen zama ta koyar da shi Dan ya San ya yi wasa da damar shi be je makaranta ya Iya ba, Allah ya bashi wadda zata koya masa ba tare da ta masa gori ba sai kawai ya saki jiki ya na koya abun shi, a cikin zuciyar Atiyyaerh kuwa ta sani kwata2 bata jin son shi, sai dai ya na da Wani matsayi Mai girma a gare ta na mijin da take aure,ta San girman matsayin miji a Islamiyya ana koyar da su, qawayen Rasheedah sun mata nasiha akan haka, Mama ta mata nasiha ta waya akan hakan, Dan haka bata tab'a manta matsayin shi da girman da iKon da yake da shi akan ta,ta d'auki Ahmad a matsayin aboki saboda zaman su ya musu sauqi ya Kuma Yi musu dad'i, ta haka ne ta ke zaune lafiya kamar wadda ta yi ninqaya a cikin son shi da jimawa,wannan dalilin ne ya sa ba zata tab'a barin shi yana neman mata ba ko dan kare mutuncin ta, cire kayan ta ta yi tai wanka ta dawo d'akin ta gyara jikin ta ta sauya kaya, sannan ta tashe shi, ta ce,
"An kusa kiran magrib, ya Kamata ka tashi haka ,ruwan wankan ka na bayi, in ka gama ka dawo sai muci abinci,"
"Na gode, amma gaskiya na dad'e ina bacci ban San lokaci ya tafi haka ba sannu da aiki,"
Murmushi ta masa ta miqa masa hannu dan ya tashi, kama wa ya yi ya tashi ya fice, kan ya dawo ta dakko masa kayan da zai saka, sannan ta zauna tana jiran kiran sallah, kan ya shigo an kira sallah, da Shirin masallaci ya bar d'akin sai zabga qamshin yake yi, tana sallah ta ji qarar faduwar abu da mugun qarfi, sai da ta idar da sallar ta ta leqa dan ta ga meye, tana fita ta fad'i qasa, sakamakon santsi daya d'ebe ta,
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, meye haka Umar?"
Dariya suka saka mata,"ke Aunty Amaryar nan baki iya abinci ba, gaba d'aya kin tuqa tuyo ya yi wani gudaji, sanan kin mana miya tsululu kamar ruwan wanke kai,"
Cewar Sadiq da yake babba akan Umar,a hankali taso tashi amma ta kasa, sakamakon gurdewa da qafar ta ta yi, da rarrafe ta bar wajen da miyar ta zube ta koma gefe ta na matsa qafar ta da ke mata radad'in zafi, ta ce,
"Ku yi hakuri Sadiq inshaa Allah gobe za ku ci mai dad'i, amma ku sani wannan abun da kuka yi ba abu bane mai kyau,yaran da basu da tarbiyya su ke yin hakan, sannan kuma kunga kunyi almubazzaranci da kuka zubar da abinci, Allah yace duk almubazzari dan uwan shaid'an ne, dan haka ni bana son ku kasance daga 'yan uwan shaidan, ko kuna so?"
Girgiza mata kai suka yi, ganin maganar ta kamar na shigar su se ta ci gaba da cewa,
"Da kyau yaran Bappan su, Allah ya muku albarka, nan gaba ko wani ya sa ku yin haka kuce yi wa babba rashin kunya haramun ne Allah ya haramtawa yaran kwarai 'yan albarka yin rashin kunya, kun ji, kuma duk mai saka ku rashin kunya baya son ku, so yake ku shiga wuta, in baku so ku shiga wuta sai ku qi yi kun ji?"
D'aga mata kai suka yi jikin su duk yayi sanyi,sun fahimci Auntyn nasu na son su, Umman su so take su shiga wuta, ita Kuma Atiyyaerh daga yanda ta ji Sadeeq na tsara zance ta San Saka su aka yi, tinda a baya Suna mata biyayya dik da ba su da kunya,cikin Murmushi ta ce musu,
"To me ake cewa wanda aka yi wa laifiiiiii?"
Ta fad'a tana karkata kai tana murmushi,
" Kiyi hakuri,"
Suka fad'a a tare, umartar su ta yi da su tafi ba komai, suka juya jikin su ya yi sanyi, duk a kunnen Hajar, in ranta ya yi dubu to ya b'aci, qwafa ta yi tace,
"Zamu had'u ne ai gaba,"
Ta shige sashen ta kafin yaran su fito, kafin Ahmad ya dawo a durqushen da take ta gyara wajen, yana dawowa, ya ganta ta had'a zufa,ga qafarta miqe ta kumbura,cikin damuwa kwance a saman fuskar shi yace,
"Me ya same ki? Ya naga qafar ki ta kumbura?,"
"Zamewa na yi na fad'i a bakin qofa, shine qafata ta yi haka, kuma zafi take min,"
Ta qarasa cikin kuka, dan ba qaramin zafi take ji ba, da kyar da sidin goshi, ta yarda ya ja qafar, ta sha kuka kuwa sosai, amma da ikon Allah yana ja mata se ta mata sauqi sosai,ciki ya kama ta suka shiga suka ci abinci,su na gamawa a wajen ta yi bacci, bayan kiran isha'i ne yace gida zai sallah ba za shi masallaci ba dan ba ya son ya fita ta sake samun wata matsala,
" Allah ne mai kare bayin shi fa, in ma ka zauna Allah ya nufa se wani abu ya samen zaman ka ba zai hana ba, kaje kawai,"
Murmushi ya mata cike da gamsuwa da bayanan ta ya fice,tashi ta yi ta na d'an d'ingisawa tai alwala ta yi isha'i sannan ta tafi ta kwanta, tsabar gajiya ko minti 3 batai ba bacci mai dad'i ya d'auke,ko da ya dawo se ya ga har ta yi bacci abin ta,kwanciya ya gyara mata shima ya rab'a gefe ya kwanta, duk da gajiyar da tai bai barta ba sai da ya d'aga ta cikin dare ya sauke buqatar shi, amma ko a fuska bata nuna masa b'acin rai ba dik da bata so hakan ba,haka ta hakura ta