Showing 63001 words to 66000 words out of 81601 words
Chapter 22 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE Hausa Novels BY HAERMEEBRAH.txt
damun ta, in mace tace a kyale ta ba wai tana nufin hakan bane,tana buqatar kulawa, ko mai zata ce hakuri za ka yi har ta daidaita,mu qara gwadawa,"
Komawa ya yi ya fara mata magana,
" Haba yar gidan Abban ta Auwaluuu,ki bud'e ki fad'an me ya same ki, me aka miki, na maki alqawarin wannan karon ina bayan ki, ba zan bari kowa ya cutar da ke ba, ina tare dake,"
Tana jin haka ta ja jikin ta ta jingina da qofar ta kwantar da kan ta a jiki hawaye na ci gaba da zuba, a hankali ta ce,
" Abba kayi alqawarin kana bayana fa kace a wannan karon,ka tabbata komai na fad'a ina so zaka min shi?"
"Na yi alqawari,domin na san tabbas cutar dake aka yi da yawa abinda ki ka yi d'innan ba halin ki bane,baki tab'a hakan ba,"
Miqewa ta yi a hankali ta bude qofar, Mama na ganin ta ta nufe ta ta rungume ta,ita kuma ta ci gaba da kukan ta,cikin kukan ta ce musu,
" Mama Ahmad ya sake ni sakin wulaqanci saki har uku a lokaci d'aya ba tare da haqqina ba, ban masa laifin komai ba, Mama Umma Rasheedah ce ta min sharri a wajen shi ya sakeni,saki Uku, Mama na saba da Ahmad, koda bana son shi, me na yiwa Umma Rasheeda da bata so na,in wani tarihi ne da ni da yasa ta tsane ni ku sanar dani, in wani abu ne take so dana mallaka ku fad'a min shi na bar mata shi bana son abun, na tsane shi, Na shane shi, bana buqatar shi in dai zai ja min tsana irin wannan a wajen Ummana,"
Kuka take kamar wadda akai wa sabuwar mutuwa, Mama ma kukan take, Abba ne cikin tausayawa ya kamo ta suka zauna bakin gadon ya ce,
"Atiyyaerh bari na tina maki ma'anar sunan ki, ke takwarar Maimunatou ce,Mahaifin ki ya sa ka maki suna Atiyyaerh ma'ana kyauta, Mahaifiyar ki ta sa maki Ablaerh, wato mai kyau, wadda kuma aka tsara wajen halitta, dukkan nin su basu yi qarya ba, qiyayyar da Rasheeda ke maki ba komai bane illa hassada, hassada kuwa mummunan ciwo ne mara kyau,in ya kama mutum maganin shi na wahala, dan haka wannan ciwo ke damun Umman ki, fatan mu mu zama masu mata addu'a Allah ya yaye mata, ba akan ki ta fara ba, ta fara da qin mahaifiyar ki ne abun ya dawo kan ki, ba abinda kk mata, ba abinda kk riqe mata, ina fatan kin gane, dan haka ki kwantar da hankalin ki, game da sakin da Ahmad ya miki, ina mai baki hakuri, da fatan Allah yasa hakan shine yafi maku alkairi da ke da shi"
A da zuciyar ta cike take da qunci, amma yanzu komai sai ta ji ya kwaranye mata se abinda ba a rasa ba na kewar Ahmad, ta samu sauqin baqin cikin ta,cikin nutsuwa ta musu godiya, sannan tace,
" Abba Mama dan Allah zan zauna da ku ba zan koma wa Umma ba, zan zauna nan har Daddyna ya gaji da zaman can in ya tina yana da 'ya ya dawo,har ya...,"
Kasa qarasawa ta yi saboda kukan da ya sarqe muryar ta, bata son tina wai tana da uba amma ya banzatar da ita sabida wani shirmen dalili, tabbas ba dan tana son shi ba,tana son ganin shi da ta yafe shi, da ta manta itama tana da uba, kamar yanda ta dauka shima.ya manta da ita, hakuri su Abba sukai ta ba ta, Mama ta debo mata tuwon shinkafa,miyar taushe, ta sata gaba, da kyar ta iya ci, dan ji ta yi gaba d'aya bata son cin komai, bayan sun d'an taya ta hira ne suka bata waje, ta koma tai addu'ar kwanciya bacci ta shafa a jikin ta ta kwanta, baccin kasa d'aukan ta ya yi, sai tinanin Ahamd ne ya cika mata zuciya, ko me yake yi a yanzu? Ko su Baba sun san ya sake ta? Allah shine masani a haka bacci barawo ya dauke ta.
