Showing 30001 words to 33000 words out of 81601 words
Chapter 11 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE Hausa Novels BY HAERMEEBRAH.txt
son kai,bayan abun a buɗe yake, amma Rasheedah na jin an ce Atiyyaerh ta fi Farhah jiki sai ta fara fad'in "To abinka da jikar so", Mama ta yi nasiha ta yi zagin,ta yi fad'an ,amma inaaa, ita haka take ganin anfi son Atiyyaerh bisa ga Farhan ta, a kullum Sakeenaah qara zama shiru take, duk da Adnan baya son hakan, amma haka take roqar shi ya kaita gidan yayar ta,cin ranshi ji yake kamar ya yi bindiga, ita ko Rasheedah in sun je ba ta da aiki sai habaici da mugayen kalamai akan Atiyyaerh, dan kawai taga ko ta ina ta wuce Farha, hasken fata kawai Farha zata nuna ma Atiyyah, kamar dai ita da Sakeenaa.
Yau yaran suke cika shekara biyu cip, inda Sakeenaah ta saka yarinyar ta a gaba mai tsanain wayo da magana kamar ta shekara uku ta na ta yi mata addu'o'i, Abban ta ne ya shigo ya dawo daga shopping ya siyo mata wasu sarqoqi masu kyau sosai na zinare da wasu kayayyakin na sawa, Sakeenaa ta yi ta mitar kaya sun mata yawa ya dinga tinawa akwai wasu yaran a dangi Yana taimaka musu mana, sannan ya daure ya dena shagwaba ta haka,yakan ce,
"Haba My love ita kadai fa muke da ita,in ban mata ba wa zan yi wa?"
Rausayar da kai kawai ta yi, ta qawata fuskar ta da murmushi, sannan ta ce,
" Allah ya qara maka bud'i Abu Ablaerh,"
"Ameen, Zo ta nan ki zauna kusa da ni, nifa sai na ga kamar kin d'an fara kyallin goshi, ko dai Atiyyaerh ta yi qani ne,"
Ya qarasa ya na mai sumbatar kuncin ta, rungume juna suka yi Adnan ya d'aga Kai ya kalli qofar d'akin Atiyyah dake a rufe ya ce,
" Ni fa na kula tin da aka haifi yarinyar nan wasan parlour ke gagarar mutum, tashi ki gani muje na duba ki, ko akwai ajiyata a jikin ki"
Dariya ta yi sosai,
"Ka duba ni ka ga akwai ajiya ko kuma ka yi ajiyar yau, dan dai ni nasan ban da komai,"
"Muje dai an gani duk kin gama rudan rutsuwa da wannan qamshin naki, " ni ko na ce tooooo da kyau Sakee baby☹
Maganar Adnan ta tabbata, ashe Sakeenaah dai ciki har ya yi wata uku ba su sani ba, sun gano hakan ne ta hanyar amai da ta gama sheqawa bayan ta sha tea da safe ta na kukan yanda take Jin kasala sai Adnan ya ce,
" Na fada maki na yi ajiya kin qi yarda ko,"
Bata fuska ta yi ta ce,
" Ni ba wata ajiya da nake da shi,"
"Tinda baki yarda ba to tashi muje asibiti in ba tsoro ba,"
Dariya ta yi tace ta dai ji tsoron take, a qasan ranta tana godewa Allah, in dai hakan ya zama gaskiya,a nutse ta futa
"Na yarda muje "
"Bismillah mu je"
Tashi suka yi suka shirya tsaf sai asibiti, gwajin farko aka gano ciki dan wata uku, murna kam ba sai na fada maku irin wadda suka yi ba ranar,biyawa ya yi da ita super market, ta kwashi kayan zaqin ta, suka dawo gida, suna isa ta sauke Atiyyaer, dake cin biscuit, sannan tai kitchen, tea ta hado ta zauna zata fara sha kenan, Atiyyaerh ta zubar mata da shi wajen qoqarin itama sai ta sha, fada ta mata ta kora ta wajen Abban ta, ita kuma tai kitchen dakko mopa, ta dawo tana ma Adnan bayanin kukan Atiyyaerh bata kula ba santsi ya kwashe ta, ta fada kan center table, kanta ya bugu, qafarta ta zame ta kifu ta gaba, wata qara ta sake tana kiran sunan Allah, Adnan da gudu ya qaraso,.........