********************************
Da asubar fari Baba Garba da Yayah suka zo gidan Abbah, inda Suna buga qofar gidan tare da sallama daga baya Auwal ya zo shima, nan fa aka hau gaishe2, da jajanta wa juna abinda ya faru, can nesa da su kad'an suka ga Abba na tahowa ya dawo daga masallaci,yana isowa ya miqa masu hannu aka gaggaisa, sannan ya bud'e gidan suka shiga, parlour suka tafi dika, bayan sun zauna ne suka qara gaishe2, Baba Garba ne ya fara magana ya ce,
" Malam Hamza, bayan mun dawo gida jiya wajen magrib, muka ga Ahmad ba yanda yake,sai an kwantar se an tayar sai da muka kai shi asibiti, jikin shi zafi saboda zazzabi, sai sambatun kiran Atiyyaerh yake,yana fadin ya cuci kanshi,ya yanke hukunci cikin fushi, da sauran kalaman nadama, da na matsa mai da tambaya ya sanar da mu duk abinda ya faru, mahaifiyar shi yanzu haka tin jiya take kukan mummunan aikin da ya jiqa mana, yarinyar nan ta zama 'ya mace d'aya da bamu samu ba a tsakanin mu, ni da mahaifiyar su, tinda ta je ita ke mana komai, ita take taya mahaifiyar su aiki, ta zama abokiyar hirar ta, girmama ni take kamar ni na haife ta, ga Yayan su nan, bata taba gaida shi a tsaye sai ta durqusa, yaran shi duk rashin kunyar su sai da ta shanye har ta sa suka zama yaran kirki, tin jiya suma suke ta neman ta da suka ji abinda ya faru kuka sukai tayi, suna a dawo masu da Aunty Amaryar su, ba munzo bane dan mu bada hakuri a maida ta ba, domin mun san saki uku ne tsakanin su, munzo ne dan bada hakurin abinda yaro ya aikata mara kyau, a yi hakuri, a yafe mashi, tabbas ya yi rashin hankali, da rashin hakuri, wanda ya jefa kan shi a nadama da dana sani, kuma muna fatan zumuncin mu zai ci gaba ba zai yanke ba,"
" Wannan haka yake Malam Garba yaro ya yanke hukunci cikin fushi, wanda ya sa su gaba dayan su a tashin hankali, sai dai mu yi fatan Allah ya kiyaye gaba, ya sa hakan shine mafi alkairi," In ji Abban su Rasheedah, Auwal kuwa ya ce,
"Nima Dake ban dawo da wuri ba sai qarfe goma na dare, saboda wata kwangila da kamfanin bulo na ya samu kwanan nan, ko da na dawo ba a Sanar da ni da wuri ba, se da na nemi Afrah ban ganta ba, Ina shiga d'aki na gan ta tana kuka, da na yi bincike se na ji mummunan labarin, na so zuwa tin a daren amma na bari zuwa yau da safe na zo, to dama rayuwa bawa baya wuce qaddarar shi, muyi fatan yanda muka roqi auren ya zama alkhairi sakin ma ya zama alkhairi,Allah ya had'a kowa da rabon shi na alkhairi"
Amsawa dika suka yi da 'Ameen" sanan suka miqe da niyyar zasu tafi, zasu wuce asibiti, wajen Ahmad, Auwal ne ya ce