*wayyooooo niiii Ummu Ablaerh plssss don't die, makaranta zasu sambaden wallah,ki tausayan😭😭😭*
[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*Dan Allah masu tambaya daga farko ku yi hakuri a gama gaba ɗaya a haɗa document sai a tura maku...masu tambayar KUN MAKARO daga farko dan Allah ku tambayi mutanen group ɗin da kuke ciki maybe ba za a rasa wanda ba ya clearing chats ba sai a Baku ko ku buɗe document da na tura group ɗin da kuke ciki ku karanta ta nan. Kar ku manta KYAKKYAWAR FAHIMTA ne kawai sabon littafin da nake yi a yanzu waɗannan dika reposting nake yi na jima da yin su...Na gode*
Page 13:
Kafin Adnan ya isa ya taimaka mata ta Kai qasa,gaba daya jini ya jiqe wajen, daukan ta ya yi suka yi waje dan zuwa asibiti,ganin halin da take ciki ne ya sa aka shiga emergency room da ita aka shiga duba ta, hankalin Adnan ya Kai qololuwa wajen matuqar tashi, jikin shi sai rawa yake ya kasa yin komai, so yake ya yi kuka ma ko zuciyar shi ta sake daga qullin da ta masa, amma inaaa hawayen sun qafe sun qi zuba,suna nan a haka ya yi tinanin Ablaerh ya baro ta ita d'aya a sashen su ga su Shamsiyyah na can wajen su ba lallai su ji me ke faruwa ba, wayar shi ya zara jiki ba kwari ya kira Shamsiyya ya Sanar da ita ta dauki Ablaerh su koma shashen su da ita, sannan ya yi wa Mama waya ya sanar da ita komai, a sannan ne ya ji Wani kuka ya zo masa sosai, kashe wayar ya yi ya kife fuskar shi a tafukan hannayen shi, ya na jin matiqar tsoro, domin yanda yaga jini na bin qafafun ta da kanta,in dai daga jikin ta ya fito to tabbas tana buqatar wani ko kuma Wani abu mara dad'i ya same ta, yana tina hakan ya miqe da gudu ya yi inda aka kwantar da ita, yana masu magana da qarfi yana kuka, akan su bude ya ga matar shi, da kyar aka rirriqe shi ya samu ya zauna ya had'e kai da guiwa yana ta zubda hawaye, ba a fi minti 20 ba Mama da Abba suka zo, tare da Yousuf, sai Ablaerh da suka biya suka d'akko, yana nan zaune suka tadda shi, Abba ne ya dafa kafad'ar shi, ya d'ago rinannun idanun shi ya kalle su, kad'a mashi kai kawai Abba ya yi, domin shima daurewa kawai yake,
"Ka yi hakuri ka k'warara zuciyar ka, kai mata addu'a kaji,"
Adnan na jin kalmar addu'a ya tashi kamar wanda aka mintsina, ya samu waje ya zauna ya daga hannaye sama, yana ta roqon Allah akan ya bata lfy, ko abinda ke cikin ta bai tsira ba yana roqon Allah ya bar masa matar shi, ba qaramin tausayi ya ba Mama da ke ta kuka ba a gefe, suna haka likitoci biyu sika fito, dayan ne ya cire glasses din shi, ya sharce zufa, miqewa suka yi a tare baki d'ayan su suka nufe su dan jin me ke faruwa, d'aya daga cikin likitocin ne ya kalli Adnan ya ce,
"Alhaji Adnan Bismillah Ina son magana da kai" Abbah ne ya kalli likitan ya ce,
"Zaka iya fad'a mana ko me ke faruwa baki d'ayan mu Doc. ni mahaifin ta ne, wannan mahaifiyar tace,"
"Ok to ku biyo ni,"
Shigar su office din ke da wuya suka samu mazauni suka zauna, inda Adnan ya samu gefe ya tsugunna ya yi jugum kawai, Doc. Ya fara magana kamar haka,
"Gaskiya 'yar ku na cikin hadari sosai Alhaji domin kuwa ta zubda jini sosai ba kadan ba, mun samu mun qara mata da hanzari, dan bari sai an nemo a dangi ma bata lokaci ne, i am very sorry to inform u that we have really tried to save the baby amma mun rasa shi, sannan ta samu rauni mai zurfi a kanta, wanda a qallah zai dau wani tsahon lokaci kafin ta warke,..... Sannan Kun San dama tana d'auke da hawan jini"
Tin da ya fara magana salati kawai Abba yake, Mama na share kwalla, tinani kawai take, ita kuma Sakeenaah haka Allah ya jarabce ta da faruwar al'amura haka, addu'a take mata na samun cin wannan jarabawa,
" Eh mun san tana dauke da shi," in ji Abbah da ya ji yanda wajen ya d'auki shiru, banda shassheqar kukan Adnan ba a Jin komai sai qarar AC.