"Wanne asibiti ne inna tashi nima zan zo duba shi,"
Fada masa suka yi sannan sukai sallama suka tafi, bayan sun zauna ne Abbah ya kira Mama da Atiyyaerh, suka zauna, kan ta a qasa dan ganin Abban nata cikin damuwa, da alama shima bai yi bacci ba, gaida shi ta yi sannan ta gaida Abbahn su Rasheedah da Maman, bayan sun amsa ne Auwal yace,
"Ablaerh ki yi hakuri da wannan mummunan abu da ya faru,jiya na dawo gida na tadda mummunan labari akan abinda ya faru, wanda ba kowa ne sila ba illa Rasheedah, na zo ne domin na baki hakurin komai da take maki, daga wannan lokacin inshaa Allah komai ya qare ba zan sake saka ido ta b'ata rayuwar ki ba, dan haka nake baki hakuri da ki zo mu koma gida,"
Kan ya qara bude baki ta riga shi da sauri ta ce,
" Abbana ka yi hakuri,ba zan iya komawa qarqashin inuwa d'aya da Umma ba, irin qiyayyar da take min ban zaci ta kai haka ba, sai jiyan, na ci alwashin ba zan sake zama guri d'aya da ita ba, in kuwa wannan karon kuka kafe sai na zauna da ita dan cika wasiyyar Mommyna to tabbas zan bijire maku, zan iya barin gidan nan akan na zauna da ita,"
Ta qarasa maganar cikin kuka, wanda gaba d'ayan su saida suka tausaya mata,
"Shikenan yanzu magana ta qare ba inda zata tafi, ina nan tare da ita, nima ina son kasancewa da ita tin fari, kawai dan an fi qarfina ne yasa na hakura, amma tin fil'azal da anbi tawa da Atiyyaerh ma bata zauna da Rasheedah ba a wannan qiyayyar da take mata, dan haka mu yi fatan alkairi a rayuwar ta kawai ta ci gaba da zama nan"
"Haka ne, kema kin kawo hanzari mai kyau Hajiya, dan haka abinda kk fada yayi daidai ta ci gaba da zama anan kawai,"
Abba Auwal ba haka yaso ba amma shima addu'ar fatan alkairi yayi suka ci gaba da tattaunawa da Abbah akan matsalar Rasheedah,anan ya karya sannan ya tafi,kafin ya Isa gida se da ya tsaya ya biya asibiti wajen Ahmad,ya tadda Ahmad cikin mawuyacin hali, duk ya fige kamar wanda ya yi ciwon watanni, bayan ya gaida shi ne ya wuce gida, kwata2 ya dauke wa Rasheedah wuta, baya kula ta baya cin abincin ta, baya komai da ita na ma'a malar aure, dan gaba d'aya ta fice masa a rai, Afrah ma ba kula ta take ba banda gaisuwa, sai ta qarata zage2n ta da fadace2n ta amma ko mai ba zata ce ba, Sulaiman a satin ya dawo, lokacin da ya ji labarin kasa cewa komai ya yi ya qurawa mahaifiyar tasu ido, saida jikin ta ya hau kyarma, ba dan komai ba dan bata tab'a ganin fushi da tsana a idon d'an nata ba irin wannan lokacin, tinanin ta ya kai kan me Yousuf zai ce kenan idan ya ji????
*BAYAN KAMMALA IDDAR ATIYYAERH*
Atiyyaerh na zaune a Parlour ta na hutawa bayan kammala aikin gidan da ta d'auke wa Mama tin zuwan ta, zaune take cikin Kwalliya mai kyau da d'aukan hankali wadda ta jima ba ta yi irin ta ba, haka kawai yau ta ji ta na sha'awar yin Kwalliya, wayar da Abba ya sai mata take dannawa,wani qamshi ne mai dad'in shaqa da kwantar da hankali ya daki hancin ta, sannan sallama ta biyo baya da muryar da ba zata tab'a mantawa da ita ba a rayuwar ta, d'aga kan ta ta yi a hankali idanun su ya had'e dana juna, sun dad'e suna kallon juna kafin ya katse kallon da cewa,
"Ba za ki min iso ciki bane, anan zaki bar baqon naki?,"
Cike da jin kunya ta kauda kan ta daga kallon shi, ta yi masa nuni da ya shigo, miqewa ta yi ta shiga ciki,shi kuwa ba abinda yake face bin kyakkyawar surar ta da kallo,wani yawu ya hadiya da qarfi sannan ya ce,
" Allah ka mallaka min qanwar nan tawa a matsayin matar aure na a wannan karon"
Dawo wa ta yi sanye da mayafin da ya rufe jikin ta yanda ya Kamata,hannun ta d'auke da farantin da ta d'ora jug din da ta zuba zob'on da ta had'a ba jimawa Wanda ya sha kayan qamshi da cucumber da abarba, sai lemon zaqi da na'ana'a, ta aje masa a gaban shi,sannan ta sanar da Mama zuwan shi ta dawo, zama ta yi ta gaida shi, ya amsa idon shi kamar zai fad'i qasa Dan kallon ta,
" Yah Kallon fa? "
Cike da shagwaba ta fad'i hakan shi Kuma cikin kashe murya ya ce,
" Ya ba zan kalli dimond dina ba, sannan kina Wani abu kamar baquwa? Ko gaisuwa ma Babu, any way na yafe gaisuwar, kallon ki ma da na yi ya wadatar da ni,na San ke Baki ma yi kewa ta ba, dama wanene ni a wajen ki da Zaki kewa ta? Ni kuwa kin ga kullum cikin kewa da tinanin ki nake,na jima rabona da na saki a Ido na,ke Kan ki yaushe rabon da ki ganni? Tin lokacin da na dawo na tadda daddad'an labarin nan,na wuce kaduna wajen abokina, na hau fafutukar neman aiki, har Allah yasa na dace, a kullum sai na yi waya da Afrah na ji ya kk, takan ce min tazo kun yi hira kala kaza da kaza, nai ta jin dad'i, saboda so nake na dawo da kwari na Ablaerh bana son rasa ki wannan karon,akwai sanda na sa ta ta yi min recording muryar ki inda kk ta dariya akan labarin miyar da ki kai wa Mama mai yaji, na ji matuqar dad'i kasancewar fara'ar ki ta dawo, na qudurta dawowa tin a lokacin to kamfanin da nakewa aiki, na sarrafa kayan gine2 ba zai ban damar tafiya daga fara aiki da su ba,sai da na yi wata hud'u da su sannan na dawo, tinda na dawo na so zuwa amma ina tsoron me zaki ce game da buqata ta a wajen ki,"
Cikin sauri ta daga kan ta tace,
"Wacce buqata ce zata tsorata ka zuwa waje na Yayah, kasan yanda na yi kewar ganin ka kuwa, a lokacin da komai ya faru na so kana nan, nasan zaka ban kafad'ar ka na koka baqin ciki na amma baka zo gare ni ba Yayah , nasan zaka min tattausan lafazin ka domin na kwantar da hankali na ammma shiru ba ka zo gare ni ba Yayah Babu kai babu dalilin ka, Yayah na zata kai zaka taimaka ka dawon da farin cikina amma haka ka tafi ka barni ba wata kulawa Daga wajen ka, sannan yanzu ka zo da wata buqata a gare ni?"
Kuka take sosai dan tinawa da yanda ta tsallake ramukan baqin ciki ita d'aya ba mataimaki a gare ta, hawayen ta duk ya bata mata kwalliyar da ta yi, tashi ya yi ya zauna kusa da ita, ya goge mata fuska, sannan ya dafa kafad'ar ta yace,
"Ablaerh my dear ki daina kuka,ki yi hakuri ki yafewa Yayan ki, na sani ni Mai laifi ne a wajen ki,amma inshaa Allah komai yazo qarshe, ni zan maye maki gurbin duk abinda ki ka rasa a rayuwa, Ina fatan na zama *JARUMIN KI* "
" Yayah na san da hakan sanin cewa *KAI NE JARUMI NA* ne yasa na ji takaicin rashin ganin ka a lokacin da nake da buqatar ka,babu Kai babu Daddy na, Yah ka taimaka min Daddy ya dawo gareni na kasa yin fushi da shi dik yanda zuciya ta ta so tsanar shi sai na kasa, ka taimaka min yayah "
"Share hawayen ki nace ai ko? yanzu gani na dawo, kuma ba zan sake barin ki ba ko mai rintsi komai wahala, ina tare da ke, ina fatan zaki qarawa Yayan ki matsayi ya tashi daga Yayah ya koma masoyi?"