"Ya na da matuqar mahimmanci a kula da lafiyar ta saboda a wannan yanayin da take ciki bamu da buqatar abinda zai dame ta in har Allah ya sa ta farka, hakan ba zai faru ba har sai Kun taimaka mata ta hanyar yi mata dik Wani abinda take so, kar ana dinga sanya ta cikin damuwa,... zata iya farkawa daga nan zuwa gobe amma sallamar ta sai yanda muka ga jikin nata ya yi sauqi dan haka ku kwantar da hankalin ku a yi Imani da Allah shine Mai warkar wa Alhaji zata samu lafiya, ka daure ka ci gaba da bata kulawar da muka sanka da shi, ni anjima zan tafi d'an uwan ka zai zo ya ci gaba da bata kulawa,(cousin din Adnan dake aiki a wajen) Inshaa Allah zata samu lafiya, Allah ya bata lfy,"
" Ameen" suka amsa dika, miqewa suka yi zasu fita,har a wannan lokacin Adnan na tsugunne, Abba ne ya kama hannun shi suka fita, d'akin da aka kwantar da ita suka leqa ga tanan kwance kamar matacciya, wasu hawaye ne masu zafi suka wanke fuskar Adnan, zuwa ya yi ya zauna kusa da gadon a kujera, ya jingina kan shi da gadon, ya kama hannun ta, kuka yake kamar qaramin yaro, Ablaerh ta matsa kusa da shi, ta kwantar da kan ta a jikin guiwar shi, itama tana kukan, ba qaramin tausayi suka ba Abba da Mama ba, fita suka yi waje, wannan karon Abba ma kukan yake,
"Kar ki tafi ki barmu, muna matuqar buqatar ki a wannan lokacin, yarinyar mu is just 2years she needs u, pls ki taimaka ki zauna da mu, Yah Allah ka d'aga kafadun ta, ka sa mata kaffara, Yah Allah ina son mata ta, ni maraya ne,ka ban ita dan ta zama haske a rayuwata, Allah ka rayan ita ta ci gaba da tallafa ma maraicina," Adnan shiru ya yi da magana dan Yana tsoron kar ya yi sab'o,ci gaba ya yi da kuka ya na riqe da hannun Sakeenaah, kukan shi ne ya sa Ablaerh qara fashewa da kuka, d'aga ta ya yi ya na rarrashin ta,dan shi yanzu ta matar shi yake, a hankali ta yi bacci se ya rungume ta a qirjin shi.
Har safiya ta waye Sakeenaa shiru ba alamar motsi a tattare da ita, hankalin Adnan da su Abbah ya yi matuqar tashi, nan da nan Adnan ya miqe ya fita, a waje yaga su Abba da tin jiyan Suna nan basu tafi ba, Suna leqa su lokaci zuwa lokaci, tashi suka yi suka nufe shi ganin tashin hankali a kwance a fuskar shi,
"Me ya faru?" In ji Abba da tin da gari ya waye ya ga bata farka ba yake cikin damuwa,
" Abba har yanzu bata motsa ba, zuwa zan na kira Doc." Ya qarasa magana idon shi taf da kwalla, numfashi Mama ta sauke, dan ta matuqar tsorata, Doc ya kira, ya je d'akin, duba ta ya yi yace zata tashi nan da kamar awa d'aya inshaa Allah, zama Adnan ya koma ya yi a gefen ta, Mama da Abba suka zauna a saman gadon dake d'akin a gefen ta , tin daren jiyan dama ya kwantar da Ablaerh akai, ido suka zuba mata baki d'ayan su kawai, kowa bakin shi da addu'ar Allah ya bata lafiya ya bata iKon farfad'o wa........
[01/07, 12:42 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 15:
Ko da na bi inda Rasheedah ke kallo sai na hango Mama d'auke da Atiyyaerh a cinyar ta, tana shafa bayan ta a hankali a haka har ta yi bacci, komai akan idon Rasheedah ke faruwa, d'auke idon ta ta yi ta zumbura baki gaba dan ganin ga ta ta yarinyar a gefe amma a qasa ko Maman ta d'an jingina ta da jikin ta, nan da nan abun na ta ya motsa, ta d'aure fuska, ta kira Afrah, maqe kafada yarinyar ta yi taqi zuwa, sai ta matsa kusa da Mama sosai, daidai wajen Atiyyaerh, itama ta kwantar da kanta, murmushi Mama ta yi ta shafa gashin ta, a qasan zuciyar ta tana nema wa Atiyyaerh sauqin zama a wajen Rasheedah Koda ta hanyar Afrah ne.
Bakwai na cika dangi na nesa da na kusa kowa ya tattara ya koma mahallin sa, Mama sai ta wuce da Atiyyaerh gidan ta, Rasheedah ba qaramin Jin dad'in hakan ta yi ba, dan a zaton ta sun manta da wasiyyar da Sakeenah ta bar musu, ko Kuma tinda sun San halin ta ba za su yarda yarinyar ta zauna a wajen ta ba, Dan haka gida ya rage Daga Masu aiki sai Adnan,Adnan d'in kuwa dama shi ko zaman makoki da ake a farfajiyar gidan shi ba zama yake a wajen ba, ko waye ya je masa gaisuwa sai dai ya tarar da su Abba ya musu gaisuwar ya juya, Koda yaushe ya na sama cikin d'akin shi, daga sallah sai tasbihi da roqar wa matar shi da iyayen shi Rahamar Allah, Jin shi yake kamar ba zai tab'a Iya ci gaba da rayuwa Mai dad'i ba a yanzu da ya rasa jigon rayuwar ta shi.
A qarshen satin Abba yace ma Adnan ya qoqarta had'awa Atiyyaerh kayan ta da dik Wani abu da ya dace dan damqa ta wajen sabuwar Uwar ta ita wasiyya ana so a gabatar da ita da gaggawa, hankalin Adnan ba qaramin tashi ya yi ba, yayi kuka ba iyaka, da kan shi ya lallashi kan shi, dan ya san cika umarnin Sakeenaahn shi zai yi ya riga ya mata alqawari, yana daga cikin wasiyyar ta da ta dinga jadaddawa kafin ta mutu, kuma ya kamata a cika mata ita, had'a kayan Atiyyaerh ya shiga yi idanun shi na zubar da hawaye, yana cikin hadawar ne ya ga wasu takardu guda biyu, daya duba sai yaga
*Zuwa Ga Ablaerh My Love*
Sai dayar kuma an rubuta,
*KAI NE JARUMI NA*
Daukan ta Atiyyaerh ya yi ya ajiye a gefe ya bude tashi, gaba d'aya fuskar shi ba komai sai hawaye, tayi jawur da ita,
*Mijina*
*Kai ne jarumi na, kai ne hasken idaniya ta, kaa zauna dani cikin so da qauna, tare da amana, ka zama jigon rayuwa ta, kai ne Wanda in nayi kuka kk sharen hawaye na, in nayi dariya kk tsayawa ka kalli kyau na ka yaba min,in nayi girki kai santi ka yabi aiki na*
*Jarumi na, ina qara roqon ka akan ka daure akan abinda na yi wasici akai, ba dan ba ka da iko akan d'iyar ka ba, sai dan na san Jarumtar ka zata sa ka yi hakuri, dan cikar burina, fatana ka yi ta min addu'ar samun sa'a akan quduri na kar ya zama ba nasara*