Wata kunyar shi ce ta kama ta ta miqe ta shige ciki da gudu, a hanya suka had'u da Mama, mama ta ce,
"Ke meye haka zaki ture ni na fadi?"
Bata kula ta ba ta shige d'aki ta rufe ta jingina da qofa, tana ajiyar zuciya, tare da murmushi,ta dafe qirjin ta dake bugawa da sauri da sauri, hawayen ta ta share ta ce,
" Oh Ya Allah kasa Yayah ya zama farin cikin rayuwa ta, nima ina son ka Yayana na baka dama ka zamo masoyi a gare ni,"
Da qarfi ta fada gado ta hau juyi tare da murnar kalaman shi a gare ta, bayan ya gaida Mama sun tab'a wasanni na jika da kaka ya yi mata sallama ya tafi, dan yasan yanda Atiyyaerh ta tafi ta na Jin kunyar shi ba zata dawo ba.
******************************
Zaune suke dikkan nin su a parlour kowa da abinda yake yi, Muryar Yousuf ta karad'e parlourn da....
" Abba game da maganar na nemo mata da ka min ina son sanar da kai cewar Atiyyaerh itace macen da ta kwanta min a raina Kuma nake son na aura," a zabure Rasheedah da ke jefa inibi a baki ta hau tari sakamakon Wani guda d'aya da ta jefa Dan ta tauna ya wuce mata maqoshi da kyar ya fito, cikin Maida numfashi ta ce,
"A ina za a yi hakan, a wanne gidan, sai dai bayan raina kai da ka auri wannan yarinyar Yousuf na fad'a Maka, gwanda ma tin wuri ka janye wannan banzar maganar mara amfani da ka yi "
"Sannu uban shi me Iko da gidan Baki d'aya, Kuma in ji waye ya ce ba zai auri Atiyyaerh ba? Ke? To in kece dan Allah yanzu ma ki fad'i mana, mu kuma ana arba'in din mutuwar ki zamu d'aura auren Yousuf da Maimunatou,shashasha kawai, Kai Yousuf ka kwantar da hankalin ka wannan karon da kaina zan tsaya Maka sai ka auri Ablaerh"
Miqewa ya yi ya shige d'aki,ya bar Yousuf da sauran 'yan uwan shi a wajen, yana ganin zata fara surutu ya miqe shima ya yi dakin su, fad'a take kamar zata ari baki, ba mai kula ta
"To a yi mu gani, in dai ni Rasheeda ina raye d'an dana haifa ba zai aure ki ba Ablaerh...
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 28:
" A gaskiya ba zan lamunci abinda ka ke shirin aikatawa ba na fada maka,ta ya za a ce d'an nawa ya auri ragowa yana saurayi? Ba zai yu ba ba zan lamunta ba, saboda nima ina da haqqi akan shi, ni nai cikin shi wata tara ba tare da kowa ya taya ni da riqon shi ba, ina da 'yancin zabar ma d'ana abinda ya fi dacewa da shi,"
"Zaki matsan a hanya ko sai na make ki? Domin ke ba matar da za a ragawa bane saboda qima ko daraja, dan baki tare da su, in ba a taya ki daukan cikin shi ba ai bake kikai wa kan ki cikin shi ba ko? Sannan abubuwan da kk ci a cikin nashi da kulawar da kk samu ko da kudin asibitin da aka biya na haihuwar d'an naki iyayen ta ne suka biya in kin manta na tina maki butulu, matsan ni malama ina da abin yi,"
Matsawa tai tana qunquni, dan rabon da