*Allah ya had'a fuskokin mu a jannatul firdaus, mu d'ora rayuwar aure fiye da wadda muka yi a nan duniya Mai Cike da tsafta da jin dadi, INA SON KA MIJINA JARUMI NA*
*DAGA MATAR KA SAKEENAA*
Saka takardar ya yi a qirjin shi yana kuka, a qasan zuciyar shi kuma yana jin kwarin guiwar rabuwa da gudan jinin tashi, ci kaba ya yi da had'a kayan ta, bayan ya gama da kayan nata ne ya dauki wayar shi ya koma d'akin shi, (ban san me ya ke fada ba tinda ya rufe ta ciki☹) bayan zuwa kamar awa d'aya cur ya fito d'auke da wasu akwatuna da jaka a rataye a kafad'ar shi, qasa ya sauka ya kira driver din shi, bayan ya shiga ya gaishe da Adnan,sai Adnan ya bashi umarnin d'iban akwatunan daya d'akko daga d'akin shi zuwa qasa, sanan ya koma ya dakko kayan Atiyyaerh, ya zauna a kujera ya na kallon cikin gidan, daga baya ya miqe ya fita cikin hanzari yana share kwalla, zuciyar shi na tinano masa irin zaman so da qauna daya faru tsakanin shi da Sakeenaah a cikin gidan, d'aya motar ya bude ya zuba kayan Atiyyaerh a ciki,ya ja da kan shi, ya nufi gidan Mama, yana zuwa ya yi parking a farfajiyar gidan sannan ya shige ciki, Atiyyaerh na ganin shi ta daka tsalle ta d'ale shi tana masa surutai, wani ya gane wani Kuma bai ganewa, shi dai ba ya buqatar ganewar ma, kallon ta kawai yake kamar wanda ba zai sake ganin ta ba, Abba ne ya fito Mama na biye da shi,
"Aa Adnan kaine tafe, barka da zuwa, Bismillah zauna mana ka ke tsaye"
Isa gaban Abba ya yi ya bashi hannu kan shi a qasa kamar yanda suka Saba gaisawa, bayan sun gaisa ne ya gaida Mama ta amsa cikin sakin fuska da tausayawa, janyo kayan Atiyyaerh ya yi gaban su, sannan ya miqa wa Mama dan akwatin da ake saka mata kayan adon ta, musamman na gashi, share hawayen da ya gangaro masa ya yi sannan yace,
" Abba ina neman izinin ku akan tafiyar dana yanke hukuncin yi, zuwa Dubai, domin ci gaba da kasuwanci na, a yanzu banda sauran dalilin zama anan, sai dai inna tafi zan din ga zagayowa domin ganin ku,ku kad'ai nake kalla a matsayin iyaye, dan haka ba zan dad'e ba zan dinga zuwa ganin ku, sai dai duk abinda nake fad'a yanzu sai fa Kun bani izinin ku zan aikata shi,"
Kan shi a qasa, yana sauraran amsar su,ya na addu'ar Allah kar ya sa su dakatar da shi, dan baya Jin zai iya ci gaba da Zama a Nigeria kusa da 'yar shi ya na ji ya na gani ta na rayuwa a hannun Rasheedah,
"A gaskiya Adnan dole na jinjina Maka domin kuwa na yarda da sunan da Sakeenaah ke Kiran ka da shi na *KAI NE JARUMIN ta* domin kuwa a iya tsahon rayuwar ka ka ga abubuwa kala2, dan haka ina son wannan karon ma ka zama jarumin wajen sanyawa zuciyar ka hakuri, in dai tafiyar ka zata sama maka kwanciyar hankali ni dai na maka izinin tafiya, Allah ya sanya albarka, ya kare mana kai dik inda ka shiga, nasihata a gare ka ka zama mai tsoron Allah, kar ka zama mai sab'a masa ko ketare dokokin shi, in kai haka Allah zai kare ka ya kiyaye ka,sannan Kuma ka samu ka je wajen Baffanin ka